Makauniyar Kaddara 17

 


Page 17*


...........Tarba mai ban mamaki da tu'ajjibi Zinneerah ta samu daga hajiya iya, harma da wasu daga cikin jikokinta dake gida ta iske a sashen. Duk yanda taso ta takura kanta saboda baƙunta da rashin sabo sunƙi bata damar hakan. Dan sai faman jera mata tambayoyi suke tamkar ƴan jaridu.

      Dolenta ta saki jiki dasu dan su biyun duk sa'anninta ne. Biyu mata, Bahijja da Meenal wadda taci sunan Hajiya Iya kenan. Sai É—aya Namiji mai suna Jamal.

    Harga ALLAH Zinneerah taji daÉ—in kasancewa dasu, dan ta fahimci sunada tarbiyya da sauÆ™in kai sosai, sannan son É—an uwansu ko yaya yake wannan trianing da akai musu ne tun asali.

      Cikin katsesu Hajiya Iya dake shafa man zafi a Æ™afarta tace, “Niko kun isheni da subaÉ—i Bahijja. Kuma barni nai hira da Innon tawa kunbi kun hana. Sai ku tashi ku kaita wancan É—akin kuÉ—an Æ™ara gyarawa duk da dai ko jiya Rahi ta garasa ta samu taÉ—an watsa ruwa ta huta dan shine zai zama É—akinta”.

       Wani irin waro idanu Jamal yayi tare da zabura. Haka Meenal da Bahijja ma duk sai da suka zaro idanun. Jamal yace, “Granny kina nufin É—akin Yayanmu fa kenan?”.

      Harara sosai Hajiya iya ta watso musu tana Æ™yaÉ“e fuska. “Eh shi dinfa nake nufi ba waniba. Zuwa yake Æ™asar ne da har za'a wani cigaba da faman barin É—aki haka aljanu na dubulwa a cikinsa? Ubansama dana haifa bai tuna inda nakeba shekara guda balleshi da ke neman haÉ—a kusan uku”.

       Yanda ta Æ™are maganar cikin É—acin rai ya saka jikinsu duk yay sanyi. A sanyaye Meenal tace, “Kiyi haÆ™uri Granny, mu dama zaki yarda sai mu tafi da ita sashenmu, kinga saita zauna a É—akinmu dan ALLAH”.

        “Hakan zaifimin daÉ—i kuwa Amina. Sai dai kuyi haÆ™uri nafison zamanta kusa dani akoda yaushe. Koba komai zanga fuskar Innota naji sanyi”.

      Kansu kawai suka iya kaÉ—a mata, dan tunda ta faÉ—i haka basu isa jayayya da ita ba. Ko min roÆ™on da zasu mata kuma bazata canja ra'ayintaba. Zinneerah dai najinsu kanta a Æ™asa, sai dai babu abinda ta fahimta a zancen nasu kuma. Amma ganin yanda fara'ar fuskar Hajiya iyan ta É“ace tun daga maganar ne ya saka jikinta yin sanyi itama......

      “Taso muje kiga É—akinki Sister”. Bahijja ta katse tunanin Zinneerah tana kama hannunta cikin nata. Babu musu ta miÆ™e tabi bayanta, Meenal da Jamal ma suka mike suka biyosu.

     Kallo Hajiya Iya ta bisu dashi idanunta na cika da Æ™walla. Dan maganar nan ta tado mata da wani babban miki dake zuciyarta tsahon shekaru, wanda a shekarin can da suka shuÉ—e kusan biyar sun fara ganin haske, amma a wannan karon al'amarin na neman komawa baya. Dan inhar lissafinta bai Æ™wace mataba kusan shekararsa É—aya kenan rabonsa da Nigeria. A take wasu hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Saurin saka hannu tai ta sharesu tare da miÆ™ewa ta nufi hanyar É—akinta tana É—an É—ingisa Æ™afarta dake mata ciwo tinda safe.


        “Sister Zinneerah lallai keÉ—in mai sa'a ce”. Meenal ta faÉ—a tana tura Æ™ofar É—akin da suka iso a É—an lungun corridor É—in dake facing jikin É—akin Hajiya Iya. Kafin Zinneerah ta iya cewa wani abu Jamal ya karÉ“e da cewa “Mai sa'a kuwa ta gasken gaske. Dan kece ta farko a tarihin gidannan kaf da zaki rayu a wannan É—akin na Yayanmu bayan shi kaÉ—ai dake rayuwa a cikin kayansa idan yazo Æ™asar”.

