Gurbin Ido 35

 


Ficewarsu sai falon ya zamana daga shi sai annin,yaja kwanukan yayi serving kansa da kansa,ya dauki plate din ya dora saman qafafunsa ya fara ci.


          Duka anni na karantarsa ba tare da tace komai ba,yadda yake cin abincin nasa ya sake tuna mata da ja'afar din,har yanxu qasaitarsa da jan girman nan nasa yana nan,rashin daukan wasa qarancin magana da rashin walwala,saidai kuma baya wasa da cikinsa,har yanzunma haka abun yake,yadda taga yana cin abincin ya tabbatar mata babu komai a cikinsa


"Ni na rasa wanne irin wayo da dabara ne wannan,ka baro abincin mata har biyu a gidanka kazo kana cinyewa bayin Allah abinci?" Idanunsa ya sauke ka fuskar anni,da gangan take musu gorin abinci,duk sanda kaji tana gorin abinci to 'yan rigimar nata ne a kusa,batasan cewa shima yau da tasa rigimar yaxo ba,don haka baice mata ta tafas ba,sai daya gama yana goge hannunsa da tissue,duk da ba da hannun yaci ba,ya janyo takardun da yasa a shigo masa dasu ya ajjiye a gabanta.


         Kallon takardun tayi sannan ta maida dubanta gareshi tana bata fuska


"Meye wannan din?,kasan dai ba wani bokonku nayi ba da zaka turon takardu gaba ko kana wani cushe fuska kamar tsohon kashi" can qasan ransa ya murmusa,amma ko days ba alamun murmushin a saman fuskarsa,yasan zata fadi sama da haka ma idan tana jin rigimarta


"Takardun makaranta ne da kika nema a samar mata" fuska ta yatsine


"A samarma wa?" Ta fada tana jifansa da kallo


"Kin manta maganar da mukayi kenan?"


"Na manta,saika tunamin" hannu ya miqa ziwa gabanta zai janye takardun nasa yana fadin


"Duk randa kk tuna zan dawo saimu qarasa tattaunawar"


"Kaniyarka.....kaniyarka nace" ta fada bayan ta danqe hannunsa


"Ka kirata da maimunatun kake ganin asara?,manya....manya ka kiyayeni" sakar mata takardun yayi,ya koma baya yayi relaxing yana dubanta cikin calmness din nan nasa,har ta gama fadanta,sannan don kanta tace


"Ina jinka,wacce makaranta ce?"


"Pen resources academy" ya amsa mata a taqaice,shuru ta danyi don makaratar ta kwanta mata,kafin ta sake cewa wani abu hisham yayi sallama falon,saita diba takardun ta miqa masa tana cewa


"Dubamin da Allah,wacce makaranta ce wannan?,tana da kyau ko kuwa lullubin biri ce?" Qunshe dariyarsa yayi,da alama yayan nasa ya yiwa anni halin nasa,sabgarsu shida annin babu me shiga,idan ka shiga kunya zakaji wajen anni,saidai kuma idan suka tashi al'amarinsu saisu.


        Duba biyu ya yiwa takardun ya gama fahimtar komai,me yasa yayan nasa zai dauki maimunatun ya kaita boarding school,duk da cewa ba nisa bane a tsakaninsu,amma koma meye ita din a yanxu ai matar aure ce,eh makarantar nada kyau da kuma tsari me kyau,saboda private ce da ake biyan maqudan kudaden da sai dan wane da wan ke yinta,to amma ya manta igiyar aurensa dake kanta?.


"Ya ka tsaya?,tana da kyau?"


"Sosai ma anni,makaranta kwana ce,tana gombe bauchi road" da fari a zafafe ta daga kai ta dubi ja'afar din da niyyar qare masa tatas,saidai kuma yadda ya kashingida hankali kwance kamar baisan abinda ke faruwa ba ya tabbatar mata da biyu ya aikata hakan,saita jinjina kai,ta kuma maida dukka wani fadanta data debo niyyar yi masa,zata bishi ta yadda ya biyo,amma kuma tabbas yaci bashi ne,zai kuma gane ta yaro kyau take bata qarko.



