Gurbin Ido 8
08
Fitar jauro daga gidan sai dukkan bala'i da masifar suka dawo kan maimunatun,inna nayi gajee nayi
"Tunda ya daure miki gindi ko?,to wallahi baki isa ki kwanta kiyimin saqe saqe kamar gawar sababi ba,bayan jiya ya shirga miki
abinci kin cinye,to kin ciyoma kanki,kinci abincinki na jiya dana yau,waryo wan en jungul!,(zoki dora mana abinci)" ta fada a tsawace,har maimunatun tana jin kanta kamar zai cire.Tuwo ne na masara miyar danyar kubewa,gaba daya kayan aikin innar ta tura mata,ta baza tabarma tayi zamanta qasan bishiyar dake basu iska.
Zata iya cewa batasan ta yadda akayi take aikin ba,don komai tana yinsa ne a wahalce,cikinsu kuma babu wanda ya taimaka mata koda da firfita wuta ne,yadda bata da lafiya haka aikin yaja lokaci yaqiyin sauri,saboda rashin kazar kazar da kuma qwarin jiki,abinda ya qara iza wutar masifa da bala'in inna,ya kuma sanya maimunatun taji inama ace kiwon ta tafi a haka,tabbas ya fiye mata wannan wahalar girkin.
Tana zaune tana niqan kayan miyan da zata dora miya saman dutsen markade taji sallama,ta daga kanta a wahalce tana amsawa,matashiyar da aqalla zatayi sa'a da ita ce(zubaida),sai kuma yaron dake gefanta(sadam),kasa dauke idonta maimunatu tayi daga kan fuskar yaron,saboda kamarsa muraran da ibrahimunta.
Shima yaron ita yake kalla,kafin daga bisani ya dauke kansa,abinda ya bata mamaki hararan da zubaidan ta wurga mata kafin su miqa zuwa inda inna ke zaune tana kada nono,maimunatun kuma ta maida kanta ga aikin da takeyi cikin mamaki,iyaka saninta da zubaida saidai kallo daga nesa,ba abinda ya taba hadata dasu,koda gaisuwa kuwa,takan jima bata gansu ba,kamar yadda suma suke jimawa basu ganta ba,domin su din zuwansu kiwo na lokaci bayan lokaci ne bawai koda yaushe ba,koda ma koda yaushe ne,tana daukar watanni kafin magana ta hadata da wani a wajen kowo har taje ta dawo,saidai idan baqin makiyaya da ba 'yan asalin rigarsu ba sun ratso ta dajin da suke kiwo.
"Maraba da zubaida da saddam" innar laulo ta fada cikin wani irin kirki da kuma fara'a,wanda ya sanya har sai da maimunatu ta tasa kanta dake mugun sarawa ta saci kallonta.
Daga gefan tabarmar da take kai suka zauna,gaisheta yaron ya farayi sannan zubaidan
"Dama daada ce ta ailo na gaya miki,akwai baqi da sukazo daga gombe,naggen bappa suka saba siya,to wannan karon babu,bappan ya fita dasu gaba daya,shine tace nazo na gaya miki,tasan cikin naki akwai irin wadanda sukeso,gobe zasu zo da safe kafin a fita dasu su gani" madaukakin farinciki ya kama inna furera,cikin ranta ta sake jin duk duniya bata da masoyi sama da daada din,dama ta jima tana shawarin saida wasu daga ciki,ko don ta saku ta sake badda dukka wata alama da zata iya zama shaidar rashin zamowarta mallakin dabbobin,to amma kuma batason saidawa anan kusa,tafison waje me nisa inda zasu siya da daraja
"Miyatti Allah,miyatti daada,amma naji dadi wallahi,Allah ya kawosu"
"Ameen,sannan tace na gaya miki,anjima yaaya himu zaizo wajen gaaje,su sake ganin juna" kamar inna furera zafa taka rawa haka tayi,takai ta kawo ta rasa wanne tukuci zata bawa zubaida,qarshe dai har suka bae gidan bakinta yaqi rufawa.