      Haka kawai gaban Zinneerah ya faÉ—i batare da tasan daliliba. Har suka shige É—akin ita tama kasa motsawa balle É—aga Æ™afarta. Ganin hakan yasa Jamal dawowa da baya yaja hannunta suka shige ciki, duk da taso Æ™oÆ™arin Æ™wace hannun nata amma yaÆ™i bata dama sai da suka shigo tsakkiyar Æ™aton É—akin da batamasan yanda zata fasaltashi ba a fahimceta.

           Sakin hannunta da Jamal yayi ya bata damar É—ago idanu tanabin É—akin da kallo. Yayinda hancinta ke shaÆ™ar mata wani irin mayataccen Æ™amshi mai sanya zuciya salama. Wani irin saki gaɓɓanta sukai a lokaci É—aya, ta zubama su Bahijja daketa yaye fararan Æ™yallayen da aka lulluÉ“e komai na cikin É—akin dasu saboda gudun Æ™ura ta hausu.

         Sai da suka gama yaye komai ya bayyana Meenal ke faÉ—in, “Bara na É—akko kayan shara mu tayaki É—an Æ™ara gyarawan baÆ™unta. Kuma mufa kibar mana wannan É—ari-É—arin Madam”.

     Cikin tsokana Jamal yace, “Barta sotake mu kirata baÆ™auya maybe. Gwarama ki sake damu kafin su Yah Haneef su dawo gidannan gobe idan ALLAH ya kaimu, dan zasu cinyeki da bakine”.

       “Kaji munafiki, saina faÉ—a musu yasin”. Bahijja dake hararsa ta faÉ—a.

    Yanda Jamal yay da fuskane ya saka dariya kufcema Zinneerah batare data shiryaba. Hakan yay dai-dai da dawowar Meenal É—auke da kayan shara É—akin. “Oh ALLAH, kokefa Æ´ar uwa. Ni kuwa an taÉ“a faÉ—a miki keÉ—in Æ™yaÆ™yÆ™yawa ce musamman idan kina dariya?”.

          Kasa bata amsa Zinneerah tayi, sai dariyar tatace ta koma murmushi kawai. Hakan datai ya saka su Jamal kwashewa da dariya a tare. Bahijja tace, “Kinga kinsatama ta haÉ—iye abinta da wannan bakin naki da bai gani ya Æ™yale”.......

       “Wai nikan sharar zakuyi ko damuna da shegen surutu?”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya dake tunkaro É—akin.

       A take kowa ya nutsu suka fara Æ™oÆ™arin sharar. Shigowa tai har yanzu fuskarta a dagule da É“acin ran É—azun. Tabi É—akin da kallo da Æ™yau kamar mai nazari. A Æ™arshe ta sauke idonta akan Zinneerah dake Æ™oÆ™arin tayasu itama. Haka kawai kuma sai taji É“acin ran nata ya sassauta. Ta sauke ajiyar zuciya da juyawa ta fice a É—akin.


      Tsaf suka gyara komai dan an horar dasu aiki tuni. Cikin kanÆ™anin lokaci Æ™yawu da tsaruwar É—akin ya Æ™ara bayyana a idon mai kallo. Musamman da suka cire labulayen É—akin duk suka sake canja wasu fararen tas dan dama fararen suka cire. Kaso mafi yawa dake a É—akin kalar blue and white ne. Sai wasu colors É—in É—ai-É—ai da ba'a rasaba. Da yawansu kuma an É“aɓɓoyesu ma.

      Idanu ta lumshe a hankali tana maijin wani abu mai nauyi dake a Æ™irjinta yana narkewa sannu-sannu zuwa cikinta. Nannauyar ajiyar zuciyar da bata shirya fitartaba ta kufce mata a karon farko. Kusan a tare Meenal, Bahijja, Jamal suka dubeta. Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, dan sun fahimci Zinneerah bata da sakewa da mutane, gata kuma da alama akwai miskilanci tattare da ita.


