Makauniyar Kaddara 23
*Page 23*
...........Mamakinta ya sakashi ɗago manyan idanunsa ya zubasu cikin nata. Ɗunbin al'ajabin sabon salon nata na bayyaya ƙuru-ƙuru a cikinsu. Dan wannan salon iskancin tabbas ba nata bane aroshi tayi saboda wani dalilinta.
Itama ganin yanda ya zuba mata idanunne yasa gwuyawunta yin sanyi, ta sakar masa Murmushin ƙarfin hali da cije leɓenta na ƙasa tana janye jikinta baya.
Duk da yaji ɓacin ran ganin nata bayan ya gargaɗeta jiya da daddare akan kar tazo amma tay watsi da maganar tasa tazo, ga kuma salon isanci data shigo dashi gidan alhalin hakan ba ɗabi'arta baceba sai ya basar ya sakar mata wani lallausan murmushi daya sata sauke ajiyar zuciya babu shiri.
Su Saifudden kam dake dining jin shiru ya sakasu ɗagowa daga duƙar da kawunansu da sukayi, ganin abinda sukai tunanin zatayi bashi ya faruba duk sai suka saki numfashi. Musamman da suka hangota zaune a gefensa suna kallon juna da murmushi kamar ba yayansu ba. Itama kuma kamar ba itace ta shigo da salon rawar kai ba yanzun. Ta koma Farah ɗinta da suka sani mai tsanin miskilanci a garesu da jan aji.
Cikin magana ƙasa-ƙasa da babu wanda yake iya jiyosa. Dan saima ka ɗauka wani magana mai daɗin gaske yake faɗa mata, yace, “Wannan salon bai dace da ke ba, kowaye ya baki shawarar shigowa cikin shirawa dashi ya ɗoraki a kan keken ɓera da ta zubewar mutuncikine, da sakaki a layin masu ƙarancin tarbiyya”.
Shiru kawai tai tana kallosa cikin ido, tabbas gaskiya ya faɗa mata, dan ita kanta yanda ƙannensa duk suka zubo mata ido sanda ta shigo sai taji kamar ta muzanta a cikin idanunsu.. Dama da ƙyar ta iya dauriyar hawa kan shawarar auntynta da tace ta shigo musu gidan a salon gatse-gatse zasuji shakkarta fiye da da da take musu isa da shariya kawai. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗago tana kallon sashen dining ɗin.
Ganin duk yanda sukai ƙasa da kawunansu yasa ta wani yatsine fuska tana taɓe baki, dubanta ta maida ga Yah Adnan daya sake maida hankalinsa ga aikinsa. “Baby ku baku iya tarbar baƙo bane da masauki a gidan naku?”. Tai maganar a Farah ɗinta daya sani mai tsananin son nuna isa da miskilanci.
Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin da yakeyi. Sai dai bai ɗago ya kalletaba. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yay wani guntun murmushi na takaici ya cigaba da abinda yakeyi batare daya tanka mataba.
Ganin zata ƙara magana Khalipha yay saurin tareta da faɗin, “Sorry Aunty. muko muka iya tarar baƙi. Amma muje ki gaisa da Granny first”.
“Oh no Khalipha, zan fara wanka kafin na iya gaisuwa-gaisuwa ɗin nan naku da baya ƙarewa”.
Saurin girgiza mata kai Khalipha yay yana nuna mata Yayansu da ido, dan yasan hakan da zatai ba ƙaramin kuskure bane duk da yasan itama ta sani, tunda tafi kowa sanin halin Yayan nasu ai.......
“Kai lafiya na ganku cirko-cirko?”.
Hajiya iya dake fitowa daga ɗakinta ta faɗa batare da hankalinta yakai ga Farah ba. Kafin wani ya samu damar bata amsa Farah ta miƙe tsam cikin komawa ainahin takunta ta nufi hajiya iyan. Idanu Hajiya iya ta zuba mata harta ƙaraso gareta dan ta ganeta sarai duk da zuwanta gidan uku ne kacal, kuma duk kwananta bibbiyu ta koma
“Granny barka da safiya” ta faɗa tana ɗan kai jikinta ga hajiya iyan ta rungumota kamar yanda larabawa keyi. Duk da abun yazo banbarakwai Hajiya Iya bata damuba. Dan tasan akwai banbancin al'adu da yanki a tsakaninsu, kuma ko wancan zuwan da tayiyyi haka ta dinga mata gaisuwa, shiyyasa takemata uziri idan tayi wani abun. Hannu biyu ta karɓeta tana sake faɗaɗa murmushinta. Kafin ta ɗagota tana faɗin, “Uhm lallai yau munada manyan baƙi ashe”.
