Makauniyar Kaddara 18

 


Page 18*


...........Washe gari daga sallar asuba Baffah ya zarto sashen Hajiya iya. Bayan ya zauna sun gaisa ya zayyane mata shawarar da ya yanke a wannan karon. Cikin jimami tace, “Amma Kabiru baka gani wannan shawarar tana kamanceceniya data baya kuwa?”.

        “Eh to Inna tana kama da ita. Sai dai akwai ɗan banbanci da waccan ɗin. Ki dai tayani addu'a, kuma ki ƙara nazari kema akan hakan mugani”. 

      “To shilenan. Ai ba'aƙi ta mutumba inji masu iya magana. ALLAH ya shige mana gaba”.

      “Amin ya rabbi Inna nagode. Ina mutuniyar takine banji motsintaba?”.

      “Oh kana maganar Zinneerah ne? Tana ɗakin Moddibo tunda ba zuwa yakeba ita ai saita zauna. Dan nace ja'iran nan suzo su rinƙa tayata kwana harta saba wai tsoro sukeji sudai. taya zasu iya kwana ɗakin Yayansu bayan kowa yasan dokarsa ba'a shigar masa ɗaki sai da dalili mai ƙarfi”.

       Dariya Baffah yayi yana faɗin, “Inna sunsan halinsa ba wasa yake dasuba ai. Itama Zinneerah ɗin dai gara a gyara mata wani karki haɗa rikici Inna”.

       “Oh to nima tsoron nasa nakeji kenanma ashe?. To yaci ƙaniyarsa shida dokar tasa babu inda zataje. Idan yazo ni basai ya dakeniba mai bauɗaɗɗen halin tsiya irin na uwarsa”.

      Dariya Baffah ya mike yanayi shidai da faɗin, “Ai kunfi kusa Innata.  Wazai yarda ya shiga tsakaninki da Adnan da Khalipha a gidan nan”.

       “Aikam ni yanzu bana yayin wani Moddibo can. Garama Khalipha ɗin duk da shima ja'irin kansane, daka ɗakko laifin takwaran nasa zai fara karewa da yayansu kaza-kaza, saikace akansa aka fara ɗan uwa”.

     Shi dai Baffah dariyarsa yaketa sha harya samu ya gudu domin zuwa yay shirin fita kasuwa.


       Lokacin da Hajiya iya kenan suna maganarsu da Baffah Zinneerah datai kwanan baƙunta a ɗakin data fahinci mai shi mutum ne mai matuƙar daraja da girma ga jama'ar gidan, dan su Meenal ƙiri-ƙiri sunƙi zaman ko mintuna goma a ciki, tana can ta shige cikin masu aikin Hajiya Iya tana tayasu aikin gyaran sashen. Lokacin da Baffah ya fito ya fice suna Kitchen domin haɗa breakfast kasancewar kullum anan Baffah ke karin kumallon safe tare da mahaifiyar tasa, weekend ne kawai bayayi anan.

    Masu aikin sunso hanatayi amma taƙi. Dole suka barta saboda sunsan yaran gidan dama kan shiga ai aiki dasu suma bisa dokar Hajiya Iya. Amma da dan ta iyayensu matane kam da ba hakaba. Itako Hajiya Iya ta tsaya tsayin dakane domin taimakonsu tunda tasan gidan wani zasuje.

     Bayan sun kammala komai tsaf Baba Rahi tace taje tai wanka kafin Hajiya Iya ta fito dan batason ƙazanta ko kaɗan. Shiyyasa kosu kansu idan baka saniba bazaka taɓa ɗauka ƴan aiki bane a gidan ma, sai an faɗa.

         Babu musu ta nufi komawa ɗakin data kwana. Ɗakin da kallonsa kawai saka mata wani shakkar zama a cikinsa take shiga. Dan har cikin ranta tanaji cewar matsayinta bai kai na ta zauna wannan ɗakinba da take ƙyautata zaton na musamman ne.

       Kamar yanda ta kasance a ɗarare daren jiya yanzunma a ɗararen tai komai. ALLAH ya taimaketa ma hatta da soson wanka da kayan shafarta ta taho da abinta. Komai na ɗakin bata yarda tai amfani da shiba bayan ruwa, sai bargo data saka a ƙasa ta kwanta a daren jiya.