★★


       Æ˜arfe bakwai da wasu mintuna Alhaji Kabir ya iso katafaren family House É—in nasu. Bayan samun wajen fakin da direba yayi ya tsaya aka buÉ—e masa ya fito riÆ™e da leda a hannunsa wadda kowa yasan mai ita. Dan babu fashi kullum sai ya shigo da irin wannan ledar domin mahaifiyarsa koda iyalansa basu samu hakanba. Sanin baya bama kowa dakon É—aukarta, shi yasa babu wanda ya tunkaresa domin karÉ“a. Sai dai sauran kayansa da É—allami driver ya kwasa zuwa sashensa shi da iyalansa. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya Iya kansa tsaye.

        ÆŠauke da cikkakkiyar sallama a bakinsa ya shigo falon duk da yasan a irin wannan lokacin Hajiya iya na Æ™uryar É—akinta. dan idan tai sallar magriba bata fitowa sai isha'i. Amma yanada tabbacin baza'a rasa wasu daga cikin Æ´aÆ´ansaba da basa rabo da sashen a koda yaushe.

    Ilai kuwa yana shiga da fuskar Zinneerah da Meenal ya fara tozali dan sune ke facing Æ™ofa. A take falon yay tsit kowa ya Æ™ara nutsuwa. Sai Meenal ce datai saurin miÆ™ewa ta nufesa domin amsar ledar hannun nasa. “Baffah sannu da zuwa?”.

      “Yauwa uwata kune anan?”.

“Eh Baffah, munzo tarbar Sister Zinneerah ne tun É—azun”.

     Murmushi Alhaji Kabir yayi yana maida kallonsa ga Zinneerah data risinar da kanta Æ™asa tun bayan amsa sallamarsa. Ya Æ™araso cikin falon sosai su Bahijja ma na masa barka da dawowa. A hankali Zinneerah ta zamo Æ™asa tana faÉ—in, “Sannu da zuwa Baffah. Ina wuni”.

     Murmushinsa ya sake faÉ—aÉ—awa da faÉ—in, “Yauwa É—iyata. Welcome to Shira's family”.

       “Thanks you Baffah”. Ta faÉ—a a hankali cike dajin kunya. 

       Ya cigaba da faÉ—in, “Yaya kika barmin Æ™anwata da Æ™annanki da Abbanki?”.

      “Lafiya lau Baffah, sunce suna gaisheka”.

     “Ina amsawa. Alkairin ALLAH yakai garesu. Tashi ki zauna”.

    Babu musu Zinneerah ta miÆ™e ta koma kusa da Meenal data kaima Hajiya Iya leda ta dawo ta zauna. Shikuma ya wuce bedroom É—in Hajiya iyan domin gaisheta.


       Tunda yay sallama a yanda ta amsa masa ya saka gabansa faÉ—uwa. Cikin Æ´ar ruÉ—ewa ya Æ™araso Æ™aton É—akin nata itama da sassarfa. Gabanta ya zube jikinsa na rawa. “Innata mike faruwa naji muryarki tamkar baÆ™yajin daÉ—i?”.

       ÆŠago kyawawan idanunta da mafi yawan Æ´aÆ´a da jikokin gidan suka gada a wajenta tai tana kallonsa. A take hawayen da taketa maÆ™alewa tun É—azun suka silalo mata tare da murmushi a lokaci guda. Sake ruÉ—ewa Alhaji Kabir yayi idanunsa shima na kawo ruwan hawaye.

     Kanta ta girgiza masa a hankali tana share nata. “Hawayena basu zuba domin kai ba Kabir. Dan kai É—a ne tamkar da dubu ga kowaÉ—anne irin iyaye. Nagodema ALLAH domin yayimin ni'imomi masu yawa a rayuwa da har wanda ke a nesa dani bazai É—auka inada wata damuwa ko jarabawa nima tattare dani ba, kuma har da samunka matsayin É—a a cikin ni'imomin. Kabir tabbas É—an uwanka shine jarabawata. Dan ALLAH ka tayani addu'a ALLAH ya bani ikon cinyewa. A lissafin danai yau shekarar Ahmad É—aya da watanni biyu kenan rabonsa da Æ™asarnan. Yanzu ace Kabir har Inno ta rasu Ahmad ya gagara É—akko iyalansa suzo sumin ta'aziyya. Idanma ita data nisantani dashi bazatazo ba shi bazai iya zuwaba koda shi da Modibbo ne?. Moddibo fa kansa shekararsa uku kenan rabonsa da Æ™asarnan. Tunda nai maganar yay auren nan bai sake zuwaba, uwarsa kuma ta hana wannan Æ™oÉ—aÉ—É—iyar yarinyar zuwa nan É—in koda ta haihunma. To kosai na mutune zata barsu suzo su raÉ“i gawata......”

