Gurbin Ido 30
Ko sau daya bacci ko gyangyadi basuyi nasarar fusgarta ba,hakanan ko qwaqwaran motsi batayi tsahon a wannin da suka dauka suna tafiya,hakazalika motar haka ta kasance shuru,ba zata ce ga ainihin abinda yake faruwa cikin motar ba,sai daga bisani ne tadan janye mayafin dake kanta kadan saboda ta samu damar kallon gefan hanyoyin da suke wucewa da mugun gudu.
Taraba suka wuce kai tsaye saboda su raba tsahon tafiyar,uwa uba kuma yammaci tayi lis,babu security ace sunyi tafiyar dare,don haka suka yanke sauka a wani hotel dake kan babbar hanyar da zata sadasu da gombe,kafin su iso ma tuni jabir yayi booking dakuna,don haka suna isa kowa key na dakinsu aka bashi.
Itakam tana zaune cikin motar,har zuwa sanda anty maama ta qaraso ta fiddota,ran anty maaman cike da haushin ja'afar din,ta yaya sunsha wannan doguwar tafiyar xai fita yabar diyar mutane cikin mota?.
Yana tsaye a tsakiyar dakin yana amsa waya sanda anty maama tayi knocking,ya qarasa bakin qofar ya murza handle din ya bude mata ba tare da ya tsaya tambayar waye ba,kana yaja da baya yana ci gaba da amsa wayar.
Bakin madaidaicin gadon dake shimfide da farin lallausan bedsheet,tadan duqa kadan dai dai kunnuwan maimunatun,ta yadda ita kadai zataji abinda take gaya mata
"Ki saki jikinki da mijinki,ki samu kiyi wanka da brush kafin ki kwanta,zan ciro miki wasu kayayyaki cikin akwatinki za'a miqo miki,ki saki jiki kinji ko?" A hankali maimunatu da kanta yake a duqe ta gyada kan nata,tana jin zuciyarta na wani irin bugawa,a tsahon shekarunta na goma sha shida tunda take bata taba kebewa da wani d'a namiji ba a daki daya kamar haka,balle har ta kaisu da kwana kamar haka,yau gashi za'a fita a barta da wani,wanda yake amsa sunan miji a gareta.
Juyawa anty maama tayi ga ja'afar wanda har yanzu bai gama wayar ba,sai ta kada kanta ta fice a dakin,qarar rufe qofar dakin ya sanyashi waiwayowa,don bai lura dawa suka shigo ba,ya zaci tazo wajenshi ne zasuyi wata maganar,kuma sai yaji ta fice ba tare da tace komai ba,abinda ya sanyashi juyowa kenan.
Cikin mamaki idanuwansa suka sauka ga maimunatun,kawo masa ita sukayi kenan?,lallai dai sai sun qure haqurinsa da juriyar da yaketa azawa ransa?,sai ya dauke idanunsa yana sallama da wanda suke wayar dashi,ya yanke kiran yana neman number jabir.
Bugu daya ya daga,muryarsa cike da wani irin nauyi yace
"Baku da wani extra dakin?"
"For who?" Ya tambayeshi kai tsaye,don dama yasan dole ko yaya sai ya nuna turjiya
"Ban sani ba,am asking you ne,it's simple question,just answer me bawai ka tsaya tuhuma na ba"
"Oh...oh sorry, let me ask abbi first,but dakin kadan ya muku ne?" Ya tambaya cikin zolaya izgili da neman fada,haushi da takaici ya sanya ja'afar jan dogon tsaki kana ya tsinke kiran,wai dole sai jabir ya sanyashi dogon magana ne?,baisan abinda yakeji bane?. Sai ya cilla wayar saman madubu,sannan ya jawo kujerar gaban mudubi ya zauna a kai.
