Makauniyar Kaddara 15

 


Page 15*


...........Tunanin basusan mi zasu tarar a inda zasujeba Maman Sadiq ta yanke shawarar barma Zinneerah little a gida tunda yau bazataje Islamiyya ba, Alhaji yace saita warke. Su Abdul kam duk sun wuce makaranta dama. Sai da Mama ta jama Zinneerah dogon gargaɗi akan su Maman sakina sannan sukai mata sallama suka tafi. A tsakar gidanma sallama sukaima Maman Halima harma da Maman Sakinar duk da ba kulasu tai da ƙyau ba.

      Sai da Alhaji ya ɗauka hanyar barin anguwar tasu sannan ya kira wayar buba dazai musu kwatancen asibitin da Inno ke kwance a yanzu haka. Bayan sun gama wayarne ya ɗan duba Maman Sadiq dake a gefensa yana ajiye wayar. “To ashema asibitin da aka kwantar da ƴata Innon take”.

          Batare da kawo komai a raiba Maman Sadiq tai murmushi da bashi amsa, “Oh to abin yazo da sauƙi Alhmdllh. Dama inata tunanin karmu baka wahala musaka makarar zuwa kasuwa”.

      “Kenan saboda Inno takuce ku kaɗai?”.

     Yanda yay maganar cikin raha ya sakasu suma fara dariya suna faɗin, “A'a Yaya harda kai ai mana afuwa”.


       Sun iso *_SHIRA HOSPITAL_*. Alhaji ya kira Buba ya fito ya shiga dasu har ɗakin da aka kwantar da Inno ɗin. Wajene na musamman a cikin asibitin da iyalan family ɗin Shira ne kawai keda hurumin shigarsa koyin jiyya a wajen idan hakan ta kama. Wajen tsitt yake sosai babu wata hayaniyar komai. Gashi a gare tsaf duk da kuwa sun tadda mutane kusan shidda tare da Inno ɗin.

     Ɗakin da take ɗakine babba da komai na kulawar marasa lafiya wanda ko ƙasar ka bari iya abinda zaka iya zuwa ka tarar kenan acan ɗinma. 

       Inno ta tsufa sosai, sai dai ba irin tsufan nan da za'ace ta fita hayyacintaba. Dan tana gani ras tana kuma magana. Matsalarta kawai ciwon ƙafa dake damunta kasancewar ta mace mai jiki a da can. A yanzu hakanma bawai ramammiya baceba.

        Tunda sukai sallama a ɗakin kusan duk waɗanda ke a ciki suka zubo musu idanu suna mai amsa musu sallamar tasu. Tsohuwa mai ɗan yanayin kamanni da Inno, sai dai bata kaita tsufaba, sannan alamar jin daɗi fiye dana Inno ɗin ya bayyana a gareta ta tsaresu da idanu tamkar maison gano wani abu.

    Ganin duk sun tsargu da kallon da take musunne ya sata sakin murmushi da faɗin, “Wannan dai kamar Maryama idan idanun nawa na gani da ƙyau?”.

     Murmushi Gwaggo Maryama tayi a karo na farko, dan sai yanzune ta gane Hajiya Iya. Cike da girmamawa tace, “Nice Gwaggo. Tare da Yaya Hauwa da mijinta”.

           “Eh to naganki dai ke da na sani, sai kuma mijin nata zan masa na baƙunta, amma ita kam idona bai gantaba tunda itama nasan bason ganin nawa takeba kamar yanda bana tunanin tama sanni. Mutuniyar da aka sanarmin an bata adireshin inda nake a garin nan kusan shekara huɗu kenan amma bata nemeniba sai yau dalilin zuwan Inno, ai nikam banace nama santaba tunda dama canɗin ba sanin nata nayiba”.

        Sanin halin Hajiya Iya ya saka sauran mutanen ɗakin kowa yin murmushi harda Alhaji da Gwaggo Maryama. Maman Sadiq ma kanta a ƙasa take murmushin. Inda Hajiya Iya ke zaune kusa da Inno ta ƙara ta durƙusa akan gwiwoyinta tana faɗin, “A gafarceni Gwaggo. Nasan ni mai laifice amma dan ALLAH ina mai neman afuwarki”.

