Makauniyar Kaddara 26

 


page 26*


...........Baki ya buɗe zai bama wanda suke maganar amsa dai-dai da isowarsa gab dasu hakan ya gagara. Dan a take harshensa ya sarƙe saboda sauka da idanunsa sukai akan fuskar Little dake ɗauke a kafaɗar Zinneerah ya wani lafe jikinta hannunsa na wasa da

jelar kitsonta ta bayanta. Ita kanta sake shiga ruɗani zuciyarta tayi kasancewar kusancinsu sosai yau da little ɗin ya ƙara fiddo mata da kamanninsu ainun.

       Sannan ganin yanda yake kallon little ɗin shima sai da hanjin cikinta suka motsa. Ba ita da shi bane kawai a ruɗanin hatta da mmn sadiq sai da tayi kamar zata kifa daga bayansu. Ƙirjinta kuwa yay wani mummunar bugawa tanabin AK ɗin da kallo. Duk da ƙarancin shekarun Sadiq da Abdull suma dai su kalli little su kalli AK ɗin da ayanzu yay ƙarfin halin ɗauke idanunsa yana maida hankalinsa ga wanda suke wayar duk da a baɗini sam hankalin nasa baya tare da shi.

      A haka suka wuce juna su Sadiq na waiwayensa, hakama mmn sadiq sau kusan uku tana waiwayowa ta kallesa, kamar yanda shima ɗin ya kasa daina binsu da kallo. Zinneerah kam da ƙar ta cigaba dajan ƙafafunta ta ƙarasa dasu sashen hajiya iya. Inda acanma kallo ya koma sama. Dan tun sallamar da sukayi kowa ya amsa su Meenal suka taso da gudu suka rungume Mmn sadiq suna mata sannu. Sun juyo da nufin ma su Sadiq sannu da zuwa idanunsu ya sauka akan little.

      “What!”.

Jamal ya faɗa a hankali yana tsare little ɗin dake lafe a kafaɗar Zinneerah har yanzu da ido. Sam hankalin Zinneerah baya tare dasu a yanzu, dan yau tafi kowacce irin rana shiga ruɗani akan kamannin little da Yah Adnan. Shiyyasa harta sauke little ɗin ƙasa bama tasan tayi ba. Hakan kuma dataine ya bama duk sauran yaran gidan ganinsa sosai. A take sannu da zuwan da suke Mmn sadiq ya shiga maƙalewa a maƙosansu. Dan yau harsu Momie suna a sashen suma.

         Cikin ƙarfin hali Khalipha da yay mutuwar tsaye shima ya nuna musu hanyar ɗakin hajiya iya yana faɗin, “Mama ku shiga tana ciki”. 

     Kai Mmn sadiq ta ɗaga masa tana murmushin yaƙe dabin Khalipha ɗin da idanu itama dan ta ganesa duk da ya ƙara buɗewa fiye da wancan sanin datai masa. 

    Duk wannan al'amari dake faruwa Farah na ɗaki kwance dan taƙi sakewa a cikinsu kamar yanda takeyi dama idan tazo gidan. Saboda karma Adnan ɗin ya zargeta catai masa bata da lafiya. Yarda yay tunda yasan tana laulayin ƙaramin ciki kamar yanda Mammah ta sanar masa.

        Hajiya iya na kwance suka shigo. amma tunda idonta ya sauka akan little itama babu shiri sai gata zaune. Ta haɗiye yawu da ƙyar tana miƙa masa hannu shi dasu Aliyun. Babu musu duk suka nufeta. Sai da suka gaisheta da jiki sannan suka zazzauna inda ta nuna musu a kusa da ita kan gadon. Little kuwa matsawa yay jikinta ya kwanta dan shi dama akwai son jiki. Su Sadiq sun shagwaɓa shi, harma dasu Mmn Sadiq ɗin.

         Hajiya iya takai hannu kan little ta shafa zuciyarta na wani irin harbawa. A ranta ko rayawa take tamkar Moddibo na ƙarami. A fili kuma saita maida hankalinta ga Mmn sadiq dake gaisheta cike da kulawa.


