Gurbin Ido 31

 


31


      Ya samu nasarar dasa tsoronsa sosai cikin zuciyar maimunatu har ma fiye da yadda yakeso,washegari da suka fito tafiya kasa hada idanu tayi da anty maama,wani irin

kunya da nauyinta ta dinga ji,cikin motar kuwa tana cure waje daya,kamar xaka ce ket! Ta zura da gudu,wannan karon a bayan ya zauna,ya kame owners corner abinsa,duk wani motsinsa tana ankare dashi,saidai da kunnuwanta don tuni ta saye idanuwanta cikin mayafi.


        Duk tsahon awannin da suka diba suna tafiya aiki yake da na'ura,daga system zuwa wayar hannunsa,tsahon wadan nan awannin ko daya baiji tayi wani qwaqqwaran motsi ba,abinda ya sanyashi daga kai suna dab da shiga garin gombe ya dubeta.


        Ko ta cikin yalwatacce mayafin data lulluba har saman kanta yana iya hangen zallar quruciua da kuma qanqantar data yi masa,wani takaici na sake kamashi kan anni,sam ita babu ruwanta da duba da cancanta ne ko kuma dacewa?,gwara unaisa ta cika shekarun da zai kirata da mace,saidai ko ita din ma bata burgeshi ba ballantana wannan rabin macen,ta yaya ma idanuwansa zasuji wata diya mace ta burgeshi?,baya zaton zuwan wannan ranar,wannan duka shaheeda ta tafi dashi,tabar masa fankon zuciyar,ta yaya fankon zuciya kuwa zata san dai dai daba dai dai ba?,sai yaja dan qaramin tsaki acan ciki,yana maida dubansa ga allon computer,yana karanta saqon rubutun da ya mamayr fuskarta.


            Katafaren wuni ake cikin gidan dr marwan,don sanda duka isa gidan a cike yake maqil,abinda ya sanya ammi ta bada maqullin wani kebantaccen waje dake gidan aka sauki maimunatu da danginta,aka kuma cikasu da cimaka kala kala,kafin yammaci inda suka hau shirya maimunatun bisa jagorancin anty maama,don Allah ya sanya mata matuqar qaunar maimunatu,tana burgeta ainun.


          Sanda suka kammala sunso su kaita cikin gidan wajensu anni da amma,amma sai annin tace a wuce da ita gidanta kawai,maimunatu tasu ce,babu wani abu sabo da zasu gaya mata,don haka direct aka fito da ita zuwa jerin gwanon motocin da aka aje domin miqata gidan captain ja'afar marwan khalid akko.


         Duk abin nan da ake tana jin komai ne tamkar a mafarki,wasu hawaye masu dumi suka zubo mata sanda taji.motocin sun fara motsawa zasu bar gidan dr marwan,babu abinda ya fado mata a sannan sai


"Allah ya nunan ranar aurenki,ya baki miji na gari" sai gata yau a bigiren zuwa gidan mijin da batasan yadda zasu rayu dashi ba,a lokacin da qasa ta jima da rufe idanun mahaifiyar tata


"Allah ya jiqanki daada"ta fada cikin ranta,wannan din addu'a ce da kullum rana batasan sau nawa take yinta a ranta da kuma sarari ba.


         Tana jin sanda 'yan uwanta da sauran 'yan rakiya ke yaba kyau da kuma tsarin gidan,kowanne bakinsa na furta addu'o'i a kanta,abinda ita ta rasa gane kansa har yanxu,Allah ya zaunar da ita yakuma dawwamar da ita a gidan mutumin nan?.


          A hankali yake takawa zuwa sassan ammansa,sanye da wani irin sassalkan yadi ruwan hanta,wani irin dinki aka masa me kyau wanda yake nuni da zallar zamani da kuma wayewa,takalmin fata ne a qafarsa budadde wanda ya dace da kayan jikinsa,kamar yadda saman kansa yake sanye da hular da itama ta dace da kalar takalmin qafarsa.


          Wata irin tafiya yake,sam jikinsa babu kuzari hakanan Babu karsashi a tattare dashi,ya tura qofar falon amman,akwai sauran baqi da suka rage cikin gidan,umma ce qanwa ga ammansa ita da wasu mutum uku,su suka gaya masa amman tana bedroom dinta,sai ya wuce kansa tsaye.


