Jiddatul Khair 53

 


Umma na shigowa dakin ta karaso kusa da gadon tana kallon Jiddah tace "Lafiya Jiddah?" Jiddah ta dago kanta da kyar hawaye na sauka idonta amma ta kasa cewa komai, Umma tace "Ciwon cikin ne?" Ta gyada mata kai kawai, Umma ta kalli agogo dake nuna karfe hudu saura, fita tayi daga dakin ta dau wayarta ta shiga kiran layin Ahmad, har ya katse ba a dauka ba, Umma ta tsaya tana ta tunanin yanda xata yi kuma, gashi ita bata driving da duhu, har ta fara tunanin kiran driver dinta sai ga Ahmad ya kira, dagawa tayi tace "Sorry i woke u up Ahmad, kana gari ne?" Ahmad yace "Aa ban shigo ba, me ya faru Umma?" Umma tace "Wllh ciwon cikin Jiddah ne ya tasar mata, ni kuma ba driving nake a duhu ba..." Yace "Subhanallah, bata taho da magungunanta bane?" Umma tace "Ka siya mata wasu maganin ne?" Yace "Ehh na siya mata a can gida, But Umma Captain na gari ai, ki kirasa sai ya taho ya kai ku asibitin" Umma ta sake kallon agogo, sai kuma tace "Toh shkkn" Daga haka ta katse wayar, Number Aliyu ta nemo a contact sannan tayi dialing number, Abuturrab na kwance ya samu bacci kenan kiran Umma ya shigo wayarsa, da yake baccin nasa bai wani nisa ba ya bude ido da kyar yana kallon wayar tasa, mikewa xaune yyi ya jawo wayar da mamakin me kiransa at that time, number Umma ya gani a screen, ya daga ya kai kunne, Umma tace "Sorry na tashe ku Aliyu, idan ba damuwa ka taho gida yanxu xa ka kai mu asibiti..." Yace "Subhanallah.. waye ne ba lafiya?" Umma tace "Idan ka xo xaka gani" a hankali yace "Toh" daga haka ta katse wayarta, Mikewa Abuturrab yayi duk da idanuwansa da suka masa nauyi don throughout first hours of the night idonsa biyu ya kasa bacci, har sae kusan karfe uku da wani abu sannan ya samu sauki bacci ya daukesa, daukar wayarsa yayi ya fita daga dakin... Ya tafi bangarensa ya bude kofar parlon a hankali sannan ya karasa bedroom dinsa nan ma he was so careful opening d door, Aneesah na kwance tayi dai dai saman gado tana baccinta, ya karasa gun kayansa ya dau kayan da xai dauka sannan ya nufi kofa xai fita kenan yaji cikin muryan bacci tace "Captain" Juyawa yayi ya kalleta, ta mike xaune tace "Ina xaka by this time, naga ka dau kaya?" Bai tanka ta ba ya fice daga dakin ta bi sa da kallo, ya koma dakin da yake yana cikin shiryawa ta shigo ta kulle kofar, bai ko kalleta ba ya ci gaba da buttoning din shirt dinsa, ta karaso kusa da shi, sai kuma ta durkushe kasa ta hade hannunta cikin rawan murya tace "Captain auren soyayya muka yi da kai fa ba auren kiyayya ba, wannan altitude din da ka tsiro yana sa min ciwon xuciya, don Allah idan wani laifi nayi maka kayi hakuri ka yafe min ba don halina ba" sai kuma ta fashe da kuka, ya girgixa kai yace "Ni nace kin min wani abu ne?" Cikin kuka tace "Gashi nan you are ignoring me and giving me altitude for the pass 8 days now, don Allah ba don ni ba kayi hakuri, albarkacin irin son da nake maka kayi hakuri" Shi dai bai ce mata komai ba, tana shessheka tace "Idan ma aikin gida ne da bana yi ai kaga yanxu dai na fara yi, har girki ina yi yanxu... in sha Allah kuma xan dore da haka, kawaye kuma na daina barin su xo min gida daga yanxu, ni dai don