**********washegari*******


       Daya idar da sallar asuba bai koma ba,saboda tafiyan dake gabansa,zaibi flight ne da zai tashi qarfe goma na safe,waya ya amsa me dan tsaho da CEO na wani company da yakeson zuba hannun jarinsa a kamfaninsu,yaci a qalla awa daya cikin wayar,har sai daya fara murza goshinsa saboda maganar ta fara hawan masa ka,bai fiya jurewa doguwar magana ba,ya bashi excuse kan cewa idan ya gama abinda yake bayan ya shigo lagos din zai nemeshi,da haka sukayi sallama.


         Ajiye wayar yayi yana lanqwasa yatsun hannunsa da yaji sun sage masa,ya kalli agogo,qarfe takwas da ashirin,yana son shiga gym room amma lokaci bazai bashi dama ba,don haka ya miqe yana nufar falonsa don ya hada koda coffee yasha ne ya dumama cikinsa.


           Coffee powder din ya duba yaga ya qare,dole kenan sai ya sauka kitchen dinsu ko zai samu wani,sai ya zura slippers dinsa masu taushi,ya nufi qofa yana gyara maballin pyjamas din dake jikinsa.


           A hankali yake saukowa daga stairs din,falon shuru yake kamar kowanne lokaci,ya ratsa ta cikinsa ya wuce dining area ya wuce kitchen,hankalinsa da tunaninsa yana can ta wani waje daban.


            Dai dai lokacin da take kwashe gasashen dankalin data hada masa wata 'yar source data wadata da albasa da koren tattasai da nama da aka yiwa yankan cube shape,tana sanye da wata night gown mai taushi,me dogon hannu ce data sauka mata har qasa,ta sanya baby hijab dinta shima kalar rigar,abinda yasa baby face dinta sake fitowa sosai,quruciyar dake tattare da ita na sake fitowa.


        Kusan a tare suka daga kai suka kalli juna,saura kadan ta saki frying pan din dake hannunta,tayi hanzarin ajjiyeshi,sannan ta duqa har qasa ta fara gaidashi kamar yadda take masa.


         Ciki ciki ya amsa idanunsa na sauka kan dankalin,ya mishi wani kallon qyanqyami yana matsawa gaba ya fara duba kayan da suka kawoshi kitchen din,ci gaba tayi da tsugunnawa a wajen,turarensa na cike ilahirin kitchen din,kamar a yanzun ya fesa shi a jikinsa,ya gama daukan abinda zai dauka,ya nufi qofa.


        Har ya kusa fita ya tsaya,yadan tako baya kadan yana cewa


"Ki shirya anjima kadan hisham zaizo ya daukeki,zai kaikai makaranta zasuyi miki interview,next week zaki fara zuwa,ko ince za'a kaiki keda kayanki,after every Three month zaki dinga dawowa hutu kafin ki koma" ya mata maganar gwari gwari,saboda gani yake babu abinda ta sani,babu kuma abinda take ganewa,idan ma yace mata boarding school ba lallai ta fahimceshi ba.


           A ba zata albishir din yazo mata,don ko a mafarki bata taba kawo hakan ba,bata taba tsammanin haka ba,tunda a society din data tashi bata ga ana hakan ba,cikin ruhinta ta dinga jin wani farinciki da bashi da misali yana kutsawa,ashe dai tana da rabo,ashe dai burinta zai cika?,tana shirin buda baki tayi masa godiya ya fice abinsa,yana fitar ta miqe cikin farinciki,tayi wani dan tsalle,ta qanqame jikinta waje guda tana fadin


"Alhamdulillahi,miyatti Allah" cikin walwala karsashi da kuma kuzari taci gaba da aikin nata,Allah Allah take ta gama ta shirya,batason yaa hisham din yazonya jirayeta,tunda bai gaya mata qarfe nawa zaizo din ba.