A hankali ya duqa yana zare takalmin qafarsa,idanunsa suka kan farar qafarta dake dauke da dogayen yatsu da suka sha jan lalle wanda ya sake qawata qafan,ya kuma zame mata ado sosai,sai ya janye idanuwansa,qafafun are tiny,abinda yake alamta masa tana da qarancin shekaru kenan?,haka kawai sai yaji zuciyarsa na darsa masa son ganinta da tantance wacece ita?,ta yaya zasu dubi kamarsa suce zasu aura masa yarinya kamar haka?,sakanni qalilan zuciyarsa ta kacame da wasuwasin yarinyar ce ko kuma hasashe ne irin nasa?.
Miqewa yayi yana sake jan tsaki duk a qoqarinsa nason mantawa da wannan wasuwasin da yake azalzalarsa a rai,ya taka zuwa qofar bandaki bayan ya kalli agogo yaga lokacin sallar magrib yadan gota kadan,ya daura alwala,ya sake fitowa yana sauke hannun rigarsa daya nannade kafin fara alwalar,yana son ce mata taje tayi alwala suyi sallah amma kuma ya rasa ta yadda zai gaya mata,bawai kuma baisan yadda zaice mata bane,a'ah,kawai qyashin maganar yakeji,har ya fidda abun sallah ya shinfida tana zaune,sai daya sake jan tsakin nan nasa dai,wanda ya kuma sanya maimunatu faduwar gaba ta kuma rintse idanunta kamar kowanne lokaci idan yayi tsakin,don tana jin tsakin ne har tsakiyar kwanyarta,faduwar gabanta kuma nada nasaba da muryar dake mata kama da wata firgitacciyar murya data taba ji shekarun baya da suka wuce
"Kiyi alwala kizo" ya fadi mata yana jona qaraman kettle dake a gefansa.
A hankali ta miqe,ta kuma dan ja mayafin nata baya kadan,sannan ta wuce zuwa bandakin.
Gaban madubi ta tsaya bayan ta yaye lullubin kanta gaba daya,tana sakin wata ajiyar zuciya me nauyi gami da kallon fuskarta,wadda lallausan gashinta me azabar santsi da yasha gyara daga wajen yakumbo saratu ya fito kadan ta gaban dankwalin nata,saita debe ruwan dake zuba daga famfo ta fara alwalar,tana yi tana kallon fuskarta a madubi,zuciyarta nata mata saqa abubuwa masu yawa harta gama,ta maida dankwalinta da mayafinta ta fito,ta kuma tsaya a inda ya mata nuni suka tada sallar.
Yadda yake sallar cike da nutsuwa yayi matuqar burgeta,ko banza alamune dake nuni da sanin addininsa.
A hankali ya sallame,idanunsa suka sake sauka akan dogayen hannayenta suma da suka jiqu da jan lallae cikin ado me ban sha'awa,hakanan ya samu kansa da juyowa gaba daya yana fuskantarta,idanunsa suka sauka gaba daya a kanta,ta tanqwashe qafafunta sosai tana zaune,sai ya ganta 'yar qarama a gabansa,tazarar dake tsakaninsu ba mai yawa bace
Shuru ne ya baquncin dakin,numfashin kowannensu yana fita tare sa tulin tunanin dake zuciyar kowannensu,yaci gaba da zama a haka yana fuskantarta tare da wassafa me zayace da ita?,duk sanda yadan dubi sashen da take zaune sai yaji wani abu ya tokare masa wuya,yanzun haka bayan ita akwai wata daban dake gombe tana jiransa?,for god sake anni zatayi masa haka ne wai?.
Kamar wadanda aka umarta daga shi har ita kowanne ya daga kanshi zuwa ga dan uwansa,take fuskarsu ta hade waje daya kamar yadda idanuwansu suka cudanya da juna,fari qal din idanuwan nan nata da baqaqen qwayar idanunta masu digon zaiba jiki,kyakkyawan idanunwansa dake da wani irin shape,tare da wani irin maganadisu dake cike da zallar kwarjini.
