Makauniyar Kaddara 12


 Page 12*


.........Iya ruɗewa Maman Halima ta ruɗe. Tun tana leƙe-leƙe ita kaɗai harta nufi reception ta sanarma wanda ke zaune a wajen shi da wata budurwa. Ganin yanda take a rikice suka shiga tambayarta ko lafiya?.

      “Inafa lafiya bayin ALLAH, ina salla wani ya shigo ya ɗauke jaririnmu. Dan ALLAH ku taimakeni na shiga uku”.

        “Kinga mama kwantar da hankalinki, mu anan ba'a wannan dan asibitine dake tare da tsaro ta ko ina da kike gani” saurayin ya faɗa da sauri yana mikewa.

       Katsesa Maman Halima tai, “Wane tsarofa anan yaro, inda da tsaro a shigo a ɗauki Jariri har cikin ɗaki? Ku taimakeni yaron nan ko uwarsa da tasha wahalar haihuwarsa bata dawo hayyacintaba, balle tasan mita haifa”.

      Ganin bata cikin hayyacinta budurwar ta fito a inda suke a killace tana faɗin, “Mama dan ALLAH ki taimakemu ki nutsu, boss yana cikin asibitin nan karki ja mana matsala dan girman ALLAH”.

     Sam Maman Halima ba saurarensu takeba, saima hankalin mutane data fara jawowa kansu saboda kwakwazonta. A wannan yanayi Maman Sadiq da Alhaji da Maman Sakina data biyosu yau saboda cin mutuncin da Alhajin ya mata suka iso. Jin abinda ya farune ya saka hankalinsu suma tashi, sai dai kafin suce wani abu sai ga Nurse Salima ɗauke da jaririn a hannu tana faɗin, “Wannan taron lafiya kuwa?”.

     Yanda taɗanyi maganar da ƙarfine ya saka yawancin mutanen wajen juyawa suna dubanta. Kafinma wani ya bata amsa idon maman Halima ya sauka akan jinjirin, hakan yasata kwasa da gudu gaban Salima tana faɗin, “Ya ilahi, to aiga yaron ma anan”.

       Kusan duk saida jama'ar wajen suka sauke numfashi. Saurayi da budurwar nan dake a reception sukace, “Mama abinda muke sanar miki kenan, amma kika gaza fahimta. Mudai munsan babu yanda za'ai mutum ya bata a asibitin nan”.

      Salima data ɗan fahimci zancen tai ƙaramar dariya tana faɗin, “Kai mama wai kin ɗauka sacesa akai?. Asibitin nan yanada matuƙar tsaro fiye da yanda kike zato. Oga ne da kansa yazo gittawa zaije office ɗin Dr Mahmud yaji kukansa, shinefa ya shiga ɗakin danya duba. Sai ya samu kina salla shine ya ɗaukesa ya fita da shi. Yanzu na shiga wajen Dr Mahmud shine ya bani shi da faɗamin lambar ɗakin daya ɗakkosa. gashi ma yace a bashi wannan”. Ta ƙare maganar da miƙa ma mama wata ƴar takarda dake a linke da alamu suka nuna cheque ne na kuɗi.

        Takardar Mama ta amsa batare data fahimci ta minene ba, yayinda su kuma mutanen wajen suka sami damar yin dariyar yanda ta ruɗe musu ɗazun.

       Mama ma dasu Alhaji duk dariyar sukeyi, daga haka suka ɗunguma ɗakin da aka kwantar da Zinneerah. Mamaki ya kama Mama ganin ashema ta farka har likitan daya shigo ɗakin dubata yana ɗan musu faɗa akan fita su barta ita kaɗai haka.

     Haƙuri mama ta bashi, tare da masa bayanin dalilin fitar tata. Ya ɗan murmusa yana faɗin, “A mama ai asibitin nan akwai tsaro sosai, motsin kowa dake ciki ana ganinsa ta cctv, dan haka ku kwantar da hankalinku babu abinda zai faru harku tafi insha ALLAH”.

       “ALLAH yasa hakan” suka faɗa kusan a tare.

