Gurbin Ido 23

 


23


      Sallamar jauro ita ta kubutar damaimunatu daga tulin tambayoyin inna furera,shikam karon farko ya gane maimunatun,yayin data miqe kamar yadda ta saba a baya tana masa sannu da zuwa gami da karbar ledar hannunsa.


          Yana shirin xama ta duqa har qas ta gaidashi,ya amsa cikin nuna kulawa,tamkar diyarsa gaje


"Baki tafi gida kin kwanta ba?" Wani kallo inna furera ta jefeshi dashi a fakaice


"Akwai inda yafi nan ne?,naga dai nan dinne gidan"


"Qwarai kuwa"


"Tun daxun ma nake tsimayin shigowarka..."


"Eh nadan tsaya ne muna magana da labaran,ashe bidar alkhairi ne ya kawosu garin ma" sosai inna furera ta bada hankalinta ga jauro


"Kamar yaya kenan?" Huffijen qafarsa ya cire,ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa


"Wato Allah ne kadai yasan alkhairi dake tattare da yarinyar nan,uwar dakinta hajiya anni,ita tazo ta shaida mana cewa,suna so mu basu dama zasu turo a nemawa jikanta auren maimunatu"


         Kamar ya dauko qaton qarfe ya doka mata a tsakiyar kai haka inna furera taji,sai taji gaba daya ta daina ganewa,kwanyarta ta dode


"Ban gane abinda kake magana akai ba jauro,kace me?"


"Nace gidan da taje aiki,uwar dakinta tazo nemawa jikanta izinin turo magabatansa neman auren maimunatu" zumbur kamar wadda kunawa ta harba haka nan ta miqe,take ta hada zufa da kuma gumi,zallar tashin hankali yana nuna kansa saman fuskarta


"Wallahi wallahi ba zata sabu ba,aini ba haka mukayi da ita ba,ba kuma abinda na turata yi kenan ba,ni arziqi na turata nema mana bawai aure ba,hasalima ni ban shirya aurar da ita yanzu ba....."saita waiwaya bangaren da maimunatun take


"Don uwarki don ubanki dama karuwanci kika je yi?,aure nace kije ki samo ba kudi ba?,shegiya mayya,kinje da idanunkin nan kin lashe kurwar dan mutane?" Inna furera ta fada cikin hargowa da fada matuqa


"Ah.....kinga dakata furera,me kikeson kice ne?,.....ke maimunatu,tashi ki wuce daki wajen 'yaruwarki ki kwanta" ya baiwa maimunatu data cure waje guda saboda tsoro umarni,ta manta da irin wannan rayuwar sam,ta manta rabon da wani ya daga murya a kanta sai yau,sai ta miqe da hanzari ta durfafi dakin gaje,duk da shima batasan me zata taras ba.


         "Zauna furera" jauro ya bata umarni kai tsaye yana dubanta


"Na zauna nayi me?,aini na gama magana,babu uban da ya isa yasa maimunatu tayi aure yanzu ehe" cikin matuqar mamaki yake kallonta


"Awala hankali furera?,wanne irin batu ne na wai maimunatu ba zatayi aure ba?,ina cewa nan tanadin auren gaje kike yi?,sai kuma yanzu zaki ce ita maimunatu ba zatayi aure ba?,.....to......to,na gama fahimtar inda kika saka gaba,tsaf na karanceki,to bari kiji,idan kin saba watangaririya da rayuwar yarinya,idan kin saba saka rayuwar yarinya a gaba kiyi duk yadda kikaso ina zuba miki idanu,to wannan karon tayi qaura,kuma baki isa ba,yadda suka zo neman izinin auren maimunatu zasu sameshi kuwa da yardar Allah,muddin bake kadai kika rage a doron qasa jinin shatu da maimunatu ba" ya miqe cikin tsananin fushin data jima bataga yayi ba,sai tabi bayansa da kallo tana cewa


"Me kake nufi jauro?" Ko tankata baiyi ba,yasa kansa abinda ya wuce dakinsa.


