Makauniyar Kaddara 28

 


*Page 28*


............Ƙarfe takwas da kwata dai-dai jirginsu ya tashi zuwa ƙasar London. Farah nata ƙunci akan ita batai shirin komawaba yau. Sai dai shi uban gayyar yasan haushinta bai wuce na tafiya da Hajiya iya ban. Har cikin ransa mamakinta ke ƙara faɗaɗa a ransa.

Yanaji kuma lokaci yayi dazai maidota cikin hayyacinta akan danginsa.

     Ita kanta Mammah wannan karon ya shirya mata tsaf, dan yasan ba ƙaramin rikici zadu kwasaba akan wannan tahowa da Hajiya iyan da yay, shiyyasama ko faɗa matai biyiba sai sun isa ta gansu. Ita kanta Farah sai da suka isa airport hankalinta ya ƙara tashi.


          Tun bayar wucewarsu zazzaɓi mai zafi ya rufe Zinneerah. Ta kuma maƙale a sashen hajiya iya taƙi tafiya wajen Momie da yace mata. Sai da su Meenal da suma suka gama shan nasu kukan suka biyota sannan. Ganin halin da take ciki suka koma suka sanarma Momie. Da kanta tazo har sashen hajiya iya ta lallaɓata da lallashinta sannan suka kashe komai na sashen ta ɗauki duk abinda take buƙata na amfaninta da kuɗin da Yah Adnan ya bata, dana Khalipha suka wuce. Sai dai fa wayarta ce sunsha nema yanzun ma amma basu ganiba. Ta rasa inda ta jefata tun jiya da rana bayan tayi waya da Mmn sadiq. Momie ce tace subar wayar da safe azo a sake dubawa tunda an kira ma a kashe take. Haka ta haƙura suka tafi can sashen duk da dama ta saba kwana wani lokacin.


   Tun daga wannan ranar rayuwar Zinneerah ta koma sashensu Jamal, tanajin daɗin zama da kowa dan babu mai tsangwamarta ko nuna mata banbanci, sai ma wani al'amari mai ƙarfi dake neman saƙuwa tsakaninta da Yah Moos'ab duk da har yanzu bai firta mata cewar yana sonta ba. Yabarma ransa har sai ta kammala secondary kamar yanda yaci buri.

         Amma sai kaf-kaf yake da ita musamman da yaga tafiyar Granny ta sakata shiga wani hali. Itako tsaf ta fahimci inda ya dosa amma take nuna masa bata gane komai, ɗaukarsa take kamar sauran samarin gidan kawai, dan ita bata saka soyayya a lissafin rayuwarta duk da tanajin Yah Khalipha a ranta shikam. Amma sai take ɗaukar hakan matsayin ganin girmansa akan taimakon da yay mata wancan karon da bata da gata.

       Kullum takanyi waya da Khaliphan a wayar su Jamal, anan ne takejin cigaban da ake samu game da jikin hajiya iya da Yayansu keta kashe kuɗi akan ganin ta samu lafiya. Bata taɓa waya da shi ba. Sai dai duk santa ta buɗe akwati zata ɗauka abu takanci karo da kuɗin da ya bata bandir guda na ɗari biyar, sai turarensa shima daya bata tare duk a ranar da zasu tafin, duk da ko sau ɗaya bata taɓa shafashiba ya gauraye mata kayan cikin akwatin da ƙamshinsa.

           Sai da suka cika sati uku cif da tafiya Zinneerah taji muryar Hajiya iya. ALLAH sarki zokaga murna da farin ciki ita dasu Bahijja. Bama suba duk wanda yake a gidan ranar saika fahimci yana a cikin farin ciki, dan duk sai da ta gaisa dasu. Kwana biyu dayin haka kuma Baffah ya dawo daga can ya ƙara sanar musu da cigaban da aka samu.

