Idon Naira 13

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

13

Cikin dan boye mamakinta tareda kokarin basar da tsananin fushi da bacin ranta akansa na tun jiya daya kasa ko daukan wayarta Sam yaqi lokacinta..,


Ahankali tace,


"Allah ya raya abinda tasamu din,

Jaime kuma yau ya kamata kazo kasan abinda duk Zakayi kasan dai zuwa Jibi zaka wuce.


Numfashi yadan sauke kadan yana cewa,


"Ummn insha Allah zan samu time naga yanda zan qarasa sauran shirin nawa.


Miqewa yayi daga zaman da yayi yabar gurin

Kai tsaye mai aikin gidan yakira ya bata umarnin hada breakfast lafiyayye a basket tukuna ya wuce bangarensa. 


Tubewa yayi ya zari towel qarami ya rataya a wuyansa daga shi sai Qaramin boxers ya nufi toilet.


Wanka yayi yafito ya shirya Kansa na tsananin sarawa da alamarma idan ya kwanta zazzabi shigarsa zaiyi

Gaishi da komaima a gabansa yana neman rikice masa dan kuwa a yanzu da maminsa tayi irin wannan haihuwar bazai iya tafiya yabarta ba,


Ga rasuwar Mijinta,

Ga haihuwar bagatan,

Ga babyn na incubator 

Tayaya zai tafi yabarta a wannan yanayin bayan yasan babu Wanda zai iya kular masa da ita.


Cikin black qananun kaya yafito yasa samira takai masa basket din mota ya fice daga gidan Kai tsaye batareda yaje gurin ummansaba tasan da fitar tasa dan zata iya kawo masa wani uzurin dazai hanasa fitar.


Koda yakoma asibiti Maminsa ta tashi tana zauna fes cikin wasu kayan da alama sun taimaka mata tayi wanka ta sake shiryawa 


Fuskarta ya kalla yaga babu walwala ko farin ciki saima sake shiga damuwa da tsoron babynta kada itama ta rasata,


Tea ya hada mata dakansa ya zauna gefenta yana kallonta cikin tsananin kulawa da bata tabbaci yace,


"Mami kada ki taba yankewa kanki rahama dan rahamar ubangiji bata yankewa,

Ina nan,matuqar ina raye mami dake da babyn nan bazaku taba rasa gatanku ba insha Allah,

Wannan babyn zan zama gatanta,

Zan bata farin cikin da kowanne dan yake fatar samu wannan alqawarina ne idan Allah yabani tsawon rai da lafiya to tabbas nine babban yayanta kuma ubanta dazai tsaye mata a komai dan haka mami kada kisa damuwa kiyi mata adduar samun lafiya baba Malam kuma adduar samun rahamar ubangiji.


Da yake kukanta ya qafe qyam baya zuwa tun jiya dan haka bata iya cewa komaiba saima Jin nauyin zuciyarta daya qaru duk da alqawarin da Aqeel din yayi mata akan future din 'yarta sai hakan ya sata shiga fargaba idan aqeel din ya tafi kafin yadawo waye sukedashi.


"Allah",zuciyarta ta tinatar da ita 


Daqyar ta iya cin abincin daya tilasta mata ci dan daga bakinta har maqoshinta zuwa cikinta abincima kamar yankar matasu yakeyi a halinda take ciki.


Bayan tagama akace zaa kawo mata abubuwan da zata ja Nono zaa je abawa babyn.


Aqeel ne yakuma bada kudi aka siya komai aka kawo mata nurses biyu suka taimaka mata aka dan samu nono shima daqyar da wahala.


Neman alfarmar ganin babyn Aqeel yayi suka tafi tare harda Mamin wadda take tafiya a hankali sbd rashin karfi da damuwar data gama ci da mamaye kuzarinta.


Suna isa saida aka dauki mintina kafin nurse ta fito da babyn kointa a rufe dunqule cikin tattausan bargo mai tsada da kyau pink ta miqawa Aqeel din ita.


Nauyi yaji zuciyarsa tayi lokacinda aka miqo masa babyn saida ya sauke numfashi boyayye kafin ya miqa hannayensa ya Karbeta cikeda tsananin so da Kaunarta tun baiga fuskartaba.


Gefen mamin ya dawo ya zauna tareda dan bude musu babyn suna zubawa 'yar qaramar fuskarta idanuwansu kowanne cikeda Kauna da tausayin tazo duniya a marainiya.


Wani numfashi mai zafi da qunci Zainab ta sake tareda  Dagowa ta kalli Aqeel daya kasa dauke idonsa akan babyn Ahankali ta iya furta,


"Aqeel kai kadai takeda kayi mata huduba da suna..


Dama abinda yake shirin yi kenan saidai sunan dayake Ransa yana fatar idan ya saka hakan yasa kaunar babyn yashiga ran mai sunan...


Ahankali ya dagota sama yakawo daidai fusktarsa yayi mata huduba tareda kiranta da sunan MARYAMAH..


Kallon maminsa yayi alokacinda ya furta sunan daya sakawa babyn a fili...