       “To zanɗan haƙura kaɗan idan mijinki ya sanarmin bashi da laifi wajen hanaki neman inda nake. Shi zuminci ai daɗine dashi koda na zaman anguwane balle ace na ɗan uwanka na jini. Uwa ɗaya uba ɗaya fa mahaifiyata suke da Inno, hasalima itace ta riƙe mahaifiyar tawa harta aurar da ita, dan itace ƴar zaman ɗakinta. Da hannunta ta raini mahaifiyarku har tsahon shekara huɗu kafin a aurar da ita. Amma ace yau ƴaƴan Hafsat na gudunmu saboda mahaifinku ya nisantamu daku a dalilin Hafsat bata raye a duniya”.

    Yanda ta ƙare maganar tana sharar hawaye ya saka ɗakin yin tsitt, itama Maman Sadiq sai hawayen suka shiga silalo mata saboda tinawa da mahifiyarsu da ALLAH yayma rasuwa tun suna yara. 

      “Kiyi haƙuri Gwaggo munyi kuskure. amma insha ALLAH zamu gyara, na tabbatar miki zamu gyara”. Alhaji ya faɗa cike da girmamawa.

     Gyalenta tasa ta sake share hawayen nata, sai kuma ta kalli Alhajin tana murmushi. “Shike nan ɗana ALLAH ya tabbatar da hakan. Tunda harkun gane kunyi kuskure na haƙura. Amma dan ALLAH ku gyara dan shi zuminci babban abune mai girma da ta silarsama za'a iya zuwa aljanna. Mu daina biyema sharrin sheɗan dana zamani zukatanmu nayin nisa da juna. Ina daɗi ace ƴaƴan Hafsat basusan inda nakeba saboda iyayenmu basa raye. Wajen gwaggo kawai kuke zuwa”.

        “Tabbas ba'a ƙyautaba Gwaggo. Amma dan ALLAH ayi haƙuri. Kamar yanda ya faɗa insha ALLAH zamu gyara. Wlhy zuwanma da kikaga banyiba nima rasa takardar da aka rubutamin adireshin da lambar wayar nayi. ALLAH kuma bai ƙaddara duk sanda na shigo bauchi na sake amsar wani adireshin ba a wajen Buba”.

        Hannu Hajiya Iya tasa ta kamo na Mman sadiq mai maganar, sai kuma ta kamo na Gwaggo Maryama duk ta haɗa cikin nata tana murmushi. “Ya wuce insha ALLAH, nima namuku hakane danku ƙara sanin muhimmancin zuminci, mu kuma sake dunƙulewa tsintsiya naɗaurinki ɗaya. ALLAH yayi muku albarka kuda zuri'arku damu baki ɗaya”.

     Cikin jin daɗi su mmn Sadiq suka amsa mata. Daga haka aka koma gaishe-gaishe kamar ba yanzu Hajiya Iya ta gama sharar ƙwalla ba.

     Sai da aka gama gaishe-gaishe da tambayar jikin Inno daketa kallonsu kawai dan ko magana bata iyayi amma tana jinsu. Hajiya Iya ta koma nuna musu sauran jama'ar ɗakin.

       “To ga ƴan uwanku nan nasan duk baku sansuba. Waɗan nan biyun matan yayanku ne. Waɗan nan kuma ƴaƴanku ne dukansu gasu nan. Badai zaku gane lissafinba anan sai munje gida”.

       Su mmn Sadiq dai murmushi sukeyi cike dajin ƙaunar ƴar tsohuwar, suka sake gaisawa da waɗanda ta nuna musun. Yanda suma babu alamun wulaƙanci a garesu yasaka jin farin ciki a zukatansu Mmn sadiq ɗin.

    Hajiya Iya ta nuna su mmn sadiq kuma garesu suma tana faɗin, “Ku kuma waɗannan ƙannenku za'ace kenan ko. Dan ƴaƴan Yaya Hafsat ne da ALLAH yayma rasuwa babbar ƴar Gwaggo da aure ya kai can Katsina, nasan dai bazaku gaza jin sunantaba a hirata ma. mahaifinsu ne bai barsu sakewa a cikinmuba tun suna kananu shiyyasa baku sansuba basu sankuba kuma. Amma insha ALLAH daga yau kowama zai sansu ɗin”.

