Gurbin Ido 2

 


Free page 02*



         "Migodake" ta fada a hankali tana sharce ruwan fuskarta,dubanta yayi,ya sakar mata murmushi,wani abu me suna nutsuwa da sanyin halin daya karanta tattare da ita na dan qaramin lokaci yana burgeshi


"Karki damu,ba komai" kai ta jinjina,saita juya tana nufar cikin gidan tana qudundune jikinta waje daya saboda yadda sanyi ya fara ratsata,da alama akwai damuwa kenan,yayin da shi kuma ya juya ya dauki torch dinsa ya fara gangrawa yana barin wajen,saidai sau kusan uku yana waiwayarta kafin ta qule masa yabar ganinta,ya sauke ajiyar zuciya yana maida hankalinsa sosai ga hanya,zuciyarsa na qissima masa ita,tsahon wanzuwarsa a rugar bau taba kula da ita ba,hakanan bai taba ganin macen da Allah ya zubawa kyau me sanyi da tsari irinta ba,ko wacece ita?,da wannan tunanin ya isa kofar wani gida,wanda shi dayane kaf kafin wajen dake dauke da ginin qasa da bulo.


           Babban tsakar gidane daya kasance wayam babu kowa saboda ruwan daketa sauka,yakai dubansa ga dakunan dake jere a tsakar gidan,har ya nufi wani daki daga ciki,sai kuma ya dakata ya juya akalarsa zuwa wani daki dake daura dashi,muqullin ya taba,a rufe dakin yake dole dai ya karbo muqullin,abinda yasa ya juya da dan sassarfa ya nufi daya dakin,yasa hannu ya dage asabarin da aka saukema qofar dakin saboda kaucema shigar ruwa.


         Dumine ya fara dukan fuskarsa kafin hasken fitilar aci bal bal dake dakin ya cika masa idanu,matasan mata ne guda biyu da yaro namiji guda daya zagaye da fitilar,kowannensu d kwanon tuwo a gabansa yana ci,sai babbar mace guda daya da alamu suka nuna mahaifiyarsu ce zaune gefe daya tana dubansu,jikinta nannade da mayafi me kauri,da alama sanyi takeji


"noi saare daada"


"Jam....alhamdulillahi,ina ka tsaya?,inata taraddadi ruwan nan sai daya dakeka" murmushi ya saki


"Zan canza kaya daada,a bani maqulli" hannu ta miqa wata qwarya dake kusa da ita da alama a nan take ajjiye ajjiyenta ta dauko,ta miqawa daya daga cikin yaran


"Nabugol(karbi)" ta fadi,sai yasa hannu ya karba din,sannan ya miqe zuwa inda yayan nasa ke tsaye


Cikin girmama ya miqa masa muqullin yana cewa


"Hamma....." Dakatar dashi yayi


"Micanjato kayaa sadam,ina zuwa"


"To" ya amsa yana murmushi,saboda ya qagu ya bashi labarin dake bakinsa,a nutse ya juya ya fice daga dakin ya sake nufar dakin da yayi nufin shiga dazu.


            Batayi wani hanzari ba wajen isa dakinsu,saboda ta riga data jiqe,kuma koda ta isa dinma tasan bata da wani wajen zama daya wuce bakin qofa,dakinsu ne su biyu,amma kuma ya zama gaba daya kamar mallakin mutum guda,wato 'yar uwarta gaaje.


        Cikin kula da takatsantsan ta dage assabarin dakin,hasken fitilar dake dakin ya bayyana,motsin shigowarta ya sanya matashiyar dake amsa sunan gaje din daga kanta tana dubanta,gabanta akushi ne madaidaici cike da dambu tana ci,wanda shine yawa yawan cimarsu,tuwo ko dambu,ba kasafai zaka gansu da shinkafa ba


Wani kallo ta watsa mata kamar wadda taga qullin kashi


"Dirdutu malama(matsa malama)" tasan neman bala'i ne kawai irin na gaje,amma inda take tsaye ma sam bashi da alaqa da wajen da gajen ke zaune,sai ta matsa gefan don kawai a zauna lpy,ta miqa hannunta zuwa ga wata tsohuwar baqar  jakar bacco dake saqale jikin bango,darajarta wajen maimunatu dai dai yake da akwati a wajen kowa,duk kuwa da cewa duba daya zaka yimata kasan cewa ta sha duniya ta kuma ji jiki,a nan din take ajjiyar duk wani abu nata,duk da dewa ba komai ta mallaka ba face kayan saqinta kala daya da take boyansa saboda sallah ko wani sha'ani idan ya tashi,duk da cewar ita din ba shiga jama'a take ba,rayuwarta na maqale da wani tabo da ya hanata duk wani 'yanci da walwala da kowanne dan adam kan samu,laifin da bata da masaniya a kansa,bata kuma san sanda aka aikatashi ba.