       “Amin ya rabbi. Yanzu ga wannan, shine list ɗin komai na kuɗaɗen da zaku biya, sai kuma jini da zaku samo yanzu dan za'a ƙara mata. Dama jiran farkowarta muke mugani koda yuwuwar hakan, to yanzu kam naga alamar tana buƙatar jini leda ɗaya”.

     Amsar takardar Alhaji yayi yana masa godiya, daga haka Doctor ya fice. Gaban gadon suma duk suka ƙarasa sunama Zinneerah sannu, da kai kawai take iya amsa musu batare data iya kallonsu ba. Sai faman haɗiyar zuciya take dan ita kaɗai tasan mitakeji a ranta. Ganin kamar batason hayaniyar ne ya saka Nurse Salima dake ɗauke da ɗan jinjirin daya gama shige mata rai har yanzu faɗin, “Inaga batason yawan hayaniya yanzu, idan kun gama dubata sai muɗan fita waje a bata waje”.

     Gamsuwa da bayaninta ya sakasu amsa mata. Mama ta kalli Salimar tana faɗin, “Yauwa ƴarnan kinma sa na tuna. Ina dabinon da kika bada shawarar a tauna a bashi? Kinga yanzu tunda ga Alhaji sai ya bashi ɗin ko”.

       Cikin ɗan nuna shakku Salima tace, “Aiko mama na muku laifi ko nace shishshigi, nazo da dabinon danna kawo mikine na biya office ɗin Dr Mahmud ɗin inda na sami Oga acan. To daya sanar min ɗakin da zan kawo yaron sai nake cewa dama can zani nakai dabino a bashi ko zai rage kukan yunwar da yakeyi. Jin hakan da kuma kukan da yaron keyi har lokacinne ya saka Oga ya amshi dabinon da kansa ya tauna ya bashi, har yana faɗin ALLAH yasa ya gaji sunansa”.

       Alhaji dake saurarensu yace, “To masha ALLAH, ALLAH ya saka masa da alkairi duk da mu bamusan shi wanene ba”.

      Salima tace, “Baba ai shine mai asibitin nan”.

        Dukansu sai da suka ɗan ƙwalalo idanu waje. Mama tace, “Babbar magana, shima likitanne kenan?”.

      “A'a mama, shi ba likita baneba, ɗan kasuwane. Nasan dai bazaku gaza sani kojin sunan *_AK SHIRA_* ba a garin nan ai”.

         “Lallai kam sani bana wasaba, duk da dai ba sani na zahiri bane, amma wannan sunan ba ɓoyayyen suna bane, dan a Shira Family kowa yasan *AK SHIRA* ba ɓoyayye bane, kodan gidajen mansa kawai ai sun isa ka sanshi, balle kuma hidimar da yake ga bayin ALLAH mara iyaka”.

       “To aiko Baba shine da kansa ya bama jaririn nan dabino yau, tare da wannan takarda da nake kautata zaton kuɗine rubuce a ciki”.

     Sosai maganar ta sake girgizasu, mama ta mikama Alhaji takardar cheque ɗin. Amsa yay ya duba yana jinjina kansa. “Uhm lallai wani aiki kam sai manya. ALLAH ya saka masa da alkairi. ya azurtashi da duk alkairan duniya da lahira, ya kuma cigaba da karesa a duk inda ya saka ƙafa. Kuɗine zunzurutu harna dubu ɗari biyu ya rubuta anan”.

     Sosai suka ƙara jin mamakinsa, ace lokaci guda mutum yay ƙyautar dubu ɗari biyu wa jariri kawai. Alhaji ya katse zantukan nasu da faɗin, “To lallai kam abokina dole kaci sunan AK Shira ai”.

     Dariya duk sukayi banda Maman Sadiq datai ɗan murmushin kawaici. Hakama Zinneerah dake saurarensu kawai tana share hawayenta a ɓoye.

     Alhaji ya buƙaci Salima ta rakashi yaymasa godiya, daga nan yaje wajen neman jinin da biyan kuɗaɗen da sukace. Bata musaba ta miƙama Mama jaririn suka fita. Office ɗin Dr Mahmud sukaje. Bayan Salima tai knocking ya basu izinin shiga suka shigo.