Murmushi Farah tayi cikin basarwa, dan tanajin hausa ras yine saita gadama take, tafi yin larabcin ƴan Morocco da turanci.
Sai a yanzu suma yaran gidan suka fara gaidata, duk da mamakin a yanda ta shigo gidan ɗazun ya kasa barinsu. Binsu kawai take da kallo tana amsa musu a yatsine. Kowa ta gane a cikinsu tunda tanada hotunansu na biki, duk da sanda akai auren nasu su Meenal basu da wayo sosai, amma tana jin hirarsu bakin Khalipha koshi uban gayyar idan yaso, musamman idan ƙanwarsa tana tare dashi.
Kafe Zinneerah dake can ƙarshe tai da idanu, kamar zatai magana sai kuma ta basar abinta ta maida kallonta ga Khalipha da Hajiya Iya ke masa magana ya rakata ɗakin Moddibo ta huta.
Da to ya amsama hajiya iyan.
Shi dai oga na zaune har yanzu yana aikinsa kamarma ya manta dasu a falon, sai da Hajiya iya ta zauna a kusa dashi sannan ya ɗago ya kalleta. Ganin yanda launin idonsa ya canjane ya sata sakin murmushi ta shafa fuskarsa.
“Babba da haƙuri aka sanshi, tunda ta kawo kanta karka wani saka damuwar hakan a ranka. Mu dama ai burinmu ta dinga shiga cikinmu a koda yaushe. Ba daɗin nisantarmu da kuke mukejiba”.
“Amma Granny sau nawa nake cemata tazo domin gaisheku tace batason zuwa. Sai yanzu dan son fitina. Wai kinmaga a yanda ta shigo gidannan da farko ma kuwa?.......”
“Shiii! ya isa, koma dai a wane dalili tazo ko ta shigo kai ka ɗaukesa ƙyaƙyƙyawa a ranka, ka kuma ɗauki ɗamarar canjata yanda kakeso duk da kayi sakaci tun farko, amma lokaci bai ƙure makaba”.
Huci ya ɗan furzar kawai yana jingina da kujera da lumshe idanunsa.
Sudai su Zinneerah da bajin mi su Hajiya iyan ke faɗaba sauri-sauri duk suka kammala cin abincinsu suka miƙe dan suna neman makara. Ɗakin hajiya iya ta nufa ɗakko school bag ɗinta, lokacin data fito su Yah Moos'ab duk sun fice, harsu Jamal ma. Da alama ita kaɗaice ta rage. Sau ɗaya ta kalli sashen da yake zaune har yanzu yanata faman aiki a lap-top, shi kaɗai ne a falon yanzun. Hajiya iya ta tashi zuwa kitchen saka su Baba Rahi haɗama Farah breakfast tare da Khalipha dake nuna musu yanda zasuyi.
Sum-sum ta wucesa a tunaninta baya ganinta saboda aikin da yake kamar ya kwashe dukan hankalinsa.
“Zonan”.
Ta tsinkayi muryarsa cikin kunnenta a bazata. A lokaci guda ƴan cikinta da jinin jikinta suka yamutsa na tsoro, tuna maganar su Jamal da sukace baya maimaita magana idan yay maka yasata nufosa. Zinneerah yarinyace mai tarin nutsuwa, sam bata da garaje akan komai, hakan yasa ko tafiya takeyi saika ɗauka yangace. sai dai sam ba haka bane, halittartace hakan. Komai nata cikin sanyi da nutsuwa bana sakarciba ko rawar kai.
Gabansa takai tsugunne kanta a ƙasa tana faɗin, “Yayanmu gani”.
Batare daya ɗago daga abinda yakeba, a daƙile yace, “Ɗiba tissue ki kwashe wannan jambakin”.
Ɗagowa tai babu shiri ta kallesa tare da waro manyan idanunta masu tsananin haske, cikin suɓucewar baki tace, “Iyeee Yayanmu miye laifinsa? Malaman basa faɗa f.....”
Sai kuma tai saurin ɗora hannunta a baki saboda tuna a ida take.
A karan farko yaɗan ɗago ya dubeta, hararar data saka kayan cikinta sake hautsunawa ya wulla mata tare da maida kansa ga aikinsa. Da sauri takai hannu ta cira tissue ɗin dake a centre table ta kaisa kan bakinta ta kwashe pink lipstick ɗin da yay mata ƙyau sosai tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallarta. Cikin ɗan rawar murya tace, “Na kwashe”. Yanzun ma batare daya ɗagoba yay mata nuni da hannu alamar taje.