        Hajiya iya na cikin sati na bakwai a london su Zinneerah suka sami hutun makaranta. Kai tsaye ta sanarma Momie tanason taje gida hutu, duk da tana waya dasu kullum ta wayar su Bahijja dan ita dai tata wayar an rasa inda ta faɗa har yanzun, harma ta haƙura dan tasu Meenal ma ta wadatar da ita tunda dama daga amsa waya da kiran su mama sai games suke da wayoyin, sauko abinda ya shafi karatu idan ta kama. Yah Khalipha kuma ya mata alƙawarin zuwa mata da wata idan zaizo.

       Shiri Momie tai mata na zuwa gida ita da Baffah duk da kuwa anan cikin garine. Ranar da suka cika kwana biyu da samun hutu Moos'ab da kansa ya kaita gida tare dasu Jamal. Ganin little ɗinta daya ƙara girma da ƙannenta da mama ya mantar da ita kewar su Bahijja da suka wuce. Tuni suka shiga hira tana ƙara bama mama labarin yanda jikin hajiya iya keta ƙara ƙyau. Amma Yayansu yace bazata dawoba sai bikin su Aunty Safiyya.

     Mmn sadiq taji daɗi sosai, dan tana ƙaunar hajiya iya da zuri'arta kodan karamcinta garesu. Sai dai kuma a wannan karon ta shirya binciken Zinneerah akan samuwar little. Dan tun ganin AK datai hankalinta bai sake kwanciya ba. Ita harma zargi take itama Hajiya Iya dalilin little ɗinne ciwonta ya motsa.

      Ba ƙaramin girgiza zukatansu Sakina wannan zuwan ma Zinneerah tayiba. Dan su kansu sunsan ta wuce da ajinsu yanzun, samarin anguwar kuwa da suka nuna suna sonta a baya suka dingi ɓata Zinneerah a wajensu ganinta ya sake dawo dasu gareta. Sai dai taƙi bama kowa fiska dan burinta bana aure bane yanzu karatu ne.

      Tana kwana huɗu da zuwa sai ga Yah Haneef da Yah Mas'ood sunzo wai zasu kaita ai mata passport inji yayansu. Bata fahimci inda zancen ya dosaba amma saita shirya suka tafi harda Little da tun zuwansu gidan suka janyesa. Shiko duk da rashin son mutanensa sai gashi ya saki jiki dasu kamar yanda yayi randa su Jamal sukazo. 

        Wajaje sukaje kusan uku kuma duk sun jima. basu dawoba sai yamma lis tare da siyayyar kayan ciye-ciye fal leda da suka yima little. Bayan wucewarsu ne Mmn Sadiq dakema little shirin barci ta duba Zinneerah ɗin.

       “Niko nace dama tunkan kizo nan kinsan wannan Yayan naku ne Zinneerah?”.

     Zinneerah dake cin gyaɗa ta ɗago tana kallon mama. “Mama wane Yayan a ciki?”.

       Kai tsaye Mama tace “Adnan”. Shiru Zinneerah tai tana kallon Mama na wani ƴan sakkani, a ranta tambayar na bata mamaki. “Wai badake nake maganaba ne kika tsaya kallona?”. 

       Numfashi Zinneerah ta sauke dan itama ta tafi wani tunani ne kuma daban. “Yi haƙuri Mama, tambayarce wlhy ban ganeba”.

      “Basai kin fahimceniba dama ai. Amsa zaki bani”. 

      Da ƴar dariyarta tace, “A'a wlhy mama ban sanshiba sai a wannan karon da yazo gidan, bamma taɓa ganinsa ba nikam. To shi dama akace baya zuwa ma ƙasar a ina zan sanshi Mama?”.

      Idanu Mmn sadiq ta zuba mata cike da nazari, kamar zatayi magana sai kuma tai shiru ta barta kawai. “Tashi ki kai Wannan ɗaki tunda barcin nasa yayi nisa”. Miƙewa tai ta ɗauka little da yay barci tunkan su dawo, sai da maman zatai masa wanka ya farka. Ana gamawa kuma ya sake komawa dan ya gaji matuƙa sunsha yawo.