         Sai da yayi knocking ta bashi izini sannan ya tura ya shiga bakinsa dauke da sallama,luf luf dakin yake a tsaftace gana fidda wani irin qamshi me dadi,kai baka ce ba biki akeyi cikin gidan ba,tana saman gado tana gyarawa amna kwanciya,sai ya matsa ya rusuna gabanta yana gaidata,ta amsa kana shuru na sakanni ya biyo baya,ta gama gyarawa amnan ta saka mata pillow sannan ta waiwayo ga ja'afar


"Zaku wuce kenan?" Kai ya jinjina mata,yana zare hular dake kansa,can qasan zuciyarsa kuwa wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke,yana jin komai har yanzu kamar a mafarki


"Ma sha Allah,Allah ya tsare,ubangiji yasa a shiga a sa'a,Allah ya kauda dukkana abunqi,ya albarkaci tarayyarku,kayi qoqari ka riqe amanar yaran mutane,ka kuma ji tsoron Allah a zamantakewarku,ka sauke nauyin da duka Allah ya dora a kanka,na horeka ka zama adali,ka kiyaye haqqin kowacce akan 'yar uwarta,karka yi zalunci,kada kuma ka bari a zalunci kowa,Allah ya shige muku gaba"


"Ameen ya rahman,na gode amma" ya fadi yana jin jikinsa yana yin sanyi,wannan daren yana tuna masa da daren aurensa na fari ne da shaheeda,wanda akwai tarin bambance bambance masu yawa.


        Matsawa yayi gaban gadon ya dora hannunsa saman kan amna ya shafa,sannan ya duqa yayi kissing kuncinta,ya maida mata abun rufar ya miqe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa


"Sai da safe" yace da amma yana takawa zai fice


"Allah ya bamu alkhairi" ta fada tana bin.bayansa da kallo,duk yadda yake qoqarin boye damuwar dake saman fuskarsa ita ta karanci hakan,saita rakashi da addu'a


"Wannan hadin ubangiji kasa ya zama silar waraka a rayuwarka".


         Motarsa ya wuce kai tsaye kamar yadda ya zaba tafiya shi kadai babu dan rakiya ko daya,don zuwa yanzun ma yasan abokansu sun tsufa gidan jabir koma suna shirin juyowa,yace baya buqata,shi din ai ba auren fari xaiyi ba.


        Yana shirin bude motar yaji sallamar khadim a bayansa,sai ya waiwaya yana amsawa,cikin girmamawa ya miqa masa wasu ledoji dake hannunsa


"Gashi inji ammi" jim yayi na sakanni yana bin ledar da kallo,sai kuma ya bude masa back seat bau tare da yace komai ba,khadim din ya fahimta abinda yake nufi,don haka ya qarasa ya saka musu su a baya,har ya juya zai tafi yace masa


"Kace mata na gode" yayi maganar ne sanda yake shigewa cikin motar,ya maida.murfin ya rufe ba tare daya jira cewar khadim ba.


         A hankali yake tuqin kamar wanda baison isa gidan,tafiyar data daukeshi mintuna masu tsaho fiye da mintunan da zasu isheshi a al'adance,horn daya mai gadin gidan ga dage masa gate din,sai a sannan yadan ja motar da gudu ya shige da ita farfajiyar gidan,sannan ya faka ta a parking lot idanunsa na sauka kan wata qaramar sabuwar mota ruwan zuma,ya dauke kansa yana kashe tasa motar.


        Har ya fito ya tuna da ledojin da ya bari cikin motar,sai ya koma ya debosu,tun kafin ya bude ma ya fuskanci meye a ciki,sai ya riqesu a hanauyensa,dai dai sanda me gadin gidan ya iso cikin rusunawa ya fara gaidashi,amsa masa yayi cikin kulawa,saboda yana daga cikin dabi'arsa girmama duk wanda yake aiki a qasansa,barshi dai da zafinsa miskilanci rashin daukan raini da rashin son wasa da aiki,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya fiddo 'yan dari biyar biyar sababbi guda shida ya miqa masa,hannu biyu ya sanya ya karba yana ta zabga godiya,yayin da shi kuma yayi gaba abinsa ba tare da yace tak ba.


       Sai da yayi addu'ar shiga gida sannan ya kutsa kai cikin babban falo,shuru yake babu alamun motsin me rai cikin gidan,cikin nutsuwa ya fara takawa zuwa stairs,sai kuma ya tsaya cak saboda maganar da abbi da kuma amma suka gaya masa a daren jiya da yau,ledojin hannunsa ya kalla,a hankali sai yayo baya,ya kuma nufi qofar dake hannun dama na falon.


