Gurbin Ido 9

 

  09


     Tarba cike da fara'a da nuna matuqar kirki inna furera ta yiwa su anni


"Ina kwana daada" gajee ta fada tana dan

zamowa kadan daga saman kujerar da take zaune a kai hannunta riqe da mudubi tana ta faman kallon fuskarta da kuma kankare duk wani dan tabo ko ciwo da ta gani akan fuskar tata,so take lallai ta hango dame maimunatu ta fita ne,da har jiya himu zai iya duban fuskarta yace mata baya sonta?.


"Lafiya lau gajeje,ya akaji da baqi kuma jiya?" Murmushi tayi ta noqe tana komawa saman kujerar,ita ala dole kunya,saidai hakan bai sanya tabar wajen ba,hakanan kuma batayi yunqurin gaida anni ba,duk da cewa ta girmi duk wanda yake wajen.


           Kallo daya itama annin ta yiwa sashen da take ta maida dubanta ga inna fureran,tana matuqar mamaki idan akace mata wadan nan din fulani ne,saidai kuma duk da ita da zafinta,amma mutum ce da ba kasafai zaka ga ta shiga abinda babu ruwanta ba,saidai idan ta kama.


        Gaisawa suka fara yi,sannan innar ta fara yi mata bayanin yawan dabbobin da kuma farashin da ta yankewa kowanne


"Farashi ba tsada bane,indai sunyimin shikenan.......laila,leqa ki kirayi salihu ya shigo" tace da laila,salihu shine kusan manager din gidan gonarta,a yawancin lokuta shike bi rugage ya qaro mata dabbobi a duk sanda ta buqaci hakan.


           Ba jimawa suka dawo tare,innar tayi musu jagora zuwa makwantar dabbobin,suna tafe tana qara yi musu bayani,burinta ta gamsar dasu,su siye ta caski kudinta.


          Tun daga nesa idanun anni suka sauka akan maimunatun,gefanta kayan share wajen ne a zube,tana tsugunne a cikinsu,hannunta riqe da qafar wata akuya tana dubawa,idan ka kalleta da kyau zaka fahimci magana takeyi saboda yadda bakinta ke motsawa,tana kuma shafa bayan akuyar da hannunta daya cikin nuna tausayawa da tausasawa.


           Suna sake riskarta annin na ci gaba da kallonta,tana kallon tarin baiwar da yarinyar ke da shi,yadda take nuna kulawa da tausayawa ga dabbobin yana burge anni,tana mamakin yadda take magana dasu tare da isar musu da saqo da bakinta,tayi imani akwai wani abu tattare da yarinyar na musamman wanda ba lallai wadanda ke kewaye da ita sun fahimci haka ba.


         Sosai ran inna furera ya baci,ta kuma tunzura sanda ta fahimci maimunatu bata share wajen ba,ta cika tayi fam,tanason jawo mata asara ne?,ta yaya zata kawo baqi irin wannan wanda duba daya zaka yi musu kasan duniyar da suke rayuwa ya banbamta da tasu amma tabar wajen a haka?,yanzu idan suka ce sun fasa fa?.….….tunanin da ya sanyata ta kwatsawa maimunatun da batasan da tahowarsu wajen ba tsawa


"Ke maimunatu!!!" Kiran yayi matuqar razanata,saboda bata tsammaceshi ba,abinda yasa tayi wata miqewa cikin matuqar hanzarin daya rage kadan ta kifa,sai data dai daita tsaiwarta sannan ta dawo da dubanta zuwa sashen da kiran ya fito,ta sauke manyan idanunta da suka rusuna saboda tsoro a kansu.


         Yadda take dubansu haka anni itama ke dubanta,wani abu yana taba ran anni haka kawai,matsowarsu kusa da ita da yasa ta sake kallon maimunatun sosai,akwai wani yanayi tattare da ita


"Uwarki kike tun dazu baki gyara wajen nan ba?,ban gaya miki baqi zasu zo ba?,lallai dai sai kin nunawa duniya zallar baqinciki da adawar da kikeyi dani ko?,to ni nafi qarfinki,nafi qarfin kiyi takun saqa dani......" Tayi maganar yana zarar wani sanda dake jingine wajen ta durfafi maimunatun a fusace.


