Makauniyar Kaddara 10

 


*Page 10*


............Tunda suka iso gidan Zinneerah keta kalle-kalle. Basai an faɗaba a ganin gidanma kasan mahaifiyar tata yanzu kam tai gaba, kuma tana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Bawai ƙaton gida baneba irin na masu kuɗi, babbane dai kam amma gini irin na mai rufin asirin ALLAH. Dan da Alhaji

Bashir Ɗanmusa kam yayi kuɗi sosai, sai dai daga baya ya fuskanci ƙalubalen karayar arziƙi, tun daga nan ne dai har yanzu bai koma yanda yake daba, amma ko a hakan Alhmdllh dan yana iya ɗaukar nauyin komai na gidansa harma ya taimakawa ƴan uwa da maƙwafta. Hatta da motar da Nasiru keja a yanzu haka shine ya siya masa ita. Sannan duka ƴaƴansa suna karatu gwargwadon ƙarfinsa danshi mutumne maison ganin zuri'arsa ta samu ilimin addini dana zamani.

        Zinneerah ta samu tarba maiba mamaki a gidan na kawunta, kuma mijin mamanta. Hakama yaran gidan duk da ba saninsu tayiba suma basu santaba sunzo sun zagayeta sunata kallo. Bata wani sake da kowa ba dan har yanzun damuwar tafiyar Khalipha bata saketa ba. Tanajin raɗaɗi da zafi a ranta wanda ita kanta batasan dalili ba.

      Duk da a yanayin da take na rashin sakin jiki hakan bai hana Mama Sadiq nuna zumuɗin ganintaba, danma tana ɗan kawaicine wa Maman Halima kasancewar Zinneerah ƴar fari ce, sannan kuma yanda Maman Haliman ke nuna kara ma ta cancanci a ɗaga mata ƙafa ai. A yanzu hakama duk da tare suka dawo a ɗakinta ta sauketa. Sai dai an kawo kayan Zinneerah ɗakin Maman Sadiq ɗin alamar anan zata zauna.

       Da ƙyar Maman Halima ta lallaɓa Zinneerah taci abincin da Maman Sadiq ɗin ta tarbesu da shi, bayan ta ɗan tsatstsakura aka kaita tai wanka, tare da bata kaya sabbi fil da Maman Sadiq ɗin ta ɗiɗɗinka mata a ƴan kwanakin nan gudun kar'a sallamosu tazo babu sitirar da zata saka, dan a yanzu haka gidan nasu ƴammatan dake sa'annin Zinneerah duk ƴaƴan Saude ne, Saude kam ba bari zatai su bama Zinneerah kayaba, ballema yaran suma sun rigada sun haddace karatun uwarsu suma kishi suke da su, danma sunajin tsoron ubanne, suma kansu su Maman Sadiq ɗin kuma basu basu fuskar rainiba suna ɗan shakkarsu.

         A zahiri Maman Sadiq cike take da murnar kusantowar ɗiyar tata kusa da ita duk da batasan dalilin barowarta gidaba har yanzun. sai dai ƙasan ranta cike yake da fargabar yanda Zinneerah taƙi sakin jikinta ita. Haka dai ta daure ta danne damuwarta a ƙasan zuciyarta bayan sallar isha'i da Zinneerah ta dawo ɗakin nata bisa rakkiyar Maman Halima. Alhaji yayi tafiya, hakama Saude bata gidan, tana can gidansu bikin ƙanwarta akeyi, yaran natama suna dawowa Islamiyya da yamma yau suka bita can. Dan haka gidan ya kasance daga ita Maman Sadiq sai Maman Halima. Sai yaran Maman Sadiq uku duk maza ƙannen Zinneerah data haifa anan. Abubakar Sadiq, Abdul-Salam, sai Aliyu auta. Itako Maman Halima yaranta duk matane, huɗu sunyi aure ma, sai biyu yanzu a gabanta ƴan biyune sa'annin Sadiq. Sai itama Saude nada biyar, yanzu haka akwai ƴammata biyu da suka isa aure, sai ɗaya zasuyi kusan sa'a da Zinneerah, da ƙannensu biyu ƙanana suma kusan sa'annin su Sadiq ɗin dai.

