Gurbin Ido 4


 Free page 04



           Sallamarsa ta yanke mata dan qaramin bacci mai dadi data fara yi,ta daga kanta tana amsa masa,da murmushi ya bita,hannunsa dauke da baqar leda qananu guda biyu,inda ya tashi dazun ya koma ya zauna,sannan ya bude ledan yana cewa


"Ga magani kisha" idanunta ta lumshe gami da budesu lokaci guda cike da.mamaki,yau ita ake cewa ga magani?,anya kuwa ita dince......maimunatu?,bata sauka daga wannan mamakin ba ta sake jin muryarsa yana sake miko mata wata ledar


"Amma ki fara cin wani abun tukunna,na sani idan baku da lafiya bason cin abinci kuke ba,haka innata ke fama dasu zubaida idan basu da lafiya" ya qarashe maganar yana miqewa


"Bari na baki waje,amma idan bakisha maganin ba zan dawo" saiya juya yayi nesa da ita,yayin da ta rakashi da kallo har sai data daina hangoshi,sannan ta janye manyan idanunta ta mayar kan ledojin,ta sanya hannu ta jawosu tana budewa.


         Ledar farko magunguna ne,qwayoyi tablet sosai,sai leda fa biyu dake dauke da gurasa mai kyau,wani yawu ta hadiya,duk da yanayi na lalurar rashin lafiya da take amma sai da tsohuwar yunwa ta taso mata,batayi qasa a gwiwa ba ta dauka ta fara ci,tana ci tana lumshe idanunta tsananin azabar yunwar data tarawa cikinta,dama don bata da lafiya ne,amma duk sanda inna  ta gwada mata irin wannan rashin imanin......a nan gurin kiwo take samun daya daga cikin naggen ta tatsi nono mai dumi tasha,duk da ta sani,yawanci da safe shine lokacin tatsar,amma dole tasa wasu lokutan take hakan,idan kuma ta samu ta faki idon innar sanda take tatsar da sassafen ta ɗaɗɗaki wani,shine zata wuni nata damu ba,yunwa kuma bata addabeta ba kamar yanzun,har shan nonon ya zame mata jiki,ya koma kamar shine abincin nata,abinda yasa ko kadan bata da wani jiki kwata kwata,duk sirantaka irin ta bafullace tata ramar ta fita daban.


           Bawai don ta qoshi ba ta janye hannunta,a'a,tayi hakanne saboda kunya kara da alkunya,kada yazo ya taras ta tashi da ita,ta bude ledar maganin wanda ya sanya ledar ruwan pure water guda daya,ta daga pure water din ta jujjuya shi a hannunta,ba zata iya tuna sanda tasha ruwan leda ba a rayuwarta,saita koma kan magungunan,ta balli kowanne kamar yadda taga anja sandunan layi ajiki ta kora da ruwan.


         Idanunta ta mayar tana sake lumshesu,tana jin yadda numfashinta yadan fara daidaita albarkacin gurasar data ci tun kafin magani ya soma mata aiki,a hankali take zuqan iskan wajen tana kuma sauraren koke koken dabbobi dake kai kaw a wajen,jikinta yana mutuwa murus kamar wadda aka yiwa dukan tsiya.


       Tun daga nesa ya kafeta da ido,idanunta dake lumshe sai suka sake qarawa fuskarta kyau,yana ganin baqonnin yanayi tattare da ita,yana son sanin wace ita sani na haqiqa,da kuma dalilin da yasa take kebance kanta take nesa da jama'a haka.


          Sallamarsa ta sanyata bude idanunta


"A henyi?(Kin gama?)" Kai ta gyada masa tana kallon qasa,kunya tana cikata,tanajin yadda tayi abun kunya,na yadda zata zauna taci abinda ya futo daga hannun saurayi


"hokkoyon dunni sauro(miko min sandar can)" ya fada yana nuna sandarta dae gefe,sai data kalli sandar sannan ta maida dubanta kanshi,ya fahimci me take nufi,don haka murmushi kawai ya sakar mata,ya taka da kansa zuwa gefanta ya dauki sandar,ga bishi da kallo mamaki fal zuciyarta

"waye shi?" Tambayar da taketa nanatawa kanta kenan.


