Gurbin Ido 5

 


LAST FREE PAGE 05*


*AREWA BOOKS::HUGUMA*




            Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya kusan rabi da rabi na dawowar maimuntu daga kiwon ibrahim ne,wasu lokutan yakanyi gaba wani lokaci kuma tana biye dashi a baya,har sukai gida,ya tayata

daure na daurewa ko sharar wajen idan bata samu tayi ba,sudan taba hira sannan ya wuce zuwa gida. Duk da cewa fiye da rabin hirar shi kadai yake abarsa,na maimunatun baya wuce eh ko a'ah. Haka kawai fa tsinci kanta da jin dadin tarayyarsu ita dashi,sai takejin wani canji na zuwa ma zuciya da rayuwarta,gaba daya wannan kadaicin babu shi,tana jin kamar ta samu wani bango da zata raba ko ta jingina dashi ko yaya yake,sabanin daa da bata da wanda zai magana da ita,magana da ake kirame dadi,idan taji magana daga bakin wani to fada ne,idan taji hira akanta to ta tsangwama ce,wani lokaci takan jima kwance duk sanda taje bacci,tana tuno irin hirarrkinsu da ibrahim,wani abun takan saki murmushi ne ta kuma juya ta gyara kwanciyarta.


         Ta bangaren ibrahim din wani matsayi na musamman yakeji maimunatu na sake damu cikin ruhi da zuciyarsa,a dan zamansu ya fahimci abubuwa masu tarin yawa tattare da ita,ta banbanta qwarai da duka yaran rugar tasu,tana da wata irin nutsuwa da fasahar magana wadda ya jima baiga irinta jikin wata 'ya mace ba,komai nata na hankali ne da sanin ya kamata,yakan zauna yana kallon yadd take iya controlling dabbobinta da baki kawai ta hanyar basu umarni,lokaci dai daiku ne takanyi amfani da sandarta wanda xaiyi wuya ma kaga hakan.


         Yadda take tausayin dabbobin kamar 'yan adam,bayan dukka alamu sun nuna sun fita samun gata da kulawa,duk da har yanzu bata taba bude baki tayi masa wata magana data shafi gidansu ba,yadda take communicating dasu kawai abun burgewa ne,duk da shima cikakken bafullace ne amma ba kasafai yake ganin hakan ba,lokuta da dama idan ya tsokanetan saidai tayi murmushi kawai,wanda kusan wannan din dabi'arta ne.


           Ko sau daya himu baiyi nufin zuwa ga gaje ba kamar yadda daada ta buqata,wani lokaci ma sai ya rako maimunatu yake tunawa da batun,saidai yana ganin ba abu bane mai yiwuwa,yana da tabbacin komai zai daidaita da zarar bappansa ya dawo,wanda ya qara kwanaki kan wadanda yace zai dawo,saboda jiran haduwar kudadensa dake hannun mutane.


**************Yammacine lis,wanda yake busa wata ni'imtacciyar iska me dadi,yanayi ne da ya yiwa halittu da dama dadi,bawai ga dan adam kawai ba,hatta da sauran tsirrai da kuma dabbobin daketa kai kawo suna kiwo a farfajiyar wajen da ya zame musu wajen yini.


        Daga can qasan bishiyar idan kakai kallonka wajen,bafullatana maimunatu ce cikin baqin saqinta,zaune saman koren hiramin da himu ya shimfida mata,shi kuma yana zaune daga gefanta saman wani dan mulmulallen dutse da bai cika girma ba.


         Murmushine ke fita daga saman fuskarta,murmushin da kana kallonsa kasan kunyace cike dashi,ko a iya zamanta idan ka.kalla da kyau kasan a takure take,hannayenta sarqafe cikin juna tana kallonsu,yayin da shi kuma ibrahim ya zuba mata dukka idanunsa yana jiran amsar tambayar daya jefa mata.


         Wani irin nauyi ibrahim din ke aza mata duk lokacin da ya zaunar da ita irin haka yana karanta mata kalaman soyayya......daga qarshe kuma a yau din ya tirketa kan lallai sai ta furta masa da bakinta tana sonshi,saboda bai taba jin hakan daga bakinta ba.


