Jiddatul Khair 36


Jiddah ta juya tana Kallonsa, ya shigo ya kulle kofar, tana ajiye plates din a plate Rack tace "Ina yini?" A takaice yace "Ki daina gaisheni idan kin gan ni, bana so" tace "Toh" Ta dau plate daya ta bude warmer ta debi abinci still bata kallesa ba tace "Ya jikin" Yace "Ke yanxu a xatonki da tunaninki 'yancin kanki kika

samu ko?" Sai a sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, ya hade rai yace "Don kinga Maimoon na daukan mayafi karami ta saka ta fita titi kema sai kika fara saka mayafi karami, kin ma mance ke wacece koh" Shiru tayi bata ce komai ba ta kai hannu ta dau cokali, ya wani daure fuska yace "Kin saba saka mayafi daga can hayin rigasa ne, balle kuma gidana da kika xauna?? Kina tunanin ke da Maimoon daya ne?" Tace "To amma ai Umma ta gani bata ce komai, kaga da tace min in cire ai baxan sa ba" Yace "Toh daga yau ko nan da gate kada ki sake sa mayafi ki fita..." Da mamaki take kallonsa, can dai tace "Ko saboda me?" Yace "Saboda haka na fada" Bata kuma ce masa komai ba, yace "And yanxu kina ganin kin fi kowa freedom shi yasa kike shiga motar maxa har da xama gaban mota ko, uban wa ya ce ki bi ta ku hau motar wani kato har kika shiga gaba, a can hayin rigasar ku haka kike yi" Tace "Kamawa tayi in hau shi yasa na hau ba wani abu ba, kuma ai an san sa a gida" Bude baki yayi yana kallonta, yace "Kin san mene?" Ita dai ta xuba masa ido, yace "Akwai wani wanda yayi dalilin dawowarki cikin gari a duk wa enda kike xaune da su yanxu cikin garin kaduna??" Kallonsa kawai ita dai take, yace "Toh dama ai nine na fito da ke cikin gari, don haka yanxu sai in mayar da ke in da na dauko ki, duk me son sake fitowa dake cikin gari sai ya koma hayin rigasa ya dauko ki na musamman... Kin fahimce ni??" Murmushi kawai tayi tace "Toh" yace "Ehh, ni na raboki da baabarku kuma ni xan maida ki" Tace "Yaushe xan shirya kenan?" yace "Sai kin shirya ashe, dama kin xo da wani abun ne ban sani ba?" Tace "To shikenan" Ya jefa mata wani irin kallo ya fice daga kitchen din ta bi sa da ido, hawaye taji ya kawo idonta, ta rufe abincin ta fita ta koma daki ta kulle kofa ta kwanta saman gado tana iya kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba... Har karfe uku Jiddah na kwance daki, Huraira ta xo ta kwankwasa kofar jin an sa makulli tana kiran sunanta, Jiddah ta mike da kyar ta isa gun kofar ta bude Huraira tace "Jiddah malamarki ta xo fa tun daxu..." Shiru tayi tana kallon idonta tace "Me ya faru Jiddah?" Ta girgixa mata kai tace "Kaina ke ciwo" Huraira tace "Subhanallah, to ki fito Umma na kiranki" Komawa tayi ta dau hularta ta sa sannan ta fito dakin, a hankali ta nufi parlor ganin Umma da Hajja a xaune, ta sunkuyar da kanta ta xauna a kasa tace "Umma gani" Umma tace "Amma dai nace ki daina barin malamanki na jiranki ke ya kamata ki dinga jiransu ko Jiddah, dole sai kinyi wani bacci idan malamar safe ta tafi bayan kin san cewar dayar na kan hanya ita ma" Jiddah ta kasa dago kanta cikin sanyin murya tace "Kuyi hakuri Umma, ciwon kai nake" Sai a sannan Umma ta kalleta da kyau tace "Ciwon kai tun yaushe, shine kike kuka?" Ta girgixa ma Umma kai kawai, Umma tace "Toh kin ci abinci" Ta gyada mata kai kawai, Umma tace "Toh Allah ya sauke kije dakina akwai paracetamol kan bedside drawer ki dauka, amma xaki iya karatun kuwa yau?" Cikin sanyin murya tace "Xan iya Umma" Umma tace "Toh je ki dauka ki sha ki dau qur'anin ki ki fita, Allah ya sauwake" Mikewa Jiddah tayi ta wuce dakin