Makauniyar Kaddara 21

 


Page 21*


...........Khalipha kam da zuciyarsa tayi matuƙar nisa a cikin tunani sam baiji mi yayan nasuma ya faɗaba. Yaɗan ɗago ya dubi Moos'ab ɗin kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana binsu da kallon mamaki su duka ganin yanda duk suka sake nutsuwa. Sashen da yayansu yake ya maida kallonsa, sai yaga hankalinsama baya kan kowannensu.

      Maida kansa kawai yayi ga abincinsa shima, sai dai gaba ɗaya hankalinsa ya tafine ga tunanin sake son ganin yarinyar ɗazu da sukace sunanta Zinneerah.

      Har aka kammala breakfast ɗin babu wanda ya ƙara ƙwaƙwaran motsi. Shine ya fara tashi a dining ɗin, suka bishi da kallo harya shige ɗakinsa. Tamkar jira suke yabar wajen suka fara ƙus-ƙus na gulma. 

        “ALLAH ya baku sa'a ya fito ya jiku”. Khalipha ya faɗa yana miƙewa shima ɗauke da kofin shayi ya nufi ɗakin Hajiya Iya. Zaune take a gaban gadon saman carpet ɗin dake a malale, ta mimmiƙe ƙafafunta dake mata zugi, dan ciwon da suke matannema ya hanata zama cin abinci a dining ɗin yau.

       Fuska ɗauke da murmushi take duban Khalipha. Ya zauna a kusa da ita yana ajiye kofin ya amshi man zafin ya fara shafa mata. “Moddibo fa?”. Hajiya iya ta tambaya tana kallon Khalipha.

    Ya buɗe baki zai bata amsa sallamarsa ta katsesa. Duk suka kalli ƙofar dai-dai yana ziro ƙafarsa ciki. Kallonsu yay ya kauda kai, sai da ya shigo ciki sosai yakai zaune a bakin gadon dai-dai ƙafafun Zinneerah dake ƙudindine a bargo sannan yace, “Ciwo ƙafan yake ne?”.

        “Ba wani da yawa bane ai. Yanzuma zakaga ta saki tunda Khalipha ya daddana min ita”.

      Kansa ya maida ga wayarsa dake haske alamar kira ake batare da yace komaiba.

     “Fita zakayine Yayanmu?”. Khalipha ya faɗa yana kallonsa.

         Kansa ya girgiza masa da faɗin, “No, Phones ɗin yaran nan ne”.

       “Woow, autoci an shigo gari kenan”. Khalipha yay maganar yana jawo ƙyaƙyƙyawar ledar gabansa. Kwalayen wayoyi masu ƙyau da tsada guda shidda ya fiddo a ciki. Ya miƙama Hajiya Iya. “Granny ga wayoyin jikokinki Yayanmu ya cika alƙawari”.

      Murmushi tayi a karan farko da miƙa hannu ta amsa ɗaya tana kallo. “A to lallai munyi rabin shiri da ja'irin nan yau. ALLAH ya saka da alkairi ya bada ladan zuminci”.

     Da amin suka amsa shi da Khalipha. Hajiya iya tace, “To ga kuma Zinneerah ta ƙaru, sai itama kasan yanda zakai da ita, dan ba'a basu wayoyiba ita batada ita”.

      Kamar bazai tankaba sai kuma ya ɗan dubi Hajiya Iyan. “Tunda bansan tana a gidanba sai tai haƙuri sai wani karon”.

      “A'a bazai yuwuba gaskiya Moddibo. A duba mata dai ko anan ita sai a saya mata”.

     Shiru yay bai sake tankawaba duk da sarai yaji mi Hajiya iyan ta faɗa. Sanin halinsa yasa Khalipha saurin faɗin, “A'a Granny a bar Yayanmu ya huta. insha ALLAH ni saina saya mata kawai”.

        Hajiya Iya tace, “To shikenan hakanma yayi ALLAH ya saka muku da alkairi. ya ƙara haɗemin kanku”.