          Gam ta runtse idanunta tana jiran jin ta wanne sashe dukan zai fara sauka a jikinta?,tana wassafa radadi da azabar da zata fuskanta lokacin da dukan zai sauka kan mikin wancan dukan da yake jikinta?,ashe kiwon da take tafiya ta wuni acan wani bangaren rahama ne a gareta?.


"A'ah dakata 'yar nan" muryar anni ta katse inna daga yunqurin dukan da take shirin kaiwa maimunatu,sai dukka hankula suka koma kan anni


"Banda abinki.....mu ai dabbobi muka zo gani ba wajen kwanciyarsu ba,muyi abinda ya kawo mu kawai"


"Allah hajiya da kin barni na bubbugeta,tsinanniyar yarinya babu abinda ta sani sai mugun hali da baqar zuciya,ka bata ci ka bata sha ka bata suttura....."


"Ba haka akewa yaro ba,haquri akeyi dashi ana nuna masa dai dai da ba dai dai ba,sannan ma yarinyar nan inacewa ba itace ke fita da dukka dabbobin nan kiwo ba?" Anni tayi tambayar tana duban fuskar inna


"Eh itace,haqqun"


"To a ganina ai ba cancanci a daketa ba,don ko dabbobin da take kiwon idanuna bai taba gani ita din ta dakesu ba,don me ita ta cancanci duka da irin wannan sandar?" Jikin innar ne ya mutu,bawai don tana jin ta aikata kuskure ba,a'ah.....don sai tana tsoron kada tayi abinda zata jawo ma kanta asarar cinikin da za'ayi mata,don haka ta jingine sandar tana cewa


"Haka yake......Allah ya shirya muna"


"Ameen" anni ta fada tana maida dubanta ga maimunatu dake tsaye,wadda har yanzu bata iya bude idanuwanta ba


"Muje ki nunna mana su maimunatu" anni ta kira sunanta a tausashe,abinda ya sanyata bude idanun a hankali cikin mamakin daga inda kiran ya fito,ta tsammaci dama baquwar fuska ce,hakanne kuwa,akan fuskar anni idanun nata sauka sauka,idanunsu cikin na juna,saita sadda kanta qas kana cikin girmamawa tace


"Sannu da zuwa,ina kwana?" Murmushi ya wadaci fuskar anni,cikin kulawa ta amsa mata


"Lafiya lau 'yar fillo,ya hidima da kai kawo?"


"Alhamdulillahi" ta amsa.mata wani sanyi yana sauka cikin rai da zuciyarta,zata iya cewa tsahon lokacin da ta dauka tana bauta,bata taba jin wanda ya buda baki ya tambayeta irin haka ba.


         Waiwayawa tayi ta gaida daada,ganin idanun anni yasa ta amsa mata babu yabo ba fallasa,saita juya ta gaida laila,lailan ta amsa mata cikin kulawa,tana binta da kallo,kyakkyawar yarinya data tasamma zama budurwa.irin wannan,me tsananin kyau da sura,inda a birni take rayuwa.wanne irin rububi za'ayi a kanta,sai taji maimunatun ta kwanta mata a rai,yanayin nutsuwarta da sanyin halinta baiyi koda.kama dana 'yaruwarta da suka baro a bakin dakunan can ba.


       Cikin nutsuwa take nuna musu kowanne a ciki,yanayin yadda take musu bayani tare da zabosu kawai ya isa ya gaya maka tayi musu sani na haqiqa ba qaramin sani ba,sosai anni ta yaba da dabbobin,kamar yadda salihu yace,akwai alamun cikakkiyar lafiya tattare dasu,zasu bada nono da iri me kyau yadda ake buqata.


"Waccar sanuwar fa?" Anni ta tambaya tana nuni da ita


"Wancan naggen basu fiya bada irin abinda akeso da kyau ba,ba kowa keson irinsu ba,irin ne da wasu ke kasheshi don kada a sake samunsa" maimunatu ta fada tana duban saniyar.


