Idon Naira 3


 *_IDON NAIRA_*

_Mamuhgee_

_Arewabooks@Mamuhgee_

_ZAFAFA BIYAR 2023_




3

Wata biyar da yin bikin Maryamah Zainab ta shiga Ss1 alokacin Kuma Allah yabata ikon saukar hizifi talatin na alqur'ani daga Nan zuwanta islamiyya yafara qaranci sosai sbd ayyukan dasukai mata yawa na gida,


Barin Maryamah gidan memakon yasa Umma janta ajiki ko yayane dakuma samun saukin ayyuka sai hakan bai samu ba don kuwa Umma tsakaninta da umman umarni da aiki ne sai aikenta datakeyi kaman engine Sam duk nisan anguwa yanada wuya tabata kudin mashin ko a daidaita da qafa take zuwa wani lokaci idan nisan nada yawa sosai shine zata Bata kudin zuwa ta dawo da qafa.


Tariga ta saba aikin Bata mata rai hakama batajin qyashin yinsa,

Akan lokaci takeyin komai tunda safe Idan ta tashi aikine kaman jaka sai dare take samun damar kwantar da kafadunta taji sanyi sanyi ajikinta,


Shara,wanke wanke,wankin kayanta Dana umman,girki da sauran ayyukan komai itace hatta yankar farcen umman itace takeyi mata duk qarshen sati tareda tsifar Kai danma Bata iya kitsoba da itace zatayi mata har shi din.


Duk wannan bautar Batajin haushin umma sbd Bata rasa ciba ko sha hakama sitirar sakawa ana Bata kwancen maryamah ta rage ga karatunta tanayi Alh Barr ya dauke nauyin komai nasu Babu abinda suka rasa na Jin dadi duk da ita Yar kallo ce kawai.


Dangin mahaifiyarta mutum daya ya taba zuwa dubata so daya daga qauyensu 

Koda yaga alamar batada gadon komai da mahaifinsu yabari aka raba sai ya tattara ya tafiyarsa batareda ya sake waiwayotaba Dan haka itama batasan Ina sukeba bare inda zata samesu kota sani batada ikon kanta sai abinda umma ta zartar akanta.


Maryamah nacika wata bakwai a gidanta tasamu ciki mai tsananin wahalarwa da laulayi mai wuya Dan haka hankalin ummanta ya tashi Dan kuwa tuni aka kwantar da maryamah din a asibiti gashi basa gari itada mijin nata suna Abuja Dan dawowarsu daga Umrah kenan suka tsaya Abuja sake hutawa kafin su dawo.


A wahale tayi sati daya a asibitin suka sallamota suka tattaro a ranar suka biyo jirgi suka iso gida.


Dawowarsu da washe gari umma ta tafi dubota acan ta wuni Dan haka sai kusan dare tadawo gida lokacin zainb tagama zaman jira a tsakar gidan harta shige daki bacci ya dauketa.


Rashin lafiyar maryamah yasa komai ya rikice a gidanta gashi masu aikinta biyu duk ta koresu sbd rashin tarbiya da nutsuwarsu gashi Alh Asad mai ilimin addini ne sosai Kuma har lokacin duk bayan sallar magriba zuwa ishai karatun addini sukeyi sosai shida malamansa a harabar gidan wani lokacin kuma a masallacin kofar gidan Dan haka idan akai sallar magriba bamai iya shigowa gidan sai bayan ishai.


Ayyukan gidan Dana rashin lafiyarta suka taru suka cakude gashi lafiyayan abinci ake fiddawa idan sungama karatu shida malamansa suci acan Dan haka ba shiri takira umma akan a nemo mata wasu masu aikin.


Kafinma a samo masu Aiki sai gata an sake kwantarwa a asibiti Dole umma ce taje tayi jinyarta a wani babban tsadadden private hospital Alh Asad ya ringa zuba kudi sosai ana kulawa da matarsa wadda itama yanzu koina haj maryamah ake kiranta dashi.


Kwanciyar Maryamah asibiti yasake tsananta ayyukan Zainab sbd itace take abincin safe driver yazo ya dauka,

Hakama tayi na Rana hakama tayi na dare,

Tun shekarunta Basu gama kaiwaba ta iya kusan komai daidai gwargwado.


Ranarda aka sallami maryamah suna kawo umma gida Basu wuceba tasaka Zainab hada Yan kayanta tasakata binsu sbd ayyukan gidan maryamah din dakuma kula da cimar maryamah daketa fama da laulayin zabar abinci.