Kusan lokaci daya wani abu ya daki zuciyar kowannensu,wanda ta bangaren maimunatu ba komai bane face wani irin tsoro razani da kuma firgici da ya kusa tafiya da numfashinta,cak ta tsaya da zuqar iska zuwa huhunta na wucin gadi,hatta da ja'afar din ya karanci hakan,yayin da shi kuma zallar mamakin qananun shekarun da take dashi hadi da kamanni da tayi masa da wata suka ratsashi.
Cikin jarumta ta zuqi wani dogon numfashi ta kaiwa hunhunta cikin wasu sakanni masu mugun sauri,abinda ya tallafa mata numfashinta ya dawo da aiki,saita lumshe idanunta da kyau tana shaqar numfashin da qyar,tana kuma jin yadda zuciyarta ke mugun bugawa da sauri kamar zata tsinke daga inda take ta fito.
"Hey" ya fadi cikin mamakin yadda take wasu abubuwa kamar wadda taga giftawar mutuwarta a gabanta,maimakon maganar tasa ta taimaka wajen bude idanuwanta ko samun nutsuwarta......a'ah,sai ta sake razana,saboda muryar ta sake tabbatar mata da shi dinne dai,shine dai wannan mutumin,take jikinta ya dauki rawa,zuciyarta taci gaba da kadawa a tsakanin qirjinta,sai tayi wuf zata tashi jikinta na kakkarwa kamar wadda azababben zazzabi ya rufe.
Caraf ya damqi tsintsiyar hannunsa cike da haushinta da mamakin firgitar da tayi,riqon da yayi mata ya sanyata sakin kuka babu shiri tana dubansa,mamaki ya cikashi qwarai,sai ya janyota ta koma ta zauna a inda ta tashi.
Sosai hankalinta ya kuma tashi,ta hade jikinta waje daya hawaye naci gaba da bin kuncinta,ta yaya zata manta da wannan fuskar?,yaya zata manta dashi,mutumin da ya kusan sanadin cirewar qwayar idanunta saboda marin da ya zabga mata duka akan dabbobinta?,mutumin da ya mata barazana da kakkausar murya,wanda tun daga ranar bata sake ganinsa ba,saidai duk sanda taga mota,ko taga wani abu da yayi kama da mari saita tunda da abinda yayi mata,sau tari takan shafa kuncinta idan ta tuna da wancan lokacin,mutumin da razanata matuqa,ta tsani taba,ta kuma tsani me shanta,sai gashi ya fesar da hayaqinta saman fuskarta,abinda ya kusan haddasa mata daukewar numfashi,wanda ya aikata mata wannan duka shine zaune yanzu a gabanta,shine kuma mijinta?.
Samun kansa yayi da zuba mata idanu,abinda ba al'adarsa bace,yana dubanta tare da son tuna inda ya santa,tsahon wasu daqiqu kwanyarsa ta dauko masa komai,bafullatanar yarinyar nan,daya jima yana tunawa bayan marin da ya dauke fuskarta dashi,ya jima yana murza hannunsa a lokacin cikin fushi da jin haushinta na yadda ta qarasa tunzura fusatacciyar zuciyarsa ya aikata mata abinda ba halayyarsa bane,fuskar da yakan tunata lokaci bayan lokaci saboda qarfin halinta da kuma yadda ta bashi haushi a sannan.
Ga mamakinsa sai yaji duk wani temper na zuciyarsa ya sauka daga kaso casa'in cikin dari,zuwa kaso arba'in ciki dari,ta yaya zai zauna da wannan yarinyar?,wadda gaba dayanta baifi ya haifeta ba inda ace auren qauye akayi masa?,ta yaya zai zauna da wannan bafulatanar rugar?,wadda ya tabbatar babu abinda ta sani,babu kuma abinda ta iya?,ya aureta yace ya auri me?,ta yaya ma duniya zata kalleta a matsayin matarsa?,wanne irin rigima ce wannan ta anni?, take kwanyaraa ta hasaso masa unaisa,yayi comparing nata da wannan,sam babu hadi,ko ita unaisar bata cika mizani da ma'auni ba,tayi masa girma da yawa,don shaheeda bata kai wadan nan shekarun ba har ta rasu,barema tun halittarsa shi mace bata taba burgeshi ba,shaheeda ce mace qwaya daya tallin tal da ya taba daga kai ya dubeta da wata ma'ana ta daban,itace macen data fara bude rayuwarsa,kuma sanda ta tashi tafiya.....yanajin ta hada da muqullin komai nashi tayi gaba dashi.