         Kallon maimunatun anni tayi cike da birgewa da wani qaunar yarinyar da ya shiga zuciyarta,karo na uku kenan da tayi musu bayani makamancin haka,ta lura gaba daya cikin harkarta babu ha'inci babu rufa rufa,kayansu za'a siya,maimakon ta lullube aibunsa sai ta fidda musu da komai babu rufa rufa,gaba daya shekarunta basu taka kara sun karya ba,amma kuma dabi'u da halayenta irin na manya ne,hali na girma da muma dattako


"Ma sha Allahu,kinyi sa'ar yarinya qwarai furera,samun yaro mai irin dabi'a da halayenta abu ne me wahala" anni ta fada tana gyada kai cike da burgewa


"Gaskiya dai..." Salihu ya fada shima yana murmushi cikin mamakin halayyar maimunatun,saboda yasan halim mutane da dama kan cinikayya irin wannan,kowa kazo kana son siyan abunsa qoqari yake ya linke aibun abun ya baka shi ta fuskar da zaka gamsu da ingancinsa.


           Maganar ta sanya inna furera dauke idanunta daga hararar da take danqarawa maimunatu zuwa kan anni,bayan ta wadatar fuskarta da murmushin yaqe


"Haka ai take,kuma har 'yar uwarta da muka baro a can ta fita" ta fadi tanason fidda gajenta kunya gaban surukarta da kuma baqin idanun da suke wajen


"To ma sha Allah,Allah ya dorar dasu akan hakan"


"Uhmmm...meen ameen"inna furera ta fada tana son nuna jin dadinta.


        Yadda inna furera ta fada haka anni tasa salihu ya irga kudinta cas aka tafe mata,harda qaramar rawarta saboda farincikin ganin irin kudin data karba sama ta ka,lallai a duniya bata da masoyi kamar daadar himu,wadda ita tayi mata silar wannan ciniki mai gwaggwabar riba.


          Har sun juya zasu wuce anni ta waiwayo tana duban maimunatu


"Jikata kema ai ya kamata ace an baki wani abu ko,saboda qoqarin nuna mana zabin qwarai da kikayi" qaramin murmushi mai cike da kunya da kuma kawaici ta sake,tayi qas da kanta ba tare da tace komai ba,kamar ma kuma taga hararar da inna furera ta fara auna mata


"Basai kin ban komai ba kaaka,haqqina ne nayi hakan don fita haqqin Allah a kaina" tabbas badon idanun da suke wajen ba ba abinda zai hana inna furera kai mata mangari,qiri qiri yarinyar nason jaza musu asara?,don batasan yawan kyautar da matar tayi nufin yi mata ba


"Gaskiya ne" anni ta fada,saita karba jakarta a hannun laila wadda duk wannan abun da ake hankalinta nakan daukar hotuna cikin wayarta kusa da dabbobin,don ta samun abun adanawa ya zame mata tarihi,kuma ta bada labarin xuwanta rugar,don kuwa da wayonta ba zata iya tuna yaushe tazo rugar na qarshe ba.


         Sabbin kudi ta fitar ta irgasu a miqe ta miqa maimunatu


"Naji dadin riqe gaskiyarki,wannan kyauta ce bisa hakan" dan noqewa kadan tayi kamar ba zata karba ba,har sai da salihu ya sanya baki,sai data saci kallon inna furera taga yadda take watsa mata harara sannan tasa hannu biyu ta karba tana fadin


"Allah ya saka da alkhairi,ya maida ninkinsu"


"Ameennn" anni ta fada cikin jin dadin addu'ar maimunatun.


         Bata tsammanin ko sassan nasu su anni sun bari inna furera ta miqa mata hannu,ko batayi.magana ba tasan me take nufi,shi yasa gaba daya batayi nufin amsar kudin ba,saboda tasan cewa zata raba matar da kudinta ne,ita kuma da tayi niyyar bawa ba zata mori komai a cikinsu ba,duka ta dunqule kudin hannun nata ta miqawa inna fureran,sannan ta tsugunna ta debi kayan aikinta ta fara gyara wajen bata ko waiwayeta ba.