         Daga nan inda take tana iya hangen yadda yake tattare mata kan dabbobin nata cike da hikima da kuma qwarewa wadda ta lunka tata,da alamu shima din gwanine wajen iya kiwo,bai dauki wasu lokuta masu dama ba ya dawo gareta,yana sabe da sandar kan kafadarsa


"indillo(Muje ko?)" Yace da ita,dubansa tayi sanna ta janye idanunta gefe daya,sam maganar batayi mata ba,ta yaya zata jera dashi har cikin gari?,akwai idanun mutane masu yawa a kanta,sannan tana da kunyar da ba zata iya aikata hakan ba


"ummadillen(Tashi mu tafi),ko ba zaki iya tashi ba?"ya sake maimaitawa a tausashe,a hankali ta girgiza masa kai


"Kaje kawai,na gode,zan qarasa kaisu gida da kaina,na gode qwarai" idanu yadan zuba mata kadan,sai ya sauke ajiyar zuciya yana sauke sandar daga kafadarsa,ya fahimci me take nufi,tabbas ga cika bafulatanar gaske.


"Shikenan,zan kora miki su,tumudilli tokkirawaya gaɗa taajan banna wala kyettaiɗo ingwandi(idan na tafi ki biyo bayana,karki damu,ba wanda zai gane tare muke)" duk da hakan yayi mata,amma kuma batason dora masa wani nauyin kuma ko dawainiyarta,saidai kafin ta sake cewa komai yayi gaba,dole ta miqe,ta dauki malfajenta ta mayar saman kanta,ta dauki jakarta ta daura tabi bayansa.


         Bata sani ba ko shima ya kula,sharewa kawai yayi,ko kuma bai kula din ba.....da gaske ita daya ta lura,yadda mutane keta binsa da kallo a sanda aka ganshi yana kora shanun da ita ke da hakkin kula dasu,yayin da ita kums ke biye dasu a baya,kasan samun nutsuwa tayi kwata kwata,jinta take a daure,har sai da suka isa gida,ya miqa mata sandanta idanuwansa akanta,fuskarsa dauke da murmushi


"Sai jaaango?" Ya fada yana sake nazartar kyakkyawan fuskarta


"Miyatti" ta amsa masa a gajarce,sai ya jinjina kansa


"Alla ɗaudane jamu(Allah ya qara lafiya)kisha magungunanki da kyau"


"to Allah jaɓe" ta fada tana jin nauyin mixanin kyautatawarsa a gareta. 


            Ko sanda himu yake nufar gida tunaninta ne fal cikin ransa,kamar yadda murmushi yaqi barin fuska da bakinsa su huta,sosai yake ji cewa yayi gamo da Matar aure,ta kuma zo dai dai lokacin da ya kamata ace tazo din,bayajin zaiyi nauyin baki ko jinkirin shaidawa innarsa,duk da cewa babansu baya nan,amma dai yana da kyau innar ta sani,ta kuma shaidawa baban da zarar ya dawo.


            Da sallama ya shiga faffadan tsakar gidan nasu,kishiyar mahaifiyarsu wadda asalin sunanta shine rahama....amma sauran dangi da 'yan rigarsu na kiranta da ramatu,su kuma yaran gidan suna kiranta da yuuma,tana duqe gaban murhu,ta kammala kwashe tuwon dare tana wanke muciyar cikin tukunyar tuwon himu ya shigo.


           Fuskarta dauke da fara'a take amsa sallamar tasa,macace mai matuqar kirki haquri hagen nesa da kuma sanin ya kamata,duk da kasancewarta wadda Allah bai azurtata da haihuwar yaro ko daya ba,amma sam bata kasance mai baqin hali gabyaran mikin nata ba,mutum ce mai sauqin kai,wadda take kallonsu ibrahim tamkar ita ta haifesu,tana kulawa da kowanne daya daga cikinsu,duk da zamantowar safara'u mahaifiyar ibrahim mace mara haquri da biyema zuciyarta a wadansu lokuta,amma yuuma ta danne,suna zaman lafiyar daya sanya jama'a da dama cikin karkarar ke sha'awar zaman nasu,ba tare da sunsan cewa fiye da kashi tamanin cikin dari na zaman nasu haqurin yuuma ne ya qawatashi.


