Makauniyar Kaddara 20

 


Page 20*


..........Ƙarfe biyar da rabi motar dake ɗakko su Zinneerah makaranta ta shigo harabar gidan. Kamar yanda ta fita gidan da damuwar baƙon dasu Jamal ke kira Yayansu haka ta dawo da ita a rai. Babban damuwarta ya ganta daga ita sai guntun towel a jiki. Gashi yanda taga fuskarsa da yanda su Meenal ke labarinsa tasan ba kirki zaiyiba sam, sai kuma wani abu mai kama da almara da take hangowa, wanda ƙwaƙwalwarta sam ta kasa ɗauka.

        Kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka ta nufi sashen Hajiya iya tana mai addu'a a ranta ALLAH yasa baya nan. Koda tazo ƙofar falon sai da ta tsaya tai addu'a sannan ta shigo bakinta da sallama. Da sauri taja birki a taku huɗu, dan tun sakko ƙafarta ciki hancinta ya shaƙo mata mayataccen ƙamshin turare. Bata kawo a ranta falon yakeba idanma shine, sai da ta ƙarasa shigowa sosai idanunta sukai gamo maiban ruɗani, dan a yanzune ta sake samun damar yimasa kallo mai ƙyau.

      Zaune yake bisa kujera 1seater dake facing kofar, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya. Hajiya Iya na zaune kujerar gefensa tana dama fura. Sai wanda bataga fuskarba saboda juya mata baya da yayi. Har cikin ranta taji daɗin samunsa bashi kaɗaiba duk da bataso ganin nasaba ma gaba ɗaya.

       Sallamarta Hajiya iya ta amsa fuska ɗauke da murmushi take faɗin, “Ƴan makaranta an dawo?”.

       Cike da ƙarfin hali Zinneerah ta sakima Hajiya Iya murmushi da faɗin, “Eh Granny barka da yamma”.

       “Barka dai Inno na, da alama yau kam an dawo da yunwa naga kinyi zuru-zuru?”.

       Murmushi tayi batare da tace komaiba. Ta ɗan saci kallon inda yake zaune idonsa a wayarsa dake hannunsa yana latsawa tamkar baisan da shigowartaba. Sai dai abinda bata saniba cikin abinda baifi sakkani ashirinba ya gama ƙarema shigar Uniform ɗin jikinta kallo. Skirt ne iyakar ƙwauri pink color. Sai farar shirt dataji guga da baby hijjab fari daya tsaya mata iya ƙirjinta shima dai a gogen yake. Sai farar safa data rufe ƙwaurin nata da farin takalmi. Bayanta goye da school bag ɗinta data saki hannunta guda. Babu mai cewa Zinneerahn danya ce data taɓa rainon ciki harta haifesa yake gudu ko ina da kafarsa a halin yanzun. Baka iya hango komai tattare da ita sai zallar ƙuruciya da jin daɗin rayuwa na canjin data samu cikin ƙanƙanin lokaci.

         “Yayanmu barka da yamma”.

Ta faɗa ciki-ciki tsabar fargaba da tsoron dake mamaye da ita. Harta fidda rai zai amsa sai taga ya ɗaga mata hannu alamar amsawar kenan.

     Gaba tai zata wuce, batare da ta gaida ɗayan wanda bata ganin fuskar tasa ba. A tunaninta ko shi baisan da shigowarta ba. Sai da taɗan gitta su taji ashe waya yake amsawa. Numfashi ta sauke da nufar ɗakin Hajiya Iya da saurinta, dan bata fatan abinda zai sake tsaidata a wajen. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali dai-dai tana saɓule school bag ɗinta da zubewa akan sofar ɗakin. Zamewa tai ta kwanta ko jininta daya ɗauke na wucin gadi zai dawo aiki jikinta yanda ya kamata.

        “Kina lafiya kuwa Zinneerah?”.

Hajiya iya data shigo ta faɗa tana kai hannunta saman goshin Zinneerah dake kwance rigingine. Buɗe idanu tai a hankali tana kallon Hajiya Iyan, ta yunƙura zata tashi Hajiya iya tace, “Kinga yi kwanciyarki abunki. Amma kina lafiya dai ko?”.