          A hankali ya tura qofar,falo ya bayyana,wanda aka qawata da kalolin kujeru da curtains masu azabar kyau,royal blue da golden,komai na falon,a tsaftace yake cikin qamshi da sanyi daya gauraye da sabunta,ci gaba yayi da tafiya har ya isa qofar bedroom din,itama ya turata ya shige.


         Dai dai lokacin da take zaune saman abun sallah,saboda ganin yadda lokaci yaketa tafiya,an doshi sha biyu na dare,kuma ana binta sallar isha'i da kuma shafa'i da wuturin da batayi ba.


        Can qasan maqoshinsa yayi sallama idanuwansa suna sauka a kanta,gabanta ya buga fat,don bata tsammaci shogowarsa din ba,saboda dukkan wata magana daya gaya mata a jalingo ta haddacesu tsaf a kanta, janye kansa daga wajen da take yayi,ya isa gaban madubi ya ajjiye ledar a kai,sai ya tsaya yana goye da hannayensa a qirjinsa.


          Raka'ar qarshe take amma kawai sai ta miqe taci gaba da kawo wasu raka'o'in,abinda ya sanyashi sakin hannayensa kenan,ya kuma juya a hankali ya fice a dakin bayan yaja qofar kamar yadda ya ganta.


       Sallamewar sallarta ta fito ne hade da ajiyar zuciya,ta danyi shuru tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,tana kuma jin yadda zuciyarta take bugawa,lumshe idanunta ta sakeyi,ba shakka tana tsananin tsoronsa,tana tsoronsa bilhaqqi da gaske,hoton sanda ya zuba mata lafiyayyen marin nan ya gilma a idanunta,sai kuma sanda yake zuqar hayaqin taba yana bulbular da ita daga bakinsa zuwa hancinsa,sai ta girgiza kai,tana jin wani bala'in haushinsa yana ratsata.


       Yaya akayi ya kasance mashayin taba?,bayan shi din ya fito ne daga gidan tarbiyya kamar haka?,mutane masu karamci dattako da sanin darajar dan adam?,bata tunanin akwai wanda yasan yana sha din cikin gidan,don ko da wasa bata tabs jin anyi magana makamanciyar wannan ba.


          Tunanin ta ture gefe,ta fara karanto azkar dinta da bata samu tayi ba a yau din,gefe na zuciyarta kuma cike taf da kewar amna,tana jin cewa zaiyi wuya bata nemi su anni su bata yarinyar ba,don ko a yau ma sai da akayi wayon janyeta sannan suka tahi,wanda ita bata kawo hakan ba,ta tsammaci zasu taho ne da ita,amma sai taga akasin hakan,to me zata zauna ne tayi a gidan?,gwara gwara ma ace da amnan,zata taimaka mata wajen debe kewa.


           Kamar yadda ya shiga sasssan maimunatu haka ya shiga na unaisa,saidai ita ya sameta tsaye ne a gaban mudubi tana kallon kanta bayan ta gama sake feshe jikinta da turare tana gyara zaman rigar jikinta.


           Sallamarsa hade da turo qofar ya sanyata saurin maida mayafinta saman kanta, ta rufe ruf,saidai tana iya hangensa ta cikin mudubin,wani sassanyan abu ya ratsa zuciyarta ya kuma haifar mata da yalwataccen murmushi akan fuskarta,a fakaice taci gaba da binsa da kallo,tana jin wani farinciki yana ratsata,burinta ne na tsahon wasu shekaru Allah ya cika mata shi,duk da cewa ranta ya baci a dazun da ganin irin gidan daya zaba a jjiyeta kuma tare da wata,saidai anty talatu ta kwantar mata da hankali


"Kinsan baso yake ba,ta yiwu yayi hakanne don ya baki haushin dama harkiyi wani abu da zai janyo a fasa gaba daya,dole fa saikin anjiye rashin haqurin nan,kin janyo hankalinsa a hankali a hankali,sanda zai canza miki gida ko ya rabaki da qasar ma gaba daya bai sani ba" qwarai ta gamsu da maganganunta,don haka ta ajjiye komai gefe a ranta.


          Cikin salo ta amsa sallamar tasa cikakkiyar amsawa,bai sake cewa komai ba itama ya ajjiye mata ledar,ga zatonta zai qaraso koda gefanta ne yace wani abu da ita,saidai gani tayi yana shirin ficewa,muryarsa can qasa ya furta


"Gudnyt" ya tursasa zuciyarsa ta fada,duk don son ganin yayi abinda ya dace bakin gwargwado.