Tana miƙewa Hajiya iya na fitowa da ga kitchen, tabi Zinneerah ɗin da kallo. “Inno lafiya baku tafi bane?”.
Ɗan juyowa Zinneerah tayi kanta a ƙasa tace, “Eh Granny yanzu zamu tafi”. Daga haka ta fice da sauri kafin hajiya iya ta sake cewa wani abu. Duban inda yake zaune Hajiya iya da zuciyarta ke ayyana mata ba lafiyaba tayi, “Moddibo mike faruwane da Inno, ko wani abu akai mata?”.
“Waye haka?”. Ya faɗa yana ɗan ɗagowa ya dubeta. Harara ta zabga masa tana kaiwa zaune. “Kaifa wulaƙancinka yawane dashi Moddibo, ita Zinneerah ɗince baka saniba ko yau na fara kiranta Inno a gabanka?”.
Ɗan murmushi yayi hankalinsa a aikinsa, a taƙaice yace, “ALLAH ya baki haƙuri”. Daga haka yaja bakinsa ya tsuke batare daya amsa mata maganar farko ba.
Ƙwafa tayi ta miƙe da sauri ta nufito ƙofar fita danta leƙa. tana fitowa maigadi na rufe gate alamar su Zinneerah sun wuce. Dawowa tai ranta daɗan damuwar ALLAH yasa ba wanine yayma Zinneerah ɗin wani abuba mara daɗi. Koda ta dawo falon bata kulashi ba saima harar inda yake da tayi ta shige ɗakinta abinta.
Murmushi yayi a karo na biyu yana girgiza kansa. dan yaga hararar da Hajiya iyan tai masa. Ajiye lap-top ɗin yayi zai miƙe Khalipha ya fito ɗauke da tire. Yaɗan bisa da kallo harya ƙaraso inda yake. “Yayanmu ga abincin Aunty”.
Kauda kansa yayi yana ƙarasa miƙewa. Sai da ya raɓa Khaliphan zai wuce sannan ya bashi amsa da, “Ka ajiye mata anan mana ta fito taci inma zatacin”.
Sanin abinda Yayan nasu ke nufi ya sakashi yin ƙaramar dariya, ganin zai shige yace, “To kaima ai baka karya ba”.
“Karka damu Besty yau ina azumine”. Ya bama Khalipha amsa yana shigewa corridor ɗin ɗakin nasa.
Zaune a bakin gado ya iske Farah ɗaure da towel nashi ajiki alamar wanka tayo. Sallamarsa ta sakata saurin zare wayar dake a kunnenta ta ajiye alamar magana takeyi da wani, kuma bataso yaji. Wayar yaɗan kalla tamkar zaiyi magana sai kuma ya fasa.
Cike da basarwa itama ta miƙe duk da tasan ya fahimci waya take ya basar dan shi mutum ne mai lura. Sai dai bai zama lallai ya nuna makan ya fahimtaba sai yaso.
Ganin yanda ta ciskule fuska cike da isar tata shima sai ya basar da ita ya nufi wadrobe zai dauka abu. Bayansa ta harara da miƙewa sanin idan miskilancine ya fita iyawa. Rungumesa tai ta baya tana jero masa kalaman kewarsa da tayi a kwanakin nan da basa tare. Komai bai ceba sai janyeta a jikinsa da yayi. Tabbas yana son Farah fiye da hasashen mai tunani. Dan duk inda mace takai ƙyaƙyƙyawar Farah takai, a zaman takewarsu tana ƙoƙarin ganin ta ƙyautata masa da faranta masa. matsala ɗaya ce ke cimasa tuwo a ƙwarya game da ita zuwa uku. Na farko shine ƙin danginsa. Sai dai yasan wannan training ɗin su Mammah ne, dan mafi yawan rayuwarta a hannunta tayi. Shiyyasa yakan mata uziri da hakan da ƙoƙarin ganin ya canjata. Sai kuma shegen kishinta da sam ta tsani taga wata mace ta raɓesa koda a wayane, ga ɗan banzan zargi daya tabbatar duk kishinne yake kawo matashi. Na uku son isa da nuna gadara a dole ita isashshiyace ƴar masu mulki.
Zaune yakai saman sofa yana lumshe idanu. Da wannan damar tazo ta zauna a cinyarsa tana ɓata fuska da faɗin, “Wai kana nufin fushi kake dani? Bayan nice ya kamata nai fushi da kai Yah Mutallab”.
Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaji ta fara masa murje-murje a jiki cike da salo ya buɗe idanunsa da sauri. “Kinga tasarmin a jiki azumi nakeyi”.
“Azumi kuma? Nami to?”.