        Tunda suka shige aka shiga ƴar kallon kallo a falon, dan bakin kowa ya kasa furta komai. Sai can kamar a fisge Saffiya tace, “Wannan ai yaron dana ɗakko muku hotonsa ne. Amma kuma ba maman bace wannan”.

      Shigowar Baffah da AK ne ya hana kowa amsa zancen Safiyya ɗin. Sai ma zubama Yayan nasu ido sukai zukatansu fal ruɗani. Shima kansa a ruɗanin yake. Amma kasancewarsa gwanin kamewa yasa babu mai iya fahimtar halin da yake a ciki akan fuskarsa. Sannu da zuwa duk suka shiga yima Baffah. Ya amsa musu sama-sama yana nufar ɗakin mahaifiyarsa dan ba'a cikin hayyacinsa ya dawo ba. 

     Da sallama ya shigo, AK biye dashi a baya. Ganin Mmn sadiq ya saka Baffah nuna jin daɗinsa. Suka gaisa cikkn girmama juna. Suma su Sadiq suka gaishesu ya amsa musu da kulawa. Sai da ya maida hankalinsa ga Hajiya Iya data kafe AK da kallo sannan shima idanunsa suka sauka akan little da barci ya fara ɗauka a jikin hajiya iya.

     Wani irin muƙut, Baffah ya haɗiye yawu da ƙyar yana kallon little da ƙyau. Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kalli AK da gaba ɗaya hankalinsa ke akan little shima. Ya sake maidawa ya kalli little again zuciyarsa na wani irin rawa. Dan ƙarara zakaga shi ruɗaninsama akan fuska. Kasa jurewa yay sai da yace, “Ikon ALLAH innata kunga wani kamanni yau dake neman hargitsa tunanina anan, ɗan wanene wannan?”.

        “Bakai kaɗaiba Babangida. Ni kaina bakaga na kasa daina kallon yaron da Moddibo ba. Ai wani hikima sai UBANGIJI. Wlhy sai kace Moddibo na ƙarami. Hauwa'u wannan yaro nikam idan a wani guri na gansa ai sai nace namune ma. Ina kika samosa?”.

     Duk da faɗuwa da gaban mmn Sadiq yayi cikin juriya tai murmushi zata bata amsa Aliyu yay saurin faɗin, “Mama ƙaninmu ne”.

        Shiru ɗakin yayi, Mmn Sadiq ta sauke wani ɓoyayyar ajiyar zuciya. Dan a ganinta ba'a wannan halin da hajiya iya ke a ciki yakamata tasan matsayin little ba. Amma insha ALLAHU tayi alƙawarin tana samun lafiya zasuzo ita da Abba sumasu bayanin komai. Shiyyasa taso tunma kan Zinneerah ta taho su faɗa musu. Amma batasan dalilin Abban na hanawaba.

       Baffah ne ya katse tunanin na maman sadiq da faɗin, “Kai masha ALLAH, ALLAH ya albarkaceku, hikimar UBANGIJI ai tafi ƙarfin mamaki. Hakan na ƙara nuna mana muhimmancin zuminci da ƙarfin jini dake tsakaninmu Hauwa'u. ALLAH ya sake ƙara mana ƙarfi da kusanci, ya kuma sa muci amfanin hakan duniya da lahira”.

     Da amin duk suka amsa. Baffa ya shafa kan yaran duka har little daya ɗan buɗe ido ya dubesa na kusan sakan goma sannan ya maida ya rufe. Daga haka aka koma gaishe-gaishe duk da zuciyar kowa dai ba adaidai takeba.

              

     Bayan Baffah ya fita aka kawoma su mmn sadiq abinci da ruwa. Ruwanma kawai suka sha dan a ƙoshe duk suke dama. Suna nan zaune tare da hajiya iya har akai kiran sallar magriba Khalipha yaja su Sadiq suka tafi massallaci. Bayan an idar ne sun dawo suka iske Little ya tashi. Sai dai suna toilet Zinneerah ta kaisa zaiyi fitsari. Sannu suka sakema Hajiya iya dake zaune ta idar da salla duk suka fita. 