      Khalipha ne kawai ya amsa da amin. Shiko laɓɓansa kawai yaɗan motsa kaɗan alamar ya amsa ɗin.

        Daga Haka Khalipha da Hajiya Iya suka cigaba da hira, shiko yana saurarensune kawai amma baya saka baki sai yaso, yama maida hankalinsa gaba ɗaya akan latsa waya. 

       

        Zinneerah da tun shigowar Khalipha ɗakin ta farka taɗan motsa kafarta, jin ta dunguri abu yasata saurin matsarwa baya tana rintse ido. Hakanne ya sakashi ɗan juyawa ya kalli abinda ke bayan nasa duk da tun shigowarsa yaga alamar mutumne kwance. Kamar zaiyi magana sai kuma ya miƙe yana tura wayarsa a aljihun wandon 3quarter ɗinsa. “Ni bara naje zanyi magana da Baffah, zuwa anjima inason zuwa Jigawa”.

      “Jigawa kuma? Yin me?”.

Duban Hajiya iya mai maganar yayi, yaɗan kai yatsa gefen idonsa ya sosa kaɗan da cewar, “Akwai wani gona ne da nakeson yin noman shinkafa. So mun gama magana da Mahmud shine nakeson dubawa”.

       “Tofa, bana kuma nan aka tsallaka kenan? Kai dai duk hanyar neman kuɗi kasanta Moddibo. Kana gudunmu kuma kana son zuwa kaci arziƙin ƙasarmu”.

      “Tunda ni ba ƙasata baceba ko. Idan wannan mai barcin ta tashi taje ta gyaramin ɗaki”. Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin abinsa.

       Harara Hajiya iya ta raka bayansa da shi tana yamutsa fuska. “Bauɗaɗen banza jikan ƴan Morocco”.

    A yanda tai maganarne ya tilasta Khalipha ƙyalƙyalewa da dariya shima yana miƙewar. “Granny rigima. show ɗinki da Yayanmu nada matuƙar ƙayatarwa ga mai kallo. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani uwargida kuma amaryar Abdul-Mutallab Shira”.

         “Oh to, ko kanamin baƙin cikine ba'a taɓamin kishiyaba?”.

    “Wah? Ni?  Rufamin asiri Granny karkisa Baffah yaji ya zagemin uwa. Kinga nayinan raba tsaraba na samo tukuyci. Itama  ya kamata ta tashi ta karya”. Ya nuna Zinneerah da duk tana jinsu amma ta lafe.

       “Eh nima yanzu nake tunanin nan a raina. Barama naji jikin nata kodai batajin daɗine, dan bata saba irin wannan barcinba sam”.

       “Okay to bara naje na dawo sai naji wane hali take ciki”. Daga haka ya fice a ɗakin.


       Ihun murnar waya da su Meenal suka shigo ɗakin sunayi ya tilasta Zinneerah tashi. A take suka kaure ɗakin da sabon ihu. Koda Hajiya iya data shiga bayi ta fito tana musu maganar su fice sun dameta a guje suka fita kuwa suna cigaba da ihunsu. Acan harabar gidan suka iske su Abidah suma suna nasu tsallen murnar dan da gaske yayan nasu ya shigo dasu gari da masu zafi kam.

        Duk da babu Zinneerah a cikin masu wayar babu damuwa ko ɗigon sisi tattare da ita, hasalima itace mai farke wayoyin su Bahijja daga cikin kwalinsun. Da ƙyar hajiya iya ta tilastata zama cin abinci. tana gamawa kuma taje tai gyaran ɗakin nasa daya faɗa kamar yanda Hajiya iya ta sanar mata saƙon duk da itama taji da kunnenta.

    Koda ta kammala taje tai wanka fitowa tai suka ɗora shirmensu daga inda suka tsaya ita da su Jamal. A haka Khalipha ya shigo ya samesu, daga asibiti yake yin bincike akan Zinneerah da suka haɗu wancan karon, dan gaba ɗaya zuciyarsa ta kasa yarda cewa wannan ɗin itace waccan Zinneerah ɗin. Gadai satar kammani sunayi da juna. Amma kuma wayewar kai da wasu abubuwa da yawa ya banbantasu. Babbar matsalar daya samu na rasa Number Naziru da yayi sakamakon wani tsautsayi daya samesa acan London. Yanzu kuma yaje asibitinma a iya binciken da yayi bai samu wani bakin zaren da zai iya nemansu ba. Amma an tabbatar masa ta haihu baby boy. 