“Ina ruwanki da ko namiye?”. Ya faɗa yana tureta.
Kallonsa tayi da ƙyau idanunta na kawo ruwan hawaye dan tanada saurin kuka dama. Muryarta na rawa tace, “Dan nazo gidanku zakaimin wulaƙanci?”.
“Anmiki wulaƙancin, ni bance karkiyi abuba amma kikayi saboda kin rainani yanzu kina ganina dai-dai dake ko? Sannan tsabar iskanci wai gidanmu zaki shigo da wani salon sakarci, yanzu da Hajiya iya ko Baffah wani na falon kika shigo ɗin nan mi zasuyi tunanin kin koma kuma?”.
A take jikinta yayi sanyi, hawaye na rige-rige sake zubowa. Kamar baza tayi maganaba sai kuma mita tuna oho mata ta kallesa da sakin ƙaramin murmushi tana share hawayenta. “Kayi haƙuri nayi kuskure, kuma daka tabbatar min hakan sai naji ban ƙyautaba, nima kuma salon bai dace dani ba sam. Amma maganar tahowa ba laifina bane har da su Mammah”.
“Tunda su Mammah ɗin ke aurenki saiki kirasu ki sanar musu kin iso su nema miki wajen zama. dan ba zaki zauna a gidan nan ba. Lokacin da nake lallaɓaki kizo domin gaishesu matsayinsu na iyayena kai tsaye kike cemin bakison zuwa inda suke. To suma yanzu basa buƙatarki”.
Ya ƙare maganar da miƙewa ya fice a ɗakin batare da ko waiwayenta ya sakeyiba.
Bayansa ta raka da kallo idanunta na wani ƙankancewar bacin rai, ta cije baki zuciyarta na mata zugi da sakejin zargin jiya na dawo mata a rai sabo. Tabbas huɗubar aunty data hauce taso jamata wannan wulaƙancin nasa. Duk da dama bata isa tanƙwarashi ko juyasa yanda takeso ba tunda shima bauɗaɗɗen ne, dan ya fita zafin kai da shegen taurin kai tamkar shine jinin mulkin ma ba itamba.
Tayi alƙawarin bazata ƙara kamanta irin kuskuren dataso tafkawa a yau ba nason kwatanta zubar da kimarta. Dan wani raɗaɗi takeji a zuciyarta idan ta tuna a yanda ta shogo gidan a dole ita wayayya. Bandama shirmen aunty data bata shawarar ba ita kuma ta hau ai ko ba'a faɗaba duk wanda ya ganta yasan wayayyace ita, bawai saita nunama duniyaba kodan jinin mulki dake yawo cikin jikinta da tarihinta.
Taja ƙaramin tsaki da ɗauka waya ta kira Mammah, labarta mata duk yanda sukai yanzun tayi. Faɗa sosai Mammah keyi kafin ta yanke wayar domin nemansa.
Itakuma sai ta juya akalar kiran ga auntynta. dan dama da ita suke waya ɗazun daya shigo, itama ta labarta mata komai daya faru da nuna mata gaskiya shawaran data bata na shigowa gidan a yanayin gatse-gatse baiyiba. Dan gashi hakan da tayi yaso taɓa mata kima har a idanunsa, balle ƙannensa da tasan suma kowa ya gumtsi gulma ne dan babu damar yi a gabanta ne ko shi Abdul-Mutallab ɗin dan tasan yanda suke shakkarsa a gidan.
Itama dai auntyn tata kamar Mammah faɗan ta kamayi kamar Adnan ɗin ne a gabanta. Ta kumace ita ai batace tayi gatse-gatse a gabansu kamar wata sashasha ba ko mara tarbiyya, tadaice ta nuna musu banbancin da da yanzun kawai, daga haka ta yanke wayar itama ta koma neman Yah Adnan ɗin.
Su dukansu daga can nemansa a waya suka shigayi, sai dai babu wanda ya iya samunsa dan cama ake musu switch off. Mammah tai ƙwafa dan tasan kashe wayar yayi tunda yasan tsiyar daya shuka.
A falo kam a yanda ya fito ɗakin a fusace ya fice abinsa yasa Khalipha dake zaune yana karyawa fahimtar babu lafiya. Duk da dama dai ba wannan ne karon farkon daya fara ganin rikicin yayan nasu da matarsa ba. Duk da shi yayan nasu kan kauce faruwar hakan a gaban idonsa, amma da yake Farah mace ce mai nacin masifa da mita saita kaisa ƙarshe ya yaɓa mata maganar da zata koma rusar kuka. Dama kuma da yawan faɗan nasu ana yinsane akan zamansa gidansu nacan london ɗin, dan kullum zancenta baya wuce sai ya barmata gidanta ya koma hostel da zama.