          Barka da gida yayi mata ta amsa tana masa sannu da zuwa


"Inna walaɗon(inna bata nan ne?)"


"o'o immoder,one ɓayi e'ummakiɗo(A'ah tana ciki,don bata jima da tashi daga nan ba),kila barci ne ya saceta,don tacemin bata danjin dadin jikinta sosai" kai ya gyada sannan ya sake tambaya


"Yaran nan fa?,su safiya?"


"inna'onliliɓe,amma ɓeɓadake wartuki(Innar ce ta aikesu,amma suna gab da dawowa)" har ya taka zaiyi gaba sai ya sake tambayarta


"Yaushe baaba yace zai dawo ne?" Murmushi ta sake


"Yau kuma 'yan tambayar ne a kusa himu?,rana wata yau in sha Allah" kai ya gyada yana murmushi,yaji dadin jin cewa bazai jima ba zai dawo gidan,ya tafi ikko ne da wasu shanunsa zai saidasu,wanda dama.yawanci can yake kaisu,shi kansa ibarahim din yafi zama a can,mafi yawan rayuwarsa ta can ce wajen wani dan uwan baaban nasa,yanzu ma gajiya yayi da zaman can din ya dawo gida yadan huta sannan ya koma,uwa uba kuma sun samu hutun semester,don acan din bai zauna ba yana karatunsa.


         Ya daga labulen dakin ya samu barcinne kuwa ya dauketa,sai ya sauke ya wuce dakinsa,yayi abinda zaiyi a ciki sannan ya fito ya fara daura alwalar magriba,bai kammala ba innar ta fito tana daura dankwalinta


"denattoi ɗa himu(yaushe ka shigo himu?)" Ta fada tana dubansa,ita din duk da bafullatsna ce amma sam ba ruwanta da  wannan kunyar da kaara tadan fari


"Ban jima ba,na leqo na samu kina bacci,ya jikin naki?"


"Alhamdlh,nasha ragowar maganin nan daka taba kawomin kwanaki kafin na kwanta,kaga kuwa har ya fara sakina"


"To alhmdlh,hammiyami jula miwarta(bari nayi sallah na dawo)" ya fada yana warware hannun rigarsa,a bakin kofar shigowa gidan sukayi kacibus da qannensa,yammata masu tasowa su biyu,yace maza su shige gida an fara kiran sallah,suka amsa masa amma suna binsa da.kallo,saboda labarin da suka samu a kansa tun a hanyarsu ta isowa gida.


       Bayan sallar isha'i ya shigo gidan,babu kowa tsakar gidan sai yuuma dake zaune daga bakin kofar dakinta ita daya,gabanta fitilar aci balbal ce,sai qaramar redio da bata rabo da ita saboda jin labarai,sannu da gida yayi mata,ta amsa masa tare da shaida masa abincinsa na wajen innarsa,ya amsa mata yana wucewa kai tsaye zuwa dakin innar,bayajin dadin yadda wasu lokuta safiya da zubaida ke barin yuuma ita kadai,duk da lokaci lokaci zaka samesu wajenta,yana matuqar jin tausayinta,saboda rashin haihuwa abune mai ciwo da kuma sanya mutum cikin kewa da kadaici.


          Da sallama ya shiga dakin,ya taras dasu sunata hira abinsu dukkansu,safiya zubida da sadam qaramin qaninsu,sannu da xuwa sukayi masa,ya samu waje yana zama


"Ra nyam kima,hokkumoki sadam(ga abincinka,sadam mika masa)" inna ta fada,sai sadam din ya mika masa,yaja kwanon ya bude ya fara ci bayan yayi bismillah,ba qaramin son tuwon yuuma yake ba,bama shi kadai ba,hatta da jama'ar gidan,saboda yadda ta iya girki,duk da innar tasa ma ba baya bace.