         Wani abune kuma ita din da bata jin zata iya gaya masan,kalma ce data ji ta girmi kanta matuqa,koda baya kallonta ba zata iya fada ba,bare yadda yake zaune yana kallonta.


          ,sirara kuma jajayen labbanta ta motsa a hankali


"midelli...yamma tayi" dauke idanunsa yayi daga kanta yana murmushi,duk da yasan yau din sun gota lokacin komawarsun,amma tayi hakanne don ta kaucewa tambayarsa,yana mamakin kunya irin tata kawaici da kuma kamewa,sai ya miqe kawai ya dauki sandarta da a yanzun shike amfani da ita idan zasu koma gida.


         Kamar ko yaushe ya tayata suka kammala komai,yayi tsaye daga jikin wata rusashiyar bukka dake daura da wajen yana dubanta cikin murmushi


"Shikenan,tunda ba zaki bani amsa ba maimunatu zan tafi,sai jaaango?" A kunyace tayi murmushi tana kauda kanta gefe daya,ya sauke qafarsa da ya harde waje daya ya fara takawa a hankali yana barin wajen


"Ka gaida gida" ta fada cikin siririyar muryarta da ba kasafai ya fiya jinta ba,sai daya waiwayo cikin jin dadi ya kalleta yana jinjina kai sannan yaci gaba da takawa,hakanan taji kunya ta kamata,abinda yasa ta juya da sauri da nufin shigewa zuwa shiyyar da dakunansu suke. Saidai kuma cak ta tsaya,saboda ganin inna tsaye daura da ita,da alama taji komai ta kuma ga komai.


        Kallon da innar kawai ta tsareta dashi ya sanyaya mata gwiwa ya kuma sanya mata fargaba me tarin yawa,gabanta ya fara faduwa da wani mugun qarfi,duk da haka ta ari dakiya taci gaba da nufar inda innar ke tsaye tana ci gaba da kallonta


"Immoi'onni?(waye wancan?)"innar ta fada a tsawace cike da tuhuma da kuma zargi,yanayin yadda tayi mata maganar ya jefa tsoro a zuciyar maimunatun,ta qanqame jikinta waje guda,tana jiran jin saukae duka daga wajen innar,don wannan din ba sabon abu bane a wajenta


"Tambayarki nakeyi waye wancan din?"


"Sunansa ibrahim.....ya tayani qaraso da dabbobi gida ne"


"Meye hadinki dashi?" Inna ta sake tsareta da tambaya,saboda zargin da ya shiga ranta,taso taha fuskarsa amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba,saidai batajin wanda take tunani dinne,don bata da shakka akan alqawari da yarjejeniyar dake tsakaninsu


"Babu komai" ta amsawa innar kanta a qasa,tana matse hannayenta waje guda,tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa fat fat


"Yauwa.....gwara ki rufawa kanki asiri,ke ta buɗeri ce,shi daya zai iya rufa miki asiri ya aureki,don haka kada ma ki batawa kanki lokaci ki yaudari kanki kice zaki saurari wani,kaf fadin karkarar nan bana jin akwai wanda zai iya daukarki idan bashi ba,koda an samu to yayi miki qarya,saboda haka ki kiyaye" daga haka tayi gaba zuwa garken dabbobin,tabi tana dubasu daya bayan daya tana kuma irgasu kamar yadda ta saba duk sanda maimunatun ta dawo,kai zaka zaci tana duba kaya data bawa qasurgumin barawo ajiya ne.


           "Wuwuɗandu(ki share wajen)" ta bata umarni tana fita daga garken tayi gaba abinta,duk yadda takai ga gajiya hakanan dole babu yadda zatayi haka ta laluba kayan sharar ta fara gyaran wajen,duk da cewa a dazun kafin su tafi ta gyara wajen,batasan me ya bata wajen hakan ba,duk da tasan ko ba yaro idan innar taso bata wahala,zata qirqiro mata aikin ko kuma wanda yayi kama dashi,duk dai don kada ta huta,bata qaunar ganinta a zaune ko da na minti daya ne.