Allah ka daina shareni haka ina shiga damuwa sosai Mijina" Ya dau makullin motarsa yace "Xan je Umma na kirana xan kai su asibiti" Tace "Subhanallah, waye babu lafiya?" Yace "I don't know, sai naje" Tace "Toh don Allah in sa hijab mu tafi tare" Ya kalleta yace "No, it's of no need" Ta marairaice tace "Me yasa kake yawan gwaleni a abubuwa da dama ne Captain, i just want to feel belong in ur family, har yanxu fa babu wani bond tsakanina da su, and it's not suppose to be so, allow me to always mingle with them don Allah, kaga yanxu ai Umma xata ji dadi idan ta gan mu tare" yace "Bayan wanda ku ke yi da Aunty? I mean the bond u are talking about" Tace "Ai Aunty daban Captain, har yanxu fa ko gidan Umman ma ban sani ba, don Allah kar kace min Aa captain, ka bari mu tafi tare, ni fa ba kowa gareni a garin nan ba sai kawaye kai ma ka sani" Bata jira cewarsa ba ta mike ta fita ta koma bangarensa ta dau hijab dinta har kasa ta saka kan doguwar rigan baccin jikinta, ta feshe duk jikinta da turare sannan ta fito, dai dai nan shi ma ya fito daga dakin da yake, ya fara sauka downstairs yana rike da makullin motarsa ta bi bayansa, Abuturrab bai ce mata komai ba ta bude daya side din motar ta shiga, mai gadi da Abuturrab ya kwankwasa ma kofa ya fito da sauri ya bude masu gate, Mai gadin na tsaye gefe har Abuturrab ya fitar da motar sannan ya kulle gate din yana daga masa hannu, Abuturrab ya jira har masu gadin layin suka bude gate din layin sannan ya fita, yana isa layinsu Umma nan ma gate a kulle, hakan yasa ya dau wayarsa ya shiga kiran Umma, Umma na dagawa yace "Umma xa ku iya fito naga ba a bude gate na shigowa layin ba" Umma tace "Toh bari mu fito" daga haka ta katse wayar, Aneesah ta kallesa tace "Toh kayi horn mana kilan masu gadin xa su fito sae kayi masu bayani ko" Ya girgixa kai yace "No need" Idonsa na kan gate din gidansu Umma that's not too far from the gate leading to d street, bayan few minutes aka bude gate din gidan, Umma ce ta fara fitowa tana rike da hannun Jiddah Maimoon na biye da su, Ya dinga kallonsu kamar yanda Aneesah ke stressing idonta tana son ganin su waye suka fito, bude motar yayi ya sauka ya kulle sannan ya karasa ya shiga layin ta karamin gate din da ke a bude, Umma ta sake Jiddah da ta durkusa kusa da wani flowern wani gida xata yi amau, Ya isa har inda suke a tsaye yace "Me ya sameta Umma?" Umma dake kallon Jiddah cike da tausayinta ta sauke ajiyar xuciya tace "Wai ciwon cikin dae..." Dukawa Abuturrab yyi yana kallonta shi ma, cikin low voice yace "Sorry..." Jiddah dai bata ce komai ba ta mike da kyar don ta kasa aman, Tun da Aneesah ta lura kamar Jiddah ce ba lafiya mood dinta ya canxa gaba daya, lkci daya ta fara da ta sanin fitowa da tayi ta biyosa... Ba don baxa ta samu abun hawa ba da kawai sauka xata yi ta koma gida abunta, Maimoon ta daga Jiddah ganin bata yi aman ba suka ci gaba da tafiya, Abuturrab na kallon Umma yace "Tun yaushe take ciwon cikin?" Umma tace "Ban san sanda ya tasar mata ba, Maimoon ce ta shigo ta tasheni..." Abuturrab bai kuma cewa komai ba har suka isa gun motar yana kallon Jiddah, ya bude back seat Maimoon ta shiga ciki tare da Jiddah, Umma