Makauniyar Kaddara 22
Page 22*
.........Cikin sauri ta haɗe murmushinta dayin diri-diri na alamar rikicewa. Dan wani irin kallo da take kasa fassarawa a duk sanda yay matashi ya watso mata yanzuma ya ɗauke kansa fuskarsa na ƙara tsukewa fiye da yanda ya fito. Sum-sum ta juya gasu Bahijja da suma sukai tsitt daga ihun da sukeyi na murnar wayarta zata zauna yace, “Haɗomin black tea yanzun nan”. Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa.
Da sauri duk suka kalli Zinneerah da itama kallonsu take. Meenal tace, “Wlhy ki tashi kafin yace kin ɓata masa lokaci”. A take idon Zinneerah ya fara tara ƙwalla. Dan wannan shine karo na farko da ya sakata irin wannan aikin bayan gyaran ɗakinsa.
Bahijja tace, “Kinsan mi zakiyi?”
Zinneerah ta girgiza mata kai da sauri. “Kije kima Baba Rahi magana ta haɗa miki, dan tafi kowa sanin abinda yakeso a nan gidan bayan Granny. ALLAH yasa basu tafi ba, tunda ba gani yayba ki fiske abinki ki kai masa kawai a rabu lafiya. Dan shi inhar ya sakaka abu bakayi dai-dai yanda ya buƙataba ka shiga uku”.
Jin abinda Bahijjan ta faɗa ɗinne ya sake tsurar mata da ciki, amma shawarar saka Baba Rahi ta haɗa matan ya sata jin sassauci. Da sauri ta miƙe zuwa kitchen, sai dai wayam babu baba Rahi a ciki. Tai saurin kallon agogon dake a kitchen ɗin wanda ya bata tabbacin Baba Rahi ta wuce gida dan ba'a nan take kwanaba daman.
A take ƙwallan da take maƙalewa suka silalo mata. Jiki a sanyaye ta ɗiba kayan ƙamshi tasa a turmin ƙarfensu ɗan ƙarami ta hau dakawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama dafa shayin daketa uban ƙamshi a kicin ɗin, sai dai duk wannan ƙamshin nasa dazai iya saka mai kallo buƙatar sha ita a tsorace take. Ƙaramin flask ta samu ta juye tare da ɗorawa a tire ta saka kofuna biyu da mitsilin bowl data zuba suga a ciki ta ɗakko ta fito tana karanto addu'ar nasara a cikin ranta.
Bata iske kowa a falonba su Jamal sun gudu, hakanne ya sake ɗarsa mata tsoro a cikin rai ta nufi ɗakin tamkar an daddoke mata gwiyawu. Sai da tai sallama kusan sau huɗu sannan ya amsa mata da bata izinin shiga. Ta tura ƙofar ta shigo ƙamshinsa na rige-rigen shiga mata hanci. Tsaye yake a gaban mirror sanye cikin farar jallabiya ruwan madara yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake vibration.
Tai saurin kauda kanta ƙasa murya na ɗan rawa tace, “Yayanmu ga tea ɗin”.
Juyowa yay dai-dai yana ɗora wayar tasa a kunne ya kalleta da fararen idanunsa da suka nema ruɗata. Dan itama yayi dai-dai da ɗago nata zata saci kallonsa. Ƙasa tai da kanta shima ya janye nasa yana zama kan sofa. Ƙafa ɗaya ya ɗora kan ɗaya yana kai bayansa ya jingina da kujerar ya sake dubanta ya ɗauke kai. “Zaki cigaba da tsayamin a kaine?”.
A sanyaye Zinneerah ta ƙaraso ta ajiye tiren saman table ɗin gabansa, dai-dai yana faɗin, “Ina ruwanki da ko wacece. Ki cigaba da maganarki kona kashe wayata”. Ya ƙare maganar dajan guntun tsaki.