 

        °°°°°°°°°°°°°°


   A nutse yayi sallama cikin rumfar innar yana yafe da koren hiraminsa,dawowarsa kenan daga sallah sadam yace masa innar tana kiransa.


         Abinda ya bashi mamaki shine ganinta da yayi a tsaye tana kai kawo daga wancan bangon zuwa wannan,idanunta dake cike da fushi ta daga ta dubeshi,ba tare data amsa sallamarsa ba kai tsaye tace dashi


"Joɗa(zauna)" kasa zaman yayi,sai ya duqa daga gefe kawai yana kallonta,ta tako gabansa a hankali tana dubansa


"Inaso naji bayan ni wace mahaifiyar kake da ita?" Sosai tambayar ta bashi mamaki,har ya tada kai yana dubanta sosai kafin ya kauda kansa ganin itama shi take kallo,yaro ne shi mai tsananin biyaya,don haka bazai iya hada idanu da daadan ba


"Babu daada....amma wani abune ya faru?" Sake baci ranta yayi


"Ni kake tambaya wani abune ya faru himu?,ashe ni ba uwarka bace?,ashe ban isa na gaya maka magana kaji ba?,tun a waccar ranar ban rabaka da maimunatu ba?,ban gaya maka babu kai babu ita ba?,shine kasa qafarka kayi wancankali da maganata akan diya mace saboda bani da wani muhimmanci a wajenka?"


"Ba haka bane inna..."

"To yaya ne?" Shuru ya gifta wanda bai gaza qasa da second hudu ba


".......ko kuwa maganar yuuma ce ta shiga kunnenka fiye da tawa ni mahaifiyarka?" Girgiza kansa yayi da sauri


"Ko kadan.....kada ki saka sunan yuuma don Allah daada,ba ruwanta,batasan me akeyi ba tun wancan ranar data fita a dakinki"


"Ibrahim!" Ta kirayi cikakken sunansa,abunda ya sake tabbatar masa zata yanke tsatstsauran hukunci ne,kuma kowanne irin hukunci ne hakan zata fadeshi ne ba da wasa ba


"Daga yau.....idan ka sake ka sake zuwa inda maimunatu take Allah ya isa ban yafe maka ba,sannan koda bayan raina ka sake ka aureta ban yafe maka ba" qarasa zama dirshan yayi a qasa maimakon tsugunon da yayi,ba qaramin kaduwa da hukuncin nata yayi ba


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya dinga maimaitawa kansa a qasa,bai taba zato ko tsammanin hukuncin innar zaiyi tsaurin haka ba


"Don Allah inna ki sassauta kiyi haquri,maimunatu bata taba yi miki komai ba,banda......." Tsawa ta dakeshi tana katseshi


"Banason na sake jin komai daga gareka,wannan shine hukuncina na qarshe,tashi ka fita!" Ta fada a zafafe tana nuna masa qofa,sai da ya dafa qasa sannan ya miqe


"Himu" ta kirashi sanda yakai qofa


"Na baka kwana hudu kacal,ka shirya fara zuwa wajen gaje kamar yadda na gaya maka,umarnine nake baka" bayajin xai iya cewa da ita komai,don haka kansa da yayi masa nauyi kamar ya dauki kaya ya gyada mata sannan ya fice daga dakin yana jin jikinsa kamar zazzabi na shirin rufeshi.


           **********Sake juya rufaffen takalmin danqon hannunta tayi don ta tabbatar dabarar data yi masa zata kaita gida,ita kanta batasan adadin liqin data yi masa ba,wani gurin da garwashin wuta da leda,wani gurin kuma tana samun zaren lilo ta zarge inda yake shirin rabewa dashi.


          A hankali ta duqa ta ajjiye takalmin a qasa ta zura qafafunta,tadan motsa qafar ta tabbatar yayi,sai ta sauke ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ya sake fiddata a yau dinma dai still,takalmin bai mata tutsu ba,batasan ya zata kasance mata duk randa hakan ta faru,itadai shi daya ta sani a matsayin takalmin da take dashi,wanda ita kanta batasan adadin kwanakin ko shekarunsa ba a duniya bare ta iya tantancewa.