     Tsaf ta kammala shirinta cikin riga da skirt na atanfa ruwan bula da ratsin fari, sai ɗan baƙi-baƙi kaɗan. Hijjab ƙarami data taho dashi saboda zaman gida ta ɗauka ta saka sannan ta fita. karo suka kusanci da Jamal tai baya da sauri.

     “Oh sorry Sister, dama Granny tace ki fito ke kaɗai ake jira cin abinci”.  Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma tai shiru saboda tinawa da nasihar mahaifiyarta data tuno akan zaman gidan. Tai ɗan murmushi da faɗin, “Ina kwana”.

      Dariya yayi yana susan kai. “Uhm su Jamal an girma. Wai ni kike gaidawa ma kowa?”.

     Karon farko tai dariya da fara tafiya, har cikin rai yanda suke da barkwanci na birgeta. Shima sai ya biyota yana rawa wai an gaishesa, bayan kaf gidan shike gaida kowa. Koda suka iso ƙaton dining ɗin karaɗinsane ya saka kowa maido hankalinsa kansu. Ya ƙaraso garesu yana basu labarin yau an gaisheshi shima ya tashi daga autan gidan nan yanada ƙanwa.

        Babu wandama yaji miya faɗa dan duk hankalinsu nakan Zinneerah da duk ta daburce saboda idanunsu. Ƙasa takai tsugunne dai-dai tana isowa gabansu tace, “Hajiya ina kwana?”.

       Fuskar Hajiya Iya ɗauke da fara'a da kulawa ta amsa mata, tare da tambayarta baƙunta. Kan Zinneerah a ƙasa take amsawa. kafin ta juya ga Baffah shima ta gaidashi da girmamawa. Amsa mata yay shima cikin kulawa da faɗin, “Kinga taso ga abinci, ga kuma ƴan uwanki nan dake gida duka”.

       Kanta ta jinjina masa jikinta na ƙara saki saboda jin idanunsu duk a kanta. batare data miƙe ɗinba tace, “Ina kwanan ku?”.

     Moos'ab ne ya fara sauke numfashi da amsa mata. “Lafiya lau ƴar ƙyaƙyƙyawa, Granny ina kika samo mai kama da Inno haka?”.

      Kafin Hajiya Iya ta bashi amsa Haneef ya amshe da cewa, “Masha ALLAH ko itace ƙanwar tamune?”. Saifudden zaiyi magana shima Baffah da ke shirin fara cin abincin da Abidah ta haɗa masa yace, “Wai ni gidan nan halan duk ƴan jarida muka tarane? Indai kune yanzu sai kowa yace sai ya mata tambaya anan. Ɗiyata taso kinji”.

       Cikin jin kunya ta taso ta zauna kujerar da Ni'ima ta gyara mata. Kallonsu Baffah yayi su duka, danya fahimci har yanzu duk hankulansu naga Zinneerah musamman ƴan samarin ƴaƴan nasa. Yay ɗan murmushin manya yana lumshe ido da buɗewa. “Wannan itace Zinneerah ƙanwarku. Wadda tun kafin zuwanta an sanarma kowa dake gidan nan. Muna fatan zaku karɓeta da hannu biyu ku kuma ɗauke babu wani banbanci daku”.

      Insha ALLAHU Baffah.

Suka haɗa baki wajen faɗa su duka.

    Kansa ya jinjina cike da gamsuwa yana maida dubansa ga Zinneerah da kanta ke ƙasa. “Ɗiyata Zinneerah ɗago ki kalli kowa danki haddace fuskokinsu da sunayensu”.

       Duk da tana cikin yanayin jin nauyi bin umarnin Baffah dolene a gareta. Hakan yasa ta ɗago a hankali. Da wanda ke kusa da Hajiya Iya ya fara. “Wannan sunansa Mas'ood, ƴan biyu ne shi da Moos'ab gashinan. Wannan kuma Saifudden, wannan Haneef, wannan Abidah, wannan Safiyya, wannan Ni'ima. Sai Jamal, Meenal, Bahijja. Akwai yayunki kusan goma da babusu anan. Koda yake ba duka bane yayun naki a cikinsu dan kin girma wasu. Insha ALLAH duk zaki sansu su sanki suma a hankali. Waɗan nan dai sune yanzu tare dake anan gida, zaki kuma kasance da kusan dukansu yanzu a gida insha ALLAH”.