Umma, Hajja tace "Mu dai ba gamu mun taho jinyan wancan mutumi da har yanxu tun wayewar gari ban daura ido a kansa ba" Umma tace "Na duba na gansa yana bacci daxu" Hajja tace "Ni wllh dama ki sa duk ya tattaro kayansa ya dawo gidan nan a rabosa da yar Benuen can, ko ya kika ga" Umma tayi wani murmushi tace "Ai baxai dawo ba, wnn ma nayi mamakin da ya yarda ya biyo mu, ina ga tunda yake bai ta6a kwana gidan nan ba ko da xai kai karfe sha biyun dare"  Hajja tace "To mu dai gamu ga Allah, amma Hauwa tayi sake ai, idan ta bar ta ta kwace miji sai ta yarda har d'anta ta kwace, nima fa don ban xauna a Masar bane a banxa shi yasa har yau bata rabani da Usman ba, kullum cikin tsayuwar dare nake, kyaga a rana sai ya kirani sau uku, to amma dai ba komai tunda Allah yayi min dawowa ba dai nace maki xan nuna nata nima yar banxa bace, Allah ya ba Aliyu lafiya mu koma gidan, na ma fasa komawa gidan Kabiru" Umma tace "Allah dai ya kyauta amma abun kam sai addu'a" Ahmad ne ya shigo parlon ya gaishesu, Umma tace "Ya jikin Ramlan" yace "Da sauki Alhmdlh" Hajja tace "Yaushe xaka sallami wancan mutumin mu koma gida in san ta ina zan fara da Hafsah?" Yace "Ai yace baya son drip din kuma, magunguna kawai yake sha" Tace "Atoh ya tarkata magungunan mu wuce gida kawai sai yayi ta sha a can" Duk suka kalli kofar Jiddah ta shigo parlon da sallama, Umma ta kalli agogo tace "Ciwon kan bai yi sauki ba kenan" Gyada mata kai tayi, Hajja tace "To Malamar fa?" A hankali tace "Tace inje in kwanta, ta wuce" Ahmad dake kallonta yace "Tun yaushe kan ke maki ciwo?" jiddah tace "Daxu" Yace "Toh je ki kwanta, Allah ya sauwake" Tace "Ameen" Sannan ta wuce daki ta kwanta. Har kusan karfe shidda Jiddah na daki tana jin kanta na mata wani ciwo ba kadan ba, Umma ce xaune parlor tare da Abuturrab da fitowarsa parlon kenan, Umma tace "Ka bari gobe ka tafi" Ya kalleta amma bai ce komai ba, tace "Kuma ka bude kunnenka sosai ka saurareni" Still shi dai bai ce komai ba yana kallonta, tace "Hafsah kanwar uwarka ce ko ta Ubanka?" Sunkuyar da kansa yayi, tace "Toh bari kaji Aliyu, wllh idan kana son ka dinga ganin dai dai a al'amuranka ka fita harkar matsiyaciyar nan ka kama uwarka..." Da mamaki yace "Me tayi kuma Umma?" Umma tace "Ni kake tambaya me tayi?" Yayi kasa da kai yace "Toh Umma naga dai lafiya suke xaune, kuma ita Aunty..." Umma tace "Tashi ka bani waje mara hankali kawai" Ya kalleta yace "Aa kiyi hakuri Umma" Cikin daga murya tace "Ka fini sanin lafiya suke xaune ko ba lafiya suke xaune bane?? tunda nake ban ta6a ganin d'an da ya hofintar da uwarsa ya dauketa ba komai ba yake bama Kishiyarta muhimmanci fiye da tunanin mutum kamar kai ba, anya kana son gamawa da duniya lafiya Aliyu?? Anya kana son ganin dai dai a rayuwar ka?? Uwa fa??" Kasa ce mata komai yayi yana ta kallonta da mamaki, to me Ummi tace ya mata?? tace "Toh wllh rayuwarka na cikin tashin hankali da garari don ma kaji in gaya maka yanxu" A sanyaye yace "Umma da akwai wani abun da nake yi ne ni ban sani ba? Ko da akwai wani abun da tace na mata ne" Tace "Kaje ka xauna kayi karatun ta nutsu bani xaka yi ma nonsense question din nan ba" Bai kuma cewa komai ba maganganunta na yi masa yawo a kai, shi a iya saninsa babu abinda yake ma Ummi yana mata biyayya yanda d'a ke ma uwa, to what is Umma talking about" Sake daga kai yayi yana kallonta yaga irin kallon da take masa tana girgixa kafa, ya shafa kansa a hankali bai ce komai ba, can kuma dai yace "Toh Shikenan xan je in bata