Saukar zancan a kunnuwan maimunatu sai ta kasa tantance cikin wanne yanayi take ciki
"Ibrahimu zaizo yaga gaaje" wannan shine dalilin da yasa ta daina ganinsa kenan?,me hakan yake nufi?. Tunanin ya sanya aikin nata ya sake yin slow fiye da dazu,tun inna na mita da baki har sai data fara kai mata duka da hannu
"Me shegen baqin halin tsiya,bakyason aikinne,a haka kuma zakiyi shi".
Takanas innar ta taso gaje,ta hada mata madarar shanu da lalle ta murje mata jikinta,zaka tsammaci kamu za'ayi mata irin na amare,duka a wannan lokacin ta sanyata ta tsefe kanta mai yalwar gashi,wanda datti ya dakushe tsahonsa ta wanke mata shi fes,ta raba mata gida biyu ta zubo mata da jelarsa hagu da dama.
Tun yammaci aketa shiri gamida da gwada yadda zata tarbi ibrahim din,duk don saboda ta burgeshi,mudukaje(kayan saqin fulani) na can qasan kayanta ta ciro ta ajjiye,dukka abin nan da ake na maimunatu idanu ne,saidai gefe daya zuciyarta ta gaza hutawa da tunanin abinda zaije yazo.
Dai dai sanda maimunatun ke saman dan mayafin da take shimfidawa tayi sallah....dai dai sannan gaje keta faman fecewa fuskarta kwalliya,ta kalli madubi yafi sau shurin masaki,ta juya ta sake juyawa har sau babu adadi,burinta shine taga komai yayi,sannan ta burge ibarahim matuqa,maimunatu tana zaune a wajen,bata motsa ba bare ta waiwaya taga abinda gajen keyi,saidai kuma kunnuwanta na samun aiken saqonnin waqe waqen da gajen keyi cikin harshen fullanci,tana yi tana juyi,abinda zai nuna maka cikin zallar farinciki take a yau din.
Laulo ne ya shigo dakin,yaron da za'a iya cewa yafi gaje hankali,don wasu abubuwan da shi din yakeyi yana yinsu ne da yarinyata,da kuma rashin samun isashshiyar tarbiyya da kyau
"Himu yazo,inna tace akai masa taburma" sai yaron ya juya ya fita yana tsalle tsalle abinsa.
Juya idanunta gajee tayi cikin farinciki,ta jima tana qaunar himu tun ba yanzu ba,tun daga sanda inna ta gaya mata cewa shine mijin da suka zaba mata ta riqe hakan a ranta,bata taba mancewa ba,hakanan bata yarda ta kula kowa ba saboda ibrahim,duk da tarin masoyan da take dasu a rugar,don dai dai gwargwado tana da irin nata kyan.
"Ki dauko tabarma ki kawomin zagaye" ta bawa maimunatu umarni kai tsaye tana ajjiye madubin hannunta,har takai bakin qofa ta tsaya ta juyo tana duban maimunatun jin bata ce komai ba
"Ko ba zaki kawo bane?"
"Yanzu zan tashi" ta amsa mata murya a raunace,qwafa gajee taja sannan ta sanya kai ta fice.
Babu yadda zata kaucewa umarnin gajen,ya zame mata dole,hakanan ta miqe dauke da tabarmar ta nufi inda gaje ta umarceta.
Salon tafiya na daban ta canza kamar yadda suka wuni suna gwadawa ita da inna furera,ibrahim din na tsaye,jingine da wani kutturen ice,qafarsa harde da juna yana duban gajen sanda take tahowa,cikin salo na nuna jin kunya ta dan sunne kai sanda ta fuskanci kallonta yake,farinciki ya cika zuciyarta,tana hangen ba wani faɗi tashi me yawa zatayi ba zata samu kan ibrahim din.
Wani tattauran yawu me daci ibrahim din ya hadiye,ya rufe idanunsa yana sake tursasawa kansa da zuciyarsa daurewa da kuma bin umarnin daada,yana jin kamar zuciyarsa zata fashe saboda takaici,meye ne daada ta hango masa tattare da gaje,me yasa idanunta suka rufe ta kasa gano abubuwa masu tarin yawa da yake gani tattare da maimunatu?.