         Shi kaɗaine a ciki, sai dai mayen ƙamshinsa na nan manne da office ɗin duk da babu shi a ciki. Dr Mahmud yace, “Salima lafiya dai?”.

     “Laya ƙalau Doctor, dama Baba ne yace na rakosa yayma Oga godiya. Sune masu jinjirin nan na ɗazun”.

      “Oh ALLAH sarki, Baba ina yini”.

“Lafiya lau likita, ya aikin naku?”.

     “Alhmdllh baba. Sai dai gashi kuma shi harya tafi, kasan shi uziri ba ƙaremasa yakeba. Dama yakan zo duk irin wannan ranar a tsakkiyar shekara da ƙarshenta ne ya bada jini inhar yana kano, yanzu hakama zaije Lagos ne ya biyo tanan ya bayar, ina ƙyautata zaton yanzu haka ya isa airport”.

      Alhaji yace, “Ashsha. Naso kam na gansa nai masa godiya wlhy, sannan ya cika ladansa nama yaron nan huɗuba ya kuma saka masa sunan nasa dan ya cancanta”.

       Cikin jin daɗin wannan karamci Mahmud yace masha ALLAH, shi da ya faɗa da wasa ashe ALLAH ya amsa mai sunan nasa aka samu, duk da nasan yanzu yayi nisan kiwo, amma bara na taɓasa a waya muji ko zamu samu ya ɗaga baba ka zauna”.

      Zama Alhaji yayi yana murmushi. Dr Mahmud ya ɗauka wayarsa shima fuska ɗauke da murmushi ya shiga kiransa. Tana gab da tsinkewa aka ɗaga. Harma Mahmud ya fidda ran hakan. Cike da zumuɗi Mahmud yace, “Afuwan ranka ya daɗe kaga na kiraka”.

     Basusan amsar da aka bashi daga canba. Cikin ƴar dariya yace, “Tona gode ranka ya daɗe. Dama masu jaririn daka ɗakko ɗin nan ne sukazo maka godiya, tare da sake kawosa ka cika ladanja ta masa huɗuba da saka masa sunan naka”.

    Nanma basuji miya faɗaba, sai dai yanda fuskar Dr Mahmud ta ƙara washewa da fara'a zaka tabbatar da magana mai daɗi yake masa. Sai kuma ya saka wayar a amsa kuwwa (Hansfree) ya ajiye gaban Alhaji. 

         Wata tattausar murya mai cike da tarin nutsuwa kamar ta rowa sukaji tace, “Assalamu alaikum, baba barka da rana”.

       Da sauri Alhaji yace, “Wa'alaikissalam, barka dai ranka ya daɗe, yaya ƙoƙari?”.

     “Alhmdllhi baba. Yanzun nakejin daddaɗan albishir na samun takwara, gashi kuma nayi gaggawar tafiya”. 

     Yanda yake maganar cike da nutsuwa kamar bayasone ya saka Alhaji yin murmushi mai faɗi. “Alhaji ai kowa zaiso samun mai sunanka a gidansa kodan tarin alkairan dake tattare dakai. Munga hidima ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara buɗi. Amma naso ace kaine da kanka kaima yaron nan huɗuba da sunan daka zaɓa masa”.

      Kaɗan sukajiyo sautin murmushinsa daga can, cikin sake nutsar da muryar tasa mai sauti a tausashe yace. “Nima naso hakan Baba, dan kun bani abu mai daraja da bazan mantaba a tarihin rayuwata, amma duk da haka na bama Mahmud wakilcin yima takwarana huɗuba. ALLAH ya rayasa ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa ya zama mai tausayinmu da jin ƙanmu anan gaba”.

          Atare suka amsa da amin kowa cikin jin daɗi. Musamman ma Alhaji dake mamakin yau shine ke magana da AK Shira baki da baki ta waya. Wata hikima sai UBANGIJI. Shikam dai har abada bazai taɓa mantawa da haihuwar wannan yaro ba a rayuwarsa.


