Idon Naira 2

 


*_IDON NAIRA_*

_Mamuhgee_

_Arewabooks@Mamuhgee_

*_Zafafa biyar 2023_*
2

A hankali Zainab tafara girma tare da samun kulawa daga wajen Abbansu Malam Adamu wanda duk wata hidimi na Zainab shi ke yi tun dawowarta gidan Dan Zamanta a hannun Umma Hadeeza ya zama sunane kawai sbd bata san duk wata wahalar kulawa da ita ba sai idan Malam ɗin ya fita kasuwa ne kaɗai ta ke yi mata abinda ta ga za ta iya, amma daga wankan safe zuwa shiryata da bata abinci da duk wata hidimarta Malam ɗin ke yi da safe kafin ya fita sauran Kuma zatayi abinda taji zata iya Wanda bazata iyaba Maryamah tayi iya Wanda taji zata iya itama,

Idan ya dawo zai tadda tana buƙatar wani sabon gyaran haka zai zage ya sake mata wanka ya sauya mata shiga sannan su haɗu aci abinci yana bata abaki sbd bazata iya ci da kantaba.


Maryamah bata taɓa janyota a jikinta ko sau ɗaya ba bare ta hidimta mata,bata taɓa nuna so ko qi akan Zainab dinba yanda ta yi treating mahaifiyar Zainab lokacin tana raye haka take treating Zainab ɗin

 Hasalima ko sakin fuska daga gareta Zainab bata gani sai ya kasance ma tsoron Maryamah ya shigi Zainab ɗin ta yadda ko kusa da Maryamah bata son zuwa Dan gwara mahaifiyar Zainab din da batada irin kamewar fuskar Maryamah sosai.


Ummar ma sam bata janyota a jikiba saidaj Bata kame mata fuskarta sbd ganin bazatama iya wahalarda kanta da daure dauren fuska da damuwaba akan jinjirar yarinya hakama ba wani boyo ta fifita soyayyar ƴarta akan Zainab sosai da sosai Shiyasa Zainab din tun shekarun nata Basu wani tasaba gane batada uwa kuma ta taso da tsoransu da rashin sakin jiki da su har tayi girman fara zuwa makaranta saidai Abbansu na dawowa tana walwalarta da farin cikinta sosai kaman kowanne yaro.


Rashin kulawar umman Maryamah akan Zainab baya damun Malam kaman rashin kulawar Maryamah akanta da rashin shaquwa ko kaunar junansu..


Abin Yana tsananin damunsa da basa tsoro sbd Maryamah ita kadaice Yar uwarta dasuke jini daya yake Kuma fatar ta zamewa Zainab din gata idan sun hade kansu a gaba har zuriarsu,

Fatansa burinsa su zama tsintsiya madaurinsu daya har tsufa da zuriarsu,

 shiyasa yake jin damuwa akan halin ko inkula da rashin kulawar Maryamah din akan Zainab.


yayi faɗa yayi nasiha har ya gaji ba wani sauyin arziki ya hakura ya zuba musu ido tare da cigaba da inganta rayuwar tasu da adduar hadin kansu su dukan.

Karshe dai kasa hakuri yayi ya dauko tsarin zaunawa dasu biyun idan har Yana gida to Yana tareda Maryamah din da Zainab Yana fira dasu tareda jansu a jikinsa sosai ko hakan zaisa kauna da shaquwar dayake fata su shiga tsakaninsu.Umma Kuma tana ganin Zainab tafara girman da zata iya wasu ayyukan saita raba musu aiki wanda kusan ayyukan Zainab din sunfi na Maryamah yawa a cewar Maryamah karatunta yafi wahala tunda har yamma take kaiwa ita Kuma Zainab yanxu nema take Shirin shiga secondary.


Kafin ta tafi makaranta da safe sai tayi aikin shara da wanke wanke kafin ta tafi hakama tana dawowa sallah da kawai takeyi saita Kuma shara da wanke wanke da wasu Yan ayyukan ta wanke uniform dinta kafin taci abinci ta wuce islamiyya.


Tana qara girma kuwa hatta wankin umman da Maryamah ce keyi ya dawo kanta

Maryamah ma umman tayi tayi tabarwa Zainab wankinta taringa yi Amma tace Sam Bata buqata sbd ita irin mutanen ne da idan basa son abu ko kaunarsa to ko wahalardashi basa iyayi sbd kadama komai ya hadaka dasu shiyasa ko aikin wahala Bata damu data bawa Zainab din tai mata ba saida idan batanan umma tabawa Zainab wankinta Amma indai tana Nan Bata so itace takeyin abinta.


