Makauniyar Kaddara 24


 Page 24*


...........Koda Farah ta gama surutan haushinta gado ta faɗa daga ita sai towel ɗin da tai wanka tai kwanciyarta batare data tuna ya kamata taje ta gaida matan gidanba. Barcinta tasha sosai kafin ta miƙe saboda shigar kiran salla a kunnenta dan bata da sakaci da ibada. Ruwa ta ƙara watsowa tayo alwalar salla.

 

      Koda ta fito ta gabatar da sallar kwalliya tayi dai-dai misali ta shirya cikin baƙar doguwar rigar jallabiya mai ƙyau, ɗan kwalin rigar ta naɗa a kanta yanda larabawa keyi dai.

       Farah ƙyaƙyƙyawa ce kamar yanda mijinta ya faɗa. Tanada jiki mai ƙyau ga kuma ilimi, matsalarta kawai itaɗin ƴar gatace ta gani kasheni, ƴar shagwaɓace bugun farko kuma jinin mulki. Dan itace auta a gidansu shiyyasa kowa sonta yake. Sannan ta girmane a Morocco hanun kakarsu dan a wajen haihuwarta mahaifiyarta ta rasu, daga bayane bayan rasuwar kakar tasu itama riƙonta ya dawo hannun Mammah duk da babbar yayarsu taso ita ta zauna a hannunta. Tana da son girman tsiya da miskilanci, dan koshi kansa oga kwata-kwatan yimasa isarta da taƙama takeyi. Sai dai shima da yake gwanine wajen iyawa duk da baɗan masu mulkin bane sai sukeyin dai-dai da juna harma ya kaita ƙasa ta risina tana mitar ya cika baƙin hali.

        Tana son Yah Abdull-Mutallab kamar yanda kowama yasan shima yana sonta. Sai dai tanada matsalar tsananin kishi, wanda da alama ta gadane wajen su Mammah. Dan ita kanta Mammah ɗin ta rabu da Baffah ne saboda kalmar ƙara auren nan daya furta gareta duk da ɗunbin son da take masa har yanzu. Dan ko aure taƙi sakeyi.

      Bayan ta shirya ta feshe jikinta da turarenta masu shegen ƙamshi da ɗaukar hankalin mai shaƙa ta fito. A falo ta sami Khalipha daya shigo zaune yana lunch. Ta ƙarasa inda yake taja kujerar dining ɗin ta zauna itama. Duk da ya girmeta shine ya fara gaidata dan yasanta da son girman tsiya. Babuko kunya ta amsa masa kuwa tana buɗe kulolin dake dining ɗin. 

       Yanda take yatsina fuskarta ne ya tabbatarma Khalipha komai bai mataba a wajen. Dan haka yay ɗan murmushi da fadin, “Ki faɗa abinda kike son ci sai a sayo miki idan duk nanan basu mikiba”. 

     Kanta tsaye kuwa ta shiga zayyano masa duk abinda takeson ci ɗin. Batare da damuwar komaiba kuwa ya miƙe ya fita dan dama ya kammala nasa cin abincin.


     Khalipha na fita babu jimawa su Zinneerah suka shigo gidan. Ita kaɗai ta shigo sashen na Granny cike da ƙarfin hali dan mararta ciwo take mata. Batare data lura da Farah dake zaune a dining tana latsa wayaba ta nufi ɗakin Hajiya iya. 

    Farah da tun shigowar Zinneerah ita idanunta suka sauka gareta ta wani bita da kallo a yatsine tanajin rashin son yarinyar a ranta haka kawai. Sai dai kuma mamaki take ita wacece a gidan ma? Dan bata santaba a tarihi da labari. (To anya kuwa ƴar gidan nan ce?) ta ayyana a ranta gabanta na faɗuwa. Yunƙurawa tai ta miƙe zata bita ɗakin Hajiya iyan dan yanda Zinneerah ta wuce bata gaidataba sai abin yay mata zafi taga kamar rainine dan ta lura da yarinyar itama akwaita da nuna isa tun kallon datai mata ɗazun, sai kuma mita tuna oho mata ta koma ta zauna tana yin ƙwafa.