      Ta kasa Æ™arasa maganarta saboda kuka daya kufce mata.

      “Innata dan girman ALLAH ki daina kuka. Kiyi haÆ™uri dan ALLAH, addu'arki da tamu Ahmad yafi buÆ™ata. Kuma insha ALLAH namiki alÆ™awarin a wannan karon zanbi duk hanyar data dace domin maido É—an uwana gida. Har ita É—in da shaiÉ—ancinta dole ta biyosa. inko taÆ™i wlhy sai dai ta kama gabanta inda ta fito. Amma dan ALLAH kibar kuka Inna”.

      “Kayya Kabir. A baya fa kayi irin wannan namijin Æ™oÆ™arin amma kaga ta sake sabon shiri, harshi Moddibo É—inma da ada bayabin ra'ayinta yanzu ta sake janyesa. A zatonmu kusancin da Khalipha ya samu dasu zai kawo wani canjin sai gashi ba hakaba”.

       “Insha ALLAH Inna komai zai wuce. Ai duk abinda ya saka kuka wataran zai saka dariya. Duk kuma abinda ya saka dariya wataran sai ya saka kuka. Itama ai gasunan ta haifa indai Æ´aÆ´ane ko. kuma Alhmdllh sai ya bata mafi rinjayensu maza. Itama kukan da zatayi akansu sai ya ninka naki sau dubu. Amma dan ALLAH ki daina masa kuka Inna dan shima ba laifinsa bane, anfi Æ™arfinsa ne kawai”.

      “Humm ko anfi Æ™arfinsa kam da halima. Dan shima kaidin macen yana iske haline. Kai miyasa matan naka basu rabani da kai ba”.

     Kasa cemata komai yayi sai ban haÆ™uri dai. Sai da yaga hankalinta ya kwanta sanann ya miÆ™e ya fice domin zuwa gabatar da sallar isha'i tunda ya cinye lokacin zuwa yay wankan anan.

     Bai iske su Zinneerah a falonba yanzu. Da alama sun shige gabatar da sallar suma.


______________★


      Duk yanda Alhaji Kabir yaso rintsawa a daren yau hakan ya gagara. Ba komai ke masa kai kawoba a rai sai tattanawarsa da Mahaifiyarsu akan É—an uwansa.

       Su uku kacal mahaifiyarsu Hajiya Iya ta haifa a duniya. Shine babba, sai Æ™aninsa Ahmad, sai autarsu Bilkisu da ayanzu haka tana Lagos tana aure. Rana É—aya aka É—aura masa aure da É—an uwansa Ahmad, wanda mafi yawan mutane sukafi sani da suna AK Shira. Ba komai yasa ake kiransa da suna AK ba sai tsanain soyayyar da sukema juna tun Æ™uruciya. Kasancewar boarding school sukayi acan ake kiransa da suna Ahmad É—in Kabir. A hankali kuma sai abokai suka koma kiransa a takaice da suna AK Shira. Mai makon Ahmad Abdul-Mutallab Shira kamar yanda shi ake kiransa Kabir Abdul-Mutallab Shira. Bayan sun kammala secondary tare suka wuce Æ™asar Turkey Æ™aro karatu. Cikin amincin ALLAH suka haÉ—a digiri É—insu na farko dana biyu duk a tare. Tun suna farkon fara digiri na biyu Ahmad ya haÉ—u da matarsa ta yanzu mai suna Hindatu. Asalin Hindatu Æ´ar Æ™asan Nigeria yace. dan mahaifinta É—an nanne. Sai dai mahaifiyarta Æ´ar asalin Æ™asar Morocco ce. Amma suna zaune a Æ™asar Turkey tun tanada Æ™uruciya, acan ta girma tamafi sanin can matsayin Æ™asarta fiye da Nigeria dan sukan jima basuzoba. ƘyaÆ™yÆ™yawa ce itaÉ—in sosai kasancewarta halfcast ce. Sai ALLAH ya bata wani irin usilin Æ™yau mai É—aukar hankalin mai kallonta.