           Gida ya dawo da sabon tunani akan tunkarar wannan Zinneerah ɗin yaji daga gareta ita kuma, dan a tunaninsa da ace waccan ɗince data ganesa. To waccanma ai matar aurece miyasa zaiyi tunanin itace anan?.

      Ruwa Meenal ta kawo masa ya sha. Ya kumace ta haɗa masa abinci a dining zaije yay wanka ya dawo. Binsa Zinneerah tai da kallo a cikin wani irin bahagon yanayi. Cikin dabara takai hannu ta share ƙwallar da suka ciko mata idanu. A yanzu haka babu abinda kecin ranta da damuwarta sai yanda Khalipha ya nuna tamkar baima taɓa sanintaba. Bayan ita tunda ya barta bata taɓa hutawa da tunaninsaba a ranta. har mafarkinsa tasha yi ma. Amma insha ALLAH zata daure itama ta kama kanta gareshi, idan ya ganota fine. idan ya cigaba da pretending ɗin rashin sanin nata itama saita samawa kanta lafiya ai. Da wannan tunani ta cigaba da hidimarta har lokacin Islamiyya yayi suka fita.*_DANYA_*


            Tafe take buguzun-buguzin cikin uwar ranar dake ƙwalle ga zafi da take da shi. Ga wanda baisan halin ruɗanin da take ciki a ƴan watannin nan ba sai ya ɗauka ko mahaukaciya ce. Duk ta fige ta fita hayyacinta tun barin Baba garin Danya. Duk dukiyar datake taƙama ta tara ta dabbobi da buhunan kayan masarufi sun ƙare tas wajen bin gidajen malamai dake mata aiki akan yima Baba kiranye ya dawo gida duk inda yake.

       Aikin ake kamar ba gobe amma babu alamar yanaci dan har yau ko inda Baba yake babu wanda yazo yace yaji. Gashi kullum malam nata ƙarya suke mata Zinneerah nacan tama zama karuwa a binnin ikko. Sosai wannan labarin ke mata daɗi akan Zinneerah. dan bata da burin daya wuce taga yarinyar ta tagayyara ta wulaƙanta a duniya, saboda kawai tazo matsayin ƴar kishiyarta.

     (Ƴan uwana mata dan ALLAH mu canja, mu daina saka yara a kishinmu. sannan kishinma mu dinga sassautama zukatanmu. Nasan kishi dolene domin kamar jininmune. To amma suma mazan idan suka fahimci kana musu kishi na hauka duk da sonsu ne yake jawo hakan saisu maidaka wawa mahaukaci. ka kuma fita a cikin ransu ma baki ɗaya su koma ganin baƙinka maimakon hasken da kake dashi a garesu. Babu amfani kai burin lalacewar ɗan wani ko shigarsa wani bala'in rayuwa. Dan kaima ba tsira naka zaiyiba wlhy. dan ba'a taɓa shuka dawa a girbi shinkafa. Sai ka ƙyautata zato da addu'a ga ɗan wani kaima ALLAH zaiji ƙanka ya ƙyautata rayuwar naka ƴaƴan insha ALLAH. ALLAH yasa mufi ƙarfin zukatanmu😭🙏🏻).

       Yanzunma wani ƙauye can nesa dasu sosai akai mata kwatancen wani malami shine taje. A yanzu haka dai ya mata alƙawarin dawowar Baba nanda kwanaki bakwai, idan har bai dawo ɗinba zai biyata kuɗin daya karɓa a wajenta. Hakkane ya sata tahowa gida cike da ƙwarin Gwiwa ko ranar dake dukanta da azabar tafi bataji.

