Jiddatul Khair 40

 


Washegari har karfe goma na safe Abuturrab na dakinsa kwance, babu wanda ya san yana cikin gidan banda Aunty da ta shigo tun karfe takwas wai ya tura ma Aneesah kudin make up, wanda ya tura da farko yayi kadan, babu yanda ya iya haka ya tura kudin, bayan nan kuma bata sake shigowa ba. Goma saura yan mintuna El-Basheer ya shigo gidan tare da Ahmad, don ba gidan ya kwana ba, El-Basheer ya dinga kallon Abuturrab yana 'yar dariya yace "Wannan ai ko kaine amaryar sai haka, ka wani makale a daki tun jiya kamar wanda xa ayi ma auren dole, kamar dai ba Aneesah bace matar" Ahmad yyi murmushi shima yana kallon Abuturrab yace "Captain duk xullumin auren ne ya ramar da kai haka..." Abuturrab yace "Saboda ita ce xata aureni ba nine xan aureta ba ko?" Ahmad yace "Toh wa ya sani, ita dai tana can tana ta sabgar gabanta da kawayenta, kai kuma kana nan ka makale a daki" El-Basheer ya nufi kofa ya fita xuwa dakin Hajja, Hajja na ganinsa tace "Ina Aliyun?" El-Basheer yace "Yana dakinsa" Hajja tace "Dama yana gidan nan?" El-Basheer yace "Yana nan" Ta mike tace "Ni ba ruwana, gida duk jama'a sun cika kilan babu wanda ya bi ta kan ko ya ci abinci ko bai ci ba, ita Ramlah naga sai masu kudi kawai take ma marhaba tayi ta nan nan da su duk ina lura da ita, kaga ai ko shigowa ta tambayeni ko an kawo min kumallo bata yi ba wllh, gwara ma Hauwan ta kawo ma Nafisah da kanta...." El-Basheer ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita sannan ya xauna yana kallon Aunty Nafisah yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau Bashir, ashe baka kwana gidan ba" Yace "Ehh yanxu na shigo, ya gajiyan ku" Tace "Gajiya ta bi lafiya, karfe nawa ne daurin auren?" Yace "Sai an sauko Juma'ah in sha Allah" tace "To maa sha Allah" Ahmad ne ya shigo dakin da sallama, Aunty Nafisah tace "Bokan turai ina ta xuba idon ganinka tun jiya ban ganka ba" Yana murmushi yace "Sannu da isowa Aunty, ya hanya" tace "Alhmdlh Ahmad" Hajja na shiga dakin Abuturrab ta tsaya daga bakin kofa tace "Kunga abinda nake gudu ko? Yanxu tun safe babu wanda ya kawo maka kumallo kenan?" Ya d'an kalleta amma bai ce komai ba, tace "Toh ni ba ruwana wllh, wannan ai ba yi bane" Tana fadin haka ta fita, dakin da yan matan gidan suke ta tafi ta bude, bak'i ne kawai a dakin ta gama kare masu kallo tace "Tirrr" sannan ta fita tana girgixa kai tace "Abin dai ba tsari, wa xai yarda da wnn gayyar a Masar, wasu ma rabonka da su ya fi shekara talatin amma suna jin biki xa su taho riiii, ko yar shinkafar suke ma oho" Safiyya ta gani tace "Ke ina Jiddah?" Safiyya tace "Umma ta aikesu da Maimoon can gida" Hajja tace "Toh kije duk yanda xaki yi a kitchen ban sani ba, amma ki samu ruwan xafi da kofi me kyau ki dau kayan tea ki kai ma Aliyu, idan babu burodi ki xo in baki kudi kije ki samo masa, kowa fa ya karya a gidan banda shi don walakanci" Safiyya tace "Toh" daga haka ta wuce kitchen, Hajja to kama dakinta tana mita, Safiyya tayi duk yanda Hajja tace sannan ta kai masa daki, bayan ta gaishesa ta ajiye tray din, yana kallonta yace "Ina su Maimoon?" Tace "Umma ta aikesu" Yace "Ita