Zinneerah dai dake saurarensa haka kawai ranta ya bata matarsace. maganar su Meenal data tuna yasata kaiwa tsuggunne ta fara ƙoƙarin zuba masa a kofin. Sai dai jin kamar ana kallonta ya sata ɗan daburcewa, kamar zata ɗago sai kuma ta fasa.
Kamar ya fahimci ta gane kallonta yake sai ya miƙe gaba ɗaya yana bama matarsa dake tambayar ya bata hajiya iya amsar da cewar “Bama tare”.
Tabbas Zinneerah taji kalmar “Bama tare” daya faɗa, sai dai batajin mi matar tasa ke faɗa dagacan, a bazata taji saukar wata gigitacciyar tsawarsa cikin kunnuwanta. Ai batama san sanda ta zube ƙasa daɓar ba tana cusa kanta a ƙafafunta jikinta na rawa. Shiko da baisan tanayiba ya cigaba dayin magana a hasale matuƙa.
“Farah! Ki shiga hankalinki, ke miyasa a kullum tunaninki baya a layin na masu hankali? To kije hakaɗinne ma, ai dai nima namijine ko? Wawuya kawai mtsoww”. Ya ƙare maganar dajan wawan tsaki yana yanke wayar ya jefa saman gado. Wadrobe ya nufa ya finciki murfin da ƙarfi ransa na nasa suya, ya rasa wane irin hukunci zai fara yima Farah akan yawan furta kalmar zargi gareshi a duk lokacin da yay nesa da ita zuwa wani waje. Inhar zaiyi tafiya ta dinga bin ƙwaƙwƙwafinsa kenan tamkar wani ɗanta saboda shegen kishinta na tsiya.
“Zan koya miki hankali”
Ya fada zuciyarsa na sake kumbura. Ɓacin ran da yake a ciki ya sakashi mantawa da Zinneerah a ɗakin ya fara ƙoƙarin fara shiryawa.
Shirun da tajine ya sakata ɗago kanta a tunaninta fita yayi. Babu shiri ta miƙe ta fita da gudu ganin ya fiddo kaya alamar sanyawa zaiyi.
Shikam baimasan tanayiba, Sai da ya gama saka kayan ya nufo mirror dan saka turare idonsa ya sauka a kan kayan data ajiye, sai dai babu ita a wajen. Wani sabon takaicine ya sake lulluɓesa tuna abinda Farah ta faɗa akanta. Ya cije baki da rumtse idanunsa da ƙarfi yana raya wannan karon sai tasan shi take dangantawa da Zina wlhy.....
Yana ƙoƙarin zaman shan shayin da Zinneerah ta zuba kira ya shigo masa. Sanin mai wannan ringtone ɗin yasashi miƙewa ya ɗauka wayar yana ƙoƙarin sassauta fushinsa.
“Barka Mammah”. Ya faɗa cikin nuna girmamawa a gareta. A take zuciyarsa ta kara rinewa da ɓacin rai dan dama yasan bai wuce Farah takai ƙararsa wajentaba kamar yanda ta saba. Uffan baiceba har Mammah dake zuba faɗa daga can tayi ta gama. Sai daga ƙarshe da tace Farah ɗin zata biyowa Nigeria itama sannan yay magana.
“Mammah abinda nazoyi nanfa important ne, karki biyema shirmen.......”
“Saurara min Abdul-Mutallab!!” Ta katsesa a tsawace. “Kana nufin bansan abinda ubanka da kakarka suke shiryawa a kanka bane?, to wlhy su sani ƙwatarka a hannuna wannan karon sunyi kaɗan. Idan har bakaso Farah ta biyoka ka dawo London yau yau ɗin nan tunda kasan tanada lalura a jikinta. Inba hakaba bayan itama tazo nima zanzo dan ina dai-dai da kowa cikinku”.
“No, Mammah Please, nafa faɗa miki abinda zanzoyi tukan na taho”.