       Zinneerah kam da batasan tanayiba tana shiga suka gaisa da Hajiya Iya wanka ta shiga. Bayan fitowarta ta shirya cikin doguwar rigar boyal less da yay mata ƙyau ɗas a jiki, dan ɗinkin ya zauna da ƙyau masha ALLAH. Tayin abinci hajiya iya tai mata. Amma sai tace ta ƙoshi sai anjima. Basu jima da cin abinciba a makaranta. Daga haka ta kwanta a sofa sai barci.

       Barci tayi sosai, dan bata farkaba sai bayan sallar la'asar da Hajiya Iya ta tadata. Toilet ta shiga ta ɗan gyara jikinta ta fita zuwa falo cin abinci. Yanzu kam mafi yawan yaran gidan sun dawo. duk suna ma a falo zaune suna hira har Granny. Sai matar yayansu baƙuwar ɗazun dake zaune gefe ta haɗe fuska tamau kamar tanajin warinsu.

    Cikin ƙarfin hali tai mata barka da yamma. Batare da sauraren amsartaba ta gitta zata wuce saita dakatar da ita. Juyowa Zinneerah tai gareta fuskarta ɗauke daɗan murmushi. A ɗage sosai Farah dake ƙarema Zinneerah kallon sama da ƙasa tace, “Kema anan gidan kike?”.

      Kai Zinneerah ta ɗan jinjina mata kawai batare datace kimaiba.

    “Uhyim! Amma ban sankiba ni”.

Kallonta Zinneerah tai cikin ido kamar zatai magana sai kuma tai shiru fara'ar fuskarta na raguwa. Dan tsaf ta fahimci dizgata matar Yayan nasu da taji suna kira da Aunty Farah ke neman yi. Itama Farah ɗin da har yanzu ke mata kallon wulaƙanci da isa duk da kuwa babu wani abin kushewa tattare da Zinneerah ɗin, dan duk da take ƙyaƙyƙyawa babbar yarinya babu abinda zata nunama Zinneerah, itama idan dirin jikinne ALLAH ya bata, musamman ma yanzu da take a kan ganiyarta na kammaluwar sirrikan budurci, sannan jikinta a mulmule yake dan ba siririya bace bakamar Farah ɗin. Ga fatarta kalar ɗaukar hankali gamai kallo. ta buɗe baki zatai magana Hajiya iya ta katseta dan dama ta saka musu idone taga mi Farah ɗin zatayi.

       “Tunda ba zuwa cikinmu kikeba ta yaya zakisan kowa. Ke Zinneerah wuce kici abinci”.

     Sum-sum Zinneerah ta wuce dining tana ƙoƙarin maida duk wani ɓacin ran Aunty Farah ɗin daya fara yunƙuro mata. Dan a rayuwa ta tsani wulaƙanci da raini da disgi a rayuwarta. Zata iya jure komai banda waɗannan abubuwan.

     Sosai su Jamal sukaji daɗin abinda Hajiya tayi, itako Farah a fusace ta miƙe tabar falon zuwa ɗakin mijinta. Yi hajiya iya tai kamarma bata ganiba. Ta kuma haɗe fuska dan karma wani a cikin yaran yace wani abu. Daga hakama hirar ta watse. Dan barin falon itama Hajiya iya tayi.


         Kusan 6 Zinneerah da tuni suka fice suna can harabar gidan anata hira ta shigo sashen hajiya iya saboda matsa mata da mararta tayi. Bedroom ta nufa inda ta iske hajiya iya na waya. Sai da ta kammala ta dubeta tana ajiye wayar data gama ɗin.  “Fitinar Moddibo dabance wlhy. Inno dubamin ko su Rahi sun wuce?”.

       “Lah Granny ai sun tafi, bakuyi sallama bane?”.

     “Munyi sallama. Na zata basukai ga tafiyar banebam wannan fitinatunne yay kirana yanzu, wai ashe azumi yakeyi amma bai faɗaba tun ɗazu ba sai yanzu. Kuma wai abinci yakeson a haɗa masa. Gashi su Rahi ba tuwo sukaiba yau”.