hakuri, duk da ni dai ban san me nayi ba" Bai jira me Umma xata ce ba ya mike ya wuce dinning don tun daxu abincinsa ke can, Umma ta bi sa da kallo tana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ranta, lamarin Abuturrab anya lafiya kuwa?? Ahmad ne ya shigo parlon, Umma tace "Da wannan safa da marwan da kake a kan titi meyasa baxa ka dawo da Ramlah gidan nan ba Ahmad" Ya shafa kansa yace "Toh Umma" Umma tace "Kayi knocking ka shiga ka duba Jiddah don Allah" Yace "Alright" Abuturrab ya bi sa da kallo har ya wuce, sai da ya fara knocking Jiddah ta taso ta bude kofar ganinsa ta koma gefe kanta a kasa tace "Ina yini" ya dinga kallonta yace "Wai ciwon kan kike ma kuka Jiddah?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci" Tace "Na ci" yace "Jikin ki da xafi?" a hankali tace "Nima ban sani ba" Toh bari in siyo maki magani yanxu in dawo" Yana fadin haka ya juya ya koma parlor, yana kallon Umma yace "Umma let me get her drugs, har yanxu bata jin dadi" Umma ta mike ta tafi daki wajen Jiddah, Ahmad ya karasa gun Abuturrab yace "Kayi bacci sosai ai ko?" Yace "Yau nake son xan koma gida" Ahmad yace "Ohk toh, bari in dawo xan siyo ma Jiddah magani she isn't feeling fine" Daga haka ya dau makullin motarsa ya fita. Bayan magrib Jiddah na xaune parlor bayan ta sha drugs din da Ahmad ya siyo mata, tana cin shinkafa da miya da Maimoon ta kawo mata, a hankali take cin abincin don baya ranta, gaba daya ji tayi xuciyarta babu dadi, Safiyya da Maimoon na haddansu a daki, Hajja da Umma kuma na daki, ita kadai ce xaune parlon sai Huraira dake wanke wanke a kitchen, tun da ya shigo parlon ta kallesa sau daya bata sake kallonsa ba, ya karaso tsakar parlon, ita dai taki yarda ta kallesa, looking at her directly yace "Don nace xan mayar da ke in da na dauko ki shine kika fara rashin lafiya, sabida baki da intention din sake komawa gidanku, ni ban ta6a ganin wanda ke gudun gidansu ba sai a kanki, ai xamanki a can xai fiye maki xama gidan mutane...." Ta daga kai ta kallesa tace "Toh sai ka mayar dani ai yanxu, ni bana tsoron komawa gida... Saboda nasan Allah na tare da ni, ko kaji nace maka baxan koma ba?" Yace "Toh sai ki tashi ki dauko hijab din naki yanxu" Mikewa tayi ta wuce daki, shi ma ya tafi dakin Ahmad ya dau makullin motarsa, Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Ba Umma tace ka bari gobe ba" Ba tare da ya kallesa ba yace "Ehh ba nisa xanyi ba, i want to get something" Bai jira cewar Ahmad ba ya nufi kofa ya fita, Jiddah na daukan Hijab dinta dake linke Maimoon ta kai karshen ayan da take karantawa, tana kallonta tace "Ina xaki?" Jiddah taki kallonta balle taga hawayen dake makale idonta tace "Xan amso abu wajen Maman Abdallah ne" Daga haka ta fita dakin, yana tsaye bakin kofar parlor alamar ita yake jira, ta nufi kofar, muryar Hajja suka ji tana cewa "Ke ina kuma xaki da daddaren nan bayan nace ki min linke uwar rikon ki ta daure maki kugu wai baki da lafiya?" Jiddah ta kasa juyowa, Abuturrab na ganin Hajja ya fita parlon ya tsaya balcony, Ahmad ne ya shigo parlon shi ma yana kallon Jiddah yace "Where are you going to Jiddah?" Still bata juyo ba hawaye na sauka idonta tana gogewa da hannunta, ya karasa ya tsaya gabanta yana kallonta, buda ido yyi sosai ganin kuka take, yace "Me ya faru Jiddah" Hajja ma ta karaso tana kallonta tace "To ko dai tana da mutanen boye ne Ahmad?" Ahmad dai bai ce komai ba sai kallon Jiddah yake, Hajja tace "Aa ba ruwana bari in kira Ramlah kar abu ya lalace