           Sake waiwayawa tayi hagunta da damanta,har yanzu bata debe tsammani da ganin himu ya bullo ba,duk da cewa lokacin zuwan nashi ya gota sosai,tana da tabbacin babban abune ya tsaidashi,saidai tana fatan koma meye ya  kasance yana lafiya qalau.


          Waiwaya tayi sashen wata saniya ke zaune,gefanta jaririn san data haifa ne a dazu jimawa kadan bayan isowarsu wajen,ta tabbatar inna batasan cikin ya isa haihuwa ba,da ba zata bar mata ita zuwa wajen kiwo ba,dole idan lokaci yayi himun baizo ba,haka zata hada da kula da sauran dabbobin,da ita wannan sabuwar haihuwar su wuce gida,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,ita kadai cikin wajen,cikin tsoro da fargaba saniyar tahaihu a wajenta,wanda ita kanta tasan babbar kasada tayi,saboda samuwar matsala ta mutuwar uwar ko abinda aka haifa,dai dai yake da samuwar matsala cikin tata rayuwar,ko daya innar batasan wata aba wai ita asara ba bare haquri da ita idan ta sameta,haka ta dinga kai kawo har haihuwar ta kammala.


           Saman dan dutsen da himun ke zama ko yaushe idan yazo ta koma ta zauna,idanunta nakan abun hannunta na shirin duwatsu green da jaa,tasa yatsanta guda daya tana wasa dasu,ta warasu wani lokacin ta hadesu,tana tuna lokacin da innarta ta zura mata su,har yanzu lokacin yaqi bacewa cikin idanunta.


          Ta jima zaune a nan,tana jin wata kewa da kadaici suna shigarta,lokaci lokaci tana daga kai ta dubi yanayin yadda dabbobin ke kai kawo sannan ta sake maida kanta.


         Karo na qarshe data daga kanta ta tabbatar lokaci yayi da ya dace su koma gida,ta sauka daga kan dutsen a hankali,ta gyara zaman hularta sannan ta dauki sandanta ta fara ratsawa ta tsakaninsu tana hada kansu.


        A gaba take sanyasu mafi yawancin lokuta,idan taga zasu canza hanya ko zasuyi wani abu ba dai dai ba takan tsawatar musu,suna ji kuma suna fahimta yawancin lokuta,yau dinma haka ne,hannunta na dauke da sabuwar haihuwar da daya daga cikin shanun tayi.


         A hankali baqaqen lafiyayyun motocin guda biyu ke kutsowa cikin rugar,tana haura duk wani tudu da kwari da kuma kwazazzabo dake kan hanyar ba tare da mutanen dake ciki sunji komai wata jijjiga ko wahala ba da ire iren wadan nan hanyoyin ke dashi a duk sanda mota zata ratsasu ba,hakan ya faru ne sanadiyyar kyau da lafiyar motar,wanda hakan yake da nasaba da irin tsadar da kowacce mota guda daya ke da ita.


        Motar farko mutum hudu ne a ciki,driver salmanu,sai wani zaune a gefansa hayatu,daga seat din baya kuwa dattijuwar macace,hakimce cikin shiga ta alfarma,kyakkyawar lallausar blueblack din atamfa ce wadda tayi matuqar haska farar fatarta,duk da akwai tsufa tattare da ita,amma yanayin da take ciki na hutu da kuma jin dadi ya hana bayyanuwar tarin shakarunta,daga shekara sittin da takwas,ya maidata zuwa 'yar shekara hamsin,idan ka cika qwaqwafi kuma ka qara mata da uku,hankalinta na ga window din motar,tana duban hanyoyin da suke wucewa,wanda sukanyi gamo da mutane jifa jifa,duk mutumin da suka gifta sai ya bisu da kallo,saboda abune baqo a wajensu,zasu iya irga sau nawa suka samu labari ko sukaga shigowar mota rugar tasu,wasu sukan cika da fargabar su waye suka shigo musu?,wasu kuma kyau da motar ke dashi ne yake daukar hankalinsu har sai tayi nisa ta bacewa ganinsu.