       Babu kunya babu kuma tsoron Allah ko daya a tattare da ita ta hade dukka kudaden ta irge abunta cas ta soke su tayi gaba abinta tana rera waqa,yau itakam ranta fes,mutuwa batayi mata komai ba sai rana data yi mata,banda silar mutuwar ina ita wannan dukiyar?,ina ita ina mallakar wadan nan kudade?,kudi kam sunzo mata a dai dai,tanadin bikin gajenta zata farayi tun yanzu,saboda bikin gata takeso tayi mata.


>>>>>>>>>>"sannu anni.....an gama komai ko?" Yuuma ta fada sanda take shigowa rumfarta dauke da kwanon sha da ta cikashi da damammiyar fura da nono wadda babu surkin sugar ko kadan a cikinsa


"Mun gama komai ramatu..dabbobi lafiyayyu,har sunso sufi na labaran din ma"


"Ai sunfi ma anni,sun hadu da makiyayiya mai hazaqa da iya kiwo,irin kiwon da babu ha'inci a ciki" yuuma ta fadi tana zama sosai gaban anni tana murmushi


"Ai naga alama,ko ba wata yarinya maimunatu ba?"


"Itafa,baiwar Allah" yuuma ta fada fuskarta na dan canza yanayi


"Ai tunda na shigo Allah yake hadamu,naketa ganin abubuwan mamaki daga wajen yarinyar,na jima banga me kiwo irinta ba,sannan abinda zai sake baki mamaki da ita.....wajen cinikin nan,kowacce dabba da muka nuna manaso sai datayi mana bayanin lafiyarta da sauransu,babu ha'inci" cikin gamsuwa yuuma take gyada kai


"Bata tsinta a qasa ba ai,gado ne me kyau daga wajen mahaifiyarta,Allah ya jiqan ruma"


"Allah sarki,kice marainiya ce?" Anni ta fada tana jan kwanon furar gabanta tana qoqarin budewa


"Marainiya ce,wadda aka kasa yi mata riqo na tsakani da Allah.....kinsan mahaifiyarta anni,kin tuna matar da kikaga wata balama me juna biyu a wajenta kikai sha'awarta shekarun baya can da suka shude,ta qara miki da kyautar wata akuya,akuyar da kikace ta miki albarka fiye da kowacce dabba a kiwonki?"


"Af.....af ina zan manta da wannan baiwar Allar,dama itace mahaifiyarta?"


"Itace anni" yuuma ta amsa mata tana dauko wani kwanon da ta shaqewa anni shi da dambu me dumi tana aje mata


"Allahu akhbar......." Maganar annin ta tsaya sakamakon shigowar laila tana qananun mita.


       Daga kai anni tayi ta dubeta,daure take da zani daurin qirji da kuma qaramin hijab fari,sai jakar kayan wankanta dake riqe a hannunta,daya hannun nata kuma wayarta ce


"Wanne irin sakarci ne haka zaki fadowa mutane ba sallama?,banason tsiyatakun banza da wofi fa?" Cuno bakinta tayi gaba tana sauke wayar daga fuskarta tana kallon anni


"Don girman Allah anni ki karba wayar da abbi ya baki ko zamu huta da ire iren takurar su ya jabir" gyara zamanta tayi tana kallonta sosai


"To...idan kuma naqi sai yaya kenan uwata?" Hannu laila ta yarfe,bataso annin ta hutsance mata,lallabata takeson yi ta karba a wuce wajen


"Anni.....yanzu fa wanka zan shiga,ashe muna hanya daxun ya kirani banga miscal dinsa ba sai yanzu,ina daga wayar ko tsayawa amsa sallamata baiyi ba ya hauni da balbalin masifa,Ni bansan sanda ya koma haka ba wall....." Maganar tata ta katse saboda shigowar wani kiran,saita duba sannan tace


"Gashinan ma" gaba data tattar wayar harda earpiece din jiki ta miqawa anni ta juyawa tana shirin ficewa


"Wannan zaren na jiki da kika hadani dashi shi zan qaqabawa kunnena?,bada ni ba gada a maqabarta,zoki tsige abinki ki karbi naji da gayan wayar ma" dole ta dawo ta cire matan yadda ta buqata da sauri don kada kiran ya katse ta sake jazawa kanta wani sabon mita da qorafin.


No comments

Powered by Blogger.