Yana bude idanunsa ya hangi maimunatun biye da gaje,gaba daya sai ta wafce kallonsa,ya tattaru gaba daya a kanta,hasken wutar kara da mazauna wajen suka kunna daga can gurin zuwa can ya haske wajen sosai da har yake samun damar ganin kowacce a cikinsu
"Sannu da zuwa" gajee ta fada tana dan russunawa hadi da rausayar da idanu
"Sannunki" ya amsa mata murya a ciki,yana dauke dubansa daga maimunatu wadda ta qaraso wajen riqe da tabarmar
"Ki shimfida masa mana kin bar mutane a tsaye,sai wani abu kike kamar mara laka a jiki.....mayya...." Hannu ibrahim ya daga mata da sauri,saboda zafi da zuciyarsa ta fara yi masa,bazai iya daukan hakan ba,a nutse ya dubi gaje
"Wannan din ba bil'adama bace kamarki?,bakisan Allah ya karrama dan adam ya kuma mutuntashi ba?,matuqar wannan itace dabi'arki,to kin dauko hanyar da ba zaki sake ganina a nan ba" sosai maganar ta bata mata rai,ta kuma sake saka mata kishin maimunatu a ranta me yawa,amma a yanzun nema take,dole ta jure,don haka ta sadda kai
"Kayi haquri" bai amsa mata ba,sai ya miqawa maimunatu hannu ya karbi tabarmar,ya sani sarai anyi hakanne don a tozarta maimunatun,a sake kuma nuna masa ita din ba kowa bace,tunda daadansa bata boye masa komai ba,ta gaya masa duk irin matakin da suka dauka,tayi ne da nufin jan kunne,ta kuma gaya masa zaman lafiyar maimunatu shine ya rabu da ita,abinda basu sani ba shine,wannan abun da sukayin shi ya sake zubda darajar gajee harma da inna furera a ransa,ya kuma sake sanya masa tausayi da qaunar maimunatu.
Batasan cewa himu ya fara taka wani matsayi a zuciyarta,batasan cewa ya fara bude wata rufaffiyar qofar da bata tsammaci budewarta ba sai data koma daki,gaba daya ta gaza sukuni,ta kuma kasa kwanciya kamar yadda taso ta kwanta din,saboda yadda jikinta yake wani irin radadi da kuma zugi sakamakon aikin da tasha,ga kuma tabbai na duka wani wajen har ya fara rurucewa,abinda ya hade mata kenan,ya kuma saukar mata da zazzabin da ya tilasta mata kwanciyar da a daxu ta kasa yinta.
A hankali ta bude idanunta sakamakon muryar gaje data jiyo cikin muryar kuka
"Ke....mene....meye?" Inna furera data fito daga daki zaninta a hannu ta fada,hankali tashe tana duban gaje
"Inna,kai tsaye himu fa yake gayamin wai bani bace a zuciyarsa,zuciyarsa tuni wata ta karbeta,kuma wallahi nasan ba kowa yake nufi ba sai waccar mayyar,tunda na daka mata tsawa har ya tafi banga faraga a fuskarsa ba,ki taimakeni inna,wallahi inason himu" wani dogon tsaki innar ta saki tamkar zata tsige harshenta
"Ahaf.....aikin banza kenan,yo yayita fadi baya sonki.mana,qarewa ya samu amsa kuwwa ya daura,yayita bi rugage yana fadin hakan,ai yayi aikin banza,maganar nan babu me tashinsa,shi ya san wace uwarshi,tunda ta fada babu me tashin maganar,shi yasa ya biyo ta hakan don kice bakiyi,wadda kuma yake qulafucin haihata haihata shi da ita,qwalelen kare da hantar kura,yadda naci alwashi in sha maka Allahu....matuqar ina raye saikin aurin namijin da kaf rugar nan babu irinsa,ibrahimu ne,kuma shine naki,muje na karanta miki karatun zaman duniya" inna ta fada tana kama hannun gajee sukayi dakin innar.