        Gabanta ne ya fadi sanda yake gab da fita,ta daga kai tana dubansa ta madubin,zuciyarta tana bata shawarar tsaidashi,yayin da wata zuciyar ke hanata,tana gaya mata girman wannan rana a wajenta,ita yafi kamata ace an tsaida,an kuma nema kasancewarta cikin dakin,tana wannan shawarar da tattaunawar da zuciyarta har ya fice.


          Kasa zaune tayi,ranta ya baci sosai,ta dinga kai kawo tana tunani a ranta,shin sassansa ya tafi ko kuwa na maimunatu?,sai taji zuciyarta taqi aminta da hasashen daketa mata yawo,don bai kamata ace sassan maimunatun ya fara sauka ba,tunda a qa'ida itace babba,ta girmewa maimunatu,ita ya kamata ta fara karbar baquncinsa,tafi maimunatu sanin rayuwa dama komai da komai da za'a tarairayi mutumin da ya jima babu mata a gefansa kamarsa,don haka ta gyara rufin mayafinta,ta kuma bude qofar ta fito.


          Bata ma isa sassan maimunatun ba taji motsinsa daga sama,don haka taja birki,ta kuma koma nata sassan,girman kai yana sauko mata,tana jin ba zata iya nemansa a yau ba itama.


          Yana shiga dakin ya sauke ajiyr zuciya mai qarfi kamar zai tofar harda qirjinsa,ya soma bin dakin da kallo,an qawata masa shi yadda yakeso ya kasance,idanunsa daya bayan daya suna sauka kan hotunan shaheeda da amna da amra wanda aka musu tare yasa aka gyarasu aka shiryasu a falon gwanin burgewa,kai kace idan ka kirayesu zasu amsa,zakayi tsammanin har yanzu sune ke rayuwa cikin gidan,addu'ar da baya gajiya dayi musu yayi wani abu na motsa ransa,ya wuce zuwa bedroom dinsa.


         Sai daya gama duba komai daya ce a sanya masa a dakin,wanda yake buqatar ya canza masa waje ya canza masan ya ajjiyeshi inda yakeso,sannan ya fidda kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,sai ya wuce toilet kai tsaye,ya daura alwala sannan ya fito ya kuma bude walking wardrobe dake manne da bedroom dinsa ya shiga ya duba wasu navy silk pyjamas Natalya's company,ya shirya kansa wadata jikinsa da turaren da yake amfani dashi duk dare,sannan ya feshe kansa da BB hair spray.


         Abun sallarsa ya shimfida sannan ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarsa ga alqibla.


        Unaisa kuwa kusan raba dare sukayi suna waya da anty talatu qanwa ga mahaifiyarta haj Aayah,tana gaya mata abinda yafaru,ita kuma tana shirya mata yadda zata aiwatar da komai,sun jima sosai suna tattaunawa kafin suyi sallama


"Amma dai lafiya ko?" Haj Aayah da suke kwance daki daya da qanwarta wadda bata kai ga komawa gida ba ta tambayeta


"Eh to,lafiya amma ba lau ba" abinda ya farun ta gaya mata,sai ta sauke ajiyar zuciya


"Yaron nan fa ba lafiyar kwanya ya cika ba,idan anyi magana sai kuce depression ne ya kamashi bawai ciwon hauka ba,ni tsorona ma kada ya kama min diya ya jibga,don banjin zanyi kawaici,babu yadda banyi da unaisa ta haqura dashi ba amma ta kasa haqura" murmushi talatu tayi


"Banda abinki yaaya,ta yaya yana da ciwon hauka zan goya ma unaisa baya ta aureshi,an gaya miki ciwon damuwa ne,kuma a yanzunma komai yana wucewa tunda gashi ya amshi mata har biyu,mudai burinmu kawai diyarmu tayi zarra ta zama star dinsa,don kishi da bafulatana sai an kula,shegen surkulle garesu" haka suka yita tattauna maganar a tsakaninsu a daren.


         Itako maimunatu wani nutsuwa ta sauko mata bayan ta gama dukka addu'o'inta ta isa ga gadonta ta kwanta,gadon data dinga ji kamar ba nata ba,dakinma kansa jinsa take kamar an bata aronsa ne,kewa da kadaici suka dinga damunta,sosai ta dinga ji cikin ranta inama ace an bata amna,sannu a hankali idanuwanta suka dinga nauyi,bacci kuma me qarfi ya fusgeta.


No comments

Powered by Blogger.