        Shiru ta iske gidan babu kowa. ta zube ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu tana maida numfashi da ƙyar. Ta kusa mintuna biyar a haka kafin ta miƙe zuwa randunansu dan tasha ruwa. Wayam ta samu tabbacin dai Tinene data barma sallahon ɗebo musu ruwan bata ɗebo ɗinba kenan. A take ranta ya ɓaci taja ƙafafunta da ƙyar ta koma ta zauna dan har juwa takeji saboda yunwa. Ko karyawa bataiba ta fita, ɗan hatsin da baba ya bari a rumbu duk sun cinye ta salwantar da wani kuma wajen bin malamanta na tsiya. Hakan yasa abincima sau uku a gidan wataran gagararsu yakeyi. sai idan Yaya Gajeje taji tausayinsu ta ɗakko ta kawo musu. Koda yake mafi yawancin lokacima itace ke zama da yunwar, dan Tinene sai dai ta ganta da kayan ciye-ciye ta shigo. bata isa tambayarta kuma ina ta samosuba saita hayayyaƙo mata da rashin kunya. Wani lokacinma bata tambayar tata amsa take itama taci saboda wahala. Sa'a kuwa yanzu takan jera kwana huɗu biyar bata kwana a gidanba. Tuni ta koma gidan Baba Rabilu abinta, dan ɗansa ya maidata makaranta tana zuwa. da Inna ta nuna bata yarda bane yasa Sa'a tattara inata-inata ta kona can gidan. Sai randa ta bushi iska take zuwa ta kwana anan tunda yanzu babu talla Malamai sun cinye jarin Inna Asaben.

       Miƙewa Inna tai tana tsinar Tinene a cikin ranta, dan yunwa da wahalar tafiya tasa koma magana mai ƙarfi bata iyayi. Ɗakinta ta shige ta faɗa saman gado da fatan ALLAH ya kawo wani a cikinsu Sa'a ɗin ya taimaketa da ko kunu ne taɗan kurɓama cikinta ko taji dama-damar tashi ta bizne aykin malam.

       ALLAH kuwa ya taimaketa babu jimawa ta farajin motsi a tsakar gidan da ƙarar taunar chewing gum. ko ba'a faɗaba tasan dai Tinene ce. Dan itace mai ɗabi'ar cin cingam ɗin a koda yaushe. Idan tai mata magana tace mata ƙoshi ya sakata ci danta rage nauyin cikinta. Dole Innar keyin shiru dan Tinene kam ta fara fin ƙarfinta. Gashi kuma wani lokacin tana ɗan samun mai daɗi a wajenta taci.

     Bankaɗa labilen da akaine ya sakata ɗago idonta ta kalli ƙofar. Tinene dake tsaye a bakin ƙofa tana cakal-cakal da cingam a baki cikin rashin ladabi tace, “Oh oh, wai se yanzu kike dawowa gida Innarmu? Ke dai baki gajiya da mikama maluma kuɗi suna cinyewa mu baki anhwana mana da ko taro ba a ciki. Naga dai Baban da ƙahwarsa yabar gidan ba saceshi akaiba halan”.

     Kasa cemata uffan Inna tai, sai kanta data girgiza kawai. Hakan datai ya bana Tinene haushi, harta saki labulen da niyyar barin wajen Inna ta ƙwala mata kira cikin ƙarfin hali. “Tinene wai nikan yaushene zaki natsune? Ni yanzu duk bama wanga ba. Dan ALLAH idan da goma hannunki ko murtala kije nan gidan dije ki sayo mani kunu koba suga nasha”.

    Baki Tinene ta zunɓura gaba. kanar zatai magana sai kuma taja tsaki fuuu ta fice tana ƙunƙuni. “K kuɗinki na wajen bokaye da malamai ni kuma kin sakama nawa ido mu ramtsesu tare. Bayan duk kece kika jehwamu a wagga rayuwa ta yunwa da talauci wajen neman baƙin asirinki mtsoww”.

