Gurbin Ido 42

 


42


"Ina yini" sassanyar muryarta da 'yammatanci suka fara cikata a maimakon quruciya ta daki kunnensa,sai ya zame wayar daga fuskarsa a hankali,karon farko da yaji muryarta a nutse kuma a wajen da babu kowa saisu,a kanta idanunsa suka sauka,kanta yana qasa bata ko

qwaqwqwaran motsi,sai yaga kamar a tsorace take dashi har yanzun


"Lafiya,ya jikin?" Ya amsata a taqaice

"Da sauqi" ta amsa masa tana jin yadda muryarsan ta saka mata ciwon kai,dama kuma tun dazun da ya shigo take jin yadda jijiyar kanta take harbawa,kallonta yayi tun daga madaidaitan farare sol don qafafunta da babu digon komai sai na baqin lalle saman faratanta,wanda hakan ya sake qawata qafar ya kuma fiddo haskenta sosai,wani irin haske me surkin jaa,kamar hasken labarawan Oman,ya sauke idanunsa ga tafukan hannayenta da take murxasu suna sake jaa suma kamar kwanciyar jini,sai ya janye idanun nasa ya kaisu ga file dinta dake gefanta ya dauka sanna ya bude yana dubawa.


        Duka bayanan likitane akan ciwon nata,harda alamun firgitar da tayi daya janyo mata shivering,ya maida file din ya rufe,dai dai sanda wayarsa ta dauki tsuwwa,a maimakon ya fara daga wayar sai ya dubeta da da sexy eyes dinsa nan wanda basu bude ba gaba daya,zaka dauka bacci yakeji ko wata muguwar gajiya yayi


"Me akayi miki babba da zaki tsorata har haka?" Yayi mata tambayar yana dan hade girarsa,tambayar tazo mata da tsauri,tunda batasan amsar da zata bashi ba,sai ta xabi tayi shuru,ta kuma sake yin qas da kanta,shurun da yasa ya sake maimaita tambayar tasa,ta sake masa shurun,abinda yasa ya dan fusata


"Dago kanki ki kalleni nan" ya fada da dan kaushi da kuma kaurarawa,sai ta daga kan nata da sauri ta zube idanunta cikin nasa ba tare data shirya hakan ba.


        Wani abu me nauyi da qarfi ne ya dakeshi sanda manyan idanunta dake da haske da wani qyalli suka hadu waje guda da nasa,qarfin abun da ya sanyashi lumshe idanunsa na second biyu sannan ya sake budesu,har yanxu tana kallon nasa kamar yadda ya buqata,idanun nata sun sake wani garai garai saboda ruwan hawaye daya cikasu taf yake kuma shirin ballewa,dan bude idanun nasa yayi yana qara musu girma kadan gami da tattare girarsa,cikin kuma sigar tambaya yace


"What?,meye haka?" Wannan karon ita ta gaza jurar kallon nasa,tana jin kamar zata narke a wajen,kamar ta diba qafafunta ta zura da gudu,abu daya ya rage mata ta bashi haquri ya barta ta sarara,baisan tu daxu yadda ya cika dakin ba,tana jinta kamar wadda akaje bakin jeji aka jefar aka juya aka barta ita daya


"Kayi haquri" ta fada a wani salo da idan bakasan halinta ba zaja iya cewa shagwaba ce da zazzaqar muryarta wadda ta fara shaking saboda kuka dakeson qwace mata


"Idan kuma naqi haqura fa?" Ya tambayeta yana dage girarsa guda daya,bai kai qarshe ba ta sake cewa


"Don Allah" da wata irin murya irin ta yaran dake kukan da babu dalili,sai da ya riqe numfashinsa na wasu sakanni sanda tayi maganar


"Ya Allahu,wacce irin shagwababbiyar yarinya ce wannan?" Ya fada a ransa,gaba daya daga tambaya guda daya shine zata sanyashi a gaba tana masa irin wannan kukan?,me yayi mata?,salon anni ta dawo ta saka shi a uku?,a haka ma ba tsira yayi a wajenta ba,yana ankare da irin kallon tuhuma da bin qwaqwaqwafin da take masa,ya tabbatar idan ta gane wani abu tofa ba dashi zatayi ba,da abbi ko amma zatayi,tasan kuma hakanne zai matuqar daga masa hankali ya kuma bata masa rai.