     Duk suma amsa mata sukai da girmamawa dan babu mai jayayya da ita a kaf family ɗin harsu matan ƴaƴan nata. Sallama Alhaji yay musu ya tafi saboda ganin lokaci zai ƙure masa na kasuwa. ya wuce akan zai dawo anjima ya ɗaukesu idan ya taso.


      Sosai su Mmn Sadiq suka tsinci kansu cikin farin cikin kasancewa da dangin mahaifiyar tasu da suka gaza samun kusanta a lokacin ƙuruciya yanda ya kamata. Dan mahaifinsu baison kaisu su sake a cikinsu gudun karsu ƙwace masa su. Sukan dai je suga Inno naƴan kwanaki su dawo. Hakan yasa ko lokacin aurensu dangin mahaifiyarsu ba kowa yazoba dan haushin babansu. Su kuma bayan duk sunyi aure rashin sabon tun farko ya hanasu sakewa dasu, dan Inno kawai suka sani da wasu tsuraru a ciki.

        Babban abinda ya basu mamaki bai wuce yanda zuri'ar Hajiya Iya ke tururuwar zuwa asibitin duba jikin Inno ba. Saika rantse Hajiya Iya ɗince kwance ke jiyya. duk wanda yazo kuma saita masa bayaninsu suma sai ta musu bayaninsa. Alhmdllh kuma basuga raini ko wulaƙanci ga kowaba dukda kuwa sun shaida akwai kuɗi a wannan zuri'a kodan manya-manyan kulolin abincin da ake shigowa dasu na dubiya.

     Har dare suna a asibitin Inno bata wani san da zuwansuba saboda zafin ciwo, sai dai binsu da take da ido da kuma surarensu. Gashi kuma ɗiyar ƴar uwarta nata kaf-kaf da abunta gwanin sha'awa.

       Rigimar Hajiya Iya bata basu mamakiba sai da Alhaji ya dawo ɗaukarsu bayan ya taso kasuwa. Ta tubure akan babu inda zasuje gidanta zata wuce dasu su kwana dan asibitin Nurses ke kwana da Inno. Ana cikin wannan kicimilli babban ɗan Hajiya Iyan ya iso asibitin. Dawowarsa kenan daga tafiya ko gida bai shigaba ya wuto nan dan duba Gwaggo mahaifiyar tashi, shi kuma kakarsa.

       Tunda yay sallama cikin ɗakin Alhaji yay suman zaune. Akan laɓɓansa ya ambaci *_“Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira_* babbar magana”. 

     Alhaji Kabir Shira da baisan da zancen zucin Alhaji ba ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa duk da shekarunsa na girma ya kai har ƙasa duƙe yana gaisheta da tambayar mai jiki. 

      Amsa masa take da kulawa tare da tambayarsa yaya hanya?.

      “Alhamdulillahi innata. Ina fatan ana samun cigaban sauƙi a jikin Inno ɗin?. Dan tunda kika sanarmin halin da kuka sameta jiya da ƙyar nai barci. Inagama zuwa Laraba insha ALLAH kawai za'a wuce da ita India”.

      Cike dajin daɗi Hajiya iya ke jinjina kanta. “Wannan tunanin shine dai-dai Babangida. ALLAH yay maka albarka. jikin kam Alhmdllh dan bakamar jiya da muka baro Bauchi da ita ba. Amma dai nima nafi yarda da maganar zuwa india ɗinma a duba wannan ƙafar tata da ƙyau”.

       “Karki damu Innata, insha ALLAHU harma nayi magana da Bashir zai fara shirye-shiyen tafiyar daga daren yau ɗin nan”.

     Sai da ta jero masa addu'a sosai, sannan ta nuna masa su maman Sadiq dake gaisheshi. Bayan ya gama amsa gaisuwar yaransa da suma ke cike da ɗakin mazansu da matansu. Dan dolene kazo duba Inno saboda muhimmancinta ga Hajiya Iya.