      Sosai Saude take kishi da Maman Sadiq saboda tazo gidan ta haifi ƴaƴa maza su basu haifaba, taso su haɗe kai da Uwargidan da suke kira maman Halima amma taƙi, dan dama itama ɗin can ba zaman lafiyarne a tsakaninsuba, to mizaisa ta yarda su haɗe su cuci wani bayan ALLAH shine mai badawa. Kuma koda Maman Sadiq tazo gidan batazo musu da raini ba, su duka girmamasu takeyi dan mace ce mai sanyin hali, sai dai idan ka ƙureta kam zaku kwasa da ita. Shiyyasa duk haukan da Saude zatai a gidan ko kallonta batayi, sai idan ta kaita maƙurane ta yaɓa mata maganar da zatai kwana da kwanaki tana damunta a rai.....

         Numfashi Maman Sadiq taɗan sauke da duban Zinneerah dake a takure gefe tana magana dasu Sadiq  dake zagaye da ita a hankali. Tanajin misu Sadiq ɗin ke faɗa, amma batajin na ita Zinneerah ɗin. Gashi kuma ta duƙar da kai bata ko kallon sashen da take. 

      “Abdul!”. Ta kira sunan yaron nata na tsakkiya da yafi kowa ƙiriniya a yaran, dan a yanzu haka kusan rabin jikinsa na manne da na Zinneerah ne, gashi dama suna kamanni sosai da ita.

     Kansa ya ɗago ya dubeta, “Na'am Mama”.

      “Ku tashi aje ai shirin barci hakanan, duk kabi ka katantaneta bakaga halin da take ciki bane”.

    Baki yaron yaɗan tura gaba da faɗin, “Ayya mama ki barmu muyi barci tare da ita, muna sonta sosai”.

      A karon farko Maman Sadiq taga Zinneerah ta saki murmushi tana shafa kan yaron, sai dai bataji mita faɗaba sai da yaran suka haɗa baki wajen cewa, “Muma ai muna sonki sosai” ne ta gane cewa tai tana sonsu itama. 

      Murmushi tayi tana maijin daɗi da farin ciki a ranta, ta sake faɗin, “Karku damu ai tana nan tare da ku babu inda zata, kuje ku kwanta akwai islamiyya gobe idan ALLAH ya kaimu”.

     Badan sunso ba sukaima Zinneerah sallama suka nufi ɗakin barcinsu. Shiru falon yayi na tsahon mintuna. Ita dai Maman Sadiq kallon Zinneerah ɗin takeyi cike da nazari, itako kanta a ƙasa tana wasa da zanen carpet ɗin dake shimfiɗe a falon.

      “Zinneerah.”

Ta kira sunanta cike da rauni.

     Karon farko Zinneerah ta ɗago ta dubeta, sai kuma taɗan risinar da idonta. Murmushi mai ciwo Mama tayi, ta sake faɗin, “Taso ki dawo nan”.

    Babu Musu Zinneerah ta miƙe zuwa gareta. Sai dai kamar bazata zauna inda ta nuna mata ɗinba, sai kuma mita tuna oho ta zauna a hankali gab da Maman nata. Mama dake cigaba da kallonta ta riƙo hannunta cikin nata tana gyara zama da fuskantarta sosai. Hakanne ya saka Zinneerah maida kanta ƙasa idanunta na cika da ƙwalla.

      Itama Mama idanun nata cike suke da ƙwallan, cikin rawar murya tace, “Kiyi haƙuri Zinneerah, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Na fara da baki haƙuri ne saboda dalilai masu yawa. Nasan har ranki kina kallona ne matsayin uwa gareki mara adalci. wadda ta wofantar da ke ta manta da rayuwarki. Wlhy Zinneerah ba hakan baneba. Ni mahaifiyarki ban taɓa mantawa dakeba koda na daƙiƙa guda. A kowane sakanni kina maƙale a raina da zuciyata. Hawayena basu taɓa jinkirin fitowa ba a duk sanda na tunaki. Duk wanda ke tare dani yasan hakan Zinneerah. Nisantarki da nai itace babbar jarawar da har yanzu na kasa cimmawa wajen cinyeta, sai dai Alhmdllh, tunda yau gani gaki a yanda ban taɓa tsammataba ko tunani. Inason ki daure ki cire komai a ranki ki saki jiki dani ko hakan zai ragemin raɗaɗin ciwon gyanbon dake maƙale a zuciyata kinji”.

        Hannu Zinneerah tasa ta share hawayen dake sakko mata daga idanu zuwa kumatu, cikin rawar harshe tace, “Amma miyasa baki taɓa zuwa gareniba mama”.