      Cikin ƙarfin hali Zinneerah tace, “Granny yaya za'ai yanzu to?”.

         “Nima ban saniba to Zinneerah, sai dai ko ke zaki shiga kitchen ɗin ki haɗa masa tunda waccan malalaciyar matar tasa na tabbata ƙila ko shayi bata iya dafawaba balle wani tuwo”.

     Idanu Zinneerah taɗan waro waje da faɗin, “Kai Granny nikuma? Ta ina zai iya cin jagwalgwalona”.

      “Ci kuwa zaiyi harda santi Inno na. Kinga tashima kije kar ya dawo ya samu ba'ayiba ya fara baƙar zuciya danshi baya wasa da cikinsa. Tuwon zaki masa da ɗan wani abun mai sauƙi tunda azumi yakeyi”.

       Zata ƙara magana Hajiya Iya ta girgiza mata kanta. “Kinga babu abinda zai faru, lafiya lau zakiyi insha ALLAH kinji ƴar albarka. nina ai dana idar da sallar magrib zanzo nama tayaki muyi tare”.

    Jin abinda Hajiya Iyan ta faɗa ya sata miƙewa tana fadin to ta fice zuwa kitchen da kwarin gwiwarta. Sai da ta fara karanto addu'ar nasara kafin ta ɗauraye tukunya tasa ruwan tuwo dai-dai misali, dan itama dai tana ganin tuwon zataɗanci ko zataji sassaucin ciwon marar nan da taketa dannewa dan karta tadama hajiya Iya hankali. 

      Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala tuwon semo.. data bama nutsuwa sosai gudun yimasa kuskure, sai da ta kammala kwashewa zuciyarta keta ƙara ƙarfafata akan miyar da taketa tunanin masa tunda ta fara tuwon. Ɗanyen kifi ta cira ta gyara tasashi a wuta da kayan ƙamshi da albasa dan rage masa ƙarni. Kafin ta koma ta ɗiba kayan miya zallar attarigu da tattasai sai albasa da tumatur guda biyu kacal ta wankesu suma tasa a blender da ɗan ruwa bamai yawaba can tai musu markaɗe ɗaya da yay kamar jajjage amma yaɗara jajjagen laushi kaɗan. Kifin ta sauke ta tsamesa a ruwan ta buɗesa ta cire ƙayarsa duka ta farfasashi, ta ƙara ɗora tukunya tasa manja a wuta ta zuba wannan fasashshen kifin da albasa da magi ƙwara ɗaya ta rage wutar can ƙasa. Sallamar hajiya iyace ta sakata juyawa tana kallonta. Ta ƙaraso cikin kitchen ɗin tana magana cike da tsokana. “Wai wai, anya kuwa yau kunnen moddibo bazai kai ƙasaba Inno. Irin wannan ƙamshi haka da aka cika mana gida”.

     Dariya Zinneerah tai tana faɗin. “Kai Granny bammafa fara miyanba”.

       “Amma kuma ga ƙamshi ya cika ko ina”  Hajiya iya ta faɗa tana buɗe tukunyar data saka kifin nan dake fidda ƙamshi mai daɗi a cikin manja. “Masha ALLAH miyar mi zakiyi?”.

       “Granny ɗanyen kalkashin nan dana gani da zanyi”. 

       “Eh lallai kinyi tunani mai ƙyau, dama ɗazun Rahi tazo dashi wai ko zamuyi amfani dashi a gidanta suke ɗan shukashi”.

     “Aiko gashi yayi ƙyan fita Granny. shiyyasama ya birgeni. Kuma ta taimaka ta tsinkesa tun daga can yankawa kawai zanyi yanzu nasa a wuta”.

      “To bara na tayaki yankawa saiki haɗa miyar”.