“Amma baka sanarmin zaka daɗe haka a nanba, dama an manna maka harkar noman ne saboda munafunci ai. Sannan wannan munafikin yaron dake nane da kai ko yaushe idan kun dawo ya wuce hostel da zama, inba hakaba Abdul-Mutallab sainayi bala'i bala'in ɓata ranka, wlhy ubanka ma sai yayi dan.........”
“Mammah Pleaseeee!”.
Ya faɗa cikin zafin rai, dan ya mugun tsanar yaji tana zagar masa mahaifinsa da ƴan uwansa.
Ƙitt ta yanke wayar batare data sauraresa ba.
Kansa ya dafe saboda wani jiri-jiri dake neman kwasarsa. Shin wai wace irin rayuwace wannan mahaifiyarsu kesan taga sunyi? Gaba ɗaya ta tsani taga sun raɓi mahaifinsu da ƴan uwansu. Ta yaya kuwa hakan zata kasance bayan hausawa sunce da uba ake ado. Duk ƙoƙarin da yake wajen fuskantar da ita muhimmancin family ɗinsa bata fahimta. nata ƴan uwan kawai takeso su girmama su raɓa. Anya kuwa idan ya cigaba da biye mata bazai halaka ba. Tunda suke da Baffah bai taɓa nuna masa matsanancin ɓacin ransa akan abinda Mammah takeyi na katangesu daga garesaba irin wannan karon. Har a yanzu haka ya kasa tarosa gaba ɗaya. A da kam idan yayi masa faɗan yakan sakko ya koma nasiha. Amma wannan karon yaƙi sakkowa. Ya dage akan sai yabi umarnin hajiya iya ya ƙara aure yabar matar anan Nigeria idan ita waccan tafi ƙarfin dawowa cikin family ɗinsa ta zauna.
Zazzafan huci ya furzar yana zamewa ya kwanta a sofar da dafe kansa kawai ya lumshe idanunsa.
Lokaci mai tsaho ya ɗauka a haka batare da ya saniba. Dan har saida Hajiya Iya ta shigo ɗakin dubashi dan taga har anyi magrib bai gitoba.
“Moddibo kana lafiya kuwa?”.
Ta faɗa tana kai hannu ta cire nasa daya dafe kansa. Idanunsa ya buɗe a hankali yana kallonta, ta sake maimaita tambayar tana taɓa goshinsa.
“Lafiya kuwa kake yau har anyi salla baka fito kaje massallaci ba Moddibo?”.
Zaune ya tashi sosai, Sai kuma ya girgiza mata kansa, “Kaina ke ciwo kawai Granny, bamma san anyi sallanba ai”.
Tsura masa idanunta tai cike da nazarinsa. Dan ta riga ta gama karance halayyarsa tun ƙuruciya. Duk da ta hango damuwa tattare da shi sai batace komai a kai ba. ta nufi hanyar fita kawai tana cemasa ya tashi to yay sallar”.
Goshinsa ya murza yana cige laɓensa na ƙasa, har yanzu yana takaicin da mamakin yanda Mammah ke biyema Farah a kowanne lokaci. Duk da yasan akwai nata halin itama ya fahimci akwai zuga mai ƙarfi da akai mata a yau ɗin, a bazata wani guntun murmushi ya suɓuce masa, ya miƙe yana abinsa harya shiga toilet dan shi kaɗan yasan muguntar daya shiryama Farah da mai zuga Mammah ɗin dan ya tabbatar itace taje London ɗin kokuma sunyi waya akan tahowar tata.
Alwala yayo yazo ya gabatar da sallar magrib data wucesa. Daga haka ya fito zuwa massallaci samun jam'in isha'i. Koda aka idar tare da samarin ƙannensa suka shigo gidan abin sha'awa, su sukai sashensu shi kuma yanufo sashen Hajiya iya. Kamar yanda ya fita bai samu kowa a falonba yanzuma haka ya dawo bai samu kowaba.