"Enough.....me akayi miki?,salon a shigo ace na miki wani abu?,stop it" ya fada yana miqewa tsaye,ya matso gaba kadan yana zube hannayensa a aljihunsa,idanunsa kuma a kanta


"Ya isa nace" ya kuma maimaitawa,ganin yadda shagwababbiyar muryarta ke fidda sheshsheqar kuka.


          Handkerchief ya zaro ya ajjiye mata agefanta bayan ya duba dakin da idanunsa baiga tissue ba


"Wipe your tears" ya fada mata muryarsa can qasa,ya kuma kauda kansa gefe yana hadiye wani abu,wato ita kuma haka take kenan,babu damar fada ko tsawatarwa kai ko tambaya ma sai ta narke ma mutum?,tako ina anni ta janyo masa jagwal,ta hadashi da waccan data gama zagaye duniya yawon neman karatu,yanzu kuma ga qaramar yarinyar da inda auren qauye yayi tabbas ya haifa kamarta.


        Wayarsa ta sake kuka,yaja dan qaramin tsakin da ya sake sanya gaban maimunatu faduwa,ya ciro wayar yana duba me kiran,sai ya koma da baya ya kuma nufi window yana amsa kiran.


          Shuru dakin ya dauka,sai sautin muryarsa mai cike da kwarjini dake ratso dakin a hankali,wata irin murya Allah ya bashi me dadin sauraro,ba zaka ce muryar d'a namiji bace,sake goge ragowar lemar hawayennata tayi,tana jin yadda fuskarta ta cika da tattausan qamshin turarensa


"Mugu kawai,kamar mutumin kirki" ta fadi a zuciyarta,hoton sanda yake zuqar sigari ya gifta a idanunta haushinsa na cika mata zuciya


"Ya boye yanata halin banzansa 'yan gidansu basu sani ba,Allah sarki abbi anni da amma" ta fada a ranta tana jin tausayinsu sosai a ranta,ita a nata ganin qarshen qurewar shaye shaye kenan,abinda yasa ta tsani buderi kenan tun farko,ashe zata tadda wannan.


         Sallamar anni ta sanyata daga kai da sauri tana jin dadin shigowarta a ranta,don dama neman wanda zaya shigo ya qwacetan takeyi,suna hada ido annin ta sauya fuska tana qure maimunatu da kallo


"Me ya sameki kuma?" Ta jefawa maimunatu tambayar da bata shirya jinta ba,sai tayi shuru ta kasa ce mata komai,saboda batason tayi magana muryarta tayi rawa ta zargi wani abun


"Me kayi mata?" Ta maida akalar tambayar ga ja'afar daya kammala wayarsa yake kuma juyowa,dan tsuke fuska kadan yayi


"Ask her,gata nan ai,ki tambayeta"


"Ke me yayi miki?,da ganin idanuwanki kuka kikayi" kai ta girgiza


"Babu komai anni"


"Ko zaluntarki dama yake cikin gidan?" Kanta ta sake girgizawa alamun a'ah


"Zaginki yayi?" Ta fadi duk da tasan ba dabi'arsa bace,amma ba'a shaidar dan yau,nan ma girgiza kai maimunatu tayi


"Kodai ciki gareki ya nuna bayaso?" Dashi da itan gaba daya Duban anni sukayi,saboda maganar tazo musu a bazata,dauke kansa yayi yana ci gaba da matsa wayarsa,wani sashe na zuciyarsa nason jin zafin maganar,don shi bai taba musu yarinya bama bare tayi ciki,amma kuma sai wani bangare na zuciyarsa ke hango masa qani ko qanwa ga amna,madadin amra data rasa,tunanin ya goge daga kwanyarsa sanda yake deleting saqon daya tura a wayar tashi,don baya barin saqonni.


          Shuru anni yayi sannan ta maida dubanta garesa,wanda zaka tsammaci ma baya dakin kwata kwata tunda take maganganunta


"Idan ma jan kunne kayi mata kan kada ta fada ai Allah yana nan,duk abinda mutum yake Allah yana kallonsa ko?" Ji yayi maganar ta masa nauyi sosai,ko menene za'ayi bayason mutum ya hadashi da ubangijinsa,idanu ya zubewa anni yana kallonta ba tare da yace komai ba,koda baiyi maganar ba ta karanci abinda ke ransa,maganar ce kwata kwata baya son a yita,tayi shurun amma kuma taci gaba da qananun mitocinta har zuwa sanda yace ta wuce ya maidasu gida,da farko don tana jin haushinsa cewa tayi


"Kai,kayi ta kanka kaji,ai bakai ka kawoni ba ko?,kaje kaji da kamun da Allah zai maka da diyar mutane" maganar tata ma dariya ta bashi,amma a fuska ba zakaga hakan ba,yaso maida mata amsa,to amma yasan dogon magana zai jawo,qila ma indai anni ce ta barshi da ciwon kai,sai kawai ya barta a haka,tayi mitarta ta qoshi,ya ajjiyeta a gida ya wuce nasa gidan,bayan sun bar baba tabawa a asibitin zasu kwana tare.