Rashin sabo da haniya  da rashin abokin hira a gida da bata da shi sai ya kasance Zainab din ta taso a miskili batada surutu ko rawar Kai ko makamancin hakan shiyasa ko a makarantar boko da islamiyya batada qawa ko daya Kuma daidai gwargwado tanada qwaqwalwar daukar karatu hakan ya qarawa malam qarfin zuciya akanta da sake dauke ido akan rayuwar dasukeyiwa Zainab din tunda Basu cutatar da itaba Kuma Basu fito sun furta mata qiyayyaba Kuma lurada qaunarta dayake bayyanarwa da tausayinta shike sake neman dagula Yar qaramar zaman lafiyar da akeyi a tsakaninsu sai kawai yaringa binsu da adduar shiriya su dukan har umman 

Kuma tunda dai Zainab din na fira dashi harda dariya sosai ba laifi hakan ma Allah ya shirya masa su gashi dama Sam umma Bata taba yimata horon yunwaba abinci ake Bata yanda ya isheta tunda ubanta ke kawowa.


Maryamah tagama karatunta tuni harta gama service dinta aiki takeson farawa Amma abban nasu yaqi amincewa sbd shekarunta sun qanqanta da fara wannan rayuwar Dan hakan yabawa manemin aurenta damar fitowa ayi aurensu saita fara aikin nata acan.


Barr Asadullah Muhammed Ismail shine Wanda yake neman maraymah din da aure tun Bata gama karatu ba,


Shima tuzuru ne sosai Dan ya jima Yana aiki batareda yayi aureba harya fita cikin layin samari,


Babban lauya ne me zaman kansa hakama Dan kasuwar gaske Wanda ya Tara abin duniya maana arziki sbd gadon arziki da kamfanona dayayi daga mahaifinsa tsohon minister kafin ya rasu haka su din asalin ya kogi state ne aiki da kasuwanci ya dawo dasu arewa.


An sanya ranar auren Maryamah da Asadullah watanni uku masu zuwa Dan haka umma da abban nasu suketa Yan shirye shiryensu sbd su din bawai masu kudi bane rufin asiri ne kawai gashi gidan arzki Maryam din zatai aure sbd sosai dangin Asad suka fara hidima suna barin dukiya a harkar auren.


Zainab tafi kowa shedan son da Maryamah kewa Asad sbd Bata taba ganin abinda yake saka Maryamah farin ciki da walwala harma da bayyanuwar hakorantaba gurin bayyanarda farin ciki irin a ambata sunan Asad wanda suka jima tare Dan haka har cikin ranta sai itama take farin ciki da bikin auren.


Haka Umma kullum ta zauna Batada zance me dadi saina irin daula da arzikin da Maryamah zata shiga a gidan auren,

Alfahari takeyi sosai akan auren me kudin da 'yarta zatayi abun har Yana sirkawa da kaman gori ga Zainab wadda batama San bambamcin rayuwar aure gidan me kudi da me rufin asiriba Dan haka ita Sam batasan da ita akeba sai aikin hidimar wahala datake fama dashi kullum.


 

A ranar alhamis Babu makarantar Islamiyya wankin kayan umma tayi da nata harma dana Abbansu 

Tana gamawa tayi wanka ta shiga dakinsu ta shafa Vaseline ta saka atamparta doguwar riga tana cikin saka hijib zata fito taje Aiken umma taji sallamar maza a tsakar gidansu Dan haka ta qarasa sakawa da Dan sauri Dan fitowa taga masu sallamar sbd Dama itace me fitowa tarban baqi Koda yaushe...


Jin sallamar maza yasa yau har umma da Maryamah dake dakinta suna magana tasowa suka fito dukkaninsu kusan a tare..


Idanuwansu ne suka sauka akan Malam Adamu da ake shinfiɗewa kan tabarman da Zainab ta shimfida tun kafin tayi wanki,


Umma ce tayi saurin ƙarisowa wajen tana duban mutanen da ke gyara masa kwanciya akan tabarman cikin matsanancin firgici da tashin hankali ta ce,


 "Lafiya me yafaru da shi ne haka?"

Me nake gani haka kamar jini a tufafinsa?

Innalillahi.Cikin wainda suka shigo dashi dinne makabtansu ya dago ya duba umman a sanyaye da mutuwar jikin tausayin malam din yace, 


"Wallahi hatsari ya samu akan hanyar dawowarsa acan bakin junction na layin Nan wani me mota ya kaɗesa akan mashin ɗinsa sosai 

kuma shi me motar ya gudu abinsa shi ne muka ɗakko sa zuwa gida kafin akawo motar da isyaka da akaje Kira..