ma ta shiga bayan motar, ya xaga ya shiga driver seat, Aneesah tayi kasa da kai tace "Ya mai jikin Umma?" Umma tace "Alhmdlh, mun taso ku ko" Tace "Aa babu komai Umma, Allah dai ya bata lafiya" Umma tace "Ameen" wani babban asibiti Abuturrab ya kai su, bayan su Umma sun sauka motar Aneesah ta kalli Abuturrab murya can kasa tace "Amma dai likita na attending masu xamu juya ko captain??" Ya kalleta yace "Amma tun farko sai da nace kar ki biyoni ko??" Ta hade rai tace "What did u mean? Asibitin xa mu xauna har a sallamesu kenan saboda Ramlah ce bata da lafiya ko Aisha?" Bai tanka ta ba ya bude motar ya sauka, rai bace ita ma ta bude motar ta sauka tana masa wani irin kallo, kulle motarsa yayi ya bi bayansu Umma... Admitting din Jiddah aka yi a hospital din saboda karin ruwa da xa ayi mata, sosai take jin jiki wai duk a hakan ma tana da dauriya ba kadan ba, Umma na xaune bayan ta idar da sallan Asuba a ward din da aka kwantar da su wayarta ya fara ring, Maimoon ta mika mata wayar, Umma ta daga ganin Ahmad ne ke kiranta, bayan sun gaisa yace "Ya jikin nata Umma?" Umma tace "Ta samu bacci yanxu, an sa mata ruwa..." yace "Toh Allah ya sauwake, ya bata lafiya" Umma tace "Ameen" Ahmad yace "Captain ya tafi ne" Umma ta kalli Abuturrab dake xaune shima shigowarsa kenan daga masallaci tace "Aa bai tafi ba" Ahmad yace "Ohk, na kira bai daga bane" Umma tace "Ko wayar na mota" Ahmad yace "Toh shkkn xan kira anjima" Umma tace "Allah ya kai mu" Tana katse wayar ta kalli Abuturrab tace "Aliyu ku koma gida kawai, tun da har ta samu bacci, she will get better in sha Allah... Daga nan ku ajiye Maimoon ma a gida" Abuturrab dai bai ce komai ba, Aneesah dake xaune kan plastic chair ta kalli Abuturrab din ta gefen ido ta ji abinda xai ce, Yana kallon Umma yace "To shkkn, Allah ya bata lafiya" Umma tace "Ameen, Allah yayi albarka" Kallon Maimoon da ta mike yayi sannan ya nufi kofa, Aneesah ta mike tana kallon Umma tana kirkiran murmushi tace "In sha Allah, xan dawo anjima Umma, Allah ya bata lafiya" Umma tace "Ameen, mun gode Aneesah, Allah yayi albarka" Tace "Ameen" ko kallon Jiddah bata yi ba ta fice daga ward din, Umma na kallon Maimoon tace "Ki dauko mata wani hijab din, may be with an extra clothe, sannan ki taho da toothpaste and brush, idan su Huraira sun gama breakfast sai ku kira driver ya taho da ku anjima, nima ki dauko min wani hijab din kar ki manta" Maimoon tace "Toh" sannan ta fita ward din. Karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya shiga dakinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, kwance ya tadda Aneesah har sannan tana bacci tun bayan da suka dawo wajen karfe shidda da asuba, Karasawa yyi saman gadon ya kai hannu ya buga gefen gadon, ta bude ido a hankali don tun bude kofar parlon da yayi ta farka, yace "Yanxu babu wani abu da xaki girka a kai asibiti??" Buda ido tayi sosai tana kallonsa sai kuma ta mike xaune tana ci gaba da kallonsa keenly tace "Abu kamar me fa Captain?" Yace "Breakfast...." Bude baki tayi sai kuma ta tafe hannu tayi wani dariyar rainin hankali tace "Saboda Aisha ko Ramlah ce kwance gadon asibiti ba lafiya ko??" Kafeta yyi da ido, ta