      Kamar yanda ya bada wakilci ga Dr Mahmud hakance ta faru, dan har ɗakin da aka kwantar da Zinneerah Dr Mahmud yaje yayma yaro huɗuba. Ya kuma ajiye kuɗi dubu hamsin shima yace asai rago a yankama takwaran abokinsa, kuma ogansa ranar suna.

      Shima sun masa godiya sosai, kowa na jinjinawa a ransa yaro yazo da farin jini. yayinda Maman Sakina keta taɓe baki a kaikaice, a ranta kuwa tana ganin tsabar iya asirine na ƴan ƙauye kuma Katsinawa da kullum take ambata ga maman Sadiq.

          Tare Alhaji suka fita da Dr Mahmud. Sai bayan kusan mintuna talatin ya dawo ɗauke da madaidaicin kwali da aka zubo masa magungunan da Doctor yace su sayo da drips, sai jini leda ɗaya. Kwalin Maman Sadiq ta amsa takai ɗakin dan sun fito waje. Tana fitowane yake faɗin, “Wani iko sai ALLAH, kunga jininma da naje nema a lab ɗin nasu saina samu bawan ALLAHn nan ya bada nasa a ajiye idan masu bukata sunzo nema. Cikin ikon ALLAH sai gashi ni na fara zuwa kuma. Gashi sun bada ƙyauta babu ko sule”.

      Cikin riƙe haɓa Maman Sakina da hassada kecin ranta tace, “Oh har jini yake zuwa ya badar a asibitin kuma? Dan tsabar jin daɗi irin na masu arziƙi”.

     Alhaji ya bata amsa da cewar, “Wlhy kin gani dai, dama likitan daya kira mani shi a waya yace jinin yazo badawa kawai shiyyasa bai jimaba ya tafi”.

        Sudai su Maman Sadiq godiya suka sakeyi da jera masa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya.


★★★


         Sai yamma Zinneerah ta farka sosai cikin hayyacinta, bayan an cire mata jinin da aka gama ƙara mata. Bayan likita ya shigo ya fita suma su Maman Sadiq suka shiga. Zaune suka isketa jingine da filo ta zubama yaron dake gefenta yana barci ido. A zahiri shi take kallo, amma idan ka nutsu kaima a kallonta zaka fahimci sam batama tare da duniyar mutane gaba ɗaya. Dan yaron kuka yake iya iyawarsa amma da alama ba jinsa takeba.

     Matar Naziru ce tasa hannu ta ɗauki yaron tana faɗin, “Haba Zinneerah, yaro na kuka ke kuma kin tsaya kallonsa kawai”.

     Nan ɗinma ba jinta tai ba. Sai da Maman Halima ta taɓata sannan ta kawo numfashi. “Oh ni Binta, mi kike tunani haka Zinneerah?”.

    Maman Halima ta faɗa tana tsatstsareta da idanu. Ƙasa kawai Zinneerah tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye kukan daya tokare mata ƙirji tun ɗazun. Matar Naziru dake jijjiga yaron dai yay shiru tace, “Haba Zinneerah ai yanzu ba lokacin kuka bane, lokacibe da zamu taru mugodema ALLAH ne. Jiya iyanzu muna nan cikin tsananin tashin hankali da fargabar rasaki, amma cikin amincin UBANGIJI yau gaki zaune da ƙyauta mai girma da wasu kecan suna bulayin nema da kuɗi amma ALLAH bai ƙaddara samuwarta garesuba. Kiyi haƙuri kibar kukan nan, mu yanzu babban fatanmu kuma ALLAH ya baki lafiya mu koma gida”.

       “Maganarki kam gaskiyace Maman Abu. Zinneerah yanzu lokacine na godiya ga ALLAH kinji. ALLAH ya ƙara miki lafiya. Kinga yaron nanma ya kamata a bashi abincinsa dan wannan kukan bana komai bane sai na yunwa, tunda likita yace zaki iya ɗan gwada bashi yanzu sai a gwada ɗin ai ko”.