           Daga gefan dattijuwar kuwa kyakkyawar matashiyar budurwa ce wadda duka duka ba zata haura shekara ashirin ba a duniya,shigarta kadai zai gaya maka cewa ta fito daga gidan ilimi wayewa da kuma wadata,kacokam ta tattara hankalinta ga wani littafi dake da shafuka masu dan dama,da alama nazari takeyi.


            "Salmanu........saukemin gilashin nan.....naga alama wannan baqin abun da kuka lafta masa bazai bar idanuwa suyi kallo yadda ya kamata ba" ta fadi tana hade gira.


         Karaf matashiyar ta daga kanta daga kan littafin


"Haba anni....me kuma za'a sauke miki kiji?,an kunna ac ne fa,ta yaya za'a sauke glass,kuma ta hakan ma ai ana ganin komai,tunda ba dare bane" harara ta juyo ta watsa mata


"Ke....kiyi ta kanki,ni ba dake nake ba,toke da wanne mataccen idon ma kike iya gani daga nan din?,idon da komai za'ayi saida gilashi?,salmau zaka saukemin ko kuwa?"


"Za'a sauke anni" yayi maganar yana sauke mata da hanzari kamar yadda ta buqata.


           Sai da aka sauke mata gilasan tas sannan ta sake matsawa jikin window din tana fara'a


"Yawwa,yanzu naji batu,amma daa an qunshe mu kamar 'yan kidnapping,ni ba baqin hali gareni ba da kullum xan fita zance a rufeni cikin gilasai" sarai matashiyar ta fahimci da ita take,kuma idan da sabo ta saba ko kuma tace sun saba da halin anni,duk wanda ke zaune da itama ya riga da yasan halinta sarai,don haka sai ta maida mayafin da yake kafadarta zuwa saman kanta,ta kuma rufe littafin saboda hasken ya mata yawa,karatun bazai mata dadi ba ta maida jakarta,ta ciro wayarta a maimakon littafin ta soma qoqarin kunna data,saidai yanayin rashin network mai kyau ya hana wayar tata amfani,dole ta maidata itama jakar.


         "Ma sha Allah,kai ma sha Allah,lallai na jima rabona da adamawa,wai" anni keta fadi,fuskarta na nuna alamun jin dadin tafiyar sosai.


          A dan rude maimunatu ta maida hankalinta ga marabar hanyar da shanunta ke tsallakawa saboda jin wani sauti,hango motocin suna tahowa yayi matuqar daga mata hankali,na farko yadda zata tsaida dabbobin da sukayi nisa da tsallakawa ta bawa motocin dama su wuce,na biyu kuma motocin sunyi matuqar sanya mata fargaba da tsoro kamar yadda suka sanyawa mutanen da suka baro a baya,su waye a ciki?,me sukazo yi cikin rugar tasu?,wadanne irin motocine wadan nan da sam bata taba ganin koda me shigen kamarsu ba?.


         Yadda suke sake kusanto inda suke ya sanyata yunqurawa da hanzarinta ta fara bawa dabbobin nata umarni da dukka salon da tasan suna iya karbar umarni da hani daga gareta,tanayi tana kutsawa ta cikinsu tare da dan daga muryarta.


           "Kai salmanu......dakata" anni ta fada da sauri,idanuwanta suna sauka akan maimunatu,sosai ta zuba mata idanu cike da mamakin yadda take iya bawa dabbobin umarni da baki take kuma iya sarrafasu ba tare da takai duka ma ko daya daga cikinsu ba,idanun anni ya sauka ga dan qaramin dabbar dake hannunta,fari qal dashi sabuwar haihuwa,abinda yaja hankalinta kenan zuwa ga garken dabbobin,ta dinga binsu da kallo daya bayan daya


"Ma sha Allah,wadan nan dabbobin gaskiya na qwarai ne,sun samu kiwo da kulawar data kamata"


"Abinda nake fada a raina kenam hajiya yanxu hajiya,babban abun mamakin yadda qaramar yarinya kamar wannan take iya kula dasu gaba dayansu" cewar hayatu shima idanunsa akan maimunatu


"Bari hayatu,kaga inda ake mata,ba irin 'ya'yanmu ba cima zaune da komai suna zaune ake musu" anni tayi maganar tana tabe baki.