        Komawa tayi jabar ta zauna a wajen tana fidda zazzafar iska daga bakinta,kwanyarta ta cika taf da tunani,mutanen nan koda bataje ta ganewa idanunta ba tabbas tasan masu tarin arziqi da wadata ne,ta yaya maimunatu zata shiga cikin irin wannan ahalin alhalin gaje na zaune a qauye?,duk da babbar sa'a tayi na samun himu cikin qauyen?,shawara ta qarshe da zuciyarta ta bata shine,ta tunkari jauro kai tsaye,ta fayyace masa abinda yake zuciyarta,ai shima gaje diyarsa ce,kuma bazaizo ci gaban maimunatu fiye da diyarsa ta cikinsa ba.


           Wani kallo ya dago ya watsa ma furera sansa ta kammala bayananta


"yanzu na fahimci bayan ciwon mugunta da hassada dake damunki,harda ciwon hauka kadan a kwanyarki,toki sani.....ni ba qaramin mutum bane,yadda suka furta maimunatu babu abinda zai sauya wannan in sha Allah saidai idan sauyin daga wajensu ne" maganar ta sake harzuqa inna furera matuqa,ta miqe cikin masifa


"Nidai bansan ko dakai.akayi cikin maimunatu ba,banda haka,ta yaya ga jininka zaka ajjiyeta kafifita wata bare akanta?"


"Duk yadda rai da zuciyarki ya baki haka ne" abinda jauro yace da ita kenan,don ya fuskanci tayi nisa bata jin kira,ba zata fuskanci duk wani bayani sai abinda zuciyarta da shaidan suka qawata mata.


         Yadda maimunatu batayi cikakken bacci ba a daren saboda maganganun da gaje ta dinga gasa mata har zuwa sanda bacci ya dauketa......haka itama inna furera bata runtsa ba,Kuka irin wanda maimunatu ta jima bata yishi ba tun barinta gidan a yau ta yishi,tana cike da tantamar anya inna furera yayar daadarta ce da gaske kuwa?,sam ko daya cewar da tayi ba zata auri jika ga anni ba shine damuwarta ba,a'ah.....yadda a kullum ta bude baki mugunyar kalma ce ke fita daga bakinta a kanta,bata taba ambatar alheri a kansu,daga ita har marigayiyar mahaifiyarta,ta duba ta kuma dubo amma ta gaza gano laifi guda daya tak da suka yiwa inna furera wanda suka cacanci wannan abun daga gareta,bata damu da zantukan gaje ba dama ta saba dasu,amma qiyayyar inna furera tana mugun taba mata ruhi.


         Ita kuwa inna furera kaf a daren tunaninta ya tafi ga yarda zata turgude maganar auren maimunatu ne,idan da hali ma ta maida akalar zanca ya koma kan gaje,bata damu da koma wanne irin kallo daadar himun zata yi mata,indai suka haye wannan bigiren shikenan komai yazo qarshe a wajenta.


          Shawarar qarshe data yanke da ita ta kwanta,ta kuma miqe tun kiran assalatun farko ta buga sallarta,ta zauna tana dakon kira na biyu ta fice a gidan.


           Sanda ta fita din kuwa ko sallamewa daga sallar ba'ayi ba adan masallacin dake tsukin rugar tasu,sai a hanya dab da isarta gidan bappa labaran aka idar,ta kutsa kai gidan babu cikakkiyar sallama saboda bataso daadar tasan tazo,ta nufaci dakin yuuma kanta tsaye.


           Dai dai lokacin da yuuma ke tsaye tana shirin zare hijabinta daga  jikinta bayan ta idar da salla,yayin da anni ke saman abun salla tana lazumi itama.


          Tsorata yuuma tayi da ganin furera a irin wannan lokacin,ta matsa da baya tana amsa sallamarta sanda ta shigo ta yiwa kanta mazauni,tsaf anni ta gane matar,don haka bata katse lazuminta ba sai data cika dari cif sannan ta sauke carbin bayan ta shafa,inna furera ta fara gaidata cikin tsantsar ladabi,anni ta amsa tana dubanta a kaikaice,don tana da tabbacin kome meye ya futo da ita da asussubar fari to ba alkhairi bane.