     Murmushi Mama tayi itama tana sharar nata hawayen. “Zinneerah bana cikin hayyacinane, koda na baro ƙauyen Danya a yanayin ciwon hauka na barosa, sai dai Alhmdllh ALLAH ya taƙaitamin wahala maimakon na nufi wani waje saina nufi gida. Bayan isowata gida ƴan uwana sunje har Danya danjin miya faru dani amma mahaifinki yaƙi saurarensu, yama nuna bai sansuba baisan daga ina suka fitoba. Asabe kuma taci musu zarafi da musu korar kare. Duk da sunji zafin abinda akai musu sun buƙaci tahowa dake dan a gida na barki ni. amma mahaifinki ya hanasu, yama ɗora musu da cin zarafin dayafi na farko. Wannan shine dalilin yin fishinsu, amma basu haƙura akan wataran zasu amsoki ba. Ansha fama wajen nemamin magani sosai,  har takai mai gidannan dake a matsayin yayana yaje Ɗanmusa yaga halin da nake a ciki, shine ya fahimci sihiri ne tattare dani. Shine yasa aka kawoni nan kano wajen wani mutumi mai bada magungunan musulinci. Ya kashe kuɗi bana wasaba wajen ganin hankalina ya dawo tare dani, bayan wani tsahon lokaci aka dace na samu lafiya. Daga nanne ya nema aurena. Duk da banso hakanba aka tirsasani harna amince. Sosai kina maƙale a raina tunda na dawo hayyacina Zinneerah, sai dai bansan miyasaba ko sha'awar nufar hanyar Danya banayi, kai hasalima duk sanda nai yunƙurin son naje sai ciwona ya motsa min. Ƴan uwana kam bansan daliliba kowa ya bar zancen amsoki ko zuwama inda kike. Hakan na damuna a cikin rai, amma inajin kunyar yima wani magana ace na zaƙe da yawa, amma kiyi haƙuri Zinneerah ki yahe mani kinji”.

        Kuka sosai Zinneerah keyi fiye da farko. tausayi da ƙaunar mahaifiyarta na sake shigarta cikin jiki da ɓargo. sun daɗe a haka kafin Mama ta koma lallashinta da tambayarta abubuwa game da rayuwarta da Inna Asabe.

      Wani takan bata amsa, wani kuma takanyi murmushi ne kawai, hakan yasa Mama sake fahimtar ɗiyar tata tasha wahalar rayuwa kamar yanda tasani Asabe zama tayi fiye da haka. Dan ko ita ba daɗin zama taji da itaba a tsahon shekarun da sukayi tare na zaman kishi.

      Yanda Mama bataima Zinneerah zancen ciki ba itama Zinneerah batace komai game da cikinba. Ganin dare yayi Maman tace ta taso taje ta kwanta haka nan.


         Yau kam Mama da Zinneerah sunyi barci ne a gado ɗaya, hakan ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi ya saka Zinneerah ba, har takaita da shagala dogon tunani akan abinda ke a cikinta itama. Mace ne ko namiji bata saniba. Wanene mahaifinsa yaya aka samar dashi bata saniba, wace amsa zata bashi taba mutane da mahaifiyarta game dashi bata saniba. Ta shafa cikin tana sakin wani murmushi mai ciwo da saka ƙunar zuciya, daga haka barci yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin Khalipha.


*WASHE GARI*


          A yau kam Zinneerah ta sake tabbatarwa ashe itama mutum ce mai daraja kamar kowa, dan yanda ƴan uwanta da Mamanta suka kasance da ita ya jefa zuciyarta cikin matsanancin farin ciki. Kowa burinsa yaga dariyarta a gidan, ko yaya tai ɗan shiru sai ance mata mike damunta?. Abinci kam saita zaɓa wanda ranta keso ake bata taci.

        Dawowar maigidan kuma aka sake ninka tattalin da ake mata, dan shima da aka kaita ta gaidashi bayan yaci abinci ya huta janta yay tayi da hira cikin kulawa, tun tana ɗan noƙewa bata iya amsawa harta saki jiki dashi ta fara amsa masa. Ta jima a wajensa tare da sauran ƙannenta kafin ta dawo sashen Maman Sadiq suka cigaba da shirmensu ita da ƙanen nata.