Cikin rai da zuciyarsa ya dinga jin yanzu zaiyi solving daya daga cikin matsalolin kamar yadda yake kallon maimuntu da unaisa a natsayin MATSALA kuma GURBIN IDANU ne kawai,wadanda baijin zasuyi ko suna da amfani ko wata rana ga mamallakinsu,wanda dasu da babu duk daya
"Relax" ya fada idanunsa a lumshe,yana zagaya lips dinsa da yatsun hannayensa
"Yamin shuru!" Ya sake fada a karo na biyu,ganin taci gaba da rera kukanta kamar ma bataji abinda yace ba,yadda ya buqata kuwa a wannan karon....sai ta fara hadiye kukan sannu sannu har ta samu nasarar tsaidashi.
Shuru ya sake ratsa dakin,tamkar bazaiyi magana ba,kafin daga bisani ya bude dukkanin idanunsa ya watsasu a kanta
"Kinsan menene aure?" Yayi tambayar with husky voice,wani irin abu ya ratsa mata tun daga saman kanta zuwa tafin qafafuwan maimunatu,saboda girma da nauyin da tambayar tayi mata,me zata ce masa?
"Kinsan me aure yake nufi?" Ba tare da tayi dogon nazari ba ta gyada kanta alamun eh,kasancewar ba mutum ce ita wadda ta iya qarya ba.
Wani miskilin qaramin murmushi ya sake
"Okay......yayi kyau,tell me menene aure?" Ya fada yana yin qasa da muyarsa,hadi da tsareta da idanunsa nasu nauyin kallo,duk da bashi take kallo ba amma sai da taji gaba daya ta rude ta kuma daburce
"Ehhnnnnn" ya fada da madaukakin sauti,sai ta shiga girgiza kai alamun a'ah,bata sani ba
"Qarya kike kenan da farko..... okay let me show you the real definition of marriage" ya fada with confidence,zuciyarsa na gaya masa that's the only way da zai cimna gaci na abinda yakeson aiwatarwa,ba tare da yasan maimunatun was simple and peace maker ba,sai ya miqa hannu ya janyota cikin zafin nama daya sake tsoratata zuciyarsa na ingizashi,ya sanyata tsakiyar qirjinsa duk da yadda zuciyarsa ke qin hakan.
Fara yamutsata yayi,abinda yayi matuqar dukan hankalin maimunatu ya kuma kadata sosai,abinda tunda take makamancinsa bai taba faruwa da ita ba,mugun gigicewa tayi cikin tsoro da razani,ta sake sakin kuka tana riqe masa hannayensa da yakeson fara yawo dasu cikin sassan jikinta,sai ya tsaya cak numfashinsa na wani irin gudu,yana duban yadda ta riqe dukka hannayensa biyu cikin siraran tafin hannunta,jikinta na wani irin rawa kamar an kada mata gangi
"Bai kamata ba,baka kyauta ba" yaji can tsakiyar kansa zuciyarsa na gaya masa,bai musa ba,take zuciyarsa ta gamsu da cewa bai kyauta din ba,saidai kuma wannan ce hanya guda daya da zaiwa tufkar hanci,tunda baisan irinta ba yarinyar,abu daya ya sani game da ita,tsiwarsa da har ta iya buda baki tace masa Allah ya isar mata a wancan lokacin,yana jin this the only way out da zai dorata kan duk abinda ya tsarama zuciyarsa.