Maida idanunta maimunatu tayi ta rufe,tana fitar da numfashi me azabar dumi saboda zafin zazzabin daya ratsa kowanne sashe na jikinta,kadaici gami da kewar mahaifiya ya cikata,koda zata mutu a saman wannan shimfidar babu lallai a ankara,koda za'a lura din wala'alla sai ta kumbura ta fara fidda wari,ko kuma sanda suka nufaci tashinta don ta biya musu buqatunsu
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" ta samu kanta da fada tana rushewa da kuka mara sauti,addu'a ce da take yawan jin mahaifiyarta tana yi,rashin uwa wani babban gibi ne a cikin rayuwa,wanda babu wani abu da ya isa ya cike maka wannan gurbin.
Duk yadda take jin jikinta bayan ta idar da sallar asuba amma hakan baisa ta koma barci ba,tasan koda ta koma din ma wani tashin hankali da kuma firgici zata kirawa kanta,don haka taci gaba da zama,har zuwa lokacin daya dace ta fara aiki yayi,ta miqe a hankali ta yaye labulen zanin atamfa dake qofar dakin nasu tayo waje.
Duk da yadda suke da sammako da kuma tashin wuri amma wajen tsit yake,kowa yana ta sashensa,babu komai sai kukan dabbobi dake turke a muhallensu.
Sannu sannu tana aikin gari na dada yin haske,mutane na sake fitowa daga muhallansu kowa na kama sabgar gabansa.
Inna furera ce ta fara fitowa daga nasu gefan,ta saki wanke wanken da takeyi ta qarasa inda take tsaye tana gaidata,bata bi takan gaisuwar tata ba tace
"Ki saki wanke wanken,kije ki gyara wajen dabbobin can,nasan masu sayen suna hanya,tunda da wuri zasu zo,sannan inaso ki nutsu da kyau,na tabbatar sai an kiraki lokacin cinikin,saboda ke kike kiwonsu,kinfi kowa sanin wadanda sukafi kowanne lafiya da nada nono da kyau,to bance ki tsaya nune nune ba,ki barsu su zaba da kansu,ki kula....bazan lamunci ki jawomin asara ba" kanta a qasa take amsawa innar,bata miqe ba sai data bata umarni,ta taka zuwa inda take adana kayan sharar wajen ta debesu da qyar ta zagaya zuwa makwantar dabbobin.
Sanda suka ganta sai da dukkaninsu suka motsa,ta saki murmushi itama tana isa gabansu,kwanaki biyun da bata gansu ba sai takejin tayi kewarsu ba kadan ba,suma kuma tasan hakanne,don dai kawai basu da baki bare su bata labari.
Duk da jikinta babu qwari,cikin boyeyyen ciwo dake cin naman jikinta take amma cikin qawa zuci take aikin,tana yi yana musu magana kai kace da dan adam take,sai data bi kowacce dabba data saba dubawa ta dubata sannan ta fara aikin.
A hankali suke takowa da qafa,tun daga gidan bappa labaran din,anni da kanta ta zabi su tako da qafan
"Ku barni da qarfen nasaran nan,gwara mu taka da qafa tunda ba nisa ke da gidan ba" tace da daada,wadda da kanta tayi mata rakiya ita da safiya da kuma laila.
Tahowar da sukayi din ya bawa lailan dama daada damar kallon rugar sosai,bambancin rayuwa qarara na zahiri da suke gani,wanda yayi dai dai da karin maganar nan ta bahaushe da hake cewa Allah daya gari banban,suna tafe laila na tambayar sadam wasu abubuwan,tafiyar ta zama wani mabudi na ilimi a gareta.
"Maraba,lale,sannunku da zuwa" shine abinda inna furera ke faman fadi,tana kai kawo tare da qoqarin shimfida musu tabarma gaban dakinta,yayin da gajee ke zaune abinta saman kujerar tsuguno.
*Don samun ci gaban sabbin galla gallan pages,ziyarci page dina a AREWABOOKS da sunan HUGUMA*
Leave a Comment