      Da wanan mitar taje ta sayo kunun na goma ta kawo mata dukda ba wani na kirki bane. Da rawar jiki kuwa Inna ta amsa tahau sha duk da zafin da yake da shi. Ta saki gyatsa tana ajiye kofin duk da bata ƙoshi bane yanda take buƙata. Daga haka ta zame ta koma kwance tana zufa. Tinene ta taɓe baki da nufar hanyar ficewa gidan tanama Innar tasu baƙar magana.


(Hhhh yanzu aka fara wasan Hajja Asabe😂😂😜).


________________________★★


           Washe gari lahadi ma duk suna a gidan, sai dai banga Khalipha da Yah Adnan da suka tafi jigawa. Dan jiya bai samu damar zuwanba saboda wani uziri. Bayan sallar la'asar duk suna zaune a falo suna ɗan hira iyasu ƴammatan sai ga Safiyya da ita kaɗaice bata gidan. Momie ta aiketa can wajen yayarta kai saƙo.

        A yanda ta shigo falon kamar wadda aka koro ya sakasu duk suka zuba mata ido. “Ke lafiyarki kuwa?”. Hajiya iya data kasa haƙuri ta faɗa tana duban Safiyyan. 

          “Humm Granny inafa lafiya, wlhy wani abun al'ajabi da ruɗani nai gamo dashi a yanzun nan hanyata ta dawowa daga gidan Umma”.

       Duka falon maida hankalinsu sukai a kanta, kowa nason jin dami tai gamon?. Wayarta ta lalubo a jakka tai ƴan danne-danne sannan ta miƙama Hajiya iya. “Granny dan ALLAH kikalli yaron nan dawa yay miki kama?”.

      Cikin rashin damuwa Hajiya Iya ta amshi wayar. Yanda tai kasare tana kallon wayar ya saka su Meenal duk suka zuba mata ido suma. Itama da alamun makamancin irin ruɗanin da Safiyyar ta shigo da shi tace, “Keko Safiyya a ina kikaga wannan yaron haka?”.

        “Wlhy Granny a Napep. Mun taho da driver motar ta mutu a hanya. Shinefa nace masa bara na tare napep na ƙaraso gida. Mun daɗe tsaye yanason taremin ba'a samuba sai da ƙyar ya tsaida wanda ke ɗauke da maman yaron nan. 

     Hajiya iya daketa faman jinjina kanta tace, “Amma wannan kamanni da mamaki a cikinsa. Koda yake hakan kan faru koda baka haɗa komai da mutumba. Amma ita matar a ina take?”.

       “Wlhy ban tambayetaba Granny, amma da alama wani waje zatajema. Bama tasan na ɗauki hoton yaronba dan cikin dabara nayi”.

      Wani irin nannauyan numfashi hajiya iya ta sauƙe. Sai kuma ta miƙama Abidah wayar ganin duk sun zaƙu su gani. A haka samarin gidan dake shigowa a tare sukazo suka samesu. Ganin yanda aketa ƴar bayayya da waya ya sakasu tambayar ko lafiya?. Safiyya ce tai musu bayani. Amsar wayar suma sukai duk suka gani. Duk wanda ya kalli hoton sai ga mamaki ya bayyana a fuskarsa da ruɗani.

        Duk wannan al'amari dake faruwa Zinneerah nacan ɗaki tana shirya kayanta data kwaso a ɗakin Yah Adnan cikin wadrobe ɗin Hajiya iya. Hakan yasa batasan hidimar da akeyiba. Dan so take ta gama shiryasu a daren yau tunda gobe idan ALLAH ya kaimu monday akwai makaranta.

        Kasancewar dama bata fara aikin da wuriba sai gashi har Hajiya iya ta shigo domin sallar magrib bata kammalaba. Sai kusan sha ɗaya ta gama lokacin hajiya iya ta jima dayin barci mai cike da mafarkin yaron da Safiyya ta kawo musu a hoto, takan dai tashi tai salla idan lokaci yayi. Su meenal kuma sunɗan lekota, sanin hajiya iya idan ta kwanta batason surutu yasa suka fice suka barta ita kaɗai ta cigaba da aikinta. 