        Fuskarta daɗan murmushi tace, “Nagode Baffah”.

      Murmushin shima yay mata yana jinjina kansa. Yayinda su Haneef suka haɗa baki wajen, “Welcome to Shira's family ƙanwarmu”.

       “Na gode Yayuna”.

Ta faɗa ita cikin son aro jarumtar son sakewa da su. Dan taji daɗin yanda duk suka nuna jin daɗin kasancewarta a cikinsu. 

    Ƴar gajeruwar nasiha Hajiya iya tai musu akan zuminci kafin su fara cin abincinsu a tsanake. Wajen yayi shiru bakajin ko ƙwaƙwƙwaran tarin wani saboda dokace a garesu ba'acin abinci ana magana musamman idan Hajiya Iya da Baffah na waje. Uwa uba kuma Babban Yaya mai gayya mai aiki dashi ko ƙara cokalinka ya cikayi sai kasha uwar harara.


         Koda duk suka kammala duk ficewa sukai, dan dukansu karatu sukeyi a mabanbanta makarantu jami'oi. Wasunsu na gab da kammalawa, wasu kuma yanzu suka fara musamman ƴammatan. Wasu kuma na tsakkiya. Sai su Bahijja dake secondary sun wuce Zinneerah da aji daya, dan suna ss2. Sai dai yau bazasujeba dan suna wani ɗan hutun kwana biyu a gida.

      Bayan wucewar kowa ita dasu Meenal ɗin ne suka gyara dining ɗin. Hajiya Iya kuma ta nufi ɗaki gabatar da sallarta ta walha tana bar musu saƙon raka Zinneerah wajen iyayensu ta gaishesu.

     Suna kuwa kammala gyara wajen suka jata. Meenal ce taja birki lokacin da suke gab da kaiwa tsakkiyar ƙaton harabar gidan nasu. “Kunga ku tsaya a fara da nunama sister kowanne sashe first”.

       “To uwar tsari”. Cewar Jamal da shaƙiyanci.

     Hararsa Meenal tayi sai dai batace komaiba. Bahijja tace, “Da gaskiyar sister ai, a fara da waje”.

      “Naji karku cinyeni da baki malamai. Sister Zinneerah nan inda muka fito shine sashen Granny nasan kin sani ai?”.

    Jamal ya faɗa idonsa a kanta. Batare da jiran amsarta ba ya cigaba. “Wannan na kusa da shi shine sashen Daddy Ahmad ne. Sai dai basa nan suna ƙasar Turkey lokaci-lokaci suke zuwa. Yaransa biyar shima. Yah Ibrahim, Yah Sadiq, Yah Hafeez. Aunty Zuhrah. Sai Aneesa dan bazance mata Aunty ba, kwana tara kawai ta bani a duniya kamar wannan yarinyar”. Ya nuna Meenal.

      “Shashasha ai dai na girmekan ko?”.

        “Oho a banza dai tunda kammu ɗaya”. Ya bata amsa yana mata gwalo.

    Dariya abin nasu keba Zinneerah. Dan haka yanzuma tai murmushi mai faɗi.

       “Yauwa sai nan kuma Sashen Gwaggo Bilkisu ne idan tazo nan take sauka itama. Tana Lagos da yaranta huɗu itama, kada lissafin yay miki yawa zakisan sunayensu suma nan gaba. Sai nan shine sashen su Yah Saifudden. Nan kuma sashen baƙine. Wannan da zamu shiga shine sashenmu, iyalan Baffah kenan”.

    Murmushi Zinneerah tai cike da gamsuwa dajin birgewar tsarin nasu. Batare da tayi maganaba suka nufi sashen Baffah ɗin da yafi na kowa girma a gidan kasancewar yafi kowa yawan iyalai.

      Sun fara shiga katafaren falo da yaji kayan more rayuwa da ƙawa, wanda har suka fice daga cikinsa Zinneerah bata gama kammala kallon daular dake shimfiɗe a cikinsaba. Basu tsaya anan ba suka isa falo na biyu wanda shima ƙatone na gaske harma zai iya ɗara na farko kayan alatu. A tunaninta an gama kenan, sai taga sun shigo wani falon a hannunsu na dama, sai dai shikam madaidaicine bakai na baya girmaba amma ya fisu tsaruwa.