          Kayan jikinta ta zame ta matsesu da kyau daga bakin bukkar tasu,sannan ta dawo ta daura wani fallen zani guda daya da take rufa dashi,ta tara hannu a ruwa bunun dake sauka ta dora alwala,sannan ta dawo ciki ta tada sallah.


          Sallar magrib ce kawai a kanta,saboda koda wajen kiwo bata wasa da sallarta sam,duk da ba ilimin addini gareta ba mai wani zurfi,amma tun kafin takai haka,zamanin da take rayuwa da mahaifiyarta ta koyar da ita yin salla da zarar lokacinta yayi,abu guda daya da ba zata manta da shi ba,ta kuma riqeshi har yau da kyau,kasancewarta mutum da bata da yawan mantuwa da kuma qwaqwalwa mai yawan riqe abu.


         Da kyar takai sallar da takeyi din saboda tsananin yunwa,takai dubanta ga kwanon da gaje ke cin abinci,tuni ta hallakeshi,dan abinda yayi saura a ciki bazai wuce loma biyu ba,ya tabbata bata da abincin dare kenan duk da dan karen yunwan da take ji?,ta rasa wanne irin azanci ne wannan....tare inna ke hada musu abinci ita da gaje,bayan bambancinsu da gajen kwatankwacin bambacin sama da qasa ne,saboda gaje irin mutanen nan ne masu shegen cin abinci,kamar ci suka kawo duniya,duk yawan abinci sai sun tasheshi....yayin da maimunatu ta kasance wata irin mace,duk yawan yunwar da takeji dan abinda zata ci maka bai taka kara ya karya ba,har wani lokacin ma idan kawai nono tafi ganewa tasha shi ko ajiyayyar madara idan tana da sauranta,kusan duk sanda aka hada musu abinci da gaje sai gaje ta kusan cinyewa ko ta cinye ma sannan take tunawa da ita,duk da cewa a yawancin lokuta bar mata take yi,amma duk lokacin data ratso da tsautsayi irin haka tana jin yunwa tofa saidai ta lashi walqiya ko ta nemi ma duk abinda zata ci din,gajen duka duka sa'anni suke da maimunatu,har maimunatun ma ta bata tazarar kwanaki masu dan dama a duniyar.


"Gaje ya baki ragemin ba?"


"Idan kina da wani ma ki qaro min" ta bata amsa tana sude hannu tare da ture kwanon da qafa ta gicciye anan wajen tana sakin gyatsa.


             Fararen idanunta masu sheqi ta dauke daga kan gajen,dan qaramin bakinta mai dauke da jajayen labba yana motsawa kamar zata ce wani abun,saidai ba komai zata fada din ba,zallar bacin rai ne qasan ranta,wanda bata isa ta furta ba,bata jun a daren zata iya runtsawa matuqat bata sanyawa cikinta wani abun ba,ga gajiya da takeji tana nuqurqusar qashinta tare da qaramin zazzabi da taji ya fara lasarta,wanda dama tana tsammanin zuwan nasa.


         Tsam ta miqe tana leqen waje ta qaramin window din cikin ginin bukkar,ruwan yadan sassauta,amma yana sauka kadan kadan da dan qarfinsa,saita dage qofar ta sanyo kai zuwa waje.


        Gabanta na faduwa amma ta daure ta qarasa qofar dakin inna,sallama tayi,shuru ba'a amsa ta ba,ta sake sallama,a sannan aka amsa daga ciki a tsawace


"Wai waye!?"

"N.....nice inna?" Kamar ba za'a fito ba sai kuma ta jiyo motsinta,ta dage labulen ta fito tana mata wani duba daga sama zuwa qasa


"Menene kuma?" Sunkui da kanta maimunatu tayi


"Yunwa nakeji inna"


"Shine kika zo ki cinyeni?" Amsar data sanya maimunatu daga kanta da sauri tana duban innar hadi da girgiza mata kai


"A'ah inna"


"To meye?,bayan kinsan na hada muku abinci da gaje?"


"Ta cinye inna"


"Kina kallonta ta cinye?,to babu wani sauran abinci cikin gidan,saiki kwanta haka,kyaci gobe"


"A'ah,ba za'ayi haka ba" sukaji an fada daga bayansu,rabewa maimunatu tayi gefe daya,ko bata juya ba tasan waye,mutumin da shi kadai yayi saura wanda yake dubanta da idanun rahama,ya qaraso garesu yana sanye da rigar ruwa,da alama dawowarsa gidan kenan.