Umma da su Maryamah cikin matsanancin tashin hankali da tsoro suke kallonsa 


 Zainab tuni hawaye suka fara gangaro mata cikin matsanancin tsoro da tashin hankali da tausayinsa,


Umma da Maryamah jikinsu rawa kawai yake dauka

Umman ta buɗe baki kenan za ta yi magana wani matashi ya shigo da sallama yana cewa,


 "Ku fito da shi ga motar isyaku nan za mu kaisa asibiti"


Sake daukansa sukai suka fita akai asibiti dashi umma da Maryamah suka rufa musu baya cikin adaidaita aka bar Zainab din ita kadai a gida tana neman fashewa da kukan firgici da tsoron kada wani abu yasamu abban nasu.
Har aka kira sallar magriba su Umma basu dawo ba bare taji a wani hali Abban ke ciki,

Ga tsoronta sai qaruwa yakeyi musammam ganin har aka fita da abban hancinsa da kunnuwansa jini sukeyi Kuma iya ko magana ba bare budu ido ya kallesu.


Sai ana kiran sallar Isha'i su Umma suka shigo gidan Umma na kuka sosai kaman mayafinta a hannu

Maryamah kuwa ko ganin gabanta batayi sosai sbd tashin hankali tafiyar kawai takeyi kaman me koya.


hakan ya sake ɗaga hankalin Zainab da ke zaune har lokacin a tsakar gida tana zare ido cikin rashin sanin abin yi,

Murya na rawa tace"


"Umma ya jikin Abbah?

 ya yi motsi ya farfaɗo kuwa?"


 kamar Umma ba za ta ce komi ba sai kuma ta tuna yadda Abbah ke ta kiran sunan Zainab ɗin lokacin da ya farfaɗo 

sai ta juyo murya na rawa itama tace,

 

"Da sauki ya farfaɗo amma yana jin jiki, ga idanuwansa ance daya ya fashe"


Hawayen Zainab ne suka qara gudu jikinta yaqara daukar rawa a tsorace tace"


Umma dan Allah akaini can na kwana gurinsa inason ganinsa Dan Allah umma...


Kasa tankata umman tayi suka wuce sukabarta tsaye tanajin tashin hankali da tsoro na shigarta,

Abbansu kawai takeson gani itadai ko hankalinta zai kwanta,

Ita ko a kwancen ne tanason tagansa.


Ganin duk sun shige bamai kulata Dole ya hakura ta shige itama 

Haka gidan yayi tsit kaman gidan ba kowa sbd damuwa 

Su umma Kuma sunacan suna rankon sallolin da basuyiba a asibiti.Misalin ƙarfe takwas na safe Umma na tsaye a kitchen tana ƙarisa zuba farin kokon data Dama Dan zuwa asibitin duk da malam Kam yai nisan da ba iya Shan kunun zaiyiba Dan harsuka baro bai farfadoba Amma Kuma gwara takai din Koda Allah zaisa asamu sauki ya iya farfadowar,


 Zainab ce ta shigo kitchen ɗin ta gaida Umman tana tattara kayan wanke wanke zata fitar tayi batareda umma takalletaba tace"


Kibar aikin kiyi Shirin makarantarki Dan bazan iya jiran ki gamaba kafin na fita yazu nakeson isa asibiti rufe gidan zanyi idan kin dawo kinyi


Dan dakatawa tayi ahankali daga tattara kayan cikin sanyi tace,


"Umma yau ba za ni makaranta ba, ina so aje da ni in ga Abbah."


Kallonta umma tayi zatai magana sallamarsu Malam hamisu maqocinsu da isyaku ya katseta sai ta yi saurin fita ba tare da ta bi ta kan Zainab dinba sbd isyakun shine ya kwana a asibitin Bata saniba ko jikin ne kokuma sallamosu akai.


Kallo daya tayiwa fuskokinsu take ta fahimci mugun sakon da sukazo dashi saidai Bata gama yardaba Dan haka qafafuwanta dake rawa ta dago ahankali tana qarasowa tsakar gidan murya na rawa a harde cikin rudewa tahau cewa,


"Ina kwananku?"


Maryamah da zainab ne suka fito kusan lokaci daya suma suna gaida su malam hamisun Wanda bai tsaya Jan lokaciba ko Jan ransu ya sanar dasu malam Adamu dai lokaci yayi rai yayi halinsa ya rasu qarfe hudun asubar yau..


Dan gyara tsayuwa umma tayi daqyar ta iya tattaro yawu ta hadiye a makoshinta tace"


Malam ya rasu????????