         Zinneerah ta fito riƙe da little dake mata maganar da ba wani fahimta takeba sosai saboda bawani ya iya bane da ƙyau. Murmushin ƙarfin hali take masa itama tana magana ƙasa-ƙasa. Hakan yayi dai-dai da shigowar AK ɗakin da sallama. Amsa masa duk sukayi idanunsa na sauka akan Zinneerah da little ɗin. Ita dai bata yarda ta kalli sashen da yakeba, sai da a bazata suka ji little yace, “Abbah ruwa zan ca”.

         Gaba ɗaya suka kalli yaron da mamaki dan AK yake kallo, kuma shine ya shigo hannunsa riƙe da goran ruwa. 

       Murmushi AK ɗin ya saki wanda ya sake fidda kamanninsa da little ɗin ainun yana nufosu. Ƙirjin Zinneerah ya harba da ƙarfi lokacin da yazo gab da su ya miƙama little ɗin hannu alamun yazo gareshi yana faɗin, “Oh my Sweetheart zo, zo”.

      Saurin sakar masa shi tayi tana ja baya, shiko little cike da farin cikin daya bawa kowa mamaki musamman ma su su Zinneerah da suka san miskilancin yaron ya wani maƙalƙale Yah AK ɗin yana sauke ajiyar zuciya. Shi kansa AK ajiyar zuciyar ya sauke a ɓoye da sake manne yaron a jikinsa jininsa na tsinkewa. A hankali ya sumbaci goshin yaron sannan ya zauna a bakin gado ya saka masa ruwan a baki yana shafa kansa.

       Baki little ya janye yana faɗin, “Ƙoshi Abbah”.

      A bazata sukaga AK ɗin yayi dariya da jan hancin yaron yana faɗin, “Wannan hausan naka bai cikaba little Handsome”. 

      Ƙaramar dariya hajiya iya da zuciyarta ke ƙara raunana da shiga ruɗanin wannan al'amari tayi. hakama Mmn sadiq tai murmushin yaƙe kawai. Kallon Zinneerah hajiya iya tayi. “Inno na a bashi abinci ko”.

       Kai ta kaɗama Hajiya iyan da nufar kulolin da aka kawoma su mmn sadiq ɗin basu ciba. Ta buɗe ta zubo abincin kaɗan a filet. Kallo ɗaya tayima little ɗin dake jikin Yah AK yana masa firar da baya fahimta dan maganar tasa ba nuna taiba ta ɗauke kai. “Malami sakko ga abincin”. Tai magana tana dubansu.

     Kafaɗa ya noƙe alamar bai zuwa. Hakan yasa Zinneerah hararsa ta ɗauke kanta ta maida gasu Aliyu. “Kuma zakucine Abdull na saka muku?”.

       Kai suka girgiza mata alamar a'a. Dan haka ta sake duban inda little yake ganin ko motsi baiyiba har yanzun. Zata sake magana AK ya harareta kaɗan da miƙa mata hannu alamar ta bashi abincin. Baki ta ɗan tura gaba da miƙewa takai masa. Harta juya little yace, “Aunty!”.

   Juyowa tai ta kallesa, ganin ya maida kansa kamar bashi ya kiraba yasata hararsa, sai ko a cikin idon AK daya ɗago. Da sauri ta ɗauke kanta ta nufi hanyar ƙofa tana ƙunƙuni a cikin ranta.

           Baya taɗan ja saboda Khalipha da zai shigo. Ya dubeta da murmushi dan zuwa yanzu kam ya yarda wannan Zinneerah ce daya sani a Shira hospital. Sai dai little ya saka zuciyarsa a tsananin ruɗani da firgici, dan inhar zai auna da ma'aunin hankali shekarun little zasu iya kaiwa dai-dai da hasashen haihuwar Zinneerah. Amma yaƙi ya yarda da cewar shine ɗan data haifa ɗin.