Saidai kash,yana shirin sakinta anty maama ta turo qofar riqe da jakar kayanta,abinda ta gani ya sanyata fadin
"Subhanallah" da sauri tana komawa da baya,abinda yaja hankalinsa,yayi hanzarin sakinta ya kuma miqe a nutse,ya isa bakin qofar dakin ya sake bude mata ita sosai,sannan ya juya zuwa bandaki bacin rai yana cinsa kan yadda ta gansu,yayi yaqinin abinda zaizo ranta daban,abinda zata rayama ranta yasha banban da abinda yake faruwa,ya tura qofar toilet din ya shige.
Gaban madubi ya tsaya yana duban fuskarsa,hannunsa yasa yana yamutsa sumarsa zuwa bayan kansa,yadan riqeta da qarfi yana jin haushin kansa da kansa,ta yaya zai riqe yarinyar cikin jikinsa har kamar haka?,sai yaja wani irin tsaki kamar zai cire harshensa,yana jin tsantsamin jikinsa dama hannayensa,duk da cewa babu abinda ke fita a jikinta sai lallausan qamshin turaren firdaus.
Wayarsa ya ciro ya turawa jabir tex kan ya shigo masa da kayan sawarsa,sannan ya ajjiye wayar,ya soma fidda kayan jikinsa yana jefarwa,ya daidaita ruwa me dumi sosai daga shower ya shiga ciki yana sabe jikinsa kamar zai cire fatar wajen.
Da wani irin nutsuwa dakiya da kuma tsare gida ya dawo dakin,bayan ya shirya cikin wata lallausar jallabiyya da aka yiwa aiki d wani gold zare mai kauri,idanunsa suka sauka a kanta,tana lafe a wani lungu dake daura da gadon,sai ya sake jan tsaki can qasan ransa,yana jin takaici na sake kamashi,baisan me anni ma ta dauki aure totally ba data hadashi da wannan.
Bai tsawaita magana da ita ba,cikin taqaitattun mintuna ya gama tsara mata dukkan wasu qa'idoji da dokoki da yakeso tabi da kuma zauna akai,ya riga daya sani a yanzun bai isa yace ya rabu da daya daga cikinsu ba ko ta yaya kuwa sukazo masa indai bada wani qwaqwaran dalili ba,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya,yana jin yayi maganin rabin matsalarsa,ya tabbatar a yanzun bashi da wani sauran case da ita wannan yarinyar,saura dayar,ya fuskanci itakam waccar kanta yana rawa sosai,zai kuma shata mata layi tsakaninta da rayuwarsa.
Fita yayi ya barta a dakin,bai dawo ba sai da bacci suka kama idanunsa,duvet din ya yayima ya koma saman kujera yayi kwanciyarsa,bayan ya kashe hasken dakin,bai wani jima sosai ba bacci ya daukeshi,don tunani da damuwar dake kansa a yanzun ta ragu sosai.
Kasa sakewa tayi cikin dakin,motsi kadan saita tuna abinda yayi mata dazun,abinda ke sake bata tsoro kenan,duk da maganganun da yayi mata dazun sun sake nuni da girman tazarar dake tsakaninsu,wanda zuciyarta tafi raya mata cewa gargadine ya sanya ya aikata mata hakan,bawai don ta isa ko tana da wani abu ba,babban shinge da layin daya gindaya tsakaninsu kawai ya sake tabbatar mata da cewa da gasken gangancin aka aikata na hadata aure dashi kamar yadda ya gaya matan,ita kanta daga dazu zuwa yanzu da kuma sanin data yi masa a baya ta sake tabbatarwa kanta tako ina yafi qarfinta,ya kuma yi mata fintikau,tun tana takure har gajiya tasa gabbanta suka saki,ta kuma zame da jikinta a nan qasa daura gadon,bacci mai nauyi ya fara fusgarta,zuciyarta cike fal da tsoronsa daya dasa mata a wannan rana.
Leave a Comment