Idon Naira 4

 


*_IDON NAIRA_*

_Mamuhgee_

_Arewabooks@Mamuhgee_

_ZAFAFA BIYAR 2023_4*_MAAB LUXURY HOME_*🔥🔥


_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._


_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._


_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_


*_MAAB LUXURY HOME_*

*_MAAB LUXURY HOME_*

*_MAAB LUXURY HOME_*


_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _


_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_


_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._


_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _


_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._


_FACEBOOK: @maabluxuryhome._


_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_


_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_


_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_

______
********

Kasancewar maryamah nason kalolin abinci daban daban Kuma ta saba yiwa Alh Asad na Wanda ake fitarwa harabar gida da dare yasa ta Sanya zainab gurin koyan abinci Amma a online tareda siya Mata wata Yar tab wadda da ita take sake koyan komai.


Da farko zainab na Shan wuyar gane kan lamarin tab din gabaki daya kafin ma gane abinda take koya din 

Amma sanin koyar Dole ce a gareta kaman yanda aikin tasani Dole ne itace wadda zata ringa yi har lokacinda Allah zai yanke Mata wahalar Dan haka ta ringa takura kanta tana dagewa gurin fahimta da koyon har Allah yasa ta Dan fara fahimta sosai.


Sbd yanda take tsananin kiyaye doka da shakkar keta kowace irin sharadi da iyakar da maryamah ta ajiye tareda dorata akai yasa yanda ta maida hankali da nutsuwa a gurin koyan girki da sauran ayyukan gidan ko karatunta bata bawa wanna kulawar da mahimmanciba.


Ahakan saida ta Dan dauki lokaci kafin ta iya gane kan tab din harma da abinda take koya din Wanda kullum da abinda take girkawa na abinda ta koya sai gashi tafara qwarewa musamman da Inna Karima Tana qara fahimtar da ita wasu abubuwan.


Ana hakan Maryamah ta Kuma samun wani ciki me laulayi sosai kala  kala 

hakan ya sanya Zainab sake zama busy da ayyuka sbd kusan yanzu idanba aikin zainab dinba daga Alh Asad har maryamah din basa son aikin kowa

Dan haka samun cikin yasa hidimar kulawa da buqatun maryamah suka ninkar Mata wata Rana ma ko makarantar Bata samun zuwa sbd tarin ayyuka.


Yanayin laulayin maryamah me wuya ne sbd yawan amai yake sata sosai Wanda yasa yanzu a wuni so uku ko so biyu take wanke toilet din dakin maryamah din bayan gyare gurarenda wani lokacin anan yake kufce Mata.


Samun cikin maryamah yasa zainab ta qarasa figewa kamar kamun yunwa sbd rashin Hutu.


Zainab bata ga amfanin Inna Karima ba a gidan don yanzu hutawa kawai takeyi girkinma an sakar Mata na Rana ne kawai ba ita keyiba sbd kafin tadawo makaranta tayi lokaci ya shige shi dinma Tana gamawa take komawar boys quarters ta shigewarta ita kuwa Sam hidimar Maryamah baya ƙarewa, bata da wani cikakken hutu sai idan dare yayi.


*******

Alh Asad a lokacinda ya fahimci karatun Zainab din Yana rawa sbd tsallaken kwanakin zuwa saiya Dan tsaya Mata a wannan fannin ya saka dokar zuwanta makaranta duk kuwa aikin datakeyi ya soke Mata na lokutan zuwa makaranta dole Inna Karima tadawo yin wasu daga cikin aikin da ake biyan Dan tayi.


Daga wannan lokacin tasamu Tana zuwa makaranta ba dauke Rana saida ayyukanta Kam Babu Wanda ya ragu suna nan yanda suke saidai kawai ace Allah ya kyauta.


Alh Asad mijin Yar uwar tata ne kawai zatace yake kulawa da ita amatsayin Yar Adam Kuma jinin matarsa sbd duk wata kulawa da abubuwan buqata shine ya tsaya Mata kaman babban Yaya kokuma tace kamarma mahaifi sbd ya Isa haihuwarta.


Yanzu rayuwarta takeyi a natse cikin tawakkali da rungumar wannan rayuwar sbd ta Gama yarda da hakan shine tata rayuwar.


Sam Bata damuwa ko Jin takaicin yin Aiki ko daya yanzu haka zalika ma jikin nata ya saba da wahalar batajin komai yanzu saima sake nutsuwa datayi akan komai.


Sai da cikin maryamah ya shiga watanni shida sannan Maryamah din ta sama sauƙin laulayin da ta ke yi Dan haka yanzu wasu lokutan hidmar maryamah din da sauki 


Cikin Maryamah Yana cika watanni bakwai haihuwar gaggawa tazo Mata qarshe aka haife cikin Babu rai 


Babban tashin hankali suka shiga daga alha Asad din har maryamah da Yan uwansama musamman mahaifiyarsa Amma haka suka fawwala ubangiji suka dauki qaddara.