Ɗakin Hajiya iya ya shiga da sallama. Tana zaune a inda tai salla Zinneerah dake fashin salla na kan kujera kwance tana latsa waya, lokaci-lokaci takan matse idanu da baki saboda mararta dake ɗan mata ciwo can ƙasa. Saurin miƙewa tai zaune saboda jin sallamarsa. Sai dai kafin tace zata tashi harya rigada ya shigo. Akanta ya fara sauke idanunsa ya janye. Batare da damuwar ganinta zaune a Sofa ɗinba yakai zaune yana cema hajiya iya “Barka da dare”.
Zaram Zinneerah ta miƙe a sofar har tana neman faɗuwa. “A hankali mana Zinneerah. Koma saman gado ki kwanta, jira nake wani ya shigo cikin su Mas'ood su nema miki magani”.
Da sauri Zinneerah tace, “Granny yama daina ai, bara naje wajensu Bahijja”
Kafin Hajiya Iya tace wani abu harta nufi hanya da sauri. Tana gab da fita yace, “Zonan”.
Tamkar ta fasa ihu taji. babu yanda ta iya dole ta dawo kanta a ƙasa. Batare da shima ya ɗago daga latsa wayar da yakeba yace, “Ki ɗauka min lap-top a ɗaki da abinda kika kai ɗazun”.
Amsa masa tai da to tana fita cika umarninsa. Harga ALLAH yana burgeta saboda baida hargowa. Banda ɗazun bata taɓa ganin yayi faɗaba ko tsawa ma wani a gidan. Shi dai kawai baida sakewane, idan kaga fuskarsa a sake yana tare da Yah Khalipha ne ko Hajiya Iya. A zatonta yanda yasan ita ba komai bace a gidan face mai cin arziƙinsu zaita karta mata wulaƙancine. Amma sai taga saɓanin hakan.
Da wannan tunanin ta ɗakko duk abinda ya sakata ta dawo ɗakin. Magana ta samu yanayi da Hajiya iya. Amma ko a cikin ɗakin kake da wahala ka jisa.
Wani shayin ta sake zuba masa zata saka suga uku yace, “two is ok”.
Maida ɗaya tay ta saka masa biyun, daga haka ta ɗauki ƙaramin hijjab ɗinta da waya ta fice ta barsu
koda taje sashensu Bahijja da suka tambayeta labarin yanda ta ƙare da kai shayi catai musu ai babu abinda ya faru, dama takai masa shayin yana wanka ajiyewa kawai tayi ta fito abinta. Mararta ke mata ciwo kaɗan-kaɗan shiyyasa taje ɗaki ta kwanta ganin sun fito.
Meenal tace, “Yo tsoro mukaji kar wani abu ya faru yazo ya haɗa damu. dan laifinmu sai yafi naki. cazaiyi mune bamu nuna mikiba yasin”.
Ƙaramar dariya kawai Zinneerah tai ta zame ta kwanta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Daga ƙarshe ranar anan ta kwana abinta.
_____________________★
*DANYA*
Ta daɗe kwance tana maida numfashin gajiya dana yunwa daya jigatata. Kafin ta miƙe dan ɗan kunun da tasha ya taimaketa. Ledar data shigo da ita ta jawo, ta buɗe tana fiddo kayan da malam ya haɗa mata da ƙara bitarsu yanda bazata mantaba. Baki ta washe na farin ciki tunawa da baba ya kusa dawowa gareta. Ta ɗaga wata ƴar kwalbar turare tana jujjuyawa.
“Yanda ka bani wahala akan ƴarka Sule, sai na sakaka mantawa da ita na har abada acikin jerin ƴaƴanka. Duk dukiyata data salwanta dan ganin ka dawo saina fansheta a jikinka ko sisi bazanyi asaraba. Ƴan uwanka kuwa dake aibantani a gari cewar ta sanadina kabar Danya zan koyar dasu hankali a sannu, duk sai kunsan kunyi da Asabe wlhy”. Ta ajiye kwalbar tana cigana da dariyarta. Maida komai tai a ledar bayan ta ɗauka wasu layu guda biyu ta fice a ɗakin.