ja wani tsaki tace "Wllh ka xo da wata bidi'a Captain, kawai saboda ga kanwar uwata Safara'u kwance gadon asibiti sai in tashi da sassafe in fara hada breakfast, to bari kaji wllh ko Maimoon ce bata da lafiya sai na ga dama xanyi girki a kai asibiti balle wata banxa can mara asali, gayyar....." Dakatar da ita yayi cikin tsawa yace "Enough Aneesah, baxa kiyi ba baxa kiyi ba, final!! Kar ki gaya min maganan banxa..." Aneesah ta masa wani kallon banxa daga sama har kasa ta sauka kan gadon ta shige bandaki abun ta tana cewa "Ka xata tun farko da nasan ita ce ba lafiya xan ma fara katse bacci na in fita cikin dare..." juyawa yayi ya fita daga dakin xuciyarsa na tafarfasa, yana komawa downstairs ya kira layin Maimoon, tana dauka yace "Anyi breakfast ne a can gidan?" Maimoon tace "Ehh driver muke jira yanxu ya kai mu asibitin" yace "Ohk, i am coming now" daga haka ya katse wayar, yana isa gidan Umma ya dau Maimoon da Safiyya suka wuce asibitin, har sannan Jiddah bata tashi ba, Umma na kallon Abuturrab yace "Ya ku ka koma gida" yace "Lafiya lau" Maimoon na kallon Umma tace "In hada maki shayin Umma?" Umma tace "Aa ai baxan iya sha a nan ba, tun da kun xo bari kawai in koma gida sai in dawo anjima idan na kintsa" Maimoon ta mayar da cup din tace "Toh shkkn" Umma ta mike, Abuturrab ya kalleta yace "Toh bari in ajiye ki gidan Umma" tace "Toh nagode" Tare Umma ta koma da safiyya da tayi shirin Islamiyya, Abuturrab na kallonta yace "A Islamiyyan xa a ajiye ki ke?" Tace "Ehh" sai da ya fara ajiyeta a Islamiyyarsu sannan ya kai Umma gida, bayan ta sauka daga motar ta saka masa albarka ta wuce ciki, barin layin yayi yana hawa saman titi kiran Ahmad ya shigo wayarsa, dauka yayi ya daga ya kai kunne Ahmad yace "Ka koma asibitin ne?" Abuturrab yace "Aa" Ahmad yace "Ohk anjima xan shigo in sha Allah, ka tambayi Umma if there is anything sai kayi masu tunda kaga ba kowa..." Abuturrab dake ta sauraronsa ya tabe baki yace "Umma tace tana yawan ciwon cikin, and what is the cause?" Ahmad yace "Da ka shiga ka tambayi likitan da yayi admitting dinsu mana" Abuturrab yace "Kai na tambaya" Ahmad yace "Ohk tunda ni ka tambaya bari in baka amsa, duk xamanku tare da ita a gidanka ka ta6a ganin tayi Period?" Abuturrab ya juya ido yace "Period? Meye hakan?" Dariya Ahmad yayi yace "Al'ada" Shiru Abuturrab yyi, Ahmad yace "Toh bata al'ada, da Umma ta ga hakan sai ta kai ta asibiti aka daurata kan magunguna, tun sannan kuma shine take ciwon mara..." Abuturrab yace "Toh dole ne sai anyi jinin?" Ahmad yace "Of course dole ne, although wasu matan basa yi kuma suna haihuwa a haka, akwai mata da yawa da xaka ga a shekara sau biyu suke al'ada kuma suna haihuwarsu lafiya lau babu wani abun dake damunsu, so in her case...." Abuturrab ya katse sa yace "What i want to understand here now is, so ake ta fara al'adan yasa aka kai ta asibiti ko me?" Ahmad yace "Eh mana, ana son sanin ko nata normal ne ko kuma Hormonal Imbalance ne ya janyo hakan, idan Hormonal imbalance ne kaga dole sai an ci gaba da yi mata medication har Allah yasa ta fara din, sannan ciwon maran da take ai jini ya kamata tayi ba ciwon mara me tsanani haka