       Da kulawa ya amsa musu yana sauraren bayanin mahaifiyar tasa. bayan ta gama ya miƙe tsaye yana bama Alhaji hannu da faɗin, “Lallai yau ina cike da farin ciki gani ga ƙannena da ban saniba suma basu sanniba kuma. Idonku kenan a gabanmu?”.

       Cike dajin kunya da mamakin sauƙin kansa tamkar mahaifiyarsa suka shiga bashi amsa. shiko kasancewarsa mutum ɗan boko kansa tsaye yake masu magana har Alhajin dake mamaki da al'ajabin dama Alhaji Kabir Shiran haka yake da sauƙin kai ashe? Bazaka taɓa cewa shahararren ɗan kasuwar nan bane mai faɗa aji a cikin kano da wajenta a gabansu haka ba. Dan ya saki jiki dasu sosai babu wani alamun girman kai ko raini duk da ya gansu talakawa kuma yaune ya fara sanin nasu.

      Sai da suka fito zasu tafi ne dan itama ashe isowarsa take jira su tafi gida tare yakejin zancen cewar ta hana su maman sadiq bin alhaji gida.

     Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana duban mahaifiyar tasa da jinjina rigimarta dason zuminci.

       “Innata ai ba'ayi hakaba. Nasan dai ƙannena bazasu rasa yara a gidaba. Dan haka kiyi haƙuri suje yau ɗaya su shiryo kamar zaifi”.

        “Uhm-uhm Babangida banyardaba. Salon suje suƙi dawowa tunda dama gudunmu sukeyi”.

      “A'a Inna baza'ayi hakaba insha ALLAH”. Mmn Sadiq ta faɗa da sauri.

     Sudai sauran jikokinta da suke asibitin dariya suketa kwasa a gefe sanin halin kakar tasu. Itafa indai akan zumincine bata da wasa. Shiyyasa su kansu suka tashi da wanan trianing ɗin nata kansu ke a haɗe bakajin wani fitina sai wadda ke a ɓoye dan ba'a rasataba musamman a tsakanin iyayensu mata.

     Da ƙyar dai Alhaji Kabir ya lallaɓa Hajiya Iya ta yarda akan su mmn sadiq su taho da shirinsu gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga haka Alhaji Kabir ya buɗe mata motar da aka kawosa da kansa ta shiga, shima ƴaƴansu suka buɗe masa yana ma su Alhaji sallama da jaddada ma su mmn sadiq su taho da ƙatuwar jakka dan sai Iya tasha ziyararsu ta more zasu koma gidajensu.

       d sukai masa dajin daɗin wannan karamci da suka samu daga manyan mutane da ada basu taɓa tunanin ganiba ido da ido sai gashi sun kasance jininsune ma ashe.


_______★★


         Sai da suka ɗauki hanyar gida ne cikin mamakin daya kasa sakin Abba har yanzun yace, “Nifa kaina a ɗaure yake har yanzu Hauwa'u. Wai dama kunsan familyn Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira sune ƴan uwanku ɗinnan da kika taɓa bani labari?”.

        Saurin kallonsa Mmn sadiq tai da mamaki itama tace, “Kabir Shira kuma yaya? Muko a ina zamu san Shira? Bashi baneba”.

       Ƙaramar dariya yayi saboda fahimtar itama dai da gaske batasan hakanba, ya kalli Maryama ta mirror “Maryama kema baki saniba kenan?”.

     “Wlhy Yaya ban saniba. Nadai san Gwaggo Aminan na anan cikin kano da iyalanta, kuma sunda arziƙi suma, sai dai bansan sune ake kira Shira ba koda wasa”.

       “Ikon ALLAH kenan. To aiko waɗanan dai sune Shira Family da ake faɗa a cikin kano da wajenta. Kuma kenan wanda yayma Abdull-Mutallab alkairi har yaci sunansa shima jininsu ne. Wata hikima sai UBANGIJI kenan”.

      “Gaskiya kam Yaya. Dan wannan UBANGIJI ne kawai mai kusanta abinda suka kasance makusanta batare da su kansu sun saniba. Amma wlhy ni harma na tsorata. Sai dai sun bani mamaki yanda sukasan darajar mutane”.