Inda murhun girkinsu yake ta nufo. kasancewar jiyama ba girki sukai a gidanba yasa ta turbuɗa hannunta tsakkiyar tokar hankali kwance ta fara tonawa. Sai da ta ƙwakule tokar duka tasa icce ta fara tona ƙasar sannan ta saka layun nan guda biyu ta maida ƙasar da tokar ta rufesu ruf tamkar komai bai faruba. Duk da basu da isashen hatsin yin tuwon dare a gidan haka ta tattare ɗan wanda Yaya gajeje ta kawo musu daya rage ta wanke ta fita kai niƙa da kanta. Tasan ko jiran Tinene tace zatayi tayi a banza, baizama lallaima ta sake ganinta gidan a yanzuba kuma.
Da ƙyar ta samu Malam Mati yay mata niƙan akan bashi zata kawo masa kuɗin. Rai ɓace ta baro injin saboda yarfin da malam mati ɗin yay mata a gaban yara. Tai ƙwafa kawai da ayyana rashin mutuncin da zatai masa shima.
Sa'a ta iske a gidan tana shara, da alama ganin gidan datai kaca-kaca yasata takaici tana shigowa tahau aikinsa. “Sannu innarmu. Tun ɗazu nazo ai gida babu kowa ga ko ina kaca-kaca kamar ba mutane ke rayuwaba. Shiyyasa na hau aikin nan”.
Baki innar ta taɓe tana ajiye ƙwaryar da tayo niƙan dawa a ciki. “Kin san dai Tinene ba moriya takesoba, ke kuma tunda kin zaɓi dangin ubanki sama dani wazai gyara mani”.
“Kiyi haƙuri dan ALLAH Innarmu”.
Banza tai mata. saima ƙoƙarin fara haɗa wuta a murhun data saka layun nan ta farayi, itama Sa'a sai ta cigaba da sharar tsakar gidan ranta duk babu daɗin. Bayan ta gama sharar ta tattara duka kwanika ta hau wanke-wanke da ruwan data fita ta roƙo a maƙwaftansu dan gidan ko ruwa babu. Itama Inna shita samu ta ɗiba tasa ruwan tuwo. Tsaf ta gama wanke-wanken shima ta ɗauki botiki ta fita dan dama ta gyaro ɗakunan.
Sa'a na fita Inna ta miƙe ta ɗakko sauran kayan da malam ya bata ta ƙarasa yin yadda yace, sannan ta cigaba da hidimar girka tuwonta.
Haka Sa'a taita kai kawon ɗibar ruwa har sai da ta cika ko ina na gidan sannan tai zaman hutawa. Sai a lokacin Tinene ta dawo gidan niƙi-niƙi da ledar kayan ƙwalam da maƙulashe. Yanda tayi tamkar bataga Sa'a bane ya bata haushi tahau zaginta, a take suka harƙume faɗa. Inna najinsu da kallonsu taƙi ta tanka sai da ta gaji da hayaniyarsu ta kora Sa'a wai ta tashi ta koma inda ta fito ita batason fitina.
Da haushi Sa'a taja hijjabinta ta fice a gidan tana sharar hawaye......
__________________________★
*_SHIRA'S FAMILY_*
Washe gari a bazata suka tashi da baƙuncin matar Yah Adnan. Lokacin duk suna dining suna karyawa saboda masu fita makaranta. Sai dai shi bandashi, amma yana zaune a falon shi da Khalipha suna magana akan wasu takardu dake baje a centre table ɗin falon, shi yanata danna lap-top Khalipha na gefensa yana masa magana da takarda ɗaya a hannunsa.
Kasancewarsa a falon yasa babu yawan hayaniyarsu, dan Baffah ma bayanan yayi tafiya tun shekaran jiya. Iyakar sune kawai a falon suna taya Zinneerah murnar wayarta kowa na ƙoƙarin saka mata Number ɗinsa.