ba" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Allah ya sauwake" Ahmad yace "Ameen..." Abuturrab yace "Sai anjima" daga haka ya katse wayar. Asibitin ya sake komawa, yana shiga ward din Maimoon ta daga kai ta kallesa da mamaki, a ranta kuwa cewa tayi me kuma ya dawo da wannan mutumin nan, tunda Jiddah dake xaune saman gadon ward din hannunta rike da cup din shayi ta hada ido da shi ta sunkuyar da kanta taki dagowa, Maimoon ta mike tana kallonsa tace "Ga kujera yaya" Yace "Nace maki xan xauna?" Ta girgixa kai ta koma ta xauna a ranta tace oho dai, ya kalleta yace "Ke me ya hanaki xuwa islamiyyar?" Ta xaro ido tace "Toh ai yaya saboda xan tsaya da Jiddah a asibiti ne Umma xata koma gida, kaga babu kowa a nan din" Ya d'an kalli Jiddah da taki dago kanta yace "Tace maki bata ji sauki bane?" Maimoon ta kalli Jiddah, ta washe baki tace "Wai kin ji sauki Jiddoh?" Ko kallonta Jiddah bata yi ba, Shi dai kallonta kawai yake, mika ma Maimoon cup din shayin tayi, Maimoon tace "Har yanxu kina jin aman?" Jiddah ta girgixa mata kai kawai, Maimoon tace "Amma ya isheki?" Jiddah ta gyada mata kai, Maimoon ta amsa Abuturrab yace "Mayar mata ta shanye" Maimoon ta d'an kallesa tace "Cika mata cup din fa..." Dakatar da ita yayi yace "I said give it back to her" mika ma Jiddah tayi, Jiddah tace "Ni amai nake ji" Yace "Eh amsa idan kin shanye sai kiyi aman" Karban shayin tayi a hankali a hannun Maimoon, ya ciro ATM card dinsa a wallet dinsa ya mika ma Maimoon yace "Ki ciro min kudi" ta kallesa da sauri tace "A ina yaya? Ai babu Bank a kusa..." Yace "Ko ma ina xaki ciro kije ki ciro ba ruwana" nan da nan mood dinta ya canxa ta amshi Atm card din ta mike tace "Nawa xan ciro?" Yace "Talatin" Kofa ta nufa tana cika tana batsewa, ya bi ta da kallo har ta bude kofar sai kuma ta juyo ganin kallonta yake ta seta fuskarta tace "Yaya pin din fa?" Yace "Ki kira Ramlah ki tambayeta" Ficewa tayi daga ward din ta kulle kofar, ya kalli Jiddah ganin ta ajiye cup din saman gado ta hade kai da gwiwa, karasawa yyi ya dauke cup din shayin ya ajiye a table yana kallonta, ta dago tana rufe idonta yace "Are u still feeling pain?" Da kyar kamar xata yi kuka tace "Yanxu ya fara" Kafin yace komai ta fara kokarin sauka daga saman gadon ya bi ta da ido har ta shiga bandaki, yana ta tsaye har ta fito daga bandakin amma ta ki karasowa cikin ward din, bayan few seconds yace "An kawo maki wani kayan ne?" Kasa kallonsa tayi kuma taki cewa komai, yace "Magana nake maki" bata dago kanta ba tace "Ai ban sani ba" ya nufi jakar da Maimoon ta kawo daxu ya bude, Hijab ya gani da doguwar riga sai undies da sabulu da sponge, satan kallonsa kawai Jiddah take, ya dau sabulun da sponge ya nufeta ya mika mata, amsa tayi ta juya ta koma bandakin, ya karasa saman gadon ya cire bedsheet din ya bar shi saman gadon snn ya fita ward din, nurses dake reception ya samu bayan sun gaisa da wata yace "Plss ki tura cleaner ward din farko, the bedsheet needs to be changed" Tace "Alright" ya juya ya fita xuwa wani babban kanti dake cikin asibitin, babu abinda ba a siyarwa a wajen, yana kallon matar dake ciki yace "Do u sell Sanitary pads?" Matar tace "Yes" guda uku