    Babu musu ta bama Hajiya iyan, tunda dama tanason ɗan haɗa masa ko fruit salad ne haka da ɗan coconut juice idan zata iya. Ganin kifin ya mata yanda takeso ta zuba kayan miyarta a ciki da daddawa ta ƙara rufewa. Inda suke ajiye kayan fruit taje ta ɗauka komai dai-dai misali ta ajiye gefe, ta ɗauka kwakwa ta fasata itama ta ajiye gefe. Komawa tai ga miyarta taga kayan miyan yaɗan soyu, saita zuba ruwa ɗan kaɗan da kayan ƙamshi da magi amma ba star ba dan yana hana miya yauƙi. Da duk abinda take buƙata na saka miya ƙamshi ta saka ta maida ta rufe a binta da sake maida wutar can ƙasa. Dai-dai Granny ta gama yanka mata ɗanyen kalkashin. Amsa tai tana mata sannu da godiya. Granny ta bita da kallo tana murmushi. Madaidaiciyar tukunya ta samu ta saka kalkashin nan dan babu zancen wankesa shi. Tasa ruwa kaɗan da kanwa ta barsa a buɗe wutar naci daidai misali.

    Fita Granny tai dan an kira sallar isha'i, ita kuma tahau gyaran fruit salad ɗinta dan ɗan kaɗan zatayi ba yanda aikin zai mata yawaba. Saiko gashi ta gama a ƙanƙanin lokaci, tasa flavor na gwaba dana strawberry ta motsa. Kaɗan ta ɗan-ɗana, jin zaƙin ya mata dai-dai ta ɗaukesa tasa a fridge ta dawo wajen miyarta da dudduba. Komai yayi, kalkashinma ya dahu, kashe gas ɗin tayi ta koma wajen gyara kwakwar da zatayi juice itama, tabar kalkashinta dayay kauri sosai yana hucewa. Hakama miyar kayan miyanta tayi kauri yanda ko an haɗata da kalkashin bazata tsinkashiba. Sai da ta kammala haɗa coconut juice ɗinta ta saka a fridge shima sannan ta tattara kayan data ɓata ta wanke tsaf sannan tazo ta juye kalkashin cikin soyayyun kayan miyarnan ta motsa da kyau suka haɗe. Ɗanɗanawa tai taji komai dai-dai yanda take fata duk da dai akwai fargaba tare da ita har yanzun.

      “Inno an gama ko?”. Hajiya iya data sake dawowa ta faɗa tana shigiwa. “Eh Granny duk an kammala, amma dan ALLAH ki ɗanɗana wlhy inajin tsoro”.

      “Haba ɗiyar albarka nasanma komai yayi daɗi. ALLAH ya saka miki da kairan ya baki miji nagari dazai riƙemin ke gam, bar wani jin tsoro”. Kanta kawai ta duƙar tana ɗan murmushi. Sai dai a ƙasan ranta tana tunanin ita data haihu a waje ina ita ina yin aure. tafi ganema ta dage taita karatunta har itama ALLAH ya kaita lokacin da zata taimaki kanta da iyayenta......

       “Inno kinga ga naman kai nan da Rahi tai farfesu kafin ta tafi a haɗa masa dashi, sai akai masa gashi can ya dawo har yay wanka yana jira”. Hajiya iya ta katse mata tunaninta. Amsa mata tai da to tana haɗiye ƙwallar dake neman ciko mata idanu.

      Kular tuwon ta ɗauka tasa kan tire, ta zuba miyar a wani bowl mai murfi na tangaran mai haske, hakama farfesun tasa a ƙaraminsa duk ta ɗora a tiren. Fruit salad ɗin da lemon kwakwar ta fiddo a fridge duk da basuyi sanyi mai tsananiba sunyi dai-dai gamai sha. Fruit ɗin ta saka a bowl fruit salad, juice ɗin kuma tasa a jug da ruwa a wani tiren. Ta kuma gyara ɗan kwalinta cike da ƙarfin halin danne ciwon dake cinta ta ɗauka ta fito ranta fal fargaba.