Bayan wata biyu takuma samun wani cikin ko wata biyu bai rufaba shima ya bare,


A qataice saida ta dauki ciki so hudu duk ana rasawa kafin takuma samun Wanda ko wata biyu be rufa da samuwaba mijinta ya tattarata suka tafi India acan tayi renon cikin qarqashin kulawar wani likita har saida cikin yakai wata bakwai suka dawo sbd dukansu sunfi shaawar haihuwa acin Yan uwansu.


Bayan tafiyarsu maryamah zainab ta kammala karatunta na secondary 

Kuma tafiyar tasu wani nauyi ne me girma ya hau kanta Dan kuwa duk hidimar kula da gidan da duk Wanda yake gidan kanta dawo Dan kuwa Jin tayi kaman anbar Mata wata gagarumar Amana gashi Sam a duniya Bata kaunar abinda zaisa tayiwa 'yar uwar tata laifi ko abinda zai Bata ranta sbd kaucewa damuwar abinda zaije ya dawo.


******

Lokacin da cikin Maryamah ya shiga watanni tara a lokacin ne Zainab haka kawai itama taji Ta kaunaci haihuwar  anty Maryamah din da wuri musamman ganin yanda kusan kowa ya qwallafa rai a haihuwar da abinda zaa Haifa din.


Cikin na shiga wata Tara da sati biyu 

Cikin dare naƙuda ya kama Maryamah Alh Asad ya wuce da ita zuwa asibiti bayan ta sha matuƙar wahala daf da asuba ta haifo yaronta me Kama da ita sosai kyakkyawa dashi Kuma lafiyayye babba dashi. 


Ko kaɗan Zainab ba su san bikin da ake ba sai da safe da Maryamah ta kira wayarta ta shaida mata haihuwar tare da bata umurnin girka abincin breakfast da duk wani abinda ta ke buƙata ta sanar da ita cewa Alh Asad zai dawo su taho tare da ita zuwa asibitin sbd ba za a basu sallama sai zuwa can rana an sake tabbatar da lafiyarta da na Babynta.


Zainab sauke wayar daga kunninta tayi tana jin wani boyayyan farin cikin da tsawon wayonta batasan ta taba yinsaba,


can ƙasan zuciyartata jin wani irin ɗokin son ganin yaron Maryamah tayi  haka kawai duk da tasan ita dashi saidai hange Amma Zataso abata shi Koda so daya ne ta Dan dauka Dan tasan ba lallai tasamu nata rabonba kila Dan bataga alamar zata samu tata rayuwarba idan ba Allah ya riga ya nufa ba.


Aikin da Anty Maryamah din ta bada umarnin ayi tafara a tsanake kaman yanda tasan Anty Maryamah din na buqatar komai.


Tana gamawa ta harhada ta shirya komai tsaf taje tayi wanka ta shirya da sauri sbd kada ta saka megidan jira 

Ta fito hanyar Palo dauke da kayan ta tsaya Tana jiransa har saida ya Gama komai ya fito daukeda wasu kayan na na babies cikin qatuwar paper bag.


Da sauri ta karba cikin girmamawa kanta a qasa aka saka mota tashiga gaban motar tareda driver a rakube kaman Yar Aiki shikuma maigidan Yana baya yanata amsa wayoyin Taya murna daga yan uwa da abokan arziki.


Isarsu asibitinma itace tayi ta kwasar kayan Tana kaiwa Tana dawowa ta dauki wasu ganin wahalar tai Mata yawa yasa Alh Asad din Karban Mata wasu kayan suka shigo ciki gabaki dayansu.


Yan uwan Alh Asad dinne cikeda dakin da Maryamah din take anata murna da farin cikin samun babyn 

Bama kamar 'yan dakinsu Alh Asad din dasuka fi kowa murna sai yawo suke da babyn a tsakanin junansu.


Daga nesa Zainab ta saukar da kyawawan idanuwanta akan babyn dake hannun mahaifinsa nade cikin farin tattausan bargon babys 

Take taji ya burgeta har cikin ranta Kuma sai taji Tana kaunarsa duk da tasan ita da 'dan gatan sai gani sa hange Dan haka ta zare ta fice dakin Takoma waje ta zauna Tana kallon mutane masu wuce 

Marasa lafiya da masu lafiyar.


Sai guraren Sha biyu familyn Alh Asad suka fito suka tafi 

Dakin yakoma daga Maryamah sai jaririnta sbd Alh Asad yabi Yan uwan nasa yayi masu rakiya zuwa motacinsu.


Tasowa tayi a natse zta dawo dakin tareda tura kofar dakin tashigo ahankali Tana kallon yanda Maryamah take rungume da babynta cikin so da kauna.


Qarasowa tayi gefenta cikin ladabi da girmamawa da kulawa sosai tace"


Anty sannu,

Allah yabaki lafiya ya raya babyn.


Amin" Maryamah ta amsa tana kallon yaron Tana Jin sabon sonsa na ratsata.