          Sanda ta kammala girkin unaisa ta shigo,kamar ko yaushe cikin takun taqama isa da jin cewa NA FIKI FA,ta qarasa inda maimunatu ta adana warmers din,tasa hannu tana budewa,kafin ta zaqulo faranti cikin nata kayan kitchen din tasa serving spoon ta fara diba ba tare data ce da maimunatun kanzil ba.


          Bata daga kai maimunatun ta kalleta b,don kusan ta saba da hakan,ita ke girkin safe da kuma na dare amma unaisan tana rigata ci,da farko iya cikinta take,ganin unaisan tana diba ya tabbatar mata itama tana buqata,duk da bata taba budar baki ta gaya mata hakan ba,shi yasa idan ta tashi yi takeyi harda ita


"Ina kwana?" Ta gaidata kamar yadda kowanne lokaci take mata,ganin cewa ya girme mata,ita kuma tana mata kallon yaya ne a wajenta,tunda shekaru da tazarar dake tsakaninsu tana da yawa.


        Bata amsa mata ba,saima dawowa da tayi ta dubeta


"Daga yau idan kin gama girki,a cikin warmers dina nakeso a dinga xubashi,banason amfani da kayan kowa" ta fadi tamkar me magana dame aikinta.


          Maimunatun bata kawo komai cikin ranta ba,hakanan ranta bai wani baci ba,cikin girmamawa ta amsa mata da to,sai tasa kai cikin izza tana fita daga kitchen din.


        A kan lokaci maimunatun ta gama komai,ta gyara wajen ta wuce dakinta,daga nan toilet ta fada ta soma wanka.


          Yana gaban madubi yana amsa wayar muzaffar, cousin dinsa,kuma daya daga cikin ma'aikatansa dake aiki companynsa na lagos,gyara tie din suit dinsa yake,yana dai daita wuyanta yadda ba zata dameshi ba,ya gama ya dauki comb yana sake gyara qawatacciyar sumar kansa wadda take fidda sassanyan qamshi tare da wani sheqi na musamman da takeyi.


        "Okay,zan kiraka idan na iso,ka zama ready,banason jira" ya fada yana jefa comb din inda ya daukoshi tare da gyara hannun suit din nasa wanda aka yiwa wani ratsi daya sake qawata ta tare da nuna ainihin tsadar da take dashi,jikinsa sai fidda qamshin turaren bad boy yake na kamfanin carolina Herrera yakeyi,nan gaban madubin ya zauna,ya janyo sock dinsa ya sanya,sannan ya dauko takalminsa qirar qasar Italy dake daura da inda yake ya saka,sai ya miqe daga durquson da yayi yana furzar da iska cakude da ajiyar zuciya daga bakinsa,hadi da lumshe idanunsa yana tuna shaheeda,baisan dukka irin wadan nan wahalhalun ba muddin suna tare,komawa yake dan lelenta,bata barinsa yayi komai.


         Karar da yaji cikin wayarsa ya sanyashi hanzarin duba fuskar wayar,sai ya miqe yana daukan wayarsa,ya kuma janyo trolly dinsa zuwa qofar dakin,yana dora handle dinsa a bakin qofar unaisa tana turowa itama.


        Da kallo kadan ya bita dashi bayan ya janye mata baya,tana sanye da wata doguwar riga mai budadden hannu silk material butter color,tayi ado sosai wanda ya bayyanar da zallar hutu da jin dadin data samu tun daga gidan mahaifanta,saboda yadda farar fatarta take a kwance very smooth,bakinta sai qyallin lip gloss yake,tana tauna chewing gum a hankali.