       A hankali yake cin abincin yana kuma jefa baki a hirar tasu,saidai fiye da rabin hankalinsa nakan ta yadda zai gayawa inna maganar dake bakinsa,a qa'ida da yuuma zaiyi zancan,amma ya sani idan yayi hakan ransa ne xai baci wajen innar,saboda batason hakan,tafiso kowace magana suke da ita su sameta kai tsaye su shaida mata,itama yuuman tunda ta fuskanci haka,da sunzo sun gaya mata zata ce 


"Kun gayawa innarku?" Idan sukace a'ah,takan ce


"Ku sameta ku fara shaida mata muji abinda xata ce".


          Sai da ya gama cin tuwon tas ya wanke hannu sanna ya gyara xamansa cikin jin nauyi da kunya yace


"iwodi haala kaginmi gaɗen Inna....(akwai maganar da nakeso muyi inna)"


"Shine tun daxu kaketa wani mutsu mutsu ka kasa gayamin?,tawi'aayanka,mojetta bi'owaka(idan baka gayamin ba wa zaka gayawa duk duniya?)" Ta qarashe da sigar tambaya tana kafeshi da idanu,yasan me take nufi,sai kawai yayi murmushi yana cewa


"Babu"


"iminamma(ina saurarenka)" dan jim yayi kadan sannan yace


"Inna.....na samu yarinyar da nakeso fa".


       Zuba masa idanu tayi saboda yadda maganar tazo mata a bazata,bata tsammaci jin maganar ba a wannan lokacin,saboda tuntuni tana da tsari da kuma muradi a kansa,amma duk da haka saita danne wannan a ranta,tace dashi


"Emi namma,immoi 'onni?(ina jinka,wacece?)" Kansa yadan shafa kadan sannan yace


"Sunanta maimunatu"


"Maimunatu ta gidansu laulo" muryar zubaida ta ratsa hirar tasu,da hanzari inna ta juya tana duban zubaida saboda yadda maganar zubaidan ta dauki hankalinta,yayin da himu shima ya juya yana kallon zubaidan saboda baisan waye laulo din ba,saidai idan ita dince yaji dadin yin maganar da zubaidan tayi,saboda baisan ta yadda zai kwatantawa innar ita ba yadda zata fahimta


"Da gaske ita kake nufi himu?"


"Gidansu na kusa da hanyar fegin maraba" mummunar faduwa gaban inna yayi,tabbas maimainunatun ya hango,take hankalinta yayi mummunan tashi,maimunatu 'yar uwa ga gaje?,gaje dai 'yar inna furaira


"Yuuma.....yuuma.....warnano wakka haala kawela(zo kiji wani mummunan labari)" ta fara qwalawa yuuma dake xaune qofar dakinta kiran,abinda ya sanya himu zubawa innar idanu cike da mamakin meye ya gigita innar tasa haka?,har take irin wannan kiran?.


"Ku tashi ku fita" innar ta fada tana waiwayawa gasu safiya dake zaune tun dazu suna kallon kallon a tsakaninsu,tsam suka miqe suna masu ficewa kowacce bakinga fal da magana,dai dai sanda yuuma ta shigo dakin a rude


"Lafiya kuwa?" Ta tambayi inna tana laluben wajen zama hankalinta a tashe,sai da inna taja wani dogon numfashi mai nauyi ta furzar da iska sannan tace


"Yaron nan ne yakeson dauko mana jaraba rana tsaka" sake tashi hankalin yuuma yayi tana duba inna tace


"Subhanallahi,jaraba wacce iri?" Kai inna ta gyada cike da jin xafi tace


"Wai yarinyar nan maimunatu ya gani yakeso?"