         Da sauri maimunatu ta karbi kayan hannunsa tana tayashi saukewa hade dayi masa sannu da zuwa,inna na daga tsaye tana zabga mata harara amma bata kulaa da lamarinta,don ba zata iya ganinsa da kayan bata karba masa ba


"Yaya mutum zai kwana da yunwa......ki debar mata cikin nawa mana" tuni ta cika dama tayi fam da yadda yake nuna kulawarsa akan maimunatun,uwa uba kuma ya buda ledar hannunsa ya bata bread cikin tsarabar da yayo


"Wallahi ba zata ci ba....koda abincinka ne kuwa"


"Ka barshi bappa,zanci wannan" maimunatu ta katsesu da sauri,saboda tasan muddin jayayyar taci gaba to la shakka a kanta abun zai qare,inna zata yi mata hukunci ne wanda ba zataji dadinsa ba,sannan babu abinda zai sanya innar ta sauya rantsuwarta,saboda ba wai tsoro ko shakkar bappan take ba,duk da tasanshi farin sani,yana sakar mata ne,saboda kasancewar maimunatu daga tsatsonta ta fito,shi yasa yake dage mata qafa,baya zaqewa cikin al'amarinsu da yawa


"Shikenan,balejam(mu kwana lpy)"


"jam" ta amsa tana juyawa da dan hanzarinta tabar wajen zuwa nasu dakin.


       "Kiji tsoron Allah fulera,kiji tsoron randa Allah zai kamaki da haqqin marainiya" daga haka ya dauka ledarsa ya rab'eta ya wuce ciki,ta bishi da harara,sannan ta sauke idanunta tabi hanyar maimunatun ta wuce da hararar itama har zuwa qofar dakin nasu,sannan taja qwafa tana sakin labulen


"Tsoronka da zanji,rashin godiyar Allah ne yasa baka ganin qoqarina ai,banda ni ma waye zai riqeta?" Taci gaba da mita abinta,saidai ko daga kai bappa jauro baiyi ba bare ya kalleta,idan da sabo ya riga ya saba da halayyarta.


           Saman shimfidarta ta koma ta zauna sannan ta bude ledar biredin,a hankali ta dinga yaga tana turawa,cikin ranta tana godewa Allah da ya turo bappa jauro,da haka zata kwana da tsohuwar yunwarta.


        Yadda biredin ya fara mata go slow a wuya ya sanyaya bisa dole ta miqe cikin raunin da jikinta ya fara yi ta lalubi wani tsohon kofi nata ta tsiyaya ruwa a jallonsu dake dakin,ta sake komawa ta zauna,tana ci tana korawa da ruwan,kafin sannan tuni bacci yayi gaba da gaje,wadda maimunatu bata da tabbacin tayi sallar magariba bare isha'i.


         Jahilci ya sanya gaje da wata ire irensu sam basu baiwa ibadarsu muhimmanci,duk da cewa akwai makarantar islamiyya guda daya tal,wadda anan ake koyarwa da kowa da kowa cikin rugar tasu,maza da mata yara da manya,cikin hobbansa da malaman ahlussunnah sukayi suka kawo musu malami bafulatani irinsu yake zaune dasu.yana koyar dasu,saidai ba kowa bane ya fahimci alfanun hakan ba bare har yace zaije,da yawa wani kallo sukewa makarantar,dai daikunsu ke zuwa.


         Tana da.matuqar buri da kuma sha'awar kasancewarta daliba a makarantar,saidai inama taga lokacin da zai zama rara(saura) a gareta tsahon wuni guda,wanda bata bautar komai,da gar zatayi.amfani dashi ta ziyarci makarantar da sunan daukan karatu,kullum aiki take,babu dare ba rana,ba asabar babu lahadi,kamar yadda babu alhamis babu kuma juma'a,koda makara tar bokonsu dake da dan karen nisa,koda yuashe maimunatu mafarkin zuwanta take,bare wannan dake kurkusa dasu,gaje nada dama mai yawa da zata iya zuwa makarantar,saidai sam ita ba wannan bane a gabanta ba,bata taba ma kwatanta zuwa din ba.


        Dai dai lokacin da gari ya sake daukan shuru bayan daukewar mamakon ruwan saman.....dai dai lokacin da wata iska me sanyi ke kadawa,a wannan lokacin zazzabi ya fara saukar mata,yana murqushe duk wata gaba dake da sauram qwari a jikinta,takurewa tayi sosai waje guda,tana jin yadda zazzabin ke ratsawa ta qashi da tsokar jikinta,a hankali yana saukar mata da sanyi da wani irin radadi,saita cure waje daya,numfashinta na fita da qyar tana kokawa dashi.