     Zaune ta samesu shi da matarsa a dining ɗin. Tai sallama ya amsa batare daya ɗago daga latsa tab da yakeba. Farah kuwa bata amsaba saima harara data galla mata na tsananin kishin babu gaira babu dalili da haushin abinda hajiya iya tai mata akanta ɗazun. Ita dai Zinneerah gaishesu tai da masa barka da shan ruwa ta ajiye tiren ta koma ɗakko sauran kayan ba tare data damu da ƙin amsawar tataba. 

      Harta gama shirya komai a dining ɗin bai ɗago ya kalletaba. Ta juya zata bar wajen ganin ta gama aikinta taji yace, “Zoki zuba”.

        Dawowa tai da baya cike da ƙarfin hali dan mararta ƙullewa takeyi. Sama-sama take jin tsawar Farah na faɗin, “Kinga dalla kama gabanki zan zuba masa ni tunda inada hannu”. Juyawa Zinneerah tai zata wuce dan taimakontama ita Farah ɗin tayi, amma saita tsinkayi muryarsa a karo na biyu. “Malama ki zubamin abinci nace ko”.

     Jitai kamar ta fasa ihu dan takaicinsu, ta kalli yanda Farah ɗin ke watsa mata harara kamar idanunta zasu faɗo. Shima ta dubesa har yanzu kansa a ƙasa yanata danna tab. Dawowa tayi da baya tunda tasan dai itama matar tasa ai ƙarkashinsa take duk da wannan isar tata da rainin wayo. Batare data sake kallon sashen Farah ɗinba ta fara zuba masa komai tana ajewa gabansa. 

       Tana cikin zuba masa lemon kwakwar mararta tai matuƙar ƙullewa. Dole ta ajiye jug ɗin tai saurin zama a kujera tana kifa kanta a teble ɗin dan azaba.

       Karan farko ya ɗago kai ya dubeta. Farah kuma da kishi keci ta daka mata tsawa, “Kujimin ƴar barikin yarinya. bakin gama aikin da aka sakiba miye kuma na zama?”.

     Bata samu amsa daga Zinneerah ba dan bama jinta da ƙyau takeyiba. Shiko tab ɗin ya ajiye da maida hankalinsa gareta cike da nazari, ganin kusan sakan talatin bata ɗagoba yaɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. A karon farko na rayuwarsa ya ambaci sunanta cikin muryarsa mai taushi da tarin nutsuwa da rashin sakewa. “Zinneerah are you ok?”.

       Har cikin rai da jini sai da Zinneerah taji fitar sautin sunanta akan harshensa. Ta ɗan ɗago hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa ta. “Ba komai Yayanmu kaina ke ciwo”. Ta faɗa tana miƙewa tabar wajen.

     Da kallo ya bita kawai, Farah kuma ta rakata da harara tanajan tsaki da faɗin, “Lallai yarinyarnan idan kikace zakishiga gonata zanko juya fuskarki daga gaba ta koma baya a gidan nan wlhy”.

         Goshinsa ya murza kaɗan, dai-dai yana maida kansa ga abincin. Ya ɗan furzar da huci yana ɗaukar juice ɗin data zuba masa kaɗan a ƙaramin kofi ya kai baki. Duk jarabar da Farah keyi akan Zinneerah ɗin bai ma nuna yasan tanayiba balle ya tanka mata. Sai dai a ransa haka kawai yakejin dariya nazo masa.


          Zinneerah kam tunda takai ɗaki kwanciya tai a sofa tana riƙe mara dan Hajiya iya na bayi tana wanka. Taja kusan mintuna goma a wajen tana murƙususu harta faɗo a kujerar dan azaba kafin Hajiya iya ta fito.

      “Subahanallahi, Inno lafiya kuwa?”.

      Cikin kuka ta nunama hajiya iya saitin mararta. “Ikon ALLAH, nikam dai wannan ciwon mara daga ina? Keda baƙya ciwon mara mai ƙarfi irin haka amma wannan karon da alama ta canja miki sallo. Kinga tashi kije kiyi wanka da ruwan zafi sosai bara na leƙa su Haneef ko sun dawo, bansan ina Khalipha ya kwashesu suka tafiba tun ɗazun.