       “Lafiyata ƙalau Granny, na gajine sosai yau shiyyasa”.

     “Tofa, halan tsalle-tsallen wofin nan naku kukayi a makarantar ko?”. 

    Ƙaramar dariya Zinneerah tayi tana tashi zaune saboda ganin a yanda Hajiya Iya tai magana fuska a yatsine. “Granny yanzu yaya zanyi kayana nacan ɗakin fa. Ni kuma wlhy wannan mutumun tsoro fuskarsama take bani. ALLAH yasa dai baiyi faɗan ganina a ɗakinsaba”.

       “Idan yayi tsoronsa zanjine Zinneerah? Indai Moddibo ne ma bar wahalar da kanki wajen tsoron wani faɗansa na wofi. Shi haka yake baida fara'a dason hayaniya. Harkar kowa kuma ba shiga yakeba sai idan yaso hakan dan kansa. Tashi kije ki ɗakko kayan da zaki saka, zuwa weekend idan ALLAH ya kaimu sai ki tattaro kayan da zakiyi amfani dasu harya tafi kafin ki koma”.

     Cikin waro idanu Zinneerah tace, “Granny kina nufin sake koma masa ɗaki zanyi da zama?”.

       “Oh to kajimin ja'ira bakison ɗakinne?”.

      “Nidai zan zauna dake anan. Ɗazu ɗinnan da ace babu kowa a gidannan da yazo ya sameni a ɗakinsa ai kakkaryani zaiyi yasin”.

     Yanda take maganar da iya gaskiyarta yasa Hajiya Iya yin dariya. “Idan bazaki takuraba anan ɗin nima zanfi jin daɗin ganinki kusa dani. Dama danki sake yasa nace kije ɗakinsa ki zauna a binki ai. Yanzu tashi ki watsa ruwa sai kizo kici abinci duk kinmin zuru-zuru a idanuna”.

       Miƙewa Zinneerah tai tana ƙoƙarin cire baby hijjab ɗinta. Hajiya iya kuma ta fice a ɗakin.


       “Granny wai keda wa naji kuna magana ɗazun ina waya?”.

    Khalipha ya faɗa dai-dai Hajiya iya data fito tana kaiwa zaune. Sai da ta zauna ta bashi amsa da, “Ƙanwarku ce mai kama da Inno. Yanzu zata fito sai ku gaisa”. Cikin rashin damuwa da sonjin daga ina yace, “Okay. Bara naje nan waje ga Sadam yana jirana zamu ɗan fita. Yayanmu baka buƙatar komai?”.

         Har yanzu idanunsa nakan wayarsa tun yanda Zinneerah ta barshi. Ya ɗan ɗago kansa ya duba Khalipha ɗin ya maida. “No jeka abunka. Nima zuwa 6:30 Mahmud zai shigo muɗanyi magana”.

     “Okay bye, insha ALLAH zan dawo nima kafin ya tafi. Dan nasan yau tare zakuci abincin dare. Granny bye”.

       “A dawo lafiya”. Ta faɗa dai-dai yana ɗaga mata hannu zai fice. 


     Koda Zinneerah tai wankan ƙin yarda ta fito ɗaukar kayan tayi, duk da tanajin yunwa ta gwammaci ɗaukar sauran biscuit ɗinta dake cikin jakka taci, a ranta addu'a take ALLAH ya kawo wani acikin su Jamal ya taimaketa ya ɗakko mata kayan. Sai dai addu'arta bataciba. Dan muryar Hajiya Iya ta tsinkayo tana ƙwala mata kira. Hijjab ta ɗauka ta fito badan tasoba. Hajiya iya dake kallonta tunda ta fito tace, “Wai nikam bazakizo kici abinciba kika maƙale a ɗaki kamar wata sabuwar amarya?”.

        “A'a Granny dama yanzu zan fito”. Ta faɗa tana satar kallonsa ta gefen ido. Yanzu kam waya yake a kishingiɗe saɓanin ɗazun. Saurin nufar kitchen tayi ɗebo abincin a bazata ta tsinkayi nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa cikin kunnenta a karon farko. “Ki kwashe tarkacen da kika barmin a toilet”.  