       Duk da cewa wannan din ba baqon yanayi bane tare da ita,amma shi ciwo ba'a taba sabo dashi,ta jima cikin wannan yanayin tana kokawa da numfashinta,tana hangen kanta tsakanin rayuwa da mutuwa kafin ubangiji cikin tausayinsa rahamarsa da kuma jin qansa ta fara samun sassauci,numfashinta ya fara komawa dai dai,saidai qirjinta dake riqe da kuma ciwon dake ratsawa cikin jikinta yana sandarta a hankali,har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.



***********


"Maimunatu!.....maimunatu....." Can tsakiyar baccinta....sannan cikin tsakiyar kwanyarta taji ana ambatar sunanta,shurin da aka kaima gefan cikinta shi ya qarasa tabbatar mata da cewa ba cikin duniyar mafarki take ba,abinda ya sanyata zumbur ta miqe daga kwanciyarta,sai kuma ta sanya hannayenta guda biyu ta dafe kanta tana furta


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" saboda wani nauyi da taji kan nata yayi mata,baya ga dan karen ciwon da yake mata


"Ke yafi kamata a jawa innalillahi,akalluɗo(muguwa)" inna dake tsaye bisa kanta ta fada cikin fushi,bata ko motsa ba bare tace wani abu,kanta na qas tana jin yadda zuciyarta ke suya,jikinta ke tsami da kuma ciwo saboda ciwon dake jikinta


"Ananata haala maimunatu?(bakyajin magana maimunatu ko)da kika zo kika kwanta kina barshi,waye zai miki tatsar nonon,waye zai fita da dabbobin?,ko uwarki ce zatazo tayimin?" Idanunta ta runtse,tana jin xafi cikin zuciyarta fiye da kowanne irin zafi,koda wasa bata qaunar inna ta dinga sanyo mahaifiyarta cikin kowanne irin sha'ani ko laifi da zata aikata mata,ta kuma tabbatar ci gaba da shurunta xai bawa innar dama taci gaba da zagin nata ne,don haka cikin murya mai cike da rauni tace


"Minyauɗo inna(bani da lafiya inna)" idanu innar ta qanqance tana dubanta


"Wannan keta shafa,yahudillo durgul,wurtawa(zo ki tafi kiwo,fito)" ta fada a tsawace kamar zata finciko maimunatun.


         Bata da sauran zabin da ya wuce ta miqe din kamar yadda inna fa buqata,duk kuwa da yadda takejin jikinta,ta dafa a hankali ta miqe tsaye,a sanda innar ke mata wani kallo


"Nikam kin zamemin alaqaqai masifa" saita juya ta fita zuwa waje tana zazzaga masifarta,idan lokacin ka shigo gidan zaka tsammaci wani mummunan abu maimuntun ta aikatawa innar.


          Kayanta data saqale.jiya ta miqa hannu cikin juriya ta cirosu,hawaye me dumi ya subuce mata,ta zame zanin jikinta,ta fara shirya kanta a cikinsu,babu batun wanka bare akai ga abinci,dama bata lafiyarta take ba


"Wurtawa fa maimaunatu" ta tsinkayo muryar innar tana fada cikin salo na azalzala


"Mihosh shawai filkul(dan kwali zan dauko)" maimunatun ta fada tana duqawa a hankali ta dauki dan yalolon dan kwalinta ta dora kan sassalkan gashinta dake cure waje daya cikin kitson doka(bijaɗe a fulatance),sannan ta matsa zuwa bakin kofa tana laluben wuffajen ta(asalin rufaffen takalmin da fulani ke amfani dashi wajen kiwo.


         Ba zata iya duqawa ta sakasu yadda ta saba ba,dole sai datakai qasa ta zauna dirshan sannan ta samu damar sanyasu ga qafafuwanta,ta miqe tana riqe da sandarta tana takowa zuwa tsakar gidan nasu iska na kadata.


         Kamar kullum babu kowa a tsakar gidan,daga inna dake can rumfar da suke girki,sai gaje dake zaune tana cin tuwo,tuwon da take da tabbacin da safen akayishi,amma bata da darajar da za'a bata ta sanyawa cikinta,ko don darajar bautar da zata fita yi musu.


          Ganin tuwon ya tuna mata da guntun biredinta na jiya,ta sanya hannu ta dafe qaramar jakar da take daureta a qugunta taji tudunsa tabbacin yana nan,sanna ya fara takawa zuwa ma'adanar dabbobin,muggan kalaman inna sunayi mata rakiya,har zuwa sanda ta kammala kunce na kuncewa,ta kuma fara kadasu suka dauki hanya.


No comments

Powered by Blogger.