Batace komaiba kamar yanda har cikin ranta bataji komaiba na damuwa ko rashin jin dadin sunan,

Har a ranta sunan yayi tunda shine ya zaba sunan,

Kuma sunan yar uwarta ne Jininta da bata da kowa sai ita da yayanta da suka zama biyu yanzu wato AQEEL da MARYAMAH.


Hannu nurse ta miqa masa Akan ya bada babyn a maida ya maida kallonsa kan babyn yana kallon fuskarta cikeda kulawa da kauna,

Hakanan yakejin kamar idan ya bada MARYAMAH din ya Rabu da ita kenan.


Miqata yayi bayan ya sake rufeta koina kamar yanda aka kawo musu ita.


Dakin da maminsa take suka koma ko zama baiyiba ya fito yaje ya biya kudin komai da komai harna sallama dan haka babu abinda zasu Nema har ayi sallamarsu insha Allah.


Daga can gida yakoma sbd kiranda ummansa ke masa.


Yana isa ta rufesa da fada amma dai bayan hakura baice mata komaiba saima maganar data daga hankalinta dan saura kiris ta some.


Cikin tashin hankali sabo 

Da mamakinsa mai tsanani tace,


"Aqeel kace bazaka tafi UK ba ka fasa???

Sbd Zainab ne ko????


Sam rayuwarsa bai iya qaryaba da wani kwana kwana dan haka cikin nutsuwarsa kai tsaye yace,


"Umma bazan iya Barin mami da Little MARYAMAH ba natafi,

Kona tafi wlh hankalina zai rabu

Inaga gwara na tsaya nan din kawai zaifi mun nutsuwa........


Tsabar baqin ciki da takaici bata tsaya tambayar sauran zantukan nasaba sai sunan daya ambata

A qule tace,


"Wace sabuwar shigowar aka samu little MARYAMAH kuma?


Bata buqatan yace mata yar Zainab yasawa sunanta dan haka Ta zuba masa idanuwanta tana jiran amsar dazai bata dan bacin ranta qaruwa yakeyi da komaima ayanzu idan har Aqeel yafasa tafiya Akan zainab wlh wannan karon ba qaramin fushi da bacin ranta zaa ganiba.


"Umma yar maminace da wannan sunan 

Bakuma lafiyayya bace tayaya zan barsu natafi waye zai kula dasu?

Maganar tafiyata kuyi hakuri umma abarta sbd bazan iyaba.....


Kofa ta nuna masa da hannu Tana kokarin danne zuciyarta daga furta kalamanda basu daceba ga 'danta.


Yana fitowa bangarensa ya nufa ko zama baiyiba kiran Haj kaka yashigo wayarsa dan haka ya juya ya fice zuwa gidan haj kakan,

Yana isa haj maryamah na isowa nan take sabon rikici ya tashi qannan babansa ma su uku maza duka sun saka bakinsu a maganar amma Aqeel din ya tsaya cak akan bazai bar zainab da MARYAMAH su tagayyara.


Duk yanda ake tunanin kusanci,shaquwa da girman kaunar dayakewa Zainab wannan karon sun tabbatarda abin ya wuce tinaninsu dan haka hankali ya tashi cikin kwana daya lamarin ya zama babba dan kuwa su dangin mahaifinsa duka tsananin laifin  haj maryamah suke gani Dan itace tayi watsi da 'dan ta Barwa zainab din har Aqeel din yazo gashinan idanba zainab da baya Jin kowa a ransa,


Umma tayita kiran wayar Zainab din yafi so dari da dori amma bata samu dan haka takejin kamar ta zama tsuntsuwa tazo ta samu zainab tayi mata duka,


Sun rabu da ita kowa ya kama rayuwarsa amma takasa barin yar uwarta taji dadin rayuwarta da 'danta 

Yanzu gashinan itama ai ta Haifa tata yar tabarsa da tasa uwar taqi.


Hannuwansu su haj kaka suka cire sbd duk yanda sukeson tafiyarsa karatu sunfison farin cikinsa akan nasu dan haka suka hakura Akan yanda yakeso din kuma suka amince da yaci gaba da kulawa da zainab da MARYAMAH..


Jin hakan yasa zuciyar haj Maryamah bugawa qarshe dai saida aka hada da Kaita asibiti dan kuwa jininta yayi mugun hawan data kusa samun matsala.


Umma dataga zasuyi biyu babu sai gata ta iso ba shiri gashi da a ranar zai wuce Abuja Gobe su wuce UK din.


Hankalinsa sosai yatashi ganin Halinda mahaifiyarsa tashiga akan lamarin dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya zauna tareda ita yana nuna mata kulawa da kauna qarshe umma na ganin irin tsananin son dayakewa mahaifiyar tasa itama sai sukayi magana da maryamah sukai shawara.


Shawararsu suka sanarwa  Aqeel din akan haj maryamah din zata karbi zainab da 'yarta su zauna a gurinta insha Allah.