       “Ai babu wani abin tsoro Hauwa'u, sanin darajar mutane kam tarbiyyarsuce hakan daga mahaifiyarsu. ALLAH ya ƙara mana zuminci da sanin darajarsa”.

    Sun amsa da “Amin ya rabbi” dai-dai suna isowa gida. Bayan Alhaji yayi fakin a inda yake ajiye motarsa anan ƙofar gidan duk suka fito suka shiga dan ba'akai ga rufe gidanba da alama su ake jira.

    Ilai kuwa a tsakar gida suka iske Maman Halima zaune baiwar ALLAH. Ta tarbesu da sannu da zuwa tare da tambayar mai jikin?. Saida suka tsaya wajenta suma suka gaisa da sakejin lafiyar gidan sannan suka shige dan duk a gajiye suke.

     Yaran duk sunyi barci kamar yanda Maman Halima dama ta sanar musu. Sai Little ne kawai kecan wajenta shima bayan tafiyar tasu zazzaɓi ya rufesa ashe. Itama dai Zinneerah wuni tayi kwance sai yamma zazzaɓin ya saketa harta ɗan fita tsakar gida ta zauna dan Maman Sakina da yaranta basu yini a gidanba.

      Wanka kawai sukai suka nema makwanci tunda a ƙoshe suke.


        Washe gari tunda safe Alhaji ya samu kira daga Alhaji Kabir Shira daya amsa lambar hannun Buba. Da farkoma bai gane mai maganaba sai da yay masa bayani. Cikin ɗan rikicewa Abban ya shiga gaishesa dan zai iya girmarsa ma ko'a shekaru. Sai kuma yanda yaji muryarsa ya sake rikitashi.

      Daga can Alhaji Kabir ya sanarma Abba ALLAH yayma Inno rasuwa tun asubahin yau, yanzu haka ga gawarta zasu ɗauka zuwa can gidan, sai suyi ƙoƙari suzo ayi jana'izarta dasu.

      “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Abba keta faman ambata dukkan gaɓɓansa na saki lokaci guda. Da ƙyar ya iya fitowa zuwa sashen Mmn Sadiq ɗin yace musu su shirya zasuje asibiti. Sosai hakan ya basu mamaki, sai dai ganin bai basu fuskar da zasu tambaya ba ya sakasu yin shiru gabansu na faɗuwa. Dan sunaji a jikinsu lallai babu lafiya.


     Yau ɗinma dai haka suka shirya suka tafi su biyu kawai ko little ba'aje da shiba sabboda baijin daɗi. Zinneerah dai gara ita da sauƙi jikinta ba kamar jiyaba.

    Kasancewar gidan Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira ba ɓoyayye bane a birnin na kano kai tsaye Abba ya nufi can dasu bayan ya kira Buba kawai ya tambayi anguwar.

     Gidane katafare sosai, duk da kuwa gidajen anguwar ma babu ƙaramin gida. Kasancewar Buba ya fito gate ya saka suka samu damar shiga babu wani gargada dan mutane basu kai ga fara isowaba. Ruɗanin mutuwar da suka samu ya hanasu damuwa ko tsayawa duban yaya gidan yake, balle tsarinsa.  

     Kukan Hajiya Iya ya matuƙar sake tada hankalin kowa dake a gidan matuƙa. Su Mmn Sadiq kam ai ba'a magana dan suna tsananin so da ƙaunar kakar tasu, musamman daya kasance ita suka tashi suke gani tamkar mahaifiya a garesu tunda sun rasa tasu tun basusan kansuba.


       Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, dan ba'a binne Inno ba sai da tawagar ƴan bauchi ta iso. Inno uwace kuma kaka da wannan family bazasu taɓa mantawa da alkairan data ginasu a kaiba. To yau dai gashi ta tafi ta barsu da kewa da kuma alkairin data bari baya garesu. Dama ita kaɗai ta rage musu cikin iyaye. To ya rage nasu subi bayan nata da addu'a batare da gazawa ko ƙosawaba.

     (Ya rabbi kasa mu kasance cikin bayinka masu barinma bayanmu tarin alkairi ba sharriba. ALLAH yasa ranar barinmu duniya ta zama ranar farin ciki a garemu😭🙏🏻, ALLAH ka gafartama iyayenmu da bayin ALLAHn da suka rigamu tafiya badan sunyi gaggawaba🙏🏻😭).