      Duk da ba ita yake kalloba ta tabbatar da ita yake. Tuna abinda ta bari ɗinne ya saka kunya mai tsanani lulluɓeta. da sauri tabar wajen.

     Gaba ɗaya turarensa mai ƙarfi ya danne nata daya fara zama a ɗakin cikin wuni ɗaya. Toilet ta wuce sum-sum tamkar yana a cikin ɗaki. Ganin alamar yayi amfani da toilet ya ƙara saka zuciyarya shiga cikin wani irin matsananciyar kunya. Ta kwaso kayan tana rintse ido kamar ta fasa ihu. shikenan ya gama gane mata sirrinta wayyo ita Zinne. Koda ta fito sum-sum ta wuce bata yarda ko sashen da suke ta kallaba.

        

      Fitar da yay da daddaren saboda zuwan abokinsa Dr Mahmud ta bama yaran gidan damar shan sharafin hirarsu yanda suka saba. Sai dai anayi ana leƙen waje wai karya shigo. Sai ma ALLAH ya taimakesu har suka tashi bai shigo ɗinba.

     Washe gari da safe ma har suka gama breakfast kowa ya fice yana ɗaki bai fitoba. Kasancewar juma'a ce da wuri su Zinneerah suka dawo gidan. 

              A bedroom ta iske hajiya iya zaune tana karatun AL-QUR'ANI. Bata zaunaba ta ajiye school bag ɗinta da cire hijjab ɗinta ta fice zuwa kitchen dan yunwa takeji, yau bata wani zauna tayi karin kirkiba suka fita makaranta. Gaba ɗaya ta shafa'a da kasancewar sa a gidan. dan haka ta fito kanta tsaye ko ɗan kwali babu akan nata. Sai gashinta data wanke dan zuwa kitso dake ɗaure a tsakkiya. Tanada gashi duk da bamai wani uban tsaho bane, dan yakanzo mata dai har kafaɗa musamman idan ta wankosa a saloon.

        A yanda take tafiyar yasa sam bataga mutum dake tahowa a gabantaba. Gab sukai karo da juna. Ta ɗago a firgice tana murza goshinta zatai magana, amma sai maganar tata ta maƙale a maƙoshi ta tsaya kawai tana kallomsa. Shima ɗin dai kallo yake mata irin na sani, sai dai ya kasa tunano a inda yasan fuskar.

        Baki ta buɗe da nufin ambaton sunansa ya katseta yana murmushi. “Sorry Beauty. Ko kece Sister ɗin tamune?”.

        Saurin haɗiye maganar tata tai itama mamaki na neman kasheta a tsaye. Kenan bai ganetaba komi? Kokuwa basarwace irinta masu hannu da manda. Aiko inhar hakane itama ta iya ai, musamman a yanzu da take ƙara samun wayewar rayuwa da zamantakewa wajen malamta su Jamal.

       Kanta ta kaɗa masa tana ƙaƙaro murmushi. Tace, “Eh nice Yayanmu, kunzo kafiya?”.

        “Alhmdllh, amma kinma sanni kenan?”.

      “Eh mana. Na sanka a bakinsu Bahijja”.

      “Kai-kai a bakin magulmatan gidannan kenan. to ALLAH yasa dai basu koyama ƙanwar tawa gulma ba?”.

         Ƙayataccen murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana fili. Hakan yayi dai-dai da isowarsa wajen. Ta buɗe baki da nufin bama Khalipha amsa idanunta suka faɗa cikin nashi. Wani irin yarrr tsigar jikinta ta tashi, tai azamar maida kanta ta duƙar ƙirjinta na bugawa saboda abinda zuciyarta ta hasko mata a yanzunma kamar jiya data fara ganinsa, koma wanda yafi na jiyan, idanunsu iri daya hatta da kwayoyin ciki.

      Juyawa Khalipha yayi domin son ganin abinda ya hanata maganar, yay murmushi a dai-dai sanda yayan nasu ke ƙoƙarin gittasu tamkar baima gansuba. Da sauri Khalipha yace, “Barka Yayanmu”.