Zainab batada zabi ko ikon kanta sai yanda akai da ita Dan haka jiki ba qwari ta debo Yan kayanta da Basu fi kala biyarba ta fito tabi driver zuwa gidan maryamah da Bata taba zuwaba cikin wata lafiyayar Jeep black data gama daukan sanyin AC.



Babban gida ginin masu arziki na zamani sai daukan ido yakeyi ga masu gadi har biyu a gidan Nan zainab taga sun shige ta tabbarda Nan ne gidan 'yar uwarta maryamah Dan haka Bata wani qure koina da kalloba ta sauke kanta tareda sauke numfashi sbd duk wani abu daya shafa maryamah baya baya takeyi dashi tareda nutsuwa sbd yanda alaqarsu take Sam idan ba gaisuwaba Babu abinda maryamah takeyi da ita Dan haka ko yanzu dinma sanyi jikinta yayi Tana tsoro tsoron idan maryamah din tasan da zuwanta da umma tasaka.


Har kofar shiga babban palon dazai sadaka da cikin gidan yakaita ya babbuga kofar tareda juyawa yabar gurin.


Yana barin gurin wata dattijuwar me Aiki da aka kawowa maryamah daga gidan hajjar Alh Asad ta bude kofar Tana kallon Zainab da a Dan fizge Tana diban kama da maryamah Amma ba'a ganewa Kai tsaye.


Shigowa sukai bayan Zainab ta gaida matar kanta a qasa..


Babban palon alfarma ne da kusan Babu abinda ya rasa na tsarin gidajen masu arziki,


Sanyin AC da qamshi tako Ina tashi yakeyi Dan haka sai jikin Zainab ya sakeyin sanyi Dan kwata kwata rayuwarta Bata taba zuwa irin guraren Nan ba.


Can hanyar kitchen aka nufa da ita matar tace ta jirata anan bara taje ta sanar da Haj maryamah din.


Saida Zainab tayi kusan mintuna ashirin agurin kafin Maryamah ta fito sanye cikin wata maroon jallabiya 

Fuskarta da fatarta sai sheqi sukeyi tayi haske sosai taqara wani irin lafiyayyan kyau da kiba duk saita sauyawa Zainab din kwata kwata kaman wata balaraba.


Saurin sauke Kai Zainab tayi cikin girmamawa ta gaidata tareda yimata sannu da jiki na rashin lafiyar datai.


A kasalance cikeda mamaki maryamah ta amsa tareda kallon Karima tace ta wuce tabasu guri.


Maido kallonta tayi kan Zainab da kayanta cikin rashin son daga murya tace"


Keda waye kukazo?

Ina ummar?


Umma Tana gida 

Itace tace nabiyo Wanda yakaita gida nazo nan.


Shiru maryamah tai Tana tunanin me umma ke nufi da hakan 

Dan haka saita juya ta nufi palonta Dan Kiran umman taji meke faruwa.


Umma na daukar wayar Kai tsaye tace,


Me Zainab zatayi anan da kika aikota?


Ganin nayi masu aikin Nan idan aka biye halayensu haka zakiyita canjawa batareda kin samu yanda kikesoba gashi kina fama da laulayin Nan gwara ita din datake 'yar uwarki zata Miki duk yanda kikeso anhuta da neman kowace me Aiki Zainab zata iya duk wani aikin gidan..


Cikin tare zancen umman tace"


Umma kinsan aikin gidan Nan kuwa?

Ina zata iya sa,


Kina ganin girman gidan Nan ko shararsa zata iya,


Ga aikin abincin dare da ake fitarwa karatun Asad da malamansa,


Hakama umma zaginmu zaayi zaace na mun maidata 'yar aiki,


Duk ba bayan wannan Sam bana buqatarta kusa Dani umma kinsani banaso.



Cikin takaici umman tace"


Duk Wanda zaiyi magana yayi a bayana badai gabana ba Dan kuwa Babu mai iko da ita sai ni 

Ni ubanta ya barwa amanarta hakama akwai wanda ya taba damuwa da ita ko kulawa da itane bayan mu din?


Idan bamu qaru da junaba to meye amfanin riqon nata danayi.


Rashin buqatarta a gidanki kuwa hakuri zakiyi ta zauna da itace kawai zatai Miki Aiki yanda kikeso ba qirsa koba komai ai mijinki ne me biyan kudin karatunta Dan haka Kuma kwa fanshe guminku anan.



"Umma to ke kuma wa zai dinga miki duk ayyukan da ta ke yi ɗin?"