da wa?" Tace "Jiddah da Nafisah" yace "Xuwa ina?" Tace "Can gida" tsayawa tayi jin bai sake cewa komai ba xata fita yace "Xo ki bani number Maimoon din" Safiyya ta dawo ta amshi wayarsa ta sa masa number Maimoon sannan ta mika masa, ta juya ta fita, dialing number yayi, Maimoon dake compound sun fito tare da Jiddah da Nafisa xasu  wuce wajen kwalliya ta xaro ido tana kallon wayarta tace "Dama Ya Aliyu yana da number na, kuma me xai ce min yake kirana..." Dagawa tayi ta kai kunne a hankali tace "Assalamu alaikum" Daga daya bangaren ya amsa yace "Kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gida" yace "Ke da wa?" Tace "Jiddah da Nafisah" Yace "Yaushe xa ku baro gidan?" Tace "Aa yanxu dai wajen tailor xa mu je amsan kayan da xa mu saka na dinner...." Ta d'an kalli su Jiddah, jin yyi shiru tace "Hello" yace "Ina jin ki, minti nawa xa kuyi wajen tailor din" Ta d'an turo baki tace "Yanxu xa mu dawo dai Yaya, amso kayan kawai xa mu yi" Yace "Toh ku sameni a daki idan kun dawo, gaba dayan ku" Tace "Toh" daga haka ta katse wayar ta ta6e baki tace "Toh me xa mu yi masa xa mu wani samesa a daki, ni ba da ni ba wllh, ko a ina ma ya samu Digit dina" Nafisah tace "Da kince masa ma daga wajen tailor din xamu je gun make up, ni bana son komai da xai hada mu da shi fahh" Maimoon tace "Kyalesa kawai, ba sai ya ganmu ba" Ita dai Jiddah bata ce komai ba har suka fita gate din gidan. Har karfe sha biyu da rabi su Maimoon basu koma gida ba, Abuturrab ya kira numberta sau uku ya ji a kashe, ya kira Nafisah ita ma numberta a kashe, yana xaune dakin Hajja da Ahmad da El-Basheer, dukkansu fararen shadda ne jikinsu xasu tafi masallaci, Ahmad ya kalli Abuturrab bayan ya kalli agogon wrist dinsa yace "Wai da wanda kake jira ne Captain, dubi fa lokaci..." El-Basheer yace "I'm still wondering also, yace mu jira ban san wanda muke jira ba" Hajja tace "Aa gaskiya ku bi sa a hankali, ku baku san duk fargaban aure bane, yanxu fa ana saukowa sallah sai daurin auren..." Abuturrab ya kalleta ta gefen ido ya mike ya fita daga dakin, Hajja tace "Toh Allah ya tsare Aliyu, Allah ubangiji ya sa a daura a sa'a ni dai" Sai bayan da suka shiga mota Abuturrab ya sake kiran Maimoon yaji wayar a kashe still.... Bayan an sauko Juma'ah aka daura aurensa da Aneesah a kan sadaki dubu dari biyu, abokan aikinsa sun masa solidarity sosai don sun samu halartar daurin auren, Ahmad don't want to believe yak'e kawai Captain yake, gaba daya he doesn't look someone happy but he is still smiling as if all is well, suna cikin mota Aneesah ta dinga kiransa yayi silencing wayar ya jefa cikin aljihu, El-Basheer yace "Ya dai da wannan shirun Capt, isn't today ur happy day, u are wedded to the love of ur life..." Captain ya gyara xama a motar yace "Okay saman motar ka so in hau don farin ciki?" Dariya El-Basheer yayi yace "Gaskiya that's what i was expecting, yau dai Aneesah da ka ishemu ta xama matarka" Ahmad dai driving kawai yake bai ce komai ba, El-Basheer yace "Nima Allah ya nuna min ranan da xa a daura min aure da xabin nan na Hajja duk da ban santa ba amma naji har ta kwanta