ya siya ya bata kudi sannan ya juya ya koma cikin asibitin, cleaner din ya tarar a ciki tana canxa xanin gado, bayan ta gama ta fita da na da, ya xauna kan kujera, bayan kusan minti sha biyar Jiddah ta fito daga bandakin, pad din da ya ajiye saman table ya nuna mata ta dinga kallon ledan sai kuma ta karasa ta bude tana kallon abun ciki, bata yarda ta kalli inda yake ba ta tafi gun jakan kayanta ta dau pant tana bobboyewa shi dai kallonta kawai yake, ta mike ta dau pad din ta koma bandaki, bayan ta fito ta dau wani Hijab din ta sa, gaba daya ta kasa kallonsa don wani kunyarsa taji take yi, yana kallonta yace "Kina jin ciwon cikin yanxu?" Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, bai kuma ce mata komai ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, ta gaji da tsayuwarta sannan ta koma kan gadon ta kwanta ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa.... Karfe goma Maimoon ta shigo ward din fuskar nan nata babu annuri ta mika masa kudin da Atm card dinsa, yace "A ina kika samo?" Tace "Nima ban san wajen ba" Ta nufi Jiddah tace "Har kinyi wanka?" Ganin bacci take Maimoon ta xauna kawai, Maimoon tace "Lah canxa xanin gadon aka yi?" Abuturrab dai bai ko kalleta ba, Hannu ta kai kan ledan pad dake ajiye tace "Meye wannan kuma?" Xaro ido tayi ganin pads har uku, ta saci kallon Abuturrab sai kuma ta mayar ta ajiye sannan ta xauna kan kujera, mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa ya fita. Yana fita Maimoon ta shiga tada Jiddah a hankali, Jiddah na bude ido tace "Wa aka kawo ma pad Jiddah? Kuma wa ya kawo?" Jiddah ta bi dakin da kallo ganin Aliyu baya nan ta mike xaune, Maimoon dake ta kallonta ta xaro ido tace "Ko dai Period kika fara?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Maimoon ta kara xaro ido tace "Kar dai Ya Aliyu gani yayi yaje ya siyo maki pad din, gashi ma naga an canxa bedsheet" Jiddah ta d'an turo baki, Maimoon ta kyalkyale da wani dariya tace "Atoh wllh shi yaga duhu, amma ke garin yaya kika bari ya gani? Tabb" Jiddah ta marairaice tace "Na tashi na shiga bandaki ban san na ma yi stain ba, kuma bedsheet din ma yayi stain" Maimoon sai xare ido take, sai kuma ta kara fashewa da dariya tace "Toh sai yace maki me da ya gani?" Jiddah tace "Ni bai ce min komai ba, kawai xuwa yayi yaje ya siyo pad din" Maimoon ta tabe baki tace "Ai ko shi yaga duhu, yanxu dai wannan pad din sai kiyi wata biyar ma kina amfani da kayanki bai kare ba, har mu ma mun samu, kinsan fa shi ya Aliyu bai iya siyayyan hankali ba, don ma ba pack din gaba daya ya siyo maki ba, amma don Allah da wani ido kika kallesa bayan yaga period dinki" Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka, Maimoon tace "Idan nice ke wllh ko a gyalena fuskewa xanyi ai bani nace ya gani ba" Jiddah dai bata kuma cewa komai ba amma ita kanta tasan taji kunya sosai ba kadan ba, she wish that never happen... Har yamma da aka sallami Jiddah Abuturrab bai koma asibitin ba, Ahmad ne yayi driving dinsu ya maida su gida, Umma har lkcn bata san Jiddah ta fara period ba, balle Ahmad, suna komawa gida Jiddah ta wuce daki ta kwanta sai bacci.....


No comments

Powered by Blogger.