Da farko hakan bai kwanta masaba dan kuwa hankalinsa yafi kwanciya da kulawar zainab din a hannun dangin mahaifinsa amma kuma duba da yanayin unman tasa data shiga damuwar tafiya sai kawai ya amince ahakan jikinsa duk yayi sanyi.


Yanason zuwa gurin maminsa amma itama Ummansa duk takasa barinsa sbd yanayin jikin nata

Haka ya hakura.


Washe gari tunda safe ya shirya tsaf batareda lokacin wucewar yayiba ya tafi asibiti tareda umma gurin zainab.

Batayi wani mamaki ko damuwar rashin dawowarsa a jiyan ba sbd tariga tasan zuwan nasama Allah kawai yasan irin fitinar da akeyi a gidansu akan hakan.


Ganin umma ya sata jin sanyin jiki dan kuwa tasan dole sai wani abu yafaru umman ke zuwa dan haka tasan akwai wata rigimar.


Gaida umman tayi cikeda girmamawa 

Umman ta amsa tareda Yimata gaisuwar mijinta da Barkan haihuwarta duk lokaci daya.


Aqeel ne da Kansa jiki a mace cikin kulawa yayi mata bayanin tafiyarsa a yau din tareda sanar da ita daga asibiti gidansu zata koma da zama komai ya wuce tsakanunta dasu ummansa sun karbeta ita da little MARYAMAH.


Shiru tayi zuciyarta na shiga tunanin lamarin 

Shiyasa umman tazo kenan dai akwai rigimar da akeyi din Wadda tasa suka aminta zasu amsheta

Amma dai kuma a yanzu datakeda 'ya batajin zamanta gidan haj maryamah din zai yiyu sbd Dalilai da dama,


Haj maryamah bazata taba son Maryamah qarama ba sbd tun asali batason masu aiki dake da qananun yara Bare ita datakeda jinjirar 'ya,


Tayaya zata iya watsi da yarta tayita aikin bautarda ko yar tasan baa kaunaci ganiba,


Bayan haka Tayaya zata koma kurkukun da Allah yasa ta fito da qyar da 'yar marainiyar 'yarta suje itama rayuwarta ta mutu kamar Tata tun kuruciya har tsufa dan kafin Aqeel yadawo ya zama Gatan maryamah din tuni ta rasa abubuwa da dama.


Ganin yanda tayi shiru yasa umma kallonta a shagube tace,


"Ko kinfi karfin zama gidan ne tunda yanzu kema kin zama uwa babu Wanda ya isa dake.


Shiru Zainab tayi batace komaiba.


Cikin dan fada umman tace,


"Da tsufana amma kullum Ina hanyar tafiya mai shegen nisa sbd ke zainab,

Duk zuwana babu na lafiya sbd rikicin halinki ne Dana yar uwarki,


Yanzu Ana fatar yaron nan ya tafi karatun nan angama komai rana tsaka sbd ke yasake cewa bazashiba 

Yanzu an samu ya aminta Zaije tunda ya shiryaki da mahaifiyarsa kin tsaya tunanin ta yanda zaki sake hargitsa lissafinsa ya fasa tafiyar ko zainab?????


Mun koma ga wadda ta Haifi 'dan ga wadda muke rarrashi akansa sbd isa da ikonsa da Allah yabaki..


Jin hakan yasa zainab taqaita fitinar da cewa ta amince zata koma can din karya damu ya wuce karatunsa kawai Allah yabasa saa da nasara.


Batason fitina da tashin hankali da gorinsu umma dan haka ya yanke zancen da hakan dan a samu ya tafi 

Suma su umman dan asamu ya wuce din yasa sukace sun shirya da zainab din komai ya wuce duk da kusan umma ce take kidan kuma take rawar

Ita haj maryamah dai taqi saka baki sbd jikinta da zuciyarta dasuka kasa sakewa idan ba ganin tayi Aqeel din ya tafi ba dan kuwa da gaskiarsa magana daya tak yake tsayawa akai ba tafiyar zaiyiba idan ba zainab da 'yarta yaga yabarsu a cikin kulawaba.


Yaje ganin little MARYAMAH amma basu bashi damar daukantaba saidai yaganta daga cikin kwalban Dan haka yayi mata addua sosai da fatar tsarin Allah gareta yafito.


Zainab duk inda zuciyarta take tayi rauni sosai na rabuwa dashi din amma ta boye ta danne a ranta sbd kaucewa laifi gun umma kokuma hanasa tafiyar...

Addua tayi masa sosai tareda fatan samun dibbin nasara da cigaba a rayuwarsa.


Harya baro asibitin kasa hada ido yayi da maminsa sbd yana iya hango damuwa da tashin hankalinta harma da firgicin tafiyarsa ya barsu itada little amma kuma tunda yasan gida yabarsu to tasa damuwar ta dan ragu yanada nutsuwar tafiya yanzu.

#MAMUH#

#MARYAMAH AMAL IDON NERA

#DR AQEEL ASAD

#HAJ ZAINAB IDON NERA

#life#love#hotlove#marriage#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯

Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯

No comments

Powered by Blogger.