          Dariya ce taso qwacewa matashiyar amma ta danneta,sai murmushi da ya fita a fuskarta,yayin da hayatu da kuma salmanu suka dan dara kadan,saboda sunsan da wadda take,a tsakaninsu suka dinga tattaunawa,har zuwa sanda maimunatu ta ratsa ta gaban motocin suka wuce da dukka dabbobin,tana dan duba da kuma waiwayen motar tana mamakin yadda suka dakata mata suka bata dama ta wuce.


             Ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bayan data tabbatar sun tsallake lafiya,abinda ya taba faruwa da ita shekarun baya bai sake maimaita kansa ba,wanda ita daya tasan bala'i da masifar daga fuskanta a sannan,har yanzu tana iya tuna sanda motar ta taho a guje,bata kuma damu data tsaya ba ganin dabbobi suna qetarawa,tana hango sanda motar ta banke dan dalonta da take matuqar ji dashi,ya zube a qasa jini na fita ta hanci da bakinsa,ta bishi da gudu ta tsugunna a gabansa tana kuma saboda ta tabbatar bazai tashi ba,taji mugun cin birkin da motar tayi,da fadan da wata murya ke mata tsaye a saman kanta,fadan da yafi kama da a dakeka a hanaka kuka saboda cikin xafi da fadar maganganu marasa dadi ake yinsa,abinda ya sanyata daga kanta ta dubi.mai maganar.


          Kalmomin da zata gaya masa masu zafi take nema amma ta rasa,saboda ita din ba gwanar rashin kunya bace,bata ma iyata ba sam,to dawa zatayi bayan dabbobin sune qawayenta?,abu na qarshe da take ganin xata iya shine watsa masa harara gami da tsaki mai nauyi,kafin ta sauke kuwa aka sauke mata wani zazzafan mari da ya sanya wuta ta dauke mata gaba daya,ta daina gane komai,bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wani lokaci.


            Ko a yanzun data tuna sai data runtse idaunta,tana tuna zafin marin saman fuskarta,abinda ya biyo baya kuwa ta gefan inna azaba ce ta cita mai yawa,bata damu da yadda fuskarta ta tasa ba saboda marin data samu akan abinda ita ke da gaskiya,ta tattara laifin gaba daya a kanta,tare d adora alhakin mutuwar dan maraqin saniyar a wuyanta.


         Ajiyar zuciya ta sauke sanda suka iso gida,kamar kowanne lokaci ta daga murya ta sanarwa innar ta dawo,bata ajjiye dan jaririn a hannunta ba sai data qaraso ta miqa mata shi,bakinta har kunne,kai kace jika aka haifa mata na dan mutum


"Dama kinsan ta kusa sauka amma baki garzayo kin kirani ba?" Innar ta fadi haka cikin tuhuma,bata amsa mata da komai ba,itadai tana duqe tana daure wasu akuyoyi,banda abu irin na dan adam,ta samu uwa da dan lafiya,bata damu da yi mata sannu na wahalar datayi da naggen ba har ta sauka lafiya,ta buge fa tuhumarta,wanda tayi imani cewa inda ta barta a can ta taho kiranta wani abu mummuna ya faru,lallai ba zata daga mata qafa ba.


        Tunda taji maimunatun tayi shuru tasan ba zata tanka mata ba,ita kanta ta santa da wannan halin,a wasu lokutan idan tayi mata irin hakan,yaxo akan gabar da take cikin fushi ko takejin haushinta,kamata take ta nada yadda ranta yayi mata suga.


*Daga yau free pages sun qare,paid pages zasu biyo baya in sha Allah,hanzarta biyan naki kudin koki bibiyemu ta shafukanmu dake arewabooks*


No comments

Powered by Blogger.