Sai alokacin Umma ta sauke numfashi tana tausasa murya tace, 


"Maryamah ko jiya da mu kai magana a asibiti na sake maimaita Miki cewan Cameron zan koma can gida cikin 'yan uwana tunda bani da kowa anan Kuma dai Tunda ba aure yanzu nakeyiba anan din gwara na koma can din cikin dangi shiyasama na sake yanke shawarar kawo Miki Zainab din Nan Dan Kinga bazan dauketa naje da itaba acan idan dangin mahaifiyarta sun sake zuwa ki miqa musu ita idanma basuzoba Tana samun miji ko wane iri ne aura mata taje nata gidan mijin kowa ya zauna lafiya shekenan.


Shiru kawai maryamah tayi sbd batasan abinda zataceba Kuma Dan haka sukai sallama kawai ta fito Kai tsaye tasa Inna Karima takai zainab Dan madaicin dakin dake hanyar kitchen Wanda masu Aiki yakamata su zauna anan Amma maryamah dayake batason qazantar masu Aiki dakin yanan sabonsa Babu me aikin data Taba zama acikinsa komai nasa na Nan sabo 

masu aikin Kuma dakin boys quarters take kaisu Dan ko Inna Karima acan take yanzu hakan.


Dakin da aka bawa zainab qatuwar katifa ce aciki sabuwa da wardrobe sai madubi da toilet me girma sai Kuma zanin gado har biyu da daddumar sallah da fanka qarama ta tsaye sbd gidan koina pop ne Dan haka AC ne ako Ina Banda dakunan masu Aiki.


Inna Karima ta nuna mata ta saka kayanta cikin wardrobe 


Inna Kariman ce ta shimfida mata bedsheet a katifar da kanta takuma share mata dakin tai mopping tareda wankin toilet din dayake tamkar dakin wani basarake sbd kyansa da girmansa.


Duk aikin da Inna Karima tayi mata tayi mata ne dan taga yanda akeyi ta koya tun yanzu din Dan a daukarta sabuwa me aikice aka kawo wadda zata karba ragamar tsaftace koina ita Kuma taji da aikin girki.


Duk aikinda Inna ta nunawa zainab din tagane Tunda Dama aikin wahala shine rayuwarta ba Wai sabon Abu bane.


Kitchen takuma janta can ma ta nuna mata yanda zatai wanke wanke a kitchen din tareda tsaftacesa.


A taqaice dai Tunda zainab ta iso gidan a ranar Bata zaunaba sai dare sbd aikin da aka fara tarbarta dashi gashi Bata Kuma ganin maryamah ba sai dare data fito tace zainab din ta dafa mata ruwan shayin datake dafo musu da suna asibiti.


Inna Karima ce ta kunnawa zainab din gas ta dafa mata aka Bata inda ta juye mata takai mata kafin suka kashe komai tareda rufewa itada Inna Karima kowa ya nufa makwancinsa.


Sallar ishai tayi ta kwanta take bacci ya dauketa Dan Dama ita data kwanta sai bacci sbd aikin datake wuni yi jikinta a gajiye yake Koda yaushe.


A gida akan tabarma take kwana saida maryamah tayi aure umma ta saida katifar maryamah babba ta siya mata wata Yar yololuwar katifa data gama sidewa Amma dadinta takeji ko ahakan ita,.

Ganin wannan babbar katifar baisa ta hau akai ta kwanta ba sbd gudun laifi ko zaqewa dakuma shakkar yiwa maryamah laifi da haka a kan tiles ta shimfida daddumar sallah tayi kwanciyarta har safe.


Qarfe 7 Inna Karima Tazo ta tadata suka fito Dan fara aikin gidan.


Shara tafara mai kyau 

Ya goge komai cikin tsoro tsoron kada ta fasa ga jikinta dake faman Yar rawar fargabar kada tayiwa maryamah laifi da yanayin aikin.


Fes tayiwa koina saidai Kam yau saida bayanta ya amsa wahalar aikin daya bambamta Dana gidansu data saba,


Palo uku manya Manya da dakuna biyu da kitchen da corridors biyu da toilets ta share tai mopping takuma wanke Bayan goge gogen datai.


Kowanne gurin datai aikin girmane dashi Babu qaramin guri,.


Jin tayi bayanta ya riqe qyam kamar bazata iya miqewa daidaiba Amma haka ta miqe ta share babbar harabar gidan da kusan mota hudu yake dauka.


Ko data gama ayyukan tas bayanta da qugunta sun mata nauyi daqyar take iya miqewa tsaye daidai haka ta zauna kitchen taci abincinta da Inna Karima ta Bata Tana gamawa tayi wanke wanke tasake tsaftace kitchen din ta nufi dakinta.