mana" Tana fadin haka ta tafi da sauri, Ahmad yayi kasa da murya yace "Gaya min me ya faru Jiddah, kuma ina xa ki?" Ta kasa cewa komai sai hawaye, Hajja ta dawo tare da Umma, Umma tace "Jiddah" Juyowa Jiddah tayi da jajayen idonta tana kallonta, Umma ta karasa kusa da ita tace "Me ya faru?? Kukan me kike, an maki wani abu ne" Shigowa parlon Abuturrab yyi xai wuce daki, Jiddah na kallonsa tana share idonta a hankali tace "Ce min yayi xai maidani inda ya dauko ni tunda shi ne ya kawoni dama ba wani ba" Gaba daya duk suka juya suna kallon Abuturrab da yaki kallonsu kuma yaki tsayawa, cikin tsawa Umma tace "Dakata a nan Aliyu" Ba musu ya tsaya amma bai juyo ba, Hajja ta marairaice tace "Wannan wani irin Bala'i ne Usman ya haifo Ramlah?" Umma ta kalli Jiddah fuska a daure tace "Gaya min abubuwan da ya fada maki" Cikin rawar murya Jiddah tace "Kawai haka nan yace, wai duk me son daukoni sai ya je ya dauko ni idan ya maidani hayi" Umma tace "Yanxu Hijabin da kika sa hayin xai kai ki?" Jiddah ta gyada mata kai, Hajja tace "Amma daga d'an iska sai Aliyun nan wllh, Muna ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe dabanci xai xo yayi mana a nan ni Dijeee, anya kana son gamawa da duniya lafiya kuwa d'an nan, ashe haka kake Aliyu" Cikin dakewa Umma tace "Aliyu!!" sai a sannan ya juyo ya kalleta tace "Xan baka takarda kayi list din duk abinda ka kashe ma Jiddah tun daga lkcn da ka fara saninta har xuwa lkcn da ka rabu da ita, idan ma kudin sun fi karfina xan kai ma Abbanka ya bada su, sannan after that wallahil azeem ka sake kallon inda Jiddah take, i mean ka sake kallan min ita wllh sai ka sha mamakina a duniyar nan, xan maka tijara Aliyu, babu kai babu Jiddaha har abada, idan kuma kai ka cika d'an halaq ka dauketa ka mayar da ita hayin kaga, sannan maxa ka kama hanya ka koma gidanku kada ka sake xuwa min gida, idan kuwa kayi gigin xuwa sai nayi maka walakancin da baka ta6a xato ba" Hajja tayi mitsi mitsi da ido tace "Algungumi kawai, ana ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe shi abinda xai kawosa nan gidan daban, to wllh har abada kai da wannan baiwar Allahn don ta ma fiye min kai sau dubu yanxu tunda bata ta6a xagina ba balle manyanta, kai kuwa idan aka ce xa a kirga adadin xagin da ka min ai sai da a tafi kotu don xuciya xai iya dibana inki yafe maka, to meye kuma xaka sa yar mutane a gaba bayan an raba ku, ko dai har yanxu sonta kake bamu da labari? Banda tsautsayi ma da ya fada mata me xata yi da d'an banxa irin ka?" Umma da taji xuciyarta na tafarfasa tace "Wato shi yasa dama babu musu ka yarda ka biyomu don ka ci mata xarafi da mutunci, to wllh kayi na farko kayi na karshe, Jiddah da kake gani tafi karfin walakancinka yanxu tunda ba kai ke ciyar da ita ba, wanda kayi a baya ma duk nace kayi list a biyaka" Hajja tace "Ko ni sai in dage gidana daya in siyar a biyaka wllh" Sai a snn ya kalli Hajja yace "Saboda nace maki don ke nayi da xaki biyani" Da karfi Hajja tace "Huuuuu ka dai ji kunya duk ka xubda ladanka, gantalalle kawai" Ta gefen ido ya kalli Jiddah dake share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai Ahmad ya ma rasa abun cewa sai kallon Abuturrab yake da mamaki, kofa Abuturrab ya nufa ba tare da ya kallesu ba kamar xai tashi sama, Hajja ta dafe kirji tace "Mu ka xaga ka fita Aliyu?? Mu??" Ko kallonta bai yi ba har ya fice gaba daya, da karfi Hajja tace "Wawa kawai me xuciyar Hafsah, da kyar idan matar nan bata faki idon Hauwa kana jariri ta dura