     Hannu ya ɗaga masa kawai yawuce abinsa. Hakan yasa Khalipha ƙara matsawa gaban Zinneerah da kanta ke a ƙasa. Cikin raɗa-raɗan magana yace, Beauty bara muje massallaci, idan na dawo zakizo ki tayani hira”. Daga haka yabi bayan Yayan nasu ɗakin Hajiya Iya daya shiga.

        Nannauyan numfashi Zinneerah ta sauke tare da lumshe idanu ta dafe kirjinta. Zuciyarta na gargaɗinta akan abinda ƙwaƙwalwata ke hasko mata maiban tsoro da ruɗani. jiki a saɓule ta wuce kitchen dan neman abinda zata sakama cikinta ko taji dama.


      Sosai ran Zinneerah yake a jagule da tunani mai tarin ruɗani kala-kala. Ba komai ya janyo hakanba sai ganin da taima Khalipha. Wanda zuciyarta taƙi aminece mata cewar bai ganetaba. Amma har a ranta tana shiga ruɗani da al'ajabin yanda ya nuna ɗin. Itako tayi imani da ALLAH ko shekaru fiye da haka sukai bata gansaba duk randa suka haɗu saita ganesa. Kenan itace keta shirmenta shi baimasan tanayiba, koda yake alkairinsa garetane yasa ta kasa mantawa dashi bawai wani abuba. A take ƙwalla suka cika mata idanu, sai dai tai ƙoƙarin hanasu su zubo dan ba wannan matsalar kaɗai bace matsalarta, hadda wadda take tsoron bayyanar tabbatuwarta saboda ɗimuwa.

     Duk yunwar da take iƙirarin ji sai gashi ba wani abincin kirki taciba  bakuma ta yarda ta fitoba har saida ta tabbatar a ranta sunbar gidan.

    Koda ta koma ɗakin Hajiya iya wanka ta farayi itama tai salla sannan tai zaman karanta suratul kahfi. Bayan ta kammala suka gaisa da Hajiya iya take sanar mata “Af Inno na kinga ina neman shafa'a. Idan kin idar da addu'arnan jeki ki gyara Moddibo ɗakinsa”.

      Cikin dauriya da danne damuwoyinta tace, “To Granny”. Daga haka ta miƙe zuwa ɗakin nasa datai zaman watanni kusan uku a ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara komai ta baza ƙamshi. dan ita bama taga wani datti da ɗakin yayiba. Rufo ɗakin tai ta fito. Hakan yayi dai-dai da fara shigowar samarin gidan falon alamar yanzu suke dawowa daga massallaci. A ƙa'ida kuma duk irin wannan ranar anan suke lunch saɓanin breakfast kawai da sukeyi anan kowacce safiya.

       Ƙasa tai da kanta cike da jin kunyar kallon da Moos'ab ke mata tunda suka haɗa ido. Batare da tayi tunanin hardasu Khalipha ɗin suke tareba itama ta zauna a falon saboda harda Jamal daya ja hannunta suka zauna a centre table ɗin falon yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Surprise sweet sisi”..    

      Murmushi tayi tana ƙoƙarin buɗe ledar. Ganin abinda ke a ciki ya sata waro manyan idanu waje ta ɗago da niyyar yin magana taja birki wajen ganin ta haɗiye abinda ke a bakin nata saboda idanunta da suka sauka akan wanda batai fatan ganiba....

      Ledar hannun nata Khalipha ya zare yana faɗin, “Ƙanwata mi muka samu haka?”.

      Kasa amsa masa tai saboda wani kallo data kasa fassara inda ya dosa da Yah Adnan ya watso mata. Sai dai zata iya fassarashi da kamanni dana gargaɗi ko takaici.

    Tsam ta miƙe batare data iya amsa Khalipha daya fiddo agwaluma ɗaya dake a ledarba yana faɗin, “Lallai kayan daɗin nan dani za'a shashi ƙanwata”.

      Tana ƙoƙarin gittashi tace, “Na bakama Yah Khalipha kasha ma duka kawai”.