      Haka rayuwa ta cigaba da yima Zinneerah daɗi a gidan mijin mamanta kuma kawunta, a hankali tana sakin jiki da kowa da komai nagidan. Har zuwa yau kuma da zata cika kwanaki uku babu wanda yay mata tambaya akan cikin jikinta balle jin ba'asin sanin inda ubansa yake. Itakuma bataima kowa maganaba dan addu'arta bai wucema ace kowa yaƙi tambayar tataba tunda batasan wace amsa zata basunba.

        Yau ma duk suna zaune tsakar gida gab da magriba, tunda yaran suka dawo daga islamiyya anan suka yada zango inda suka sameta tana gurzama Maman Halima kuɓewa da zatai miyar tuwon dare. Anan suka shiririce bata labari tana musu dariya da biye musu kamar yanda ta saba.

      Ƴammata ne biyu suka shigo gidan da sallama a bakinsu ciki-ciki. Sai ƙananu biyu dake biye dasu da ledoji a hannu. Idanu Zinneerah ta zuba musu kawai dan bata sansuba, hakama sauran yaran kallonsu kawai suke babu wanda yay magana. Sai Aliyu ne cikin tsalle yake faɗin, “Gasu Zainab gasu Luba”.

          Ko kallon inda Aliyun yake basuyiba suka nufi ƙofar ɗakin uwarsu, dai-dai Maman Sadiq na fitowa ne uwar tasu ta shigo itama da ɗayar yarinyar da zasuyi sa'anni da Zinneerah. Cike da fara'a a fuskar Maman Sadiq ta shiga faɗin, “A'a ƴan bikine tafe. Sannunku da zuwa”.

      A ɗan yatsine Saude da suke kira Maman Sakina ta amsa idanunta akan Zinneerah ko ƙyaftawa batayi. Ganin kallon ƙurillar da take matane ya saka Zinneerah faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”.

     “Lafiya” tace kawai tana nufar ƙofar ɗakin nata itama.

     (Ashe tsugunne bata ƙareba kenan) Zinneerah ta ayyana a ranta zuciyarta fal tunanin waɗannan kuma daga ina?. Bata da mai bata amsa, dan haka ta miƙe dan ganin lokacin sallama yayi gashi wasu masallatan har an fara kira.

       Alwala tace su Sadiq suje suyi su tafi massallaci, ita kuma suka shige sashen Maman Halima ita dasu ƴan biyu domin gabatar da tasu sallar. Daga haka bata sake jin ɗuriyar Saude da ƴaƴanta ba a gidan, bakuma ta tambayaba har suka gama hira ta miƙe ita dasu Abdul suka nufi sashen mahaifiarsu dansu kwanta. 


     Washe gari da safe bayan sallar asuba gari yay ɗan sha suka tafi gaida mutanen gidan kamar yanda Maman ta horesu. Sashen Alhaji suka fara zuwa wanda yaran gidan ke kira da Abba. Yana zaune a falonsa madaidaici da redio a hannunsa da alama kunnawa zaiyi, shigowar tasu ya sakashi ajewa yana dubansu da kulawa. Aliyu yaje jikinsa ya zauna, suko duk suka durƙusa a ƙasa suna gaidashi. Da fara'a yake amsa musu yana shafa kan Aliyu, ya ɗan duba Zinneerah da kanta ke a ƙasa, “Ɗiyata ya jiki-jikin?”. 

       Takanji kunya idan sukai mata tambaya akan jikinta, ta ƙara ƙasa da kanta da cemasa “Alhmdllh Abba”. “Masha ALLAH ai haka akeso, ALLAH ya saukeki lafiya”. Daga haka ya maida hankalinsa kan Aliyu. 

       Itace ta fara miƙewa, sauran yaranma duk suka miƙe suka fito a tare. Suna gab da shiga sashen Maman Halima Aliyu ma ya iso garesu da gudu yana faɗin, “Aunty! Kinga kuɗin makarantana Abba ya bani”. Juyowa Zinneerah tai tana murmushi, tace, “kace ka gode ko?”. Kansa ya kaɗa mata yana riƙo hannunta suka ƙarasa shiga sashen Maman Halima itama. 

         A falo suka isketa tanama Hussaina faɗa akan zubar da suga da tai ƙasa, ganinsu ya sata dubansu tana murmushi. Itama har ƙasa suka durƙusa gaisheta, ta amsa musu da fara'a da kulawa tana tambayar Zinneerah yaya jikinta. Nanma dai cike da kunya ta amsa kanta a ƙasa. Sunɗan jima anan fiye da sashen Abba. Daga haka suka shiga na Maman Sakina..  