              Rai rai ta fara jerowa anni maganganun da tun a jiyan ta gama shiryawa kanta game da maimunatu,da dukkan wata siga da zatayi baqi a idanunta,anni na kallon ta,bata ce da ita komai ba hakanan bata dakatar da ita ba,har sai data dasa aya


"Kin gama?" Anni ta tambayeta


"Eh....to shine naga gwara na shaida miki,tunda dai kinga amana ce ta hadamu,bai kamata na rufeki ba kada ubangiji ya tuhumeni,ni kaina yarinyar kaffa kaffa nake da ita da kuma neman maganin tsari daga maita,shine fa kikaga mun kawo har warhaka lafiya lau bata taba kowa a cikinmu ba"


           Sosai yuuma dake zaune daga gefe ta cika tayi famm,fata take annin ta bata dama ta wanke furera mara tsoron Allah data iya kaikaicewa ta yankarowa jininta mummunar qazafi da qarya har haka saboda kawai zallar hassada da baqar zuciya


"Yanzu me kikeso ayi kenan?" Anni ta tambayeta cike da gatse,wanda ita furera bata fahinta ba,sai murna data saukar mata,ta kuma karkace ta gabatar mata da gajenta,bayan ta gama kodata


"Kinga dakata baiwar Allah,kiyi ta kanki kinji,banason wannan soki burutsun,banda ma baki da hankali........idan maimunatu mayya ce ku zaku kubuta ne?,ko ce miki akayi ba wanda yasan alaqarku da ita?" Gumin tashin hankali ne ya yankowa furera,ya akayi wata halitta tasan da wannan?dama kowa kallonta yake kenan?.


"Ai....to,ai dama ita din.....maitarta ta can jikin kakarta ne.....bawai daga ubanmu bane,daga kakarta ne......sai....sai ta tsotsa daga nonon uwarta itama"


"Ke!......ki kiyayeni fa?,wallahi tallahi ina sake jadda miki kiyi ta kanki,yo banda tambadewa irin taki,ina ake irin haka?,to bari kiji na gaya miki,ki kama.kanki,idan ba haka ba in na tashi tafiya billahuwallazi kaf garken maimunatu da uwarta da kika danne kike qafafa dasu sai nasa anyi awon gaba dasu,gwara ki.saita kanki aci gaba da tafiya ahaka,wata shari'ar sai a lahira" sosai jikin inna furere ya dauki bari jin ana shirin yi mata bankada.


         Ta tambayi kanta Wanne tsinannen ne yake fitar mata da sirri haka?,anya ba daadar himu bace?,babu shiri ta kwashi takalmanta a hannu ta fice don anni ta fara daga mata murya.


          Abinda ya sake kada mata hanji kuma shine kallon banzan da daadar himu ta watsa mata sanda sukayi kacibus a tsakar gidan,saita qarasa daburcewa,ko taji abinda yake tafe da ita ne?,don haka ta hadiye gaisuwarta tayi waje,don ta soma zargin daadar cikin ranta,saboda tasan kaf fadin karkarar ita kadai tasan da wannan maganganun.


           Tunda ta idar da sallar asuba tana zaune bata koma ba,lokaci lokaci idanunta suna kan gaje daketa sharbar bacci abinta,babu shiri ko niyyar tashi tare da ita bare ta sauke farali,har yanzu halindai ashe yana nan ta raya hakan cikin ranta.


         Haka kawai tayi sha'awar tashi tayi irin ayyukan data saba yi a baya,don haka ta miqe a hankali,ta zura hannunta inda ta cusa takalmanta watannin baya sanda zata bar gidan,cikin sa'a ta samesu,murmushi ta sake,duk da sun ratattake,suna tuna mata da abubuwa masu yawan gaske da suka gabata,saita miqe dogayen qafafunta da a yanzun suka qara haske suka kuma yi luwai luwai ta zura su,sannan tayo waje.


        Tana fitowa jauro na dawowa daga salla,ta gaidashi cikin girmamawa ya amsa mata cikin kulawa yana tsokanarta kan yau ta tuna kwanan ruga,tana murmushi ta soma aikin gidan,sai gashi ya fito yana tambayarta inda fureran taje


"Ban sani ba kawu,yanzu nima na futo" sai ya jinjina kai,har yayi gaba ya dawo yace mata ta aje aikin ta koma ta kwanta


"Ba komai kawu,hakan yana min dadi" kansa ya jinjina cikin tausayi da qaunar yarinyar,ya shige dakinsa,babu jimawa ya fito da koren hirami na maza jikinsa daya yafa,ya wuce dakinsu,tana jinsa yana rafkar gaje kan ta tashi tayi sallah,kana yayo waje yana ce mata zaije ya dawo,tayi masa a dawo lafiya tana ci gaba da ayyukanta,saidai har ta gams gaje bata futo ba.