Hajiya iya na ɗaki tana gabatar da walha dan haka batasan wainar da ake toyawaba. Sai da ta idar ta fito ne ta iske shi da Khalipha ɗin duk basu a falon. Baba Rahi ma ta sake gyara falon tsaf sai tashin ƙamshi yake. A tunaninta yana ɗaki tare da matarsa yasa bata damuba ta koma ɗakin danta ɗan kwanta itama ta huta.
________________________
*_DANYA_*
Yau a lissafi kwanaki bakwai kenan da bizne aikin Malam da Inna tayi, hakan yasa tun a daren jiya take zuba ido akan dawowar baba. Sai dai har garin ALLAH ya waye babu shi babu labarinsa. Bata damuba dan tasan akwai yau.
Aiko yau ɗinma dai tunda gari ya waye idanunta basu huta da kallon ƙofa ba. Da taji an motsa ƙyauren gidan sai ta hau washe baki, sai kuma taga bashi ya shigoba saita haɗe fuska dajan tsaki. Kamar wasa tana zaune a bishiyar tsakar gidan har aka kira azhar. Maimakon ta tashi tai sallar sai ta cigaba da zama wai idan ya shigo ta haɗa duka tayo ai.
Duk wannan zaman zuba ido da Inna keyi na dawowar Baba Tinene na a gidan tana wanki, ta ƙure waƙa a wayarta da inna bata taɓa tambayarta daga ina ta samotaba. Koda ta tambayi Innar zaman mi take ta sanar mata sai kawai ta hau dariyar shaƙiyanci tana faɗin, “Oh kice tsohon tsimin soyayya ne ya motsa Innarmu”.
Banza Inna tai mata tunda tasan ba kunyace da Tinenen ba, yanzu saita yaɓa mata wata maganar. Haka ta cigaba da zama a wajen har akai sallar la'asar. Tinene data gama wankinta har tayi wanka tana kwashe kayan da alama fita zatayi a gidan. Buga ƙyauren gidan da akai da masifar ƙarfi ya sakasu dubar hanyar zauren a firgice su duka.
A bazata Karima ta shigo gidan jaye da akwati buju-buju da ita tamkar wadda aka ƙwato daga bakin kura. Babu shiri Tinene ta watsar da kayan hannunta ƙasa. Innama ta zabura kan Karimar dake tafiya kamar ma da tangaɗi.
“Mi nake gani haka ni Asabe. Karima daga ina kike tahe da maraicen nan?”.
Ina babu bakin amsawa daga Karima, sai ma zubewa datai a ƙasa cikin hakki tace, “Innarmu ku bani abinci yunwa nakeji”.
Tinene dake tsaye tana kallonsu har yanzun tace, “Tab abu mai wahala anan gidan yanzu Yaya Karima, amma bara naga inada wazobia ko awarar gidan Rashida a samo miki idan bata ƙareba dan maraice yayi”.
“Nagode auta. Inna bani ruwa”.
Ta sake faɗa tana kaiwa kwance da zare hijjabin jikinta gaba ɗaya ta jefar. Ruwan Inna ta ɗebo mata da sauri ta kawo mata, ta ɗagota daga kwancen da take danta bata sai a lokacin idanunta suka sauka akan sayin duka dake a wuyan Karima da damtsen hannunta ruɗu-ruɗu ga tsohon ciki. Duk da kasancewarta baƙa hakan bai hana fitar sayinba da ƙyau.
“Na shiga uku ni Asabe waya maki wanga bugun haka ga ciki Karima? Badai sheɗanin yaron nanbane Babawo?”.
Karima ta sake zamewa ta kwanta cikin tirɓayar jar ƙasar batare data bama Inna amsaba. Ganin Innar zata takura mata tace, “Inna ki barni dan ALLAH, ku bani abinci nide karna matu”.
Kafin Inna ta samu bakin sake cewa wani abu Tinene ta shigo gidan ɗauke da farar leda da awara a ciki. Kwano ta dauka a wanke-wanke ta juye mata takai gabanta. Cikin rawar jiki Karima ta tashi zaune taja kwanon. Bibbiyu ta dinga haɗa awaran tana turawa a baki. Ganin tana neman shaƙewa Inna tai azamar bata ruwa ta sha. Koda ta cinye saita kuma zubewa tana sauke numfashi wani irin zufa na karyo mata ta ko ina duk da kuwa awaran bamai zafi baceba.
Sudai suna tsaye shiru cirko-cirko kowanne da kalar tunaninsa akan wannan al'amari..........✍
Leave a Comment