       Da ƙyar ta amsama hajiya iyan. Sai dama ta taimaka mata zuwa bayin, ta kuma haɗa mata ruwa mai zafi tace tai wankan tana zuwa.


      Ganin yanda Hajiya iyan ta fito da hanzari daga ɗaki Yah Adnan dake cin abinsa hankali kwance matarsa na gefe tana masa hira bayan ta gama bala'in Zinneerah ya ɗago ya dubeta. Tana gab da fita yace, “Granny lafiya kuwa?”.

      Juyowa tai ta dubesu dan ita hankalinta baima kai garesuba. Cike da damuwa tace, “Moddibo Zinneerah ce bata da lafiya. Inason na duba cikin su Moos'ab ne wani yazo ya kaita asibiti kar abin ya ƙara mata tsanani”.

       Shiru yay yana kallonta kamar bazaice komaiba. Ganin Hajiya Iya ta juya zata fita yace, “Granny su da basa nan ki jira na kammala dan zanje wajen Mahmud dama”.

      Dawowa Hajiya iya ta sakeyi tana faɗin, “To Alhmdllh shikenan ma, bara naje ta shirya kafin ka kammala”. Kansa kawai ya jinjina mata yana lumshe idanu da buɗewa alamar amsawar kenan.

         Wani irin kallo Farah ta zuba masa na tsananin takaici da kishi. Muryarta har rawa yake wajen faɗin, “Wai ban ganeba. kaine zaka kaita asibitin kuma?”.

       Idanunsa ya ɗago ya dubeta ya maida ga abincinsa batare daya bata amsaba. A ƙufule ta miƙe tana cewa, “Wlhy to sai dai mutafi tare. Dan bazan yarda ka tafi da wannan shegiyar yarinyar mai kama da aljanu kai kaɗaiba. Ni wlhy bazan iyaba ka shirya mukoma gaskiya”.

     Da kallo ya bita harta shige lungun da ɗakinsa yake. A bazata murmushi ya suɓuce masa ya girgiza kansa da ɗan taɓe baki ya ɗauke kai.

        Harya kammala abinda yake ya miƙe zuwa ɗakin bata fitoba, koda ya shigo isketa yay tana waya. Yasan dai bazai wuce Mammah ko cikin yayuntaba. Dan haka bai tsaya sanin dawa takeyiɗin ba ya shiga toilet. Cikin abinda baifi mintuna uku ba ya fito. Key ɗin mota da ke a bed side drawer ya ɗauka ya nufi hanyar fita ya barta tana wayar har yanzun.

       Yana fita itama ta miƙe ta ɗauka ɗan kwalin abayarta ta bisa tanayin sallama da yayanta da shigowarta ɗakin kiransa ya shigo mata a waya. Shine ta zauna amsawa.


        Sai da yay sallama a ƙofar ɗakin Hajiya iya ta amsa masa da bashi izinin shigowa sannan ya shiga. Zinneerah data fito wanka ta gama shiryawa cikin baƙar doguwar riga tana kwance a bakin gadon idanunta a lumshe hawaye na zirara. Kallo guda yay mata ya ɗauke kai ya maida ga hajiya iya data ɗakko mata hula da ɗan kwalin rigar.

          “Haka take ciwon kai?”.

  Ya tambaya kansa tsaye kamar yanda ta sanar musu ɗazun. Kallonsa hajiya iya tayi, “Ciwon kai kuma Moddibo? Zinneerah ce zata zauna yima ciwon kai raki kamar haka?. Ita jarumace ai da kake ganinta, tunda ka ganta haka ai abinda yafi ƙarfin ciwon kanne mararta ke ciwo, kuma da ba haka take mataba”.

       Jin abinda Hajiya iya tace ya sashi janye idanunsa daga kallonta ya maida kan Zinneerah data zumɓuro baki alamar bataso Granny ta faɗa abinda ke damun nataba. Baki yaɗan taɓe da nufar hanyar fita yana faɗin, “ta sameni waje”. Daga haka ya fice abinsa ya barsu da ƙamshinsa........✍


No comments

Powered by Blogger.