    Da kallo kawai mmn sadiq ta bita harta shige ɗauke da little ɗin. Harga ALLAH ranta cike yake fal da fargabar abinda zuciyarta ke ayyana mata a koda yaushe tun ganinta da Adnan ɗin. Shi kansa Abba data bashi labari zancen ya girgizashi, har yau kuma sun kasa daina tattauna maganar a duk sanda take tare da shi. Sai dai sun kasa fahimtar komai akan al'amarin sam. To gashi wadda ma suke da hope ɗin samun wani bakin zare a gareta tace bama tasanshiba itama. Duk da ta fahimci Zinneerah bata iya ƙarya ba wannan karon ta gagara gaskatata akan batun rashin sanin Adnan.

    Washe gari da taci burin sake zaunar da ita akan batun sai ga Moos'ab wai yazo ɗaukarta dan zasu wuce da sassafe gobe idan ALLAH ya kaimu wajen hajiya iya. A take farin ciki ya bayyana ga Zinneerah tahau shiri, mmn sadiq kuma suka hau gaisuwa da Hajiya iya ta wayar Moos'ab ɗin itama. Sai da suka gama wayarne ta miƙe ta shiga haɗama hajiya iya ƴar tsarabar data san zataji daɗinta idan an kai mata. Cikin ƙan ƙanin lokaci Zinneerah ta gama shirinta tsaf suka wuce bayan sunyi sallama da Abba ta waya duk da dama jiya mama ta sanar masa fitar su Zinneerah ɗin, shine ya ɗanyi zargin ko wajen hajiya iya zasuje dama. To amma baiyi tunanin tafiyar haka gab ba.

         Tunda suka iso gidan suka haɗu dasu Jamal suketa murnar tafiyar musamman ma ita da ko jirgin ƙasa bata taɓa ganiba😹, dan su huɗu kawai zasuje ashe. Ita, Jamal, Meenal, Bahijja. Anan ma koda ta dawo ba zaman sukaiba, fita suka sakeyi ita da Moos'ab ta ƙarasa abinda ya rage mata tunda wannan ne karon farko da zata ƙetare 9ja. Abinka da maganar kuɗi kuwa sai gashi a tsakanin fitarsu ta jiya data yau ɗin komai ya kammala, tunda dama ƙasar tamu waka sani ya sanka akeyi.

    Suna dawowa sashen hajiya iya taje ta ɗakko abinda zata buƙata suka shirya kayansu tsaf duk da bawasu uban kaya suka ɗauka ba. Gara itama ta haɗama Hajiya iya da saƙonta na wajen mama da kuma abinda tace ta ɗakko mata.


________________★★


        Abin mamaki yau sai ga Zinne ta danya mai tallar riɗi da gyaɗa a airport za'a ƙasar burtaniya. Babu wani ɓoye-ɓoye murnarta take nunawa a fili musamman da suka iso airport ɗin. Aiko su Jamal suka tasata gaba da tsokana suna dariya. Ko'a jikinta dan iya gaskiyarta ta faɗa. Bayan kammala tsarabe-tsaraben airport jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar burtaniya zuciyar Zinneerah cike taf da tsoro lokacin da jirgi zai tashi. Dan sai da ta ƙanƙame hannun Bahijja dake kusa da ita hanjin cikinta na wulƙitawa tamkar zata amayosa ta baki. Sai da jirgin ya gama dai-daita a gajimare ta buɗe idanunta tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.


       Tun Zinneerah na marmarin tafiyar da ɗoki harta fara ƙosawa, dan bata da jimirin dogon zama dama ita. Lokacin da jirgin ya samu kaiwa ga ƙasa jitai kamar tamafi kowa farin ciki tsabar gajiyar datai da ƙaguwar son ganin Hajiya Iya. A wannan gaɓar ba itace kaɗai baƙauya ba hatta dasu Jamal ɗin ƙauyawa suka koma. Dan shine karonsu na farko zuwa ƙasar london. 

       A yayin sakkowar tasu Jamal ne gaba. Ita a bayansa sai Bahijja da Meenal biye dasu. Kowanne yana jaye da trolly ɗinsa ƙarami a hannu. A kallo guda dolene su birge ka musamman da suka kasance a ganiyar shekarunsu na ƙuruciya..............✍


*_Masha ALLAH. Guys asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._*

No comments

Powered by Blogger.