     Duk da yasan ba wannan Æ™yawun bane ya ruÉ—i É—an uwansa ga sonta, amma shima ya taka rawar gani wajen jan hankalinsa gareta. Bayan sun kammala digirinsu na biyu suka dawo Nigeria kamar yanda mahaifinsu ya buÆ™ata. Dan yana bukatar suzo suyi aure. Koda suka iso suka huta babu wani jan rai iyayensu suka gabatar musu da matan aure. Shi Alhaji Kabir ya amsa da hannu biyu yay godiya dan dama baida ko budurwar. Amma Ahmad Æ™iri-Æ™iri yace shifa yanada matar aure. Hajiya iya ce ta fara nuna rashin yardarta akan hakan amma ya nuna bamai rabasa da Hindatu dan yana mata so mai zafin gaske. Gudun samun É“araka yasa Marigayi Alhaji Abdul-Mutallab zaunar da Hajiya Iya yaymata nasiha harta amince badan ranta yasoba.

       A take aka hau shirin biki, cikin kanÆ™anin lokaci komai ya kammala dan ana zuwa nemawa Ahmad auren Haindatu babu wani ja'inja aka bashi. Ansha biki na nunawa sa'a lokacin, dan Alhaji Abdul-Mutallab ya tara musu. Bayan biki duk aka kai amare garin Bauchi, harda Hindatu. Ƙyawawan halin Hindatu yasa Hajiya Iya ta fara sonta, sai kuma akazo dandanan ta samu ciki. Duk da Hindatu na karatu a jami'ar Turkey bata taÉ“a nuna Æ™orafinta nason komawa makarantaba. Tai shiru abinta har ALLAH ya sauketa lafiya ta haihu É—anta namiji da yaci suna Abdul-Mutallab. Amma saboda alkunya suke masa laÆ™ani da suna Adnan, Hajiya Iya kuma na kiransa Moddibo.

     Bayan haihuwarsa da kusan  watanni huÉ—u Ahmad ya buÆ™aci sake komawa Æ™asar Turkey dan cigaba da karatunsa. Sai dai a baÉ—ini wannan shirin Hindatu ne. Basu kawo komai a ransuba suka amince Ahmad ya É—auka Hindatu da dansu suka tafi Turkey saboda kowa yasanshi da matuÆ™ar son zurfi a karatu, shi kuma a lokacin matar Kabir ta fara laulayin nata cikin ita.

        Kamar wasa tun daga wannan tafiyar ganin Ahmad ya fara musu wahala. Dan ya samu aiki acanma ta dalilin mahaifin Hindatu. Sannu-sannu Æ´aÆ´a suka fara yawaita a wannan family, yayinda ALLAH yayma Alhaji Abdul-Mutallab rasuwa. Akan wannan rasuwa kuwa saida sukai yaÆ™i na gaske Ahmad yazo Nigeria. Inda a wannan zuwan nasane Hajiya Iya ta amshe Moddibo ko hakan zaisa Ahmad ya ringa tunawa dasu.

      Hakan kuwa yaso fara tasiri akan Ahmad É—in, saboda tsananin so da sukema Moddibo daga shi har Hindatu. Sai dai kuma yana kammala secondary daga tafiya karatu Æ™asar London aka sake samun matsala suka sake Æ™wace abinsu. ÆŠan dawowa da Ahmad É—in ya farayi garesu ta Æ™ara lalacewa. Sai dai Alhmdllh duk hutun duniya a Nigeria Moddibo keyinsa. Wannan ne ya É—an sanyaya ran Hajiya Iya. Amma duk da haka basu daina yaÆ™in son maido Ahmad jikinsu ba. A dalilin Adnan da shima rashin zuwan mahaifin nasa gida ke cin ransa suka sake dawo dashi cikinsu a shekarun nan, sai dai kuma suna murna an samu waraka shima sai Adnan É—in ya É—auke tasa Æ™afar gaba É—aya a dalilin aure da Hajiya iya ta matsa masayi.......