         “Kanwata sai ina kuma?”.

Murmushi tai masa daɗan shafar wuya. “Yah Khalipha zan fitane kawai”.

        Murmushin ya sake sakar mata shima, da matsawa ya bata hanya ta fice shikuma ya ƙarasa shigowa idanunsa na sauka akan Yayansu dake bama Little abinci a baki. Ji yay sun wani bala'in birgesa. Har yana ayyanawa a ransa inama ace yaron nan jinin yayan nasune da gaske.

       Takawa Khalipha yay ya zauna kusa da yayan nasu yana mai shafa kan little ɗin. Juyowa little yay ya kallesa sai kuma ya juya ya cigaba da karɓar abincin. Kaɗan yaci abincin yace ya ƙoshi, badan AK ya gaji da bashiba ya haƙura ya barsa. Haka ya cigaba da zama a jikinsa har ya sake komawa barci.


      Su Mmn Sadiq basubar gidanba sai wajen tara saura na dare. Da ƙyar aka raba little da jikin Yayah Adnan, dan lokacin da Khalipha dazai kaisu yazo amsarsa sai gashi ya farka a bazata. ya ƙanƙame AK ɗin yaƙi zuwa wajen Khalipha. Murmushi AK yay da lumshe idanun yana sunbatar little ɗin a goshi da shafar bayansa. Shi kansa ƙarfin hali kawai yakeyi, amma ji yake kamar karya rabu da yaron dan yayi bala'in shiga ransa. 

      Daga ƙarshe dai da ƙyar ya yarda Khalipha ya ɗaukesa dan sai da aka haɗa da masa wayo. Motar na ficewa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya hawayen da baisan kona minene ba suna ciko masa idanu. Ƙoƙarin maidasu yay yana furzar da huci mai zafi da nufa garden ya zauna dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kaɗaici.

      

        Yanda AK ya kaɗaice kansa Zinneerah ma harabar gidan ta fito can wajen motoci ta hau bayan ɗaya daga ciki ta zauna tare da faɗawa duniyar tunani. Gaba ɗaya zuciyarta a ruɗani da ɗimuwar kiɗima take. Shin a ina aka faɗi a ragaya ne? Wane darasi rayuwa keson karantar da ita a wannan gaɓarne bayan darasissikan data baro a shekarun baya?. Ko mahaukaci ya kalli little ya kalli Yah AK dolene ya danganta alaƙar jini a tsakaninsu. Dan abinda zai matuƙar baka mamaki ba kammaninne kawaiba. Hatta da wasu a cikin halayen Yah Adnan akwai alamunsu ga little. Kenan to.......

     “Kai ina”. Ta faɗa a fili tana girgiza kanta dake matuƙar sara mata. Kamar ance ta ɗaga kai can ta hango Baffah a barandar sama yana kaikawo alamar shima akwai abinda ke damunsa, wanda bata raba ɗayan biyu zancen kamanin little ne da Yayan nasu.

       “Ya ALLAH kai ne gagara misali, ka buɗemin tunani, ka yalwatamin fahimtata. Ka gafarta mini zunubaina”. Ta faɗa hawaye na silalo mata akan kumatunta masu zafi. Zurfi sosai ta ƙarayi a tunani har motar Khalipha daya kaisu mmn sadiq ta shigo gidan bata saniba. haskatan da yayne shima ya sakashi ganinta. yana gama fakin ya nufo inda take. Sau biyu yanayin sallama babu amsa, har dai ta kaisa ga ɗan bugar motar ta gefen kunnenta sannan ta kawo nannauyan numfashi tana dubansa.

       “Wane irin tafiya tunanine haka da zurfi ƙanwata?”.

      Murmushin yaƙe tai masa tana duƙar da kanta ƙasa. Hakan datai sai ya ƙara fiddo masa da kamanninta na baya sosai. Yay murmushi yana gyara tsaiwarsa da faɗin, “Zinneerah na tambayeki mana?.”

         Gabantane ya faɗi, amma sai cikin dauriya tace, “Ina jinka Yah Khalipha”.