       Sake fashewa da kuka Zinneerah tayi, dan ita kaɗai tasan yanda takeji a ranta akan wannan al'amari mai rikitarwa da matuƙar ruɗani. Tunda take bata taɓajin labari irin nataba. Tayaya zaka haifi ɗa na mutum batare da kasan yanda ka samu cikinsa ba. Anya kuwa yaron nan baɗan wani aljanin baneba?......

      Shigowar Alhaji da Maman Sadiq da gayyar yaran gidan gaba ɗaya har da ƴaƴan Maman Sakina ya katse mata tunani. A take kuma ɗakin ya kaure da hayaniyar yaran. Dan bayan sun mata yaya jiki gaba ɗaya hankalinsu suka maida ga ɗan jinjirin suna yaba ƙyawun da ALLAH yay masa. Sai da Maman Halima taga kukansa na ƙara ƙarfine ta amsheshi cikin tilastawa suka saka Zinneerah bashi abincinsa tanata kuka.

      Alhaji da Maman Sadiq ne kawai suka iya fahimtar kukan Zinneerah saboda sune sukasan labarin tushen samuwar yaron. Dan ita kanta maman Sadiq konawarsu gida tasha kuka, a yanzu hakanma kukan zuci takeyi. Su Maman Halima kuwa da basusan dawan garinba sai tunaninsu ke basu Zinneerah tana kukane saboda tunawa da mahaifin yaron da akace rasuwa yayi.

     Da ƙyar aka samu ta bari yaɗan kama na wasu mintuna. Dan kuka take sosai tana yarfa hannu wai zafi. Maman Halima ta ɗaukesa tana mata faɗa akan karta sakama ranta fargabar tsotso dan yaron nan daga gani ba wasa zaiyi da cikinsaba. Ita dai Zinneerah zamewa ma tai ta kwanta a hankali tana matse baki dan inda aka yankata na mata ciwo sosai har yanzun.

      Sun daɗe a asibitin yaran na cigaba da jagwalgwala yaron da aka samu yay shiru, yayinda Zinneerah ke kwance shiru bata sake kula kowa ba. Idonta a lumshe suke tana zirar da hawaye ta gefensu, yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake manne da jikin showal ɗin yaron da batan a ina ya kwasoshi ba.

       Ƴar hayaniyar yarance ta saka Doctor shigowa ɗakin yace suyi haƙuri a barta ta huta hakanan, ya kuma bada damar a bata abu mara nauyi tasha, kamar shayi ko kunu haka. Godiya sukai masa ya fice. Alhaji kuma ya tattara iyalansa shima sukai musu sai da safe suka tafi. Aka barta daga ita sai Maman Halina dake haɗa mata kunun da akace zata iya sha ɗin.


_____________★


        Haka Zinneerah ta cigaba da jiyya a asibiti. yayinda abokan arziƙin Maman Sadiq na anguwa da dangi ɗai-ɗai dake anan suke ɗan shigowa dubata. Kulawa da take samu na abinci ya saka komai yake tafiya kan tsari Alhmdllh. Dan jikinta yayi ƙyau sosai a kwanki shidan data ɗauka a asibitin. Idanma ba'a faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Sai dai sam babu mai ganin walwalarta, sannan ko kallo yaron bai ishetaba sai Maman Halima ta mata jan ido.

     Matsalar da suke fuskanta da yaron kawai shine idan yasha nono cikinsa sai ya kumbura yayta kuka. Da farko basu fahimci hakanba sai suke ɗauka cibiyarsa ne ke ciwon. Sai daga baya Doctor ya gane inda matsalar take. Dan haka ya dakatar da Zinneerah daga bama yaron nonon gudun kar a cutar da yaron kuma. Sai dai sun ɗorata akan magani zuwa wani lokaci sai ta cigaba da shayar da shi. shi kuma yaron suka bada shawarar a ringa bashi madara.

      Hakan yama Zinneerah daɗi, dan a shirementa ayyanawa take a ranta ta huta da ciyar da ɗan aljanu, dan har cikin ranta ta yarda aljanune sukai mata ajiyar yaron kawai a cikinta.