min" Abuturrab ya kara gyara xama bai dai ce komai ba, Ahmad yace "Hajja ta maka wani xabi ne?" El-Basheer yace "Wllh fah, tace ta samar min mata so i will be next in sha Allah" Ahmad yace "A masar?" Dariya El-Basheer yayi yace "Aa nan kasar idan mun je yanxu xan sake tada mata xancen gaskiya don na zaku, yanxu fa ni kadai ne tuxuru cikin ku ko?" Ahmad yace "Atoh, ba dai ka tsaya wasa ba" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera still bai ce masu komai ba yana kallon wajen window. Suna isa gida Abuturrab ya bude motar ya sauka ya wuce ciki yana sake dialing number Maimoon still a kashe, ya wuce bangarensa kawai, Aisha ya kira bayan ya xauna gefen gado, yana fara ring ta daga yace "Maimuna sun dawo?" Tace "Aa suna wajen make up" Yace "A ina ake make up din?" Tace "Ni ban san wanda suka je ba, kasan ba waje daya muka tafi ba" Ya d'an yi shiru sai kuma ya katse wayar, Karfe hudu saura Jiddah suka shigo gida daga wajen make up, da farko taki yarda a mata make up amma sai da su Nafisah suka yi forcing dinta, idan ba sake kallonta kayi ba ma baxa ka ganeta ba, wato tayi kyau ne ba kadan ba duk da ba heavy make up aka mata ba, basu yarda sun sa ankon Dinner din daga can ba, suna shigowa compound suka hadu da Safiyya, Safiyya tace "Ke ina kika sa wayarki ya Aliyu na ta kiranki a kashe" Maimoon ta turo baki tace "Toh wai ma a ina ya samu numberta kuma me yake nemana xan masa?" Daga haka ta kara gaba su Jiddah na ta biye da ita, gud'a da ake ta yi a ciki ne ya tabbatar masu Amarya ta iso, don bayan daurin aure da awa uku aka kawota via flight tunda a kaduna xa ayi dinner din, Mutane ne cike gidan ba masaka tsinke, Maimoon tace "Mu tafi dakin Hajja kawai, kar ma a wani ya aikeni bayan nayi make up" a kulle suka ji kofar an sa makulli, wai ashe amarya na ciki, ga mutane cike bakin kofar dakin, Hajja ta bude kofar duk ta hada xufa cikin ubansun lace din jikinta ga dankunnenta na gwal dake ta sheki a kunnenta, cike da masifa take cewa "Wallahi ba a haka a Masar, mu bama haka a masar, bamu san haka ba a Masar, ita fa wannan amaryar ba ta gwal bace kowa xai ganta idan lokaci yayi, an wani xo an cika min kofar daki kamar ina bada sadaka, ni wllh idan xuciya ta debeni sai in mayar da amaryar tsakar gida yanxun nan, wannan fitina har ina" Maimoon ta dinga rabawa ta gefenta xata shige dakin Hajja ta fincikota tace "Kun ga bala'i ko, wacece wannan kuma" Maimoon tace "Hajja nice fa da su Jiddah don Allah ki bar mu mu shiga yanxu muka dawo" Hajja ta kankance ido tana kare ma Jiddah da Nafisah kallo tace "Shampoo aka ma fuskar ko me?" Maimoon ta shige ciki ta fixgo hannun Jiddah Nafisah ma ta shige dakin sai a sannan Hajja ta kulle kofar da makulli, Aneesah na can karshen dakin saman lallausan rug duk jikinta a lullube har fuskarta, daga gefenta kawayenta hudu ne, Hajja tace "Haba mutanen kasar nan kamar mayu ni Dijee, wllh har na yi adadin shekaruna a Masar ban taba ganin kwatankwancin haka ba, komai a nutse cikin tsari ake yin sa, duk fa rubabbu yan kauye ne suka cika bakin kofar, wani me kudin ne xai wani xo ya tsaya bakin kofa ya tsaya yace sai