        Saurin bin bayanta yay dan shima yaga kallon da Yayan nasu yay mata, wanda ya tabbatar shine ya hanata zama wajen. “No. Kinga tsaya Beauty guda ɗaya ma ya isheni karɓa kayanki”. Badan tasoba dole ta tsaya ta amsa. Shi kuma yace, “Thanks” cike da wani salo daya sanya Moos'ab dake binsu da kallo cike da kishi yay azamar kauda kansa garesu.


      Koda ta samu ta shige bataso sake fitowaba Hajiya Iya ta korota domin zaman yin Lunch. Badan tasoba dole ta biyota, dan ko tace taci ba barinta zataiba sai dai ma tai mata faɗa. Duk sun hallara a dining har Baffa dasu aunty Ni'ima. Baffah ta fara gaidawa da juma'a, sannan ta zauna a kujerar data rage kusa da Khalipha da Meenal. Hajiya Iya kuma ta zauna a mazauninta da kowa ya sani.

          Sai da Ni'ima ta fara miƙewa ta zubama Hajiya iya abincin sannan Baffah. Sanin halin Yayansu itama Safiyya ta miƙe ta zuba masa dukkan abinda tasan yana buƙata a wajen. Daga haka kowa ya fara ƙoƙarin zubama kansa abinda yafi buƙata.

       Zinneerah dai duk jinta take a matuƙar takure. Kaɗan ta zuba dambun cus-cus a filet ɗin gabanta. Tana ƙoƙarin ɗaukar Mango juice ta zuba Khalipha ya rigata azamar ɗauka jug ɗin ya zuba mata a ƙaramin cup yana murmushi. “Thanks you Yaya” ta faɗa a hankali tana ƙoƙarin kai hannu ta ɗauka aka rigata..  

      Da azama ta ɗago fararen idanunta tana tsuke baki dan duk zatonta Jamal ne, kasancewar sun saba irin wannan wasan. “Malami kafa raina min....” ta haɗiye sauran maganar tata da sauri har tana sarƙewa saboda a hannun data hango juice ɗin.

       Kowa dake wajen sai da ya ɗago ya dubeta tare da kallon abinda taima kallo guda ɗin ta duƙar da kanta. Jamal ya ɗan harareta batare da yace komaiba. 

       Duk kansu suka maida ƙasa kowa na mamaki a ransa ganin Yayansune da aikin, harma ya kai juice ɗin bakinsa tamkar bashi ya aikataba. Baffah da Hajiya iya kam da basu fahimci ainahin abinda ya faruba har haɗa baki suke wajen faɗin, “Kubata ruwa mana kuna ganin ta sarƙe”.

     Saurin miƙa mata ruwan Meenal tayi a baki. Babu musu Zinneerah ta buɗe baki ta hau sha. Hajiya iya tace, “Maganin mai cin abinci yana magana ai kenan”.

       Shiru Zinneerah tayi, dan bata da bakin yin bayanin gaskiyar zance. Khalipha dai mamakin abinda Yayan nasu yayi yake a zuciyarsa. Dan shi da kansa yasan baya shan mango juice. Hasalima daga shi sai Baffah suke matuƙar sonsa. Zinneerah ɗinma dan yaga ta nuna tanaso ne ya zuba mata. kauda tunanin yayi a ransa ganin yanda Yayan nasu ya sake cin mur tamkar bai aikata komaiba, sannan kuma yafi kowa sannin halinsa, shiyyasama bai kawo komai a ransa ba.

         Kowa nama Zinneerah sannu shi banda shi, abincinsa ma yaketa faman ci hankali kwance tamkar baya jinsu.

       Tsakurar abincin kawai Zinneerah keyi a takure matuƙa. Sosai zamnsa a wajen yay masifar cika mata ido. Hakama idanun Yah Moos'ab suma sun takura mata. Ga kuma wani irin yanayi mai kama da shauƙi da takeji game da ganin Khalipha, duk da yanda ya nuna bai ganetaba yana damunta cikin rai. Ganin batacin abincin sai juya cokali yasa Baffah yimata magana.

         “Baffah na ƙoshine”.

“Ƙoshi kuma ɗiyata? Haba yaushema kika fara cin abincin, bayanma kaɗan dama naga kin zuba. Kodai baki da lafiyane?”.