"Maimunatu?....maimunatu?" Yuuma ta maimaita sunan tana son tuna aka wace ake magana


"Diyam ta gidansu laulo" take yuuma ta fahimta,sunan kuma ya fado mata a rai,saboda ita daya keda sunan kaf rugar,hakanan kuma mahaifiyarta kadai ke kiranta da sunan,sai ta sauke ajiyar zuciya,alamun tashin hakalin da ya taso tun daga zuciya zuwa fuskarta ya fara zagwanyewa


"Hankalina ya tashi sosai innar sadam,na dauka wani abun tashin hankalinne"


"Yo akwai tashin hankalin da yafi wannan yuuma?""ai abinda yasa nace haka innar laulo.....kaf fadin rugarnan anyi ittifaqi babu yarinyar dake da nutsuwa da kuma kamun kai da tarbiyya irin maimunatu....."


"Amma kinfi kowa sanin ainihin wacece ita ko?"


"Wannan duk camfi ne ko ince hasashe....duk cikin masu hasashen babu wanda yake da tabbas kan abinda yake fada koda kuwa a gaban Allah ne,dukka abinda al'umar rugar nan keyi ba komai bane illa jahilci zalla da kima gurguwar fahimta gami da mummunan zato,koda ba zato bane hakanne,babu wanda ya taba kama maimunatu da wani mummunan aibu da za'a qita,a karan kanta maimunatu bata da wata matsala ko illa....." Idanu inna ta zubawa yuuma,a hankali a kuma sanyaye tace


"Yuuma...kodai don bake kika haifi himu ba kike qoqarin wanke maimunatu gami da kore kowanne aibu daga gareta?" Ba yuuma kawai ba,hatta da ibrahim sai da maganar ta tabashi,qas yayi da kanshi yana jin babu dadi a ransa,yayin da yuuma ta rintse idanu,maganar tana sauka saman zuciyarta da wani irin dafi mai zafi,dai dai maganar take da saukar mashi saman zuciyar tata,duk yadda take zaman kawaici da innar laulon....bata taba gwaba mata magana me zafi akan yaranta ba irin wannan


"Kaico!....kaico!" Yuuma ta fada tana girgiza kanta


"Inama ace Allah ya bani d'a na cikina wanda yakai shekarun ibrahim....kai koda ace bai qarasashi ba,matuqar ya isa a daura aurensa,da ba shakka na tabbatar miki da cewa magana nake Miki da zuciya daya.....Allah ya kyauta,kiyi haquri bisa shishshigin da nayi miki" yuuma ta fada bayan ta yunqura ta miqe,zuciyarta na wani irin tafasa,wanda tana fita qofar dakin hawaye ya silalo mata.


        Shuru ne ya ratsa dakin na wucin gadi,cikin ranta innar laulo tana jin kamar bata kyauta ba,wata zuciyar kuma na gaya mata daidai ne abinda tayin,zallar mugunta ce kawai tasa yuuman bada wannan shawarar a gaban himun,bayan tasan kowa gudu da qyamar yarinyar yakeyi,ko ita bata sake ganinta tana hulda da yarinyar ba



"Amma inna abinda kika yiwa....."

"Kaga dakatamin" inna ta tsaida ibrahim dake Shirin nuna mata rashin dacewar abinda tayin


"Kada kace min komai,maganar maimunatu kada na sake jinta a bakinka,domin kuwa ba kai ba,koda wanda na isa na gaya masa yaji ne bazan bari ya aureta ba,bare kai dan cikina,bama maimunatu ba,banason ka sake kawomin maganar kowacce yarinya,na riga na zabar maka matar aure tun shekarun baya.....kaje gidansu maimunatun ka nemi gaje ku dai daita".


        Tsaf kwanyarsa fa birkice,ta yaya zaizo da maganar maimunatu inna ta umarceshi da auren gaje?,gaje dai da ya sani?,ya akayi suka zama 'yan gida daya ita da maimunatun?,babu kama ta siffa ko dabi'a ko qanqani a tsakaninsu,wanne aibu ne ma wai da innar ke magana a kai da har zai zama hujjar raba sabuwar tarayyar da yanzu aka fara kiwonta tsakaninsa da maimunatu?.


No comments

Powered by Blogger.