Makauniyar Kaddara 30

 


Page 30*


............Tunda ya turo ƙofar tsararren bedroom ɗin ya shigo da shashshekar kukanta ya faracin karo cikin kunnuwansa. Batare da damuwa da rashin amsa sallamarsa ba ya ƙaraso cikin ɗakin yana kallonta. 

      Zama yay a kujerar dake ɗakin tamkar bai damu da kukan nataba, a dakile yace, “Kinsa an tasoni daga office, gani to, mike faruwa?”.

     A fusace Farah da ke a kwance tana kukan ta tashi duk da tun farko tasan da shigowar tasa dama. Hawayenta ta share tana kallonsa, sai dai yanda ya tsatstsare ta da idanunsa dake rikitata yasa ta janye nata danta samu damar faɗar abinda ke a bakinta.

     “Babu abindama bai faruba. Ni wlhy bazan iyaba, tayaya wannan gidan zai ɗauki wannan gayyar dan ALLAH? Hidimar nawa zasuci ta kuɗaɗe tun daga kan abinci, ruwa da wasu wahalhalunsu?. Kawai sai dai muga yara batare da an sanar mana ba daga ni har kai. Ita bata tunani zamanta ma a takure muke bare tasa an ƙaro mana wannan yaran harda mara kunyar yarinyarnan data kusa min sanadin karayar ƙugu. Ko an faɗa musu rayuwar Nigeria da babu tsari da tanan iri ɗaya ce? Nasan duk Khalipha ne munafukin nan dan dashi zata haɗa bak......”

        “K ya isa haka malama!!”. 

Ya faɗa a kausashe cike da nutsuwarsa. Dan inma baka saniba sai kace ba shine yay maganarba. Babu shiri Farah tai baya dan firgita tana kallonsa dan ya fito mata a zakinsa. Ya tsatstsare ta da birkitattun idanunsa yana nunata da ɗan yatsa. “Farah! Farah! Wlhy daga yau, daga yanzu, bakinki ya ƙara kuskure akan Granny saina zubar miki da haƙora a wannan gidan. Da kike cewa ta takura miki, mizai hana bazaki tafi inda zaki shaƙata ɗinba ke?. Ki kiyayeni Farah, ina ɗaga miki ƙafane kawai saboda ra'ayina badan kai ƙarata da kikeyi wajen mahaifiyata ba. Yara kuma nine na kawosu, idan kin isa dan ALLAH ki maidasu Nigeria yau ɗin nan stupid kawai”. Ya ƙare maganar yana karkaɗa mata yatsansa alamar gargaɗi na ƙarshe ya mike ya shiga toilet.

       Da wani banzan kallo ta bisa, ji take tamkar ƙirjinta zai buɗe dan tsananin zafin da takeji na cika mata gida da akayi. Ta tsani takura a rayuwarta. Dama Mammah ta faɗa, zuwan Khalipha tamkar buɗe hanyar banbarowar danginsa ne garesa, dan sun sami ƙofar da suka kasa samu tuni. To ita kam sai dai ayi duk ma abinda za'ai waɗanan yaran bazasu zauna a gidan nanba, kai itama makirar tsohuwarnan mai ƙulla komai saita tafi.........

         Fitowarsa ta katse tunaninta. Tasa hannu ta share hawayenta tana dubansa duk da kallon fuskar tasa kawai tsoro take bata ma. Zatai magana ya katseta dan yasanta da shegen naci da mita akan abu,  “Ki kwaso duk kayanki na ɗakincan tunda ba amfani kike da shi ba su zauna. Jamal ya zauna wajen Khalipha”.

      A zabure ta miƙe tsaye tana dubansa hawaye na rige-rigen sakko mata. “Haba Yah Abdul-Mutallab, ɗakin nawa zan basu?”.

      “Zama ɗakin kikeyi ne?”.

“To amma dan ALLAH kodai bana zama a ciki ai dai sunansa ɗakina.  Suje ɗakin Granny su zauna mana”.

     Wani banzan kallo ya mata idanunsa na sake canja kala. “Wlhy Farah idan kikace zaki bani ciwon kai akan zuwan yarannan tabbas zan baki ciwon zuciya ni kuma. Garama tun muna mu biyu kije ki kwaso abinda yake naki a can ki basu ɗakin, idan kuma kinƙi zakisha mamakina dan ina nan Abdul-Mutallab ɗin ɗin da kika sani”. Yana gama faɗa ya fice abinsa.

         Khalipha kawai ya samu a falon, Granny taja su Zinneerah zuwa ɗakinta. Jamal kuma Khalipha ya kaisa nasa ɗakin. Duk ƙoƙarin ɓoye fushinsa da yake sai da Khalipha ya gane. Har cikin ransa baiji daɗiba. Shiyyasa yaso Yayan nasu ya haƙura da batun zuwan yaran tunda ba dole bane. Dan yasan Farah ba zataso suzo ɗinba. Tunda shima a yaya yake zaune gidan ma. Ita kanta Granny ɗan hali Farah ke nuna mata duk da tsufanta.....