     Babu wanda yasan da wannan shirmen nata, sai dai ranar tsabar jin daɗi har ɗan sakin jikinta tai sukai hira da Maman halima da ada take danganta rashin walwalar Zinneerah ɗin da rashin ƙarfin jiki.


       Washe gari Alhaji ya sayi raguna biyu aka raɗama yaro suna Abdul-Mutallaf a masallaci, wato dai takwaran AK Shira kenan kamar yanda akai masa huɗuba. Ba ayi wani shagaliba kasancewar mai jego na asibiti, sai dai maman Sadiq tayi abinci ta bada sadaka ko zata samu sassauci a ranta da nutsuwar rugumar wannan ƙaddara a garesu.

        Da yamma da sukazo dubasu a asibiti Alhaji yake sanarma Maman Halima cewar yaro yaci suna Abdul-Mutallaf. 

     Cike da murnarta da farinciki taita jera addu'a ga jariri tana tsokanarsa. Zinneerah kam ko motsi bataiba balle ta nuna taji sunan da yaron yaci. Sai dai tausayinsu da takeyi akan sunatama ɗan aljanu hidima batare da sun saniba. Ta tabbata wataran sai aljanin daya ajiye mata ɗan yazo ya ɗauke ɗansa batarema dasun saniba zasu gane wahalar banza sukayi. Babu wanda ya damu da rashin tankawar tata. Garama maman halima taɗan mata faɗa kamar yanda ta saba idan taga tana share yaron. Shiru dai tai batace komaiba kamar kullum, sai hawayen data share a ɓoye duk da ita Maman Sadiq na lure da ita.


         Ganin komai normal ta samu lafiya Alhmdllh washe gari aka basu sallama. tare da basu ranakun da zasu dawo domin duba lafiyarta. Daɗi sosai Zinneerah taji da wannan sallama. dama ba ƙaramin gundura tayi da zaman asibitinba.

        Koda suka dawo gida sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba daga yaran gidan, dan harda ƴaƴan Maman Halima na ma'auri duk sunzo gidan tarbarsu, dama duk sai da sukaje asibiti anan nema Zinneerah ta fara saninsu. Amma yanda suka karɓeta saika ɗauka a cikinsu ta tashi itama.

     Yau ɗinma tararwa sukai sun haɗa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafa iya su kawai ƴan cikin gidan, sai ƴaƴan Naziru da matarsa da maƙwafta na kusa da ake gaiswar mutunci. Kowa yayi mamaki dan babu wanda yasan da wannan shirin nasu. Maman Sadiq zata hana Alhaji ya hanata akan kartace komai, dan sudai basusan komaiba akan wannan haihuwa ba. Sannan kosu ɗin da suka sani ai Zinneerah batasan sun saniba. Su daure su ƙarfafa farincikinta har lokacin da za'aje gaɓar da tuhumarta zatai musu amfani, kuma dalilin hanyar samuwar ɗan bazaisa su toshe hanyoyin karɓar ƙaddarar da yazo a cikintaba, da har zasu ƙi farinciki ko nuna godiyarsu ga ALLAH.

      Badan tasoba ta haƙura ta zuba idanu itama. 

     Ita dai Zinneerah bata nuna wani alamun damuwa da hakanba, dan tunda suka shigo gidan Maman Halima tai mata gashi na musamman a jikinta sai ta samu nutsuwa sosai, aka kawo mata abinci kuma taci ta ƙoshi tasha magani sai barci. Sai gashi har suka gama walinarsu ita bama tasan wace waina suke toyawaba, sai bayan ta tashine su Aunty Halima suka shigo sukai mata sallama zasy wuce gida dan lokacin anyi sallar isha'i.

       Yanda suke nuna mata so da ƙauna su da mahaifiyarsu yasa itama take sakin jiki dasu sosai, kuma tanajinsu tamkar yayunta, dansun maye mata gurbin su Yaya Gajejen ta.............✍

      

No comments

Powered by Blogger.