    A ranar dai dole su Maman Sadiq anan gidan suka kwana. Yanda manyan mutane keta shigowa gaisuwa sai kasha mamaki da tabbatar da lallai Inno nada matuƙar daraja ga Hajiya Iya. Dan dukkan ahalinta suna ɗaukartane kakarsune uwa ga Hajaiya Iya, hakan yasa dukan harkokinsu suka tsaya cak harna tsahon kwanaki uku da aka amshi gaisuwa. Sai a ranar cikon ta huɗu ne ƴan Bauchi da suka rage suka koma gida, hakama sauran dangi dake wasu garuruwa kowa ya kama gabansa.

    Suma su mmn sadiq shirin komawa gidan sukeyi yau dan harma sunyi waya da Abba akan zuwa anjima zaizo ya ɗaukesu insha ALLAH. Shima dai kwanakin nan uku kullum sai yazo gidan wajen amsar gaisuwa, hakama mijin Gwaggo Maryama yazo harda ƴaƴanta biyu maza duk da ƙananune, amma a ranar suka koma.

      Da ƙyar Hajiya Iya ta aminta da komawar tasu, sai dai ta musu dogon sharaɗi da gargaɗin wannan karon bazata yarda da sakaci da zuminciba. dan su kaɗaine jinin inno mafi kusanci da suka rage a yanzu. Dama Inno bata wani haihu da yawaba. Yaranta biyune kacal a duniya, mahaifiyarsu sai mahaifin Buba. Kuma duk ALLAH yay musu rasuwa, shima Buba shi kaɗaine namiji a wajen mahaifinsa sai ƙannensa mata biyu duk sunyi aure anan Bauchi. Suma kuma sai da Hajiya Iya taja musu dogon gargaɗin kafin su wuce da safe. Sai su kuma su Mmn Sadiq ɗin da suka kasance suma su biyu kawai.

     Sun mata alƙawarin kulawa insha ALLAH a wannan karon. Da wannan yasa ta amince su koma gida ɗin dan Gwaggo Maryama ma da anyi bakwai zata wuce duk da ba taro zasuyiba, amma tace zata sake dawowa nan gidan taima Hajiya Iya sallama.

     Sai kusan biyar na yamma Abba ya iso tare da su Sadiq da Mama batasan dasu zaizo ba. Amma hakan da yay ya sakata jin daɗi matuƙa kamar yanda Hajiya Iya ma ta nuna jin daɗinta sosai. 

     Har ƙasa su Zinneerah suka kai suna gaisheta da mata gaisuwa. Cikin jin daɗi ta kamo hannun Zinneerah ta zaunar kusa da ita tare da Aliyu. Suma su Sadiq tace su matso gareta.

      “Ikon ALLAH, nan ai Inno ce kamar an tsaga kara an karya”. Hajiya Iya tai maganar tana nuna Zinneerah da kanta ke a ƙasa.

     Sauran dake ɗakin suma suka shiga faɗin albarkacin bakinsu akan tsananin kamanni da Zinneerah ɗin keyi da marigayiya Inno. Dan duk wanda yasan Inno yaga Zinneerah yasan jinintace. Gashima ita Zinneerah ɗin ba saninta tayiba.

     Hajiya Iya ta ƙara damƙe hannun Zinneerah dake cikin nata tana faɗin, “Lallai akwaiki da karambani, duk iyayenki damu kakanni kika tsallake sai kammanin Inno kika kwaso. Inno ta tafi ta barni ga ALLAH ya sake bani Inno a kusa dani dan na ƙwace”.

      Kusan kowa dake falon sai da murmushi ya suɓuce masa. Yayinda kuma duk suka fahimci Hajiya Iya na nufin zata amshe Zinneerah kenan ta dawo hannunta. Hakan yasaka gaban Mmn Sadiq faɗuwa, amma sai ta dake dan ba wajen da zata iya jayayya bane balle musu............✍



🤣😂Tofa, yau naga ƙarfin hali wajen wagga tsohuwa.


No comments

Powered by Blogger.