       Suma dai a falon suka samesu sunata hayaniya, dan ɗakinta yafi na kowa yawan yara a gidan. Yanda suka wani watsoma Zinneerah idanu gaba ɗayansu har uwar sai duk taji ta muzanta. amma haka ta daure takai ƙasa tana gaida Maman Sakina ɗin. A ɗan yatsine ta amsa mata. Carab Luba dake kwance a kujera ta miƙe idonta akan Zinneerah. “Tab ɗi jan, jama'a wai kuna ganin abinda nake gani kuwa? Wai wannan ƴar yarinyarce da ciki”. Kusan a tare suka sheƙe da dariya, Sakina tace, “Kinsan ƴan ƙauyen nan sai a hankali, amma dubetafa sa'a tace, koma na girmeta kamar”. Cikin taɓe baki uwar tace inako sukaga hankali, ai kamar dabbobi suke basu banbance komai sai shirme. Nanma dariyar suka kwashe dashi su duka harsu Zainab ƙananu.

       Tsam Zinneerah ta miƙe daga durƙuson da tai batare da tace komaiba ta kama hannun Aliyu suka fito zuwa sashen uwarsu.

       Suna shigowa Abdul ke faɗama Mamansu abinda akaima Auntynsu a sashen Maman Sakina. Wai su Sakinar ne ke dariyar Zinneerah ƴar ƙarama da ita tanada ciki. Shine mamansu tace wai ai kusan mutanen ƙauye ba hankaline dasuba kamar tumaki suke. Ran maman Sadiq ya ɓaci, amma saita shanye bata nunaba. Hasalina batace komaiba ta cigaba da haɗa musu abin karin da takeyi. Itama Zinneerah komai bataceba tamayi kamar ba a gabanta akai abinba.

     Bayan sun kammala karyawan ne Zinneerah tahau gyaran ɓangaren kamar yanda ta saba tun zuwanta gidan, su Sadiq kuma suka shiga shirin tafiya Islamiyya dan suna hutun boko. Tsaf ta gyara ko ina ta saka musu ƙamshi, ganin komai ya mata tsaf yanda takeso sai taje itama tayi wanka. Ta fito tana cikin shiryawa Mama ta shigo ɗakin.

        Sai da ta ƙarasa abinda takeyine Mama tace, “Zauna magana nazo muyi”. Zama Zinneerah tayi inda Mama ta nuna mata babu musu, Mama taɗan sauke numfashi tana dubanta, itako kanta a ƙasa tamkar ko yaushe.

       “Zinneerah!”.

Maman ta kirayi sunanta a karo na farko. Batare data ɗagoba tace, “Na'am mama”..   

       “Zinneerah tun zuwanki gidannan nake jiran naji miya baroki da gida? Amma shiru bakice dani komaiba. Ya kamata nasani ai, sannan nasan kuma  ta yanda zamu nema mijinki shima dan yasan inda kike ko hankalinsa zai kwanta, tunda nasan duk inda yake kodan cikin dake jikinki basai samu nutsuwar zuciyaba”.

       Yawu Zinneerah ta haɗiye da ƙyar wani abu na tattarowa a ƙirjinta. Ganin taƙi magana Mama tace, “Ke nake saurare”.

       Maimakon amsa sai kawai Zinneerah ta saka mata kuka. Idanu kawai Mama ta zuba mata kamar yau ta fara ganinta, bata kawo komai a rantaba sai tunanin harda matsalar mijin ƙila ta barota da gidan. 

       “Abinda ya faru ya riga ya faru, dan haka kuka baida wani amfani a yanzu. Ki sanarmin nasan madafar kamawa wajen samo mafita”.

       Yanda Mama tai maganar babu wasa ya saka Zinneerah bata amsa cikin dauriya da matsanancin tsoro. “Nima bansan ya akai na baro gida ba, nawayi garine kawai naga kaina a asibiti”

           “Nikam ban fahimceki ba, sai kimin bayani dalla-dalla”. Mama ta faɗa tana tsareta da idanu.

     Maimakon amsa sai hawaye Zinneerah ke faman sharewa. Shigowar Alhaji ya hana Mama sake cewa komai...........✍


No comments

Powered by Blogger.