          A falo kuwa hirarsu suka cigaba dayi bayan tasowar hajiya iya. Dan duk sun barma kansu cewar kamannine kawai da akan samu a rayuwa tsakanin wani da wani koda babu alaƙar jini saboda hikimar UBANGIJI. Basu wani jimaba suka fice duk da Moos'ab yaso ganin Zinneerah kafin ya wuce ɗin. Rashin samuwar hakan ya sakashi haƙura kawai.


        Tun daga wannan ranar babu wanda ya sake tada zance akan hoton yaro, sai dai abin na nan maƙale a zuciyar Hajiya Iya ta kasa mantawa. Tanason yin maganar kuma wata zuciya na kwaɓarta akan kamannine kawai. Idan kuma tace zata kawoma zuciyarta wani tunani daban ya zata alaƙanta al'amarin ma to. Hakan yasata tsuke bakinta ta barma ranta komai kawai.


     kwanaki sun cigaba da shurawa a hankali sai ga Khalipha da Adnan na cika kwanaki goma da zuwa. Ko kaɗan Zinneerah ta kasa sabawa da kasancewar sa a gidan duk da a kwanakin nan bai cika zamaba kullum suna hanyar Jigawa gonar da zaiyi noman shinkafa. Sukan fitama kafin su su fito, wani lokacin kuma sai sunyi barci suke dawowa. Wannan dalilin yasa takanyi kwanaki uku biyu ma bata sakashi a idontaba har Khalipha ɗin da take marmarin gani a ko yaushe.

      A kwanakin nan daya ɗauka gaba ɗaya hidimar gyaran ɗakinsa ta dawo kan Zinneerah. Kullum ita yake cewa taje ta gyara masa ɗaki. Bata damuba dan dama ta rigada ta saba.

Idan ta ganshi tsoro na matuƙar kamata, dan kullum abubuwan daya dangancesa suna sake danganta kansu da abinda sam ta kasa gaskatawa.  

       A randa suka cika kwanaki goma sha uku a gidan basuje gona ba, amma duk da haka babu wanda ya sakashi a ido sai yamma. Yana ɗakinsa yana harkokinsa na business a lap-top. 


        Zinneerah, Meenal, Bahijja sai Jamal na zaune a falon hajiya iya Yah Khalipha ya shigo. duk sannu sukai masa ya amsa yana zama kujerar dake facing ɗin Zinneerah da Bahijja. Cikin kafe Zinneerah ɗin da idanu ya miƙa mata ledar hannunsa yana murmushi.

        “Ƙanwata yau dai ga wayarki na cika alƙawari”. Kafinma ta kai ga yunƙurawa amsar wayar Jamal yay azamar zuwa ya amsa yana washe baki. A take suka rufi akan wayar suna tayata murna duk da ba irin tasu Meenal ɗin bace ba, amma itama ta haɗu. Tasowa Zinneerah tai tsam inda yake takai tsigunne kanta a ƙasa tana faɗin, “Nagode sosai Yah Khalipha, ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”.

      Kansa ya jinjina mata yana sake faɗaɗa murmushinsa. Sai kuma ya miƙe ya fice zuciyarsa na bashi ƙwarin gwiwa akan yau ya tunkareta da zancen nan. Dan yauɗin kawai ke garesa Yah Adnan yace nanda kwanaki huɗu idan ALLAH ya kaimu maybe zasu wuce Abuja. Daga can kuma bazasu dawo Kano ba London zasu koma zaiyi wasu uzirinsa kafin ya dawo akan zancen auren su Ni'ima da ayanzu haka an tsaida rana da kuma maganar Company da yake tunanin buɗew na shinkafa.

     Binsa da Kallo Zinneerah tayi ƙwalla na cika mata idanu, sai kuma ta miƙe tsaye tana murmushi saboda wani abu data tuna. Idanuntane suka sauka akan Yah Adnan dake tsaye bakin ƙofarsa da waya a kunne yayi wani kicin-kicin da fuska............✍


No comments

Powered by Blogger.