           "Gud morning dear" ta furta tana murmushi tare da sake takowa gabansa,sai ya dan goce kadan yana amsa mata can qasan maqoshinsa


"Morning" idanunta ta sauke kan akwatin hannunsa,da alama tafiya zaiyi,wanda ko alama itakam batasan da zamanta ba,tadan bishi da kallo sanda ya sanya hannu ya bude aljihun gaban trolly dinsa,kudade ya ciro,ya matso daura da ita kadan ya ajjiye yana cewa


"am going to travel somewhere,zaku iya kiran number dake jikin nan whenever you need something" binsa tayi da kallo sanda ya gama jawabinsa,ya kuma taka cikin cikakkiyar nutsuwarsa ya soma barin falon


"Ba wannan nake buqata,ba kudi nake so ba,ba kuma shine ya kawoni ba" cak ya tsaya daga tafiyar da yake,hannunsa daya na soke a aljihun wandon suit dinsa yana kallon qofa ba tare daya juyo ba,kamar kuma bazai juyo din ba,kamar yadda kuma yanayinsa ya nuna baida niyyan yin magana,saidai kuma faaida trolley din yayi,ya waiwayo ya kuma fara dawowa,cikin wani irin yanayinsa dake saurin sanya karaya da karyar da duk wata zarra jin kai da jin isa na 'ya mace ya aza mata idanunsa,a gabanta ya tsaya yana dubanta,ya sake sakaya daya.hannun nasa dake waje cikin aljihun wandon nasa,yadan raba qafafunsa kadan


"Me kike da buqata?" Ya furta with husky voice,wadda bata sauka ko ina ba sai tsakiyar zuciyarta,ta kuma nada ajiyar wani yanayi mai tsauri ga zukata.


        Nata idanun ta daga da niyyar gaya masa abinda yake ranta quru quru,saidai inaaa,zarrar ba daya bace,don kuwa kasa qarasar da kallonta tayi izuwa fuskarsa,saita zube idanunsa a qirjinta,wanda iya nata tsahon kenan


"Iya abinda zaki samu shi nake baki,indai wannan jikin kikeso,to a shawarce ki koma gida,don abune da bazai taba samuwa ba wajen wata har abada....." Daga haka ya juya abinda hankali kwance,ya riqe trolley dinsa ya fara turata waje,sai a sannan yace mata


"Idan kin gama abinda zakiyi kina iya ki rufemin dakina" sai ya qarasa tura akwatinsa ya fice.


         Wani wawan kuka ga saki sannan ta sulale a waje ta zauna,ya Allah,itakam wanne irin abune J yakeso tayi?,wanne abu zatayi taja hankalin ja'afar,saita kifa kanta saman kujerarsa tana sheshsheqa.


           A shirye tsaf cikin Egyptian hijab ta fito ruwan golden yellow,tayi matuqar kyau qwarai,kyakkyawan fuskartan nan me dauke da wani lafiyayye kuma boyayyen kyau tayi fayau tsakiyar fuskar hijabin.


         Yana zaune cikin motar w farfajiyar gidan,don bai shiga ciki ba tunda yasa daya daga cikin masu gyaran farfajiyar yayi mata sallama,wayarsa na a hannunsa yana chart,ya bude qofar mazaunun gaba dake daura dashi,takun tafiya ya sanyashi daga kansa,ya sauke su ga madubin dake gefan murfin motar,fes ta fito a ciki,tana takawa cikin nutsuwa inda yake tsimayinta din.


          Gabansa yadan fadi,ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya,kana ya kauda dubansa daga gareta,kasancewar yasan haramcin aikata hakan a yanzu,har yau yana jinta a ransa,kuma har yau yana jin zafin rasata,tun daga randa zai shiga dakin anni yaji tana masa tayin auren yayan nasa yakejin wani abu ya tsaye masa a wuya,saboda tabbacin rasatan da yayi,amma yayi namijin qoqarin ganij ya fidda komai daga ransa,tunda yana da tabbacin ya rasata rashi na har abada.