         Nannauyan numfashi Baffah ya sauke mai haÉ—e da ajiyar zuciya saboda fahimtar da yay tunaninsa yayi zurfi. A yanzu haka kuma ba tunanin abinda ya shuÉ—e bane mai muhimmanci garesa, a'a abinda zaizo shi ya kamata yay tunanin gyarawa kodan farin cikin mahaifiyarsa ma dasu kansu shi da Æ´ar uwarsa da zuri'arsu. Dan haka ya sake zurfafa a wani dogon tunanin da bai dawo hayyacinsaba sai a wani tsahon lokaci daya samo mafitar da yaji har a cikin ransa ya gamsu da ita sannan.


         ★★★★


   Washe gari daga sallar asuba ya zarto sashen Hajiya iya. Bayan ya zauna sun gaisa ya zayyane mata shawarar da ya yanke a wannan karon. Cikin jimami tace, “Amma Kabiru baka gani wannan shawarar tana kamanceceniya data baya kuwa?”.

        “Eh to Inna tana kama da ita. Sai dai akwai É—an banbanci da waccan É—in. Ki dai tayani addu'a, kuma ki Æ™ara nazari kema akan hakan mugani”. 

      “To shilenan. Ai ba'aÆ™i ta mutumba inji masu iya magana. ALLAH ya shige mana gaba”.

      “Amin ya rabbi Inna nagode. Ina mutuniyar takine banji motsintaba?”.

      “Oh kana maganar Zinneerah ne? Tana É—akin Moddibo tunda ba zuwa yakeba ita ai saita zauna. Dan nace ja'iran nan suzo su rinÆ™a tayata kwana harta saba wai tsoro sukeji sudai. taya zasu iya kwana É—akin Yayansu bayan kowa yasan dokarsa ba'a shigar masa É—aki sai da dalili mai Æ™arfi”.

       Dariya Baffah yayi yana faÉ—in, “Inna sunsan halinsa ba wasa yake dasuba ai Babana. Itama Zinneerah É—in dai gara a gyara mata wani karki haÉ—a rikici Inna”.

       “Oh to nima tsoron nasa nakeji kenanma ashe?. To yaci Æ™aniyarsa shida dokar tasa babu inda zataje. Idan yazo ni basai ya dakeniba mai bauÉ—aÉ—É—en halin tsiya irin na uwarsa”.

      Dariya Baffah ya mike yanayi shidai da faÉ—in, “Ai kunfi kusa Innata.  Wazai yarda ya shiga tsakaninki da Adnan da Khalipha a gidan nan”.

       “Aikam ni yanzu bana yayin wani Moddibo can. Garama Khalipha É—in duk da shima ja'irin kansane, daka É—akko laifin takwaran nasa zai fara karewa da yayansu kaza-kaza, saikace akansa aka fara É—an uwa”.

     Shi dai Baffah dariyarsa yaketa sha harya samu ya gudu domin zuwa yay shirin fita kasuwa.


       Lokacin da Hajiya iya kenan suna maganarsu da Baffah Zinneerah datai kwanan baÆ™unta a É—akin data fahinci mai shi mutum ne mai matuÆ™ar daraja da girma ga jama'ar gidan, dan su Meenal Æ™iri-Æ™iri sunÆ™i zaman ko mintuna goma a ciki, nacan ta shige cikin masu aikin Hajiya Iya tana tayasu aikin gyaran sashen. Lokacin da Baffah ya fito ya fice suna Kitchen domin haÉ—a breakfast kasancewar kullum anan Baffah ke karin kumallon safe tare da mahaifiyar tasa.

    Masu aikin sunso hanatayi amma taÆ™i. Dole suka barta saboda sunsan yaran gidan dama kan shiga ai aiki dasu suma bisa dokar Hajiya Iya. Amma da dan ta iyayensu matane kam da ba hakaba. Itako Hajiya Iya ta tsaya tsayin dakane domin taimakonsu tunda tasan gidan wani zasuje.

     Bayan sun kammala komai tsaf Baba Rahi tace taje tai wanka kafin Hajiya Iya ta fito dan batason Æ™azanta ko kaÉ—an. Shiyyasa kosu kansu idan baka saniba bazaka taÉ“a É—auka Æ´an aiki bane a gidanma sai an faÉ—a.............✍


No comments

Powered by Blogger.