      Kansa ya kaɗa mata yana ajiye keys ɗin hannunsa da wayarsa alamar maganar mai muhimmanci ce. “Dan ALLAH ki faɗamin gaskiya kin manta dani ko?”.

       Duk da tambayar tasa tazo mata a bazata dan ba ita tai zaton jiba sai da taji dumm. Ganin ya kafeta da idanu ya sata yin murmushin yaƙe tace, “Ban gane mi kake nufi ba Yah Khalipha”.

         “Nasan kin gane Zinneerah, amma tunda hakane bara na miki dallah-dallah”.

         “Tun randa na ganki a gidan nan nasan nasan fuskarki, amma na rasa ina na sanki dan kin banbanta da waccan ɗin dana sani a yanzu. Nasha gwadaki naga ko zaki nuna ke kin sani amma baki nunaba, sai yau da naga mama na tabbatar da cewa kece. Shiyyasa mamaki ya kamani na rashin nuna kin sanni da kikai kafin yau”.

        Tabbas taji kunya. amma sai ta dake, ta buɗe baki da zummar bashi amsa sukaji ƙamshin turarensa da takun tahowarsa. Duk kallon waje. sukai Zinneerah na haɗiye maganar da tai niyyar yi. Ganin yanda yake kallonsu ya sata jin wani iri, babu shiri ta diro akan motar tai cikin gida sum-sum duk da alamar ta zauna da Khalipha ke mata da hannunsa. 

            Khalipha da shi kansa kallon da Yayan nasu ke musu ya bashi mamaki, cikin dauriya yace, “Yayanmu na zata ka kwanta ma ai”.

        “Shiyyasa kazo nan kake taɗi?”.

Ya faɗa yana wucesa. Saurin waro idanu Khalipha yay waje da biyo bayansa. “Ni Abdul-Mutallab, jikan Abdul-Mutallab, ƙanin Abdul-Mutallab wane ni Yayanmu”.

    Ɗan juyowa yay ya dubesa. Hakan yasa kunya kama Khalipha yakai hannu yana shafa wuya da risinar da nasa idanunsa ƙasa.

         Wani irin juya idanunsa da suka ɗan fara sauya kala yayi yay gaba batare da ya sake cema Khalipha ɗin komaiba, dan harga ALLAH baya cikin hankalinshi da nutsuwar. Binsa da kallo Khalipha yay harya shige sashen Hajiya Iya. Kasa binsa yayi, sai kawai shima ya nufi sashensu zuciyarsa na ƙoƙarin karkato masa wani abu daban.


        ★★★★


    Washe gari da safe suka tashi da tashin hankalin ruɗewar jikin Hajiya Iya. Dan tunanin data kwana yi jiya game da kamanin little da AK ya ja jininta sake hawa sama matuƙa. Ita Zinneerah bata fahimtaba dan duk zatonta Hajiya Iya barci takeyi, dan itama kanta barcin nata rabi da rabi ya kasance. Sai da ta farka da asuba taji hajiya iya na wani irin wahallen nishine hankalinta ya tashi. Ruɗani ya sata fita da gudu zuwa ɗakin AK ta hau bugawa tana kiran sunansa.

     Zaune yake saman sallaya yana karatun Al-Qur'ani dan shi ko sau ɗayama bai rintsa ɗinba. Yanda yaga rana haka yaga dare, a daren na jiya. Tunda yaji bugun ƙofar yasan ba lafiyaba. Ya ajiye Qur'anin tare da miƙewa a nutse ya nufi ƙofar ya buɗe ko sauraren Farah data farka da jan tsaki baiyiba.

     A rikice Zinneerah ta damƙo hannunsa jikinta na rawa ga hawaye na kwarara. “Yayanmu Granny, Granny Yayanmu, dan ALLAH kazo Granny karta mutu”.

      A take shima ya rikice. Ya shiga binta a baya tana riƙe da hannunsa har sannan tana jansa. Tunda suka shigo yaga halin da Hajiya Iyan ke a ciki sai hankalinsa yafi nata tashi, a take yay kanta yana kiran sunanta da ƙarfi. 