Daqyar tayi wanka ta saka kaya tazo ta Dan kwanta take baccin wahala yafara daukan kenan saiga Kiran Inna Karima akan taje ta tattaro kayan dining idan su masu gidan sun gama breakfast.


Haka ta tashi taje tattara gurin tasake gyarawa Takoma kitchen tayi Wani wanke wanken tafara Taya Inna Karima aikin abincin Rana.


Wunin ranar ma Kam Bata sake samun zama ba sallah kawai ake barin taje tayi tadawo

Da yamma ma saida takuma sharar harabar gidan sbd karatun daren da akeyi.


Da daddare data kwanta tsamin da jikinta yayi ko bacci mai dadi data saba samu Bata samuba ranar.


Washe garima duk aikin datai a jiyan haka ta maimaitashi Dan haka ranar jikinta har kasa daka yayi da zazzabi ta kwana.


Haka aikin yakasa karban jikinta kusan kwanaki hudu kullum da zazzabi take kwana Amma harta Dan fara sabo da aikin jikin ne dai bai sababa sbd aikin yafi karfin shekarunta ga makaranta har lokacin maryamah batace mata komaiba akai ita Kuma Bata cika ganintaba kota ganta bazata iya Mata magana ba sbd shakka da tsoron Mata laifi.



Idan tace tana Bata gaji da zaman gidan matuqa ba ta yi ƙarya, 

don kuwa duk aikin da ta ke yi a gidan Umma bai kai nan ba sbd ko gyaran ɗakunan da take yi a can girman falukan wannan gidan na Maryamah shi ne matsayin girman ɗakunan gidan Umma kaf ɗinsu


Duka gidan dakin Alh Asad ne kawai ba itace take sharewaba Amma kaf gidan itace mai share koina ta gyara


Har aikin kitchen da Inna Karima yakamata tayi kusan duk itace take Rabi sbd Maryamah wasu lokutan tafison aikin zainab na abinci hardai na marmari.


Sati biyu da zuwanta gidan ta fara sabawa da duk wasu bautan da ta ke yi

Umma kuma a satin ta haɗa komi nata ta ɗaga zuwa Cameron bayan ta zo har gidan Maryamah sun yi sallama da juna tayiwa zainab nasihar biyayya ga Yar uwarta tareda tunatar da ita batada kowa sai su Dan haka ta zauna ta Taya Yar uwarta aikin gidanta Tunda idanma batayiba batada gurin zuwa.


Zainab ta sha kuka sosai duk da cewa babu shaƙuwa tsakaninta da Umman amma sai tafiyar nata ya ɗaga hankalinta sosai sbd koba komai tafi Jin sanyi agurin umman tun rasuwar Abbansu sbd lokuta da Dama umman na Mata wasu abubuwan kulawa sabanin maryamah dako kallon fuskar juna basayi sosai,


Kwata kwata Babu shaquwa ko kusanci ko wata qauna a tsakaninsu Dan haka takejin da umman zata taimaketa da ta tafi da ita ko bautarce ta yarda acan tayiya yi Mata har tsufa yafi Mata zaman Nan din.


Bayan tafiyar umma da sati uku maryamah tayi barin cikinta Dan haka gidan duk suka shiga damuwa musamman maigidan gabaki dayama dauketa yayi sukai tafiya wata qasar aka bar su zainab masu aiki.


Bayan tafiyarsu ne zainab tasamu Takoma makaranta shima saida aka Kira Alhaji Asad din daga makarantar Yana can suka sanar Masa ta Dena zuwa shinefa yayi waya drivern gidan na kaita wata Rana Kuma da qafa take zuwa tadawo da qafa duk nisan kuwa sbd driver ganin yakeyi Mai aikice ita Amma tasamu shigar da ake kaita makaranta da mota Dan haka Wani lokacin yake shareta ya dauki motar ya tafiyarsa nasa sabgogin.


Karatunta da aikin gidan ya taru ya hade mata gabaki daya rayuwarta Aiki ya firgitata ga kadaici,


Sam bayan aikin wahalar hidimar gidan maryamah da hidmar maryamah din batada aboki Dan haka duk Takoma kaman wata nakasasshiya karatun ma yanzu sai ahankali Bata Wani ganewa zuwa kawai takeyi.

#MAMUH#

#SISTERS#LIFE#LOVE#AQEEL#AMAL IDON NERA#



*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo




Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070



MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.