ya ga amarya kamar wata amaryar gwal, ba gata can na ganta ba sai hasken fata kawai malam, kawayen nata kuma duk bakake ne, kwalliya su ma ni ban gane kanta ba, Ai da sun sani su bari idan sun xo nan sai ku kai su inda aka maku kwalliyan Maimuna, naku yayi kyau sosai har ma ba na jiddah ba, wani ba sai yace ita ce amaryar ba" Maimoon ta dinga kunshe dariyarta, Aunty Nafisah tayi tagumi tana salati a xuciyarta, Ta cikin mayafi Aneesah da ta hade rai take leko Hajja, kawayenta kuwa sai danna waya suke ko wacce fuska a murtuke, Caraf idon Aneesah ya sauka kan Jiddah da ta durkusa jikin kujera, ita bata ma san ita ce jiddar da Hajja ke fadi ba don bata san sunanta ba, amma lkci daya ta gane ta, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallonta, Aunty Nafisah ta dau wayarta dake ring ganin Aliyu ke kiranta ta daga, yayi kasa da murya yace "Aunty su Maimunan sun dawo?" Aunty tace "Ehh yanxu suka shigo" Yace "Toh ki turo min su gaba daya yanxu ina mota a kofar gida" Aunty tace "Toh" katse wayar tayi tana kallonsu Maimoon da cikinta ya kada jin ance eh sun dawo, Aunty tace "Wai ku je Aliyu na kiranku kofar gida" Aneesah dai sai binsu take da kallo ta cikin mayafinta, Maimoon ta mike kamar xata yi kuka, Nafisah ma ta tashi suka nufi kofa, ganin Jiddah bata taso ba Maimoon tace "Aunty banda Jiddah yace ne?" Tace "Aa ya dai ce ku je ban san da wa da wa ba" Hajja dake ta fifita duk da fankan dake aiki a dakin tace "Toh me xa su masa har su uku haka, su dai su je, ina ruwansa da wata Jiddah da bata kula kowa a gidan, kilan wani laifin suka masa... Ita dai nasan ba ruwanta tayi xamanta su suje, bata shiga sabgar kowa" Maimoon tace "Laifi kuma Hajja, mu ba abinda muka masa wllh, ko ganinsa ma ban yi ba yau gaba daya" Daga haka ta fice daga dakin tare da Nafisah, ta cikin mutane suka dinga kutsawa har suka fita kofar gida, can suka hango motarsa nesa da gidan, suka nufi motar, ya sauke glass yana kallonsu, suna isa motar Maimoon tace "Yaya ga mu, daxu wayana ya mutu ne sai da na dawo yanxu na jona a dakin Hajja" Yace "Ku nawa ku ka je make up din?" Maimoon tace "Ni da Nafisah da Jiddah" Yace "Ita tafi karfin ta fito ne?" Maimoon tace "Hajja ce ta hanata ta fito wllh" yace "To koma ki kira min ita kuma kar ki fada mata gaban Hajjan" Maimoon tace "Toh" daga haka ta juya da Nafisah suka bar wajen tana sauke ajiyar xuciyar relieve, suna komawa dakin Hajja, Hajja tace "Kiran me yake maku?" Maimoon tace "Aa kawai dai tambaya yayi min" Tana fadin haka ta xauna kusa da Jiddah murya can kasa tace "Yaya Aliyu yace kije" Jidda ta xaro ido tace "Ni kuma?" Maimoon ta cunkuleta tace "Don't allow this old woman to know" Jiddah tayi kasa da murya tace "Tare xa mu je da ku?" Maimoon tace "Aa ni kaya xan sa yanxu, ya gama magana da mu, ke kadai xa ki je" Lkci daya jikin Jiddah yayi sanyi, bata dai ce komai ba ta mike har xata dau gyalen da ta saka yau ta tuna sai yayi mata fada, Hijab din Nafisah dake kan kujeran Hajja ta dauka ta fita daga dakin, tana fita gate sae ga motar Ahmad tare da El-Basheer da wasu abokansu.....


No comments

Powered by Blogger.