       “Ina suke?”.

Ya katse Khalipha muryarsa cike da ɗaci. Cike da son kauda masa damuwarsa Khalipha ya miƙe yana dariya. “Ai Yayanmu kasan waɗanan yaran ƴan gatan Granny ne. Ta jasu ɗaki wai suyi wanka da barci. Shima Jamal yana wajena”.

     Goshinsa yaɗan murza da furzar da huci yana lumshe ido. Batare da ya samu yanda yake so na daidaiton muryar tasaba ya nufi ɗakin yana cewa, “Taya zasu zauna a wannan ɗakin harsu huɗu zasu takura mata ai”.        

       Bin bayansa Khalipha yay yana magana cike da lallashi. “Yayanmu daka barsu isarsu zaiyi ALLAH, kaga munma huta da mitar Granny akan kaɗaici ko”.

        “Bazai yuwuba Khalipha ɗakin Farah zasu koma”. 

     Dama abinda Khalipha kema gudun kenan. Ya ƙara buɗe baki zaiyi magana a dai-dai isowarsu ƙofar ɗakin AK ya ɗaga masa hannu alamar ya isa. Kai Khalipha ya dafe dan harga ALLAH baya buƙatar wata fitina akan zuwan yaran nan tsakanin yayan nasu da matarsa. Idan ta gaskiya za'abi sune da laifi, gashi kuma dama ba'a sanar mata ba tun farko. To amma yasan halin Yayan nasu tunda yace haka za'ayi dole a yarda ayi hakan”.

           Daga can Granny tace, “Khalipha shigo mana”. Dan batai zaton AK ɗin baneba. Batare daya nuna shi ɗin baneba kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama ciki-ciki. Akan Zinneerah data fara wanka harta kwanta ya fara sauke idanunsa. Ya janye yana maidawa ga Granny dake gyarama Meenal kwalar riga. Bahijja kuma na toilet tana wanka.

      “A'a wai dama baka komaba?”.

Hajiya iya ta faɗa idanunta akan AK. Kansa kawai ya kaɗa mata yana kaiwa zaune. “Yanzu zan koma Granny, akan waɗannan dama na shigo, su koma can ɗakin ba'anan zasu zauna ba”.

       Shiru tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma ta saki murmushi tana girgiza kanta. “Moddibo bazai yuwuba. Ka barsu anan muyi zamanmu zai ishemu”.

       A karon farko ya kalleta shima. Ta kaɗa masa kanta da iya gaskiyarta tace, “Idan akai hakan ba'a ƙyautaba Moddibo. Inda itace taso su zauna mata a ɗaki dan kanta hakan ba damuwa bane. Amma ko nice miji yayma ƙarfa-ƙarfa akan danginsa su zauna min ɗaki zanga kamar an ƙasƙantar da nine. Ka barsu kawai suyi zamansu nan zai ishemu duka zaman kwana nawane ma”.

      Bai iya yace mata komaiba, sai idanunsa dake ƙara canja launi ɓacin ransa na bayyana a fili, miƙewa yay a hankali batare da ya sake kallon kowansuba yace, “Saina dawo”. Daga haka ya fice yabar ɗakin..   

      Da ga hajiya iya har Khalipha da su Meenal da kallo suka bisa suma damuwa fal ransu. Suna son Yayansu dan shima yana son su. Ko rashin sakewarsa a garesu kowa yasan wannan halinsane da kuma yanayin rayuwar daya tashi a hannun Mahaifiyarsa. Amma sunsan badan ƙuntatawa a garesu yake musu hakaba.

        Afusace Meenal tace, “Wlhy na tsani matarnan, danma taga ta samu Yayanmu mai haƙuri dajin maganar iyayensa shiyyasa takema mutane wani iskancin”.

      “Barta hankali zamu koyama shegiya ai a wannan karon, tunda ta yarda mukazo gidan nan wlhy tayi gamo da gamonta kuwa”. Cewar Bahijja itama muryarta har zuga take.

     Rai ɓace Hajiya iya ta kallesu tana musu daƙƙuwa. “Duk kunci iyayenku, ina ruwanku a cikin wannan zancen? Kunsan ALLAH duk wanda ya aikata wani abu a gidannan saina ɓata masa rai kuma ya koma gida. Ina kuma sake gargaɗinku shiga abinda ba'a sakakuba. Wannan ma ai rainine. Koyaya take ai matar Yayankuce taci albarkacinsa a wajenku marasa kunya”.