      Zinneerah daketa yarfe hannu kukanta na ƙara tsananta ya duba cikin sarƙewar harshe yace, “Ɗakkomin waya a ɗakina, m....”

    Batama bari yakai ƙarsheba ta kwasa da gudu ta fice. A guje ta shigo ɗakin har tana bangaje Farah data sakko daga gadon tana mitar an tasheta tana barcinta. Wanwar Farah ta zube a ƙasan tiles ɗin amma ko kallonta Zinneerah bataiba ta nufi wayar data hango a drawer gefen gado duk da bata da tabbacin nasane. Sai dai tana kaiwa garesu ƙamshinsa dake manne dasu suma ya tabbatar mata nasanne. Duka ukun ta kwasa ta sake tsallake Farah dake nishi a ƙasa ta fito.

         Da ƙyar ya iya saita kansa ya lalubo Number Baffah, shima Baffah da yake ba wani barcin kirki yayiba akan idanunsa kiran ya shigo. Mamaki da tsoro ya sakashi ɗagawa ganin sunan Adnan. 


     Cikin ƙanƙanin lokaci dukkan ƴan gidan suka gama taruwa sashen hajiya Iya dake cikin mawuyacin hali. Khalipha ne keta ƙoƙarin bata taimakon gaggawa kasancewar ɗalibin likitanci dake gab da kammalawa insha ALLAH. Da ƙyar ya samu yaɗan saita wasu abubuwa. sai dai ya basu tabbacin dolene a wuce asibiti da ita tunda nan gida ba kayan aikine da shi ba.


     Suna idar da sallar asubahi ko Shira Hospital suka wuce. A canne likitocin da sukai duty ɗin dare suka rufu kanta. Yayinda AK kuma ya shiga bige-bigen waya na shirin wucewa da Hajiya Iya London kamar yanda dama yaci buri tun da, sai dai tace bata zuwa Nigeria ma akwai likitoci ƙwararru. A yanzun kam tunda bata a hayyacinta yaci alwashin sai ya kaita insha ALLAH an duba wannan ciwon ƙafartata mai kama dana gado. Dan mafi yawan ƴan family ɗinsu na ɓangaren mahaifiyarta duk sanadin ciwon ƙafa suke barin duniya kamar dai Inno. Ga su duk ALLAH ya basu jikin ƙiba dama masha ALLAH............✍

        


*_Kuyi haƙuri naji kunata cewa bana bana yayinku naƙi muku surprise. Wannan karon abin ya haɗa da wasu uzurorine wlhy. Amma insha ALLAH zan baku mamaki indai pages ne, ina kuma sake baku haƙuri wannan karon akan tafiyar hawainiyarmu ta Typing gaba ɗaya. Ku ɗauki hakan matsayin yau da gobe sai ALLAH. Sannan wasunmu sunada lalurorin yau da kullum tattare da su, da kuma uzirorin rayuwa da duk sukazo mana tamkar an saita. Mukammu bama jin daɗin hakan, dan babban burinmu shine muga mun taru gaba ɗayanmu mun faranta muku tamkar yanda kuka faranta mana kuma kuke zuwa kuna sayen buks ɗinmu a koda yaushe. ZAFAFA TEAM na godiya gaba ɗayansu tare da fatan alkairi a gareku da ban haƙuri. da babban albishirɗin ganin gyara daga garemu baki ɗaya insha ALLAH_*


*_Masu karantawa a waje kuma dan ALLAH ku daure kuzo ku saya naku copy ɗin da halalinku kuma ALLAH zai sakama kasuwancinku albarka ta inda bakuyi zato ko tsammaniba insha ALLAHU. Dan duk wanda ya kare mutuncin wani da fita haƙƙinsa kaima ALLAH zai fita naka ya kuma kare mutuncinka da izininsa._*


*Muna godiya da zaɓin zafafa a koda yaushe😍😍😘😍😋🤗🙏🏻*.


No comments

Powered by Blogger.