        Washegari asibitin yadan cika saboda 'yan dubiya da suka dinga xuwa,har abun ya bawa maimunatu mamaki,ganin ciwon bai wani shahara ba,don ma dai likitan yaqi sallamarta ne,yace mai gidanta yace masa a barta saita warke gaba daya,tayi mamakin jin hakan,ja'afar din?,abun kuma yadan farantawa anni,tunda ko ba komai a nata ganin caring ne,a ranar harda abbi a zuwa dubiya da amma da kanta,aka kuma taho mata da amnanta,nan kuwa da dafe taqi binsu su koma,tace duk wanda yazo daga gida last zata biyoshi su dawo tare,hakanan suka tafi suka barta,amna kuwa ta bararraje abunta a gadon asibiti kusa da maimunatun,suna ta shan hirarsu,baba tabawa na daga qasa saman carpet tana tayasu,wani abun taci dariya.


        A ranar bai tashi da wuri ba kasancewar Weekend ne,duk da shi ba wani hutun weekend yake ba,ya maida kansa busy sosai fiye da kima,amma a yau din yaji yana buqatar yayi bacci ya kuma huta sosai,don a daren jiya baya dawowarsa unaisa ta bashi ciwon kai sosai,ta sanyashi a gaba tana gaya masa yadda take sonshi da kuma buqatar tasa soyayyar,ya fuskanci kamar a matse take,abinda a nasa ganin bai kamaci a samun hakan daga wajen budurwa ba,baya mantawa shaheedansa dai da ya kusa sati kafin ya samu kanta,shima a haka lallabawa aka dinga yi kafin ta saba,ta jima kafin ya samu ta tashi bayan ya bata zabi guda biyu,ko ya sallameta salin alin,ko taci gaba da haqurin zama dashi har zuwa sanda zuciyarsa zata aminta da zama da ita,surutan da yayi wunin yau duk da ba wai yawa garesu ba suka sa yaji kansa yana ciwo,wannan yasa ya kashe wayoyinsa gaba daya,ya kuma sanyawa qofarsa key don kada ma ta dawo ta dameshi.


       Bai farka ba kuwa sai dab da azahar,har sannan bai buda wayoyinsa ba,har sai da yayi wanka ya shirya cikin wani yadi da aka masa ordernsa daga qasashen yarbawa,aka kuma yarfa masa dinkin boda irin nasu,fresh chocolate color skin dinsa tayi luf ta kuma dace da yadin.


           Sai sannan ya buda wayoyin yana duba lokaci,zai isa ya samu sallar azahar a gaba cikin jam'i,yana shirin sake kashewa kiran hisham ya shigo masa


"Barka da rana yaaya"

"Yauwa,kana lafiya?"

"Lafiya lau,akwai kayan da aka maka order ne ka saka phone number dita?" Shuru ya danyi


"I don't think so,but ka kira mr farid,na bashi wani aiki last month,ban san ko shi ya saka number dinka ba"


"Okay yaaya"


"Kaman kana hanya ko?"


"Eh,ina ta wajen unguwarku,naje na duba patient din da na yiwa surgery jiya,sai na biyo wani suya spot"


"Bakaji ko?,kai ne can gobe kaine nan,ka samu standard waje daya ka tsayar dashi duk sanda kwadayinka ya tashi,kaman ba likita ba?" Dan shafa kansa hisham yayi,ja'afar din badai aqida ba,shi kam duk inda yaji taste dinsu ya masa ko yaga abinda yakeso indai ya gamsu da tsaftar wajen zaije yaci


"Am sorry" yace masa a taqaice,don yasan bazai tsaya sauraron dogon jawabinsa ba


"Sorry for your self,ka biyo ta gida ka daukeni"


"Okay" ya amsa shi yana murmushi sannan ya aje wayar,yayan masa is very different and unique,komai nashi ya bambanta dana kowa,shi yake sarawa jabir da suke zaune lumi baka jin kansu.


No comments

Powered by Blogger.