Gyada Kai isyaku yayi yana sauke kansa qasa sbd babu abinda zai iya cewa shima sbd mutuwar malam ta dakesa Dan mutumin arzikine mutumin jamaa.


Zubewa Maryamah tayi a qasa tana neman sumewa sukai kanta isyaku na zuma mata ruwa suna Basu hakuri sbd take kowannensu ya rikice da kukan tashin hankali da firgici mai tsanani.


Zainab kuka takeyi sosai mai sauti sbd asirinta yafi na kowa tonuwa rasuwar mahaifinsu.


Cikin qanqanin lokaci a yada rasuwar malam din cikin anguwa da Yan uwa da abokan hulda 

Take aka fara shigowa ana rarrashinsu umma dake kuka kaman rayukansu zasu fita.


Ahakan akai janaizarsa aka kaisa makwancinsa.


Alh Barr Asad shine kusan jagoran zaman gaisuwar malam din tunda shine tamkar 'dansa yanzu tunda baida 'da namiji hakama ba wasu dangi sosai dazasu zauna.


Haka aka share zaman makokin tsayin kwanaki bakwai Zainab na cikin ƙunci da rashin walwala gaba ɗaya ta sake zama wata shiru shiru bata magana abinci ma sai an matsa mata ta ke iya cin kaɗan ta ce ta ƙoshi Bata da aiki sai na kuka duk idanunta sun zurma ta fita a hayyacinta gaba ɗaya, 

ga rashin me rarrashi ga rashin gata da ke kewaye da ita,

 dama ƴan zaman makokin ne ke janta ajiki da bata baki yanzu an watse babu kowa daga ita sai su Umma da sam basa bi takan ta suma takansu sukeyi tunda rasuwar ta shafi kowannensu ba ita kadaiba,


Ahankali lokaci yaja har akai kusan wata biyu da rasuwar Dama bikin maryamah din an daga sai umma ta fita takaba Dan haka tuni kowa yaci gaba da rayuwarsa,


Bebar musu gadon komaiba saina gidan dasuke ciki Wanda bawani gida bane babba Dan madaidaicine Kuma bama ginin zamani bane.


Zainab taci gaba da zuwa makaranta dayake Daman ta gwamnati ce batada wata wahalar shaani kafin daga baya ko sati batai da komawa makarantarba Alhaji Asad ya sauya mata makaranta zuwa wata private school mai kyau da tsada.


 rayuwarta ayanzu Takoma tamkar Mara komai da kowa tunda Dama Abbansu shine abokinta datake iya zaunawa suyi fira da dariya,yaji damuwarta da duk abinda take ciki,


Yanzu duk bame mata wannan Dan haka ahankali Dole tayi qawa daya Nabila a makaranta wadda da ita kawai taye Yar fira yanzu.Dukkanin nau'in bauta na aikin gidan sai ya sake rataya a wuyarta musamman da bikin Anty maryamah ya gabato gashi dangin umma wasu tun rasuwar abban suna gidan,


 hatta girkin abincin yanzu Umma ta fara horar da ita akan yinsa harma ta sakar mata gaba daya,

 tun tana yi Maryamah na kushewa bataci har hannunta ya nuna a iya girkin.Anfara bikin maryamah gidan yacika da dangin umma dawasu tsirarraku daga dangin mahaifinsu dasukazo daga qauye Kuma ahakan har akai aka gama Babu ma Wanda yayi noticing dinta amatsayin qanwar amarya Koda yaushe tana cikin aiki da aike Dan haka har akai aka gama ko zanin sabuwar atampa Bata samu Wanda ya Bata ta daura ba saidai Bayan bikin umma tabata kala hudu acikin tsofin kayan Anty maryamah din Wanda sunyi mata yawa sosai saida umman ta Bata dari uku takai aka rage mata take sakawa dayake kayan Anty maryamah din duk masu kyau ne sbd umman dakuma Alhaji Asad daya tsaya mata.


An gama bikin ne cikin kwanciyar hankali da bushasha don harkar ta masu arziƙi ce sosai kuma ya sakar musu naira sun yi yadda suke so,


 Dangin Umma 'yan Cameron ne Dama Kuma duk wata riyar kudi sun iya Dan haka kudi suma suka hada sosai sukai mata wasu abubuwan na fita tsara duk da Babu abinda Alhaj Barr Asadullah din beyiba.


Amarya maryamah tabar gidansu ta tare a gidan mijinta aka bar daga umma sai Zainab wadda tun yanzu tafara hangowa kanta garari sbd rashin sanin saime Kuma Nan gaba.

#MAMUH#

#love

#sisters chldrn

#AMAL IDON NAIRA*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo
Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥 

No comments

Powered by Blogger.