maka nononta ba, don babu halinta da ka xubar al-qur'an" Umma na kallon Jiddah tace "Daga yau ko gidan uban wa kika hadu da shi kika sake kallon inda yake balle ki gaishesa ko wata magana ta hadaki da shi sai na sa6a maki, babu ke babu shi har abada, a duk inda xa ku hadu kuwa...." Hajja tace "Dama kina ganinsa ki gudu kiyi ta kanki, ko kuma ki fasa ihu kawai idan wani taimakon ne a kai maki da gaggawa, ni ai nafi kowa sanin halinsa tunda a hannuna aka haifesa, sau nawa idan an bata masa rai yake take kaza ya kasheta har lahira a lkcn ma yana d'an mitsitsi.... Yanxu ai sai dai ya take d'an mutum" Jiddah dai kanta na kasa, Hajja tace "Kuma tun ban tafi Masar ba ya xama d'an daba fa, fada ne kawai banyi ba kar uban ya kullaceni nayi tafiyata bakina alekum, wa ya sani irin mugun abun da ake koya masu idan sun daga jirgi sama, shi sa har yau ban yarda na hau jirgin da yake ja ba wllh ko don yanda ya tsaneni ma ba sai ya sake jirgin da gangan duk mu hantsulo kasa ba" tana fadin haka ta nemi waje ta xauna tana fifita saboda xufan da ta hada don bala'i, Umma na kallon Jiddah tace "Dauka abincinki ki wuce daki" Jiddah ta karasa a hankali ta dau abincin ta wuce daki, Hajja tace "Ni wllh don baxa ku yarda bane amma da kun bani yarinyar nan kawai in tafi da ita" Umma tace "Sai dai taje maki hutu" daga haka ta bar parlon. Jiddah ta maida hankali sosai a karatunta babu wasa, wanda hakan yasa Umma ke kara jin sonta a rai domin kwazonta ya wuce misali, both Islamic da western din duk she's flowing well, kusan duk bayan kwana biyu Yousuf ke xuwa gidan da daddare, kuma duk idan ya xo ba wai wani hira suke da Jiddah ba iyaka ya sake guiding dinta a karatun nata shi ma, yawanci kuma turanci yake nace mata ta koya, kuma babu laifi she is really catching up, duk weekend Ahmad ke shigowa kaduna sbda duba Ramlah dake laulayi, shi ma kuma yana assisting din Jiddah a bangarori da dama na karatunta. Umma na parlor ranan wata asabar Jiddah ta fito rike da wayarta dake ring ta karaso ta mika mata, Umma ta amsa tana duba me kiran nata, Ganin Ummi ke kira ta daga, bayan sun gaisa Ummi tace "Toh sun gama hada lefensu wai sai ki xo ki gani gobe xa a tafi da shi" Umma tace "Kai ba lallai ba yaya, Allah ya sanya alkhairi kawai" Ummi tace "Aa da dai ki daure ki xo din Ramlah xai fi" Umma ta d'an yi shiru kafin tace "Allah da kawai kin bari su tafi da shi goben Yaya, ai ba sai na gani ba" Ummi tace "Toh ni kuma nace ki xo ki gani" Umma ta d'an yi shiru sai kuma tace "Toh shkkn, bari ruwan ya tsagaita xan sa driver ya kawo ni ko da yamma ne" Ummi tace "Allah ya kai mu" ajiye wayar tayi ta ci gaba da kallon da take a Tv. Da yamma kamar yanda Umma tace ta shirya wajen karfe biyar ta fito parlor tana kallonsu Maimoon da basu je Islamiyya ba sbda ruwan da aka yi, tace "Xa ku je can gidan ne ganin lefe?" Maimoon ta mike da sauri tace "Eh Umma dama ina tsoron gaya maki ne" Umma tace "Toh sai ku shirya ni ina ruwana kuma da xan hana ku" Maimoon da Safiyya suka mike gaba daya, ganin Jiddah bata motsa ba Umma tace "Ke baxa ki ba Jiddah?" jiddah ta girgixa kai tace "Aa xanyi assignment dina Umma" Umma tace "Ai ba dadewa xa muyi ba, tunda babu kowa gidan kawai ki shirya mu je yanxu xa mu dawo, idan muka tafi ma babu ke Hajja sai ta fassara mu tace ba a haka a Masar" Jiddah bata iya tace ma Umma komai ba, amma ba don ranta ya so ba ta mike ta wuce daki, Hijab ta saka suka fito parlon tare da su Maimoon......


No comments

Powered by Blogger.