      Hamshaƙiyar mace ƙyaƙyƙyawa dake zaune da waya a kunne ta ɗago tana kallonsu. Fuskarta a sake take sai dai ba murmushi takeba. Zama su Bahijja sukai a kujera suna faɗin, “Barka da safiya Momie”.

      Kasancewar waya take bata amsa musu ba. Tadai ɗaga musu hannu kawai idonta akan Zinneerah data kai zaune ƙasa zuciyarta na harbawa da ganin kamanin matar da Khalipha sosai. Bayan ta kammala ta ajiye wayar tana faɗin, “Masha ALLAH ɗiyata sai yanzu muke ganinki?”.

       “Kuyi haƙuri Momie”. Zinneerah ta faɗa kamar yanda taji su Meenal na kiranta.

      Cikin ƴar dariya tace, “A'a aiba laifi kikaiba ƴata. muna miki maraba da shigowa cikinmu”. 

       Gaba ɗaya kan Zinneerah a kulle yake. Tadai daure ta amsa mata da godiya tana gaisheta cikin girmamawa. Hakan yasaka Hajiya Nafisa jin daɗi har ranta dajin ƙaunar Zinneerah. Sun ɗanja lokaci a sashen Hajiya Nafisa da suke kira Momie nata mata ƴan tambayiyi jefi-jefi da janta da hira. 

       Hajiya Nafisa itace Baffah ya aura bayan rabuwarsa da Hindatu. Itace mahaifiyar Khadija da a yanzu haka tayi aure itada ƴar uwarta Hafsat. Sai Khalifa, Saifudden, da auta Bahijja. Sunɗan jima Kafin su miƙe su fito dan itama wajen aiki zata fita.

    Daga nan sai sashen Hajiya Halima mahaifiyar su Meenal. Wadda suke kira Ummi. Itace ta haifi Mas'ood, Moos'ab, Ni'ima, Meenal auta. Itama ɗin dai ta tarbesu da kulawa da sakewa. Dan tamafi Momie fara'a gata da barkwanci. Yanda Zinneerah ta lura su Jamal sunfi sakewa sosai anan. Nanma sun jima sosai kafin su fito zuwa sashen Hajiya Ai'sha amaryar Baffan da suke kira da suna Ammi. Itace mahaifiyar su Haneef Safiyya, Abidah Jamal auta.

       Mahaifiyar su Jamal ba mace bace mai yawan fara'a. Amma tanada son mutane itama. Dan ta tarbi Zinneerah ɗin da kulawa sosai, harma takai hirarsu tafiyin tsaho anan fiye da kowanne sashe. Basu fitoba sai da akai kiran sallar zuhur suka koma sashen Hajiya Iya data gaji da zuba idon dawowar tasu ma.


★★★


        Lallai da gaske Shira's Family yayma Zinneerah daɗi. A cikin kwanaki huɗu kacal sai gashi ta saki jikinta da kowa, musamman ma su Bahijja dake ɗorata a hanya waɗanda bata da aminai sama dasu a gidan. Zata iya cewa shine gidan zama na farko data shigo bata fuskanci ƙiyayyar waniba a zahiri. Dan inma akwai masu ƙin nata sun danne a zukatansu basu taɓa nuna mataba.

       Daɗin zama cikinsu ya matar da ita batun kwana biyu da akace zatayi ta koma. Abinda kawai ta kasa sakewa da shi shine kwana ɗakin da aka bata matsayin nata. Komai take a cikinsa a ɗararene. Gashi su Meenal basa shiga ɗakin sam. Ko zuwa sukai tana ciki sunfi yarda su jirata a falo harta fito..    

      A randa ta cika kwana na biyar suka koma makaranta. Ranar duk sai taji kuma babu daɗi. Amma janta a jiki da Hajiya iya keyi yay matuƙar ɗebe mata kewar su Little da ke damunta a rai tun zuwanta gidan. Tamkar kuma Hajiya iya ta shiga ranta sai gashima ta kira mata Mama a waya suka gaisa. sai dai su Sadiq duk sun wuce makaranta. Gwarancin Little dake wasa kawai take jiyowa. Tanason tambayar lafiyarsa tanajin kunyar maman Sadiq. Dan haka tai shiru tunda dai ALLAH yasa ta jisa ɗin.