Hajiya iya ce ta fito daga kitchen ɗin ita da baba Rahi tana faɗin, “Oh ALLAHU ni Amina. Yanzu dan ALLAH zaman latsa wayoyi zakuyi ko karin kuyi ku tafi makaranta. Sai kuma kun makara ku ishi mutane da mitar an saku makara”.
Alamar roƙon tayi shiru suke mata wai dan kar Yayansu yaji. Basu sanma duk abinda suke tun ɗazun yana jiyosun ba. Ya sharesune kawai saboda aikin dake gabansa mai matuƙar muhimmanci ne. Suna fidda kuɗaɗen da zasuyi ginin company shinkafa ne da waken suya. Shiyyasa tun jiya yake busy. Da niyyar yin noman shinkafar kawai yazo Nigeria, sai dai Dr Mahmud da Khalipha sun canja masa tunani da shawarar mizai hana ya buɗe company kawai tunda dai yanzu Alhmdllh noma ya fara farfaɗowa a arewan. Ya yarda da Dr Mahmud sosai, dan ya jima yana bashi shawara tai masa amfani kuma, Shiyyasa ya amince babu wani ja'inja ya fara shirye-shiye. hakama Khalipha na hannun damarsane, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu kasancewarsa mutum maison ƴan uwansa. Kosu sauran yaran gidan gama fahimtarsane kawai basu yiba, shiyyasa suke nuna tsoronsa da ganin tsaurinsa a garesu, dan da shima Khalipha hakanne a tsakaninsu, sai a ɗan zaman da yake tare da shi yanzu London ya fahimci yayansu mutumne mai sauƙin kai da haƙuri, sakewace dai kawai baida ita ga mutane sai wanda yaso. A yanzu haka suna kan yin cinikin wani fili ne da za'a fara ginin company ɗin.
A fusace Hajiya Iya tace, “Anƙi ai shirun dan ubanku”.
Bakuna suka shiga turawa gaba, dan duk ɗinsu sukanji haushi idan ta zagar musu iyaye. Yanda sukayinne ya sata hararsu ta koma kitchen.
Baki Ni'ima ta buɗe baki zatai magana ƙarar takun takalma masu azabar tsini suka katseta. Su dukansu ƙofar suka zubama idanu banda shi da yayma wajen kallo guda ya maida kansa ga aikinsa duk da baisan wanene ba.
“Hii Guys!!”. Ta faɗa dai-dai tana shigowa cikin falon.
Duk idanu suka waro waje na mamakin ganinta matuƙa, dan badan ma akwai hotunan bikinta da Yayansu a gidanba, babu yanda za'ai su iya ganeta. Cikin ƙarfin hali Khalipha ya miƙe yana murmushi da faɗin, “Woow Aunty Farah Surprise Kece tafe haka?”.
Ɗan yatsine fuska tai tana wani yarfar da hannu gefe da juya idanunta manya masha ALLAH, “Oh ko bakuyi murnar ganinaba na koma?”. Tai maganar tana kafe Khalipha daya nufeta da ido. Amsar handbag ɗinta yayi da cewa, “No. no auntynmu, taya zamu ƙiyin murnar ganinki bayan duk gidanan ƙishirwar ganinki sukeyi daman”.
“Oh nice”.
Ta faɗa cike da yanga tana sauke idanunta kan mai gayya mai aiki da yay mata kallo guda tun shigowarta ya maida kansa. Inda yake ta nufa cikin takunta na izza da tsantsar gayu da yanga mai gauraye da wayewa. “I miss you my hero”. Ta faɗa tana kaiwa duƙe ta sumbaci gefen fuskarsa na dama. Tare da nufar bakinsa da ware duka hannayenta zata rungumesa............✍
*_Wa yaga ƙawar su aunty Shahudah ƴar turawa😜😂😂_*
Leave a Comment