Daga ita har Zainab gabaki daya idonsu da hankalinsu nakan fuskar babyn suna Jin kaunarsa a tare Tana shigarsu.


Shigowar Alh Asad yasa Zainab matsawa daga baya ta koma gurin kofa ta tsaya 


Ya waiwayo ya kalleta cikin kulawa fuska a sake yace"


Zainab Kingani kin samu 'da ko?


Dan sunkuyar dakai tayi Tana Dan sakin murmushin karfin Hali Tana gyada Kai tace"


Nagani Allah ya rayashi.


Amin Amin Zainab,

Kin karbesa kema kin taba kuwa?


Kallon Anty Maryamah tayi kafin ta Dan girgixa Kai ahankali.


Karbo jaririn yayi ya miqa Mata Yana cewa"


Gashi kema ki saka Masa albarka Tunda 'dan ki ne kema.


Karban babyn tayi hannuwanta na Dan rawa ta matso dashi jikinta ahankali ta Kama da kyau Tana kallon fuskarsa cikin wata irin kauna da kulawa....


Kaunarsa ta sanyata murmushinda tun rasuwar mahaifinta batai irinsaba na tsakani da Allah daya fito daga tsakiyar zuciyarta.


Yanda take kallonsa kaunarsa na bayyanuwa a fili fuskarta yasa Maryamah zuba Mata ido a karon farko rayuwarta Tana qare Mata kallon tsaf.


Komai na Zainab din kusan na mahaifinsu ne,


Dashi take kama sosai sabanin ita da mahaifiyarta ta debo sak sai dai hancin mahaifinsu da ido data biyo itama.


Tsakanin itada Zainab din baasan Wanda yafi sahirtaccen kyauba,

Duk kyanta ganin takeyi kaman Zainab zata iya finta idan tasamu rayuwar nutsuwa da Hutu gata yarinya yanzu take cikin budurcinta da 'yan matanci.


Mamakinta na biyu yanda Zainab ta bayyana Tana kaunar abinda ita din ta Haifa Wanda Bata taba tunanin hakan ba.


Dauke idonta tayi daga kan Zainab din ganin zata dago ta kalleta gudun kada taga Tana kallonta,

Amma Kuma yanayin yanda Zainab din ta rungumesa da kyau Tana Masa kallon kauna daukeda murmurshi a fuskarta yasa taji kaman mahaifinsu ne yake bayyanarda kaunarsa ga jinjirinta sbd Zainab ta zama kaman ita kadaice jinin mahaifinta Tunda basuda danginsa dama zai iya tunowa dasu.


Babyn na hannun Zainab Alh Asad ya karbesa yayi Masa huduba tareda kiransa da suna *_MUHAMMAD AQEEL_*


Sunan babyn Zainab ta maimaita a cikin ranta cikeda kaunar yaron tasake cewa Allah ya rayasa"ahankali.


Sai guraren 12 na Rana aka sallamesu suka dungumo suka dawo gida.


Koda suka iso gidan Zainab hidima ta sake ninkuwa Dan kuwa gidan rikicewa yayi da baqi kala kala Yan zuwa barka,


Tun batajin komai har jikinta yafara gaya Mata sbd abinci wani kan wani haka takeyi ga shara kusan so hudu takeyi a wuni sbd yawan jamaar daketa yawon zuwa barka Kuma kusan dukansu dangin Alh Asad ne da jamaarsa sbd mutum ne me jamaa sosai.


Washe gari qanwar umma ta iso wadda itace zataiwa Zainab din zaman jego.


Zuwanta yasa wasu ayyukan suka Dan ragewa Zainab Dan itace me girkin abincin Maryamah Dana Maigidan

Itakuma Tana na baqi da masu Aikin gidan da share share.


Suna saura kwana biyu umma tazo tareda wata matar qaninta.


Zuwan umma ko Maryamah kila batai farin cikin da Zainab tayiba saidai a iya zuciyarta ne Tunda batada kusancin dazata bayyanar Amma dai ita kanta umman taga murnar zuwanta a tattareda Zainab din 

Itama Kuma ta yaba da yanda taga Zainab din na hidima sosai da kulawa da gidan Maryamah.


Haka dai ta ringa hidima Bata zaune Bata tsaye har saida akai suna aka watse kowa ya Kama gabansa.


Bayan suna Inna Karima ma tafiyarta tayi sbd ganin yanzu ragamar komai ta Aiki da kula da gidan yakoma hannun Zainab wadda take ganin ta sameta Amma tafita samun matsayi agun Maigidan Dan kuwa ko dunkunan biki Alh Asad zannuwa masu kudi ya siyawa Zainab din duk da Bata wani sakaba sbd aiki da hidimar Kai kawo har aka Gama biki aka watse Bata samu kantaba


Daga qarshema da umma zata koma lace din babba me tsadar da atampar daya ta Bata ita Kuma ta dauki atampar daya Dama kala uku ne.

##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.