         Zinneerah na zuba ido taji ance ta shirya ta koma gida kodan karatunta sai taji tsit. A ranada ta cika kwanaki tara a gidanma Baffah yasa ta shirya Yah Saifudden ya kaita makarantar su Meenal da sunan sabuwar ɗaliba. Hakan ya bata mamaki dan babu wanda yay mata bayanin za'a canja mata makarantane. Garama Hajiya iya ta mata nasiha akan ta dage sosai karta bari su maidata baya. Tafi son karatunta da nasu Bahijja ya tafi dai-dai.

     Zinneerah ba ƙoƙarine da itaba. Sai dai tanada naci akan abinda takeso. wannan ne ya taimaka mata matuƙa wajen amsa interview da akai mata duk da dai karatun da tayi a gidan Abba ya matuƙar taimaka mata. Da ace sanda ta baro Danya ne to lallai wannan haɗaɗɗiyar makarantar babu fashi aji ɗaya zasu maidata kuwa.

      A yanzunma sunyi batun sai da ta koma js3. Saifudden ne ya roƙa alfarmar barinta a ss2 ɗin da alƙawarin zata dage insha ALLAH. Da yake maganace ta kuɗi kuma su ɗin sunada babban matsayi a makarantar yasa suka bar Zinneerah ɗin Ss2. cikin amincin ALLAH kuma aka kaita ajinsu Meenal. Zokaga farin ciki da murna lokacin da aka rakata ajin a zuwan sabuwar ɗaliba. Malamin na fita Jamal ya fita gaban aji ya sake gabatar musu da Zinneerah matsayin sister ɗinsu ce. Hakan yasa ta samu tarba mai ƙyau daga ƴan ajin dansu Jamal ƙurayene sosai akan ƙoƙari.

      A ranar kam dai babu abinda Zinneerah ta fahimta a wannan aji. Sai ma neman ruɗewa da tsorata da tayi ganin yanda tsarin karatun nasu yake. Sam babu maganar hausa a ajin ma balle ga malami. Turancine da larabci kawai ke tashi. 

    Fahimtar yanda ta shiga ruɗanine ya saka su Bahijja kwantar mata da hankali akan karta damu zata iya itama ai wataran. Badan ta yarda da hakanba tai shiru, amma har cikin ranta a tsorace take kam. Sai dai kuma tana fatan iyawar kodan wasu abubuwa masu yawa dake cimata rai da zuciya a tarihin rayuwarta. Itama tanason ta zama wani abu kodan wani dalili nata dake ɓoye mata a cikin rai game da samuwar ɗan da batasan wanene ubansa ko yanda aka samar da shi ba.


     Bayan tasowarsu ne Hajiya iya ta kira mata Mama a waya suka gaisa. A take ta labartama Maman komai har tana hawayen farin ciki dana kewarsu. Dan tasan dai tunda har aka sakata a makaranta da wahala ace zata koma zama wajen Mamanta sai dai idan anyi hutu. To koba komai dai ai tamayi nesa dasu Sakina iyayen gorin gida dana arziƙi. Kuma karatunta zaifi inganci anan fiye dacan duk da shima Abba bazata taɓa gajiya da yaba masaba a rayuwarta har ƙarahen numfashinta kuwa.


★★★


     Kamar da wasa sai ga rayuwa ta fara canjama Zinneerah alƙibla. Dan kuwa dai da alama *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_* data barota da Danya na neman zame mata ƙyaƙyƙyawar nasara mai abubuwan fata ga duk wanda ya tsinci kansa koda a makamancin irin tata rayuwarne. Yau ita Zinneerah mai tallar riɗi da gyaɗa da ɗanwake ce a wanann matsayin. Ita da kashin gidansu ma ya fita matsayi da daraja wajen Inna dasu Yaya Karima. Lallai ta yarda da yawan ƙaddara tsanine na nasara gamai haƙuri insha ALLAH. Sai dai ya danganta ga yanda ƙaddarar tazo maka da kuma yanda kai ka amsheta kai haƙuri da ita.