         Ganin ta gama saita wuce kanta tsaye zuwa haggo,tun daga nesa take kallon dabbobin cikin kewa da shauqi,tayi matuqar kewarsu ba kadan ba,amma abinda yadan taba ranta ya kuma bata mamaki,yadda yawansu kyau da tsaftarsu suka ragu sosai,taga sabbin fuskoki dake nuna an hayayyafa,to amma indai hakane me ya hana su qara yawa?.


           A nutse taje ta kwance wadanda suke daure,ta zari sandar data gani a jingine a wajen,ta kuma soma korasu cikin nutsuwa da tsohuwar qwarewa zuwa makiyaya.


          Kusan za'a iya cewa kallo ne ya koma sama,duk inda ta wuce dai ta kwashi fiye da rabin hankalin mutanen wajen,wasu da yawa basu ganeta ba,suna mata kallon baquwar fuska,don atamfa ce a jikinta dinkin doguwar riga,ba kayan saqi ba.


          Dukka wajen data saba ta'ammali dashi a wancan lokacin sai data tsaya a wajen tana tuna komai daya wuce,daga qarshe ta dangana da qasan bishiyarta,wadda a yanzun ta qara yawa da rassa,tana shirin zama taji sallama da muryar da ta kasance sananniya a wajenta.


          A nutse ta daga kai tana amsa sallamar,bafullatanin saurayin nan daya taimaki rayuwarta a shekarun baya,himu,shine yau tsaye a gabanta bayan shudewar wasu watannu masu tsaho,yana nan a yadda ta sanshi,saidai kuma yayi rama ba kamar a baya ba da yake da cikar jiki.....Ya tsinke sosai ya qara tsaho,har yanzu wannan murmushin nasa yana nan saman fuskarsa,sai ya tako daura da inda take zaune,ya zauna saman dutsen daya saba zama shima


"Maimunatu....'yammatan birni" maganar data sanya siririn murmushi kubuce mata,ta kuma soma gaidashi,ya amsa mata cikin matuqar kulawa


"Tafiya haka katsam babu bankwana maimunatu?,saidai na laluba naji wayam babu ke?" Har yanzu himu nada wata kima da daraja a ranta,yana kuma cikin jerin mutane masu muhimmanci a rayuwarta


"Kayi haquri,haka tafiyar nima tazomin,kuma a sannan bansan inda zan ganka ba" kai ya gyada,shima yasan da wannan


"Hakane,to yaya bayan rabuwa?,duk da alamu sun nuna komai yana tafiyar miki yadda ya kamata" ya fada kansa tsaye yana hango canji qarara daga wajenta,canjin da yasa ya saare,ya sake kuma sallamawa bayan kunnuwansa sunji ana zancan aurenta da wani.


            Mintuna kadan ya miqe bayan zaman shuru da sukayi shi da ita


"Sallama nazo muyi,saboda nasan ba lallai bane na sake samun dama irin wannan,ban taba kawowa a raina zan rasaki ba,sai gashi qaddara ta wanzar mana da hakan,duk da zuciyata ta soki matuqar so,bazanyi jayayya ba,saboda bansan me Allah ke nufi da hakan ba,kin cancanci samun kyakkyawar rayuwa fiye da wadda nake miki tanadi,ina miki fatan alkhairi a dukka rayuwarki maimunatu" daga haka ya juya ya soma barin wajen.


           "Na gode sosai" abinda ta iya gaya masa kenan tana bin bayansa da kallo,tausayinsa da kuma wani irin yanayi na cika mata zuciya,har ya bacewa ganinta.


         Ko awa guda bata rufa ba inna furera ta aiko kan ta tattaro mata dabbobinta ta dawo mata dasu,tayi hakanne saboda tsoron daya cika zuciyarta kan kada ta rasa dabbobin data qwallafa rai a kansu,fitar da maimunatun tayi dasu sai take ganin kamar wani shiri ne.


No comments

Powered by Blogger.