      Duk ƙasa sukai da kawunansu alamar nadama. Dan dama sunsan wannan ba tarbiyyarsu bace. Hasalima Hajiya iya bata yarda da irin wannan maganar a gabansu, yau ma dai akasi aka samu. Haƙuri suka bata. Shima Khalipha ya ƙara musu faɗa sannan yace suzo suci abinci shima zai wuce school ne.

     Duk wannan abin da sukeyi Zinneerah najinsu sarai, amma tai shiru kamar barci takeyi. da Khalipha ma yace a tadata taje cin abincin Hajiya iya hanawa tai. Catai su barta idan ta tashi sai taci nata tunda ta riga tayi barci.


      A ɓangaren AK kuwa koda ya fito daga ɗakin hajiya iya ɗakinsa ya sake komawa. Zaune ya tarar da Farah da waya a hannu kamar ba ita ta gama kukaba yanzun. Ko'a jikinsa dan ya shirya mata tsaf, ya kuma san Mammah bazatazo gidanba dan yunda Hajiya Iya ta dawo daga asibiti taƙi zuwa, dama kuma ko asibitin bataje ta dubataba. Yanzu hakama tana China batare da sanin Farah ɗin ba, dan shekaran jiya ta wuce da daddare.

        “Ki tashi ki tattara komanki dake a ɗakin nan ki maidashi ɗakinki. Karna dawo na taddaki anan ko wani abu naki”. Daga haka ya juya ya fice abinsa bai jira cewartaba.

       Fuskarta bayyane da tsantsar mamakinsa ta bisa da kallo. Yana fita ta miƙe a fusace dayin wurgi da wayar hannunta. ‘Ni zaka wulaƙanta akan waɗanan banzayen ƴan uwan naka Abdul-Mutallab? Saboda nace bazasu zaunamin ɗakiba kaima zakace na bar maka ɗakinka bayan kasan nafi son zama a cikinsa. Na rantse da ALLAH sai yaran nan da tsohuwarnan sunbar gidannan zan baka mamaki kai dasu. Bazan sake zubar da hawayena akansu a banzaba mu zuba mu gani’. 

     Yanda take surutai ita kaɗai a kuma matuƙar fusace sai ta baka dariya. Ta koma tamkar wata zararriya. Sanin halinsa yasa bata ƙetare maganarsaba ta shiga tattare duk wani abu nata tana saka mai aikinta tana kaiwa ɗakinta. Sai dai kuma alwashin ƙuntata su Hajiya iya a gidan tacisa yafi sau shurin masaƙi.

         Bayan ta gama tattare komai nata tsaf ta saka mai aikin nata sake gyara masa sannan ta jawo masa ɗakin ta rufo harda saka key. 


       Su dai duk wannan abu dake faruwa su Hajiya iya basu saniba suna ɗaki abinsu tana hira da jikokinta. Abincin ma anan sukaci kusa da ita har Jamal da yana gama kimtsawa ya tafi can. Shiko Khalipha ya wuce school kamar yanda ya faɗa.


________________★


         *_DANYA_*


   Su inna sun kai Karima asibitin kusada. Likitocin nata faɗa ganin yanda jikinta ko ina sayin duka ga tsohon ciki da a yau ma yaketa nuna alamun zai fito duniya. Dan tunkan su wuce ashe naƙuda take shiyyasa jikin nata ya nema rikicewa.

       Ɗakin haihuwa suka kaita dan shine yafi cancanta da ita a wannan halin. Daga haka suka shiga bata taimakon gaggawa. Suka bar su Inna a waje da zaman jigum-jigum. Tun suna zuba idanun jiran kukan jariri da wuri har al'amarin ya fara fin ƙarfinsu. Dan ihun Karima kawai suke jiyowa babu na jariri. A haka suka cinye wannan yinin suka shiga marece. mahaifiyar Babawo sai kiransa take a waya yaƙi ɗauka. dan tunda ta sanar masa abinda ke faruwa kafin su baro Danya bai sake yarda ya ɗaga mata wayaba. Dole sai ƙaninsa keta kaiwa da kawo akan komai har ALLAH ya sauki Karima wajen ƙarfe goma na dare.

     Tsabar wahalar data sha daga ita har jaririyar sun fita hayyacinsu ko kukan kirki batayiba. Koda aka buƙaci kayan haihuwa babu abinda sukazo dashi asibitin. Aiko Nurse ta balbalesu da masifa dan haushi. Inna ta miƙe itama a fusace tana danƙarama Nurse zagi abu ya nema zame musu faɗa sai da aka lallashi Nurse ɗin da ƙyar. Dan sun fahimci Inna ma ba kanwar lasa baceba.

      Wannan abin daya faru yasa gari na wayewa aka basu sallama suka dawo gida duk da Karima na buƙatar zama ƙarƙashin kulawar likita. To amma jarabar Inna bazaisa su iya cigaba da kulawa da Karima ɗin cikin kwanciyar hankaliba dan haka suka sallamesu..........✍

    

No comments

Powered by Blogger.