     Sosai a kallo ɗaya zakaga ɗumbin canjin data samu. Jikinta ya murje matuƙa, ƙyawunta da nutsuwarta na sake fitowa gareta. Yayinda cikakken budurci ke sake huda gaɓɓanta da surarta. Ta kuma dage da naci akan karatu da taimakon su Bahijja duk da sukan sha wahala wani lokacin kafin ta gane abu daƙyau.

     Zuwa yanzu a hankali su Meenal na jan ra'ayinta kwana sashensu fiye da ɗakinta. Wani lokacin kuma wajen Hajiya Iyama take kwana musamman idan ta tashi batajin daɗin ƙafarta haka ko jikinta. Tsakaninta da ɗakin nata bai wuce shiga tai wanka sai kuma gyarawa. Sai randa ALLAH kuma ya ƙaddara zata kwana a cikinsa.

         

       A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu Zinneerah an cinye hutun zangon farko a tsadajjiyar majaranta. Kwanansu biyar dayin hutu Baffah ya haɗa mata shatara ta arziƙi Yaya Haneef ya kaita gida wajen mahaifiyarta. Da dasu Jamal zasu tafi Baffah yace su bari sai ta tashi dawowa sai suje su ɗakkota tunta dai kwanaki goma zatai kacal ai.

     Haneef ya shiga sun gaisa. Sai dai bai jimaba ya fito ya tafi, dan makaranta zaije kuma yace yanada jarabawane. Amma daɗin tarbar daya samu ga Mama yace zai dawo. Bai iske su Sadiq gidaba suna islamiyya. Little kuma yana barci abinsa.

       Kwatanta irin farin cikin da Zinneerah ta tsinci kanta a ciki ɓata lokacine. Amma tsabar kewar Mama da tayi harda rungumeta. Little kuwa data shiga ta samu yana barci yasha kisses, harda hawayenta ganin yanda ya ƙara girma a watanni uku kacal data ɗauka bata ganshiba. Wani irin son yaron da ƙaunarsa na ƙara tasiri a ranta alamun hankali ya fara game jikinta a yanzun fiye da da.

     Lokacin kuwa data shiga gaida Maman Sakina ai baki ta saki tana kallonta tamkar sokuwa. Hakama dasu Luban suka dawo gidan daga makaranta dan suna jarabawa sai da ƴaƴan cikinsu suka hautsina da ganin canjawar Zinneerah ɗin a ƙanƙanin lokaci. Duk da sunsan dama ƙyaƙyƙyawa ce a yanzu kam ƙyan nata yafi fitowa da armashin gani gamai kallonta.

     Itako sosai ta nuna murnar ganinsu cike da sakewa alamar yanzu akwai banbanci da da kenan. Dan babu wannan yawan duƙar dakan da ɗari-ɗari tattare da ita. Miskilancin nedai kam akwaishi saima abinda yay gaba.

     Sai da suka shiga ɗaki sukaita gulma da zaginta wai dan taje gidan masu kuɗi kanta ke rawa tana musu shan ƙamshi. Duk da har yanzu basusan taka maimain a inda takeba. Har uwarsu ba sani taiba duk bin ƙwaƙwƙaafinta. Koda ta tambayi Abba cayay mata dangin mahaifanta ne suka ɗauketa dama basusan ta baro gida baneba zuwa nan shiyyasa. Daga haka kota masa maganar sai yace taje ta tambayi maman sadiq ɗin mana. Daga haka yake kashe bakin son gulma da tsugudidi.

      Maman halima kuwa taji matuƙar daɗi da canjin da Zinneerah ta samu. Koba komai itama ta samu ingantacciyar rayuwa bisa ga zaluncin Asabe ai.

     Dawowar su Sadiq aka sake kafa sabuwar murna da bidiri har takai ga tashin Little. Sosai girman nasa ya sake bama Zinneerah mamaki dan bakace ɗan shekara ɗaya da rabi bane. Da alama akwaishi da garin jiki kam. Yanda yaga su Aliyu nane da ita shima sai ya nane natan yana gwarancinsa dan maganar tasa bawani ganewa sosai akeba garama maman sadiq.

     Ganin ƴan uwanta yay mata daɗi duk da bata mance dasu Jamal ba suma. Kullum ma babu fashi sai tayi waya dasu ta wayar Hajiya Iya ko cikin wayar ƴammatan gidan............✍

      

No comments

Powered by Blogger.