         Baisan me yahau kan yayanshi ba daya kasa gane baiwar da Allah yayi masa,ya kuma yi masa musaya na abinda ya rasa,duk da baisan gaibu ba,amma yana da yaqinin idan maimunatu batafi marigayiya quality ba,to tabbas marigayiya ba zata fita ba,ko yanzun driver yaji yana zancan ya kaits makarantar,sai yaga rashin dacewar hakan yace zaije.


          Sauke qafafunsa yayi ya gyara zamansa gami da ajjiye wayar sanda ta iso dab da motar,ya sanya hannu yana laluba maqullin tare da amsa sallamarta sanda take yunqurin shigowa cikin motar cikin nutsuwa da kamewa


"Ina kwana ya hisham?" Murmushi ya sakar mata


"Haba anty moon,ai kya bari na fara gaidaki dai ko?,matar babban wa yayace itama" kunya ce sosai ta kamata,tayi qasa da kanta tana yaba karamci da kirkinsa,shi kam halinsa yasha banban dana dan uwansa,tasan hakan tun ba yau ba,tun tana gidan dr.


      Motar ya kunna suka fito daga unguwar gaba daya suka hau main titi da zai kaisu pen resources,rashin sabo ya haifar da shuru a tsakaninsu,duk da yaso yadan jata da hira ko zata sake amma sai ya fasa,sabon album na wani waqar hausa ya sanya musu,duka sai sukayi shuru kowa yana saurare,musamman maimunatu da batasan waqoqin ko kuma mawaqin ba,ta dinga bin duka baitukan cikin zuciyarta tana nazartarsu,sai taji waqoqin sun mata,suna kuma motsa mata wani da wani abu ckin zuciyarta,duka baituka ne da suka shafi soyayya da qauna,masu taba zuciyar duk wanda yake cikin soyayya.


          Sanda suka isa makarantar ayi mata dukka abinda ya dace,an kuma ce next week ne zasu fara daukan sabbin dalibai kamar yadda ja'afar ya gaya mata,sosai farincikinta ya nuna,har hisham yana tsokanarta,ya zaci hukuncin da yayan nasa ya yanke bazai mata dadi ba,sai kuma yaga akasin hakan,tabbacin mutum ce ita mai tsananin son karatu.


          Kasancewar batasan hanya ba yasa bata gane inda ya nufa da ita ba sai da suka je,gidan anty maama,abinda ya yiwa maimunatu dadi qwarai,ko babu komai zata miqe qafarta ba zata koma waccan kurkukun da wuri ba,karon farko data soma zuwa,qawataccen gida mai bala'in daukan hankali da nuna gayu da kuma dukiya,cikin tafkeken falonta na alfarma ta saukesu,farinciki fal zuciyarta,ta rasa wacce irin sauka zatayi musu,take tasa masu aikinta suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye har babu adadi


"Amma dai ba daga gida kuke ba,don nasan J bazai barku ba" anty maama ta tambayi jabir sanda maimunatu ta shiga toilet don tayi futsari ta kuma hado da alwalar sallar azahar,saboda mukhtarinta ya shiga,yana bare ayaba mutuniyar tasa ya amsa mata


"Daga makaranta,na kaita sun mata interview"


"Makaranta?,wacce?"

"Pen resources boarding"


"What?" Anty maama ta fada cikin mamaki tana kallon hisham,kai kace shine ja'afar din


"Bama day din ba?" Ta sake tambaya


"Yadda dai kikaji haka ne" ya amsa mata yana tauna ayabar,don shima bashi data cewa akan al'amarin J din


"Meye hakan yayi kenan?,mtseew lemme call him,wannan sam bai dace ba,yana son yayi avoiding nata ne akwai a fakaice,ya Allah.....wanne irin mutum ne J din?,kuma anni ta sani ta barshi?"


"To ya zata masa,badai matarsa bace?" Wayarta ta janyo ta fara laluban layin jaafar din,wanda a dai dai lokacin yana kwanye bayan lafiyayyar motar company dinsa datazo daukansa,a nutse ya daga wayar yana duba me kiran,sai ya daga ya kara a kunnensa.


No comments

Powered by Blogger.