     Kai ta girgiza masa da sauri. “A'a Baffah lafiyata ƙalau, barci nakeji”.

        “Barci kuma? A to tashi kije ki kwanta kafin la'asar tayi dan yau lokacin gudu yake ga mai yawan rai...”

     Zaram ta miƙe kafinma Baffah ya rufe baki. Ta nufi ɗakin Hajiya iya tanaji kamar ta runtse ido ta ganta a kwance ko zataji sassauci daga abinda takeji na ruɗani akan mutanen nan uku da sukazo mata da mabanbanta tunani.


       Washe gari weekend suka tashi kowa yana a gida. Sai sune zasu fita islamiyya zuwa yamma. Tunda Zinneerah ta gama taya su Baba Rahi aikin safe ta gudu ɗaki ta sake kwanciya. Har Hajiya iya na mata ƙorafin anya wannan yawan kwanciyar tata ba shawara bace ke damunta?.

      Luf tayi tamkar tai barcin, dan batason Hajiya iya tace yau saita fita dining yin breakfast. Batare da tunanin komaiba hajiya iya tace, “Oh harma kinyi barcin kenan? Dolene nazo na nema miki maganin shawara kuwa”. Daga haka ta cigaba da duba littafin hannunta, Zinneerah kuwa ta ƙara lafewa a bargo.

      Tun tana barcin ƙarya harma na gaskiyar yay gaba da ita. Kasancewar weekend basu zauna breakfast ba sai wajen tara. Iya su yaranne kawai babu Baffah. 

      Shine ƙarshen fitowa sanye cikin wando 3quarter fari da yellow ɗin t-shirt. Gaishesa ƴammatan suka farayi yana ɗaga musu hannu saboda waya dake manne a kunnensa yana magana. Ni'ima ta fara haɗa masa abinci gabansa. Kamar an tsikari Moos'ab ya ɗan wawwaiga yana faɗin. “Wai ina Zinneerah ne?”.

       Saurin ɗagowa Khalipha dake zuba kunu a kofi yay yana kallon Moos'ud saboda jin sunan daya ambata. “Dama sunanta kenan?”. Yay tambayar ga Moos'ab ɗin kansa tsaye. Wani ɗan murmushi Moos'ab yay yana sosa gefen wuyansa alamar dai akwai wata a ƙasa. “Sunanta kenan Yah Khalipha, ya haɗu ko?”. Ya ƙare maganar da ɗage gira.

     Dariya su Haneef sukayi suna masa daƙƙuwa.

         Ɗan jimm Khalipha yayi yana tunani a ransa. sai dai kafin yace wani abu Moos'ab ɗin ya sake faɗin, “Bahijja dubata a ɗakin Granny tazo ta karya”.

      “To Yaya”. Bahijja ta faɗa tana miƙewa. Sai dai babu shiri ta koma ta sake zama saboda wani malalacin kallo da Yayansu ya watso mata a kaikaice, ya kuma ɗauke kansa tamkar bashi yayiba. 

       “A'a yaya kika koma kika zauna kuma? Nace kije ki duba Zinneerah ne fa”. Fuska ta narke tamkar zata fasa kuka tana duban sashen Yayan nasu da yay tamkar baisan abinda akeba a wajen. Dan dama dai duk a hankali suke magana gudun yin laifi a garesa.

     Kallonsa shima Moos'ub ɗin yayi, mamaki ya kamashi ganin hankalinsa bama a garesu yake ba. Cikin faɗa yace, “Bazakije bane komi?”.

       Da sauri ta girgizama Moos'ab ɗin kanta, da idanu ta nuna masa Yayan nasu tana ɗan noƙe kafaɗa. Baki ya sake buɗewa zaiyi magana suka tsinkayi fitar siririn tsakinsa. yaɗan watsama sashin da Moos'ab ɗin yake  kallo. A yanayin maganarsa na rashin son sakewa yace, “Kun isheni da surutu fa”.

        Tsit wajen yay suna satar kallonsa ta ƙasan idanu da mamakin ganin yanda yay maganar tamkar a hasale..........✍


No comments

Powered by Blogger.