Gurbin Ido 19

 


19


*     Saidai shi din haka yake,komai nasa a nutse yake cike da tsari da kuma nutsuwar,yana duban mr denis ne jabir dake jingine da fridge shima yana nazarinsa,cikin kwanakin nan gaba daya aikin ja'afar din kenan,ya dawo da dukka hankalinsa akan

kamfaninsa,ganawa yake tayi da mutane daban daban duka akan kamfanin,wani irin huge change yake gani tatare dashi a dare daya,sau tari yakanyi sha'awar inama ace ja'afar din ya tabbata a haka?,wasu lokutan a baya sai yayi kamar zaici gaba da rayuwarsa kamar kowa,sai kuma abun ya sake tabarbarewa,but surely a wannan karon yana ganin yanayin kamar ya banbamta da na baya,ko wannan din zai dore?.


         Murmushi jabir ya saki,yana dora cup din saman fridge din sanda yaji mr denis na complain kan cewa


"Sir, you didn't say anything since we start the negotiation"  a ransa yake cewa da alama mr denis ja'afar din baqo ne a wajensa,sai ya fara takawa zuwa inda suke zaunen,gab kuma da zai qarasa wayar ja'afar din ta dauki ruri kiran anni ya shigo.


      Da idanu kawai ya kalla wayar,sai da yaga sunan me kiran sannan ya miqa hannu a nutse ya dauka,ya kalli mr denis 


"Excuse me" ya fada da wata deep and husky voice,saidai kuma akwai taushi da laushi daya cika muryar.


           Shi ya fara yiwa annin sallama cikin ginshira da nutsuwa gami da wani irin kamun kai kamar mace,daga can sashen anni ta amsa tana sauke ajiyar zuciya


"Anya?,anya babban mutum?" Anni ta fada tana nuni da yatsanta kamar yana gabanta


"Barka da warhaka anni" yayi fatali da zancanta ya maye gurbinsa da gaisuwa


"Barka kadai,kuna lafiya?"


"Alhamdulillahi,fatan kowa yana lafiya"


"Lafiyar dai da sauqi" anni ta fada zuciyarta fal kewa da kuma rashin dadi kan sauyawarsa


"Subhanallah,wani abu ya faru ne?" Ya tambayeta yana gyara zamansa kadan gami da yamutsa fuskarsa,abinda yasa girarsa dake cike da gashi ta kusan hadewa waje daya


"Mene ma bai faru ba ja'afar?,fisabilillahi.....yanzu ace haka rayuwa zata ci gaba da tafiya" qaramar ajiyar zuciya ya sauke,shi kansa yana damuwa,yana damuwa kan yadda ya kasa moving forward yadda ya kamata,yana damuwa kan damuwar da mutanen nan masu muhimmanci a rayuwarsa ke shiga damuwa saboda shi,yana damuwa da yadda kowa hankalinsa yake kansa,to amma ya zaiyi?,shaheeda ta daban ce,tayi masa wani mummunan tasiri me matuqar qarfi da kaifi a rayuwarsa


"Aci gaba da tayamu da addu'a, everything will be okay in sha Allah" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke


"Addu'a kam ita aketa yi babu fashi,babu kuma kama hannun yaro.....sai yaushe ka shirya dawowa qasarka?" Ta jefa masa tambayar da shi kansa baisan amsarta ba,gani yake kamar bashi da wani sauran zama da zaiyi a qasar


"Ban shiryama hakan ba anni,har yanzu da sauran lokaci" fuska tadan hade kadan


"Kamar yaya ja'afar?,bakasan har yanzu zamanka a nan bashi da wani amfani ba?,idan kuma akwai ka gayamin"ta masa tambyar da salon titsiye,maimakon ya amsa mata sai ya sanya hannu saman kansa yana shafa lallausar sumarsa


"Ina amna?" Kamar tace masa sai yanzu zai tuna da ita?,sai kuma ta bari,don a yanzun babu abinda take da buqata irin dawowarsa


"Dazun maimunatu ta kaita wajen Aishatu"


"okay.......aci gaba da yimin addu'a,ita nafi buqata,am little busy,zan kiraki anni"


"Ja'afar!" Ta kirayeshi da kakkausar murya


"Naam"


"Ina jiran kiranka,akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi dakai,ka tabbatar kome kakeyi ka kirani bayan ka kammalashi" kai ya jinjina,domin annin mutun ce me kima a idanunsa,ba kasafai yake mata kallon kaka ba,yafi mata kallon uwa


"In sha Allah" daga haka suka yanke wayar,yana dan tunani cikin ransa wacce magana zasuyi da annin?,duk da jikinsa ya bashi tatsuniyar gizo dai ba zata wuce ta qoqi ba.


           Sanda yake qoqarin kiran ammansa yaji annin ta kirayi jabir,baisan me take ce masa ba,saidai jabir din ya tashi daga wajen ya fita yana amsa wayar annin.


        Saida amma ta sauke ajiyar zuciya sanda taga kiranja'afar din nata,abune me matuqar wuya ta daga waya ta kirayeshi,saboda zallar kara da yakana irin tata,zamantowarsa dan fari a wajenta,ta ajjiye rigar amna da take ninkewa wadda yarinyar ta cire yanzun ta dauki wayar.


        Kamar ko yaushe cikin girmamawa da qanqan da kai ya gaidata,ta amsa masa cikin nuna kulawa tare da tambayarsa jikinsa,wanda daga nan bata iya qara cewa komai ba,sai shine ya tambayi amna


"Yanzun nan maimunatu tazo ta dauketa suka fita"


"Okay amma" yayi mata sallama yana ajjiye wayar


"Maimunatu,maimunatu dai?,wacece haka?" sai yaji ransa yadan sosu,don yaso jin muryar yarinyar,yayi matuqar kewarta har baisan iyaka ba,yanason yazo ko don ita,amma duk sanda ya ganta tana karya masa gwiwa ne,don tana tuna masa da mahaifiyarsa da kuma 'yar uwar tagwaitakarta.


        Last time da ya kira haka akace tana wajen maimunatu,har kusan sau uku yana kira amma ana sake gaya masa tana wajenta,abinda ba al'adarsa bace maimaita kiran waya,wacece ita din ma?,amsar da baisan ta ba,haka kawai yaji kansa ya dauki zafi,sai ya dubi mr denis


"I heard everything you said,i need a time to think about what we discuss,i will contact you " kai mr denis ya kada masa,sannan ya bashi hannu sukayi musabaha,me denis ya tattare takardunsa ya masa sallama ya fice zuwa qofar gidan,inda PA dinsa ke zaune cikin mota yana jiransa.


          Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa wadda ta fito hade da sassanyan qamshin alawa me taste din mint da baya rabo da ita,hannunsa a saman goshinsa yana murzawa a hankali,ya daga shanyayyun kyawawan idanunsa ya aza kan agogon dake manne a falon,wanda yake nuna lokaci daga qasa kuma kwanan wata.


          Duk rana irin ta yau rana ce da yake tafiya Istanbul ya kwana,washegari ya shiga ziyartar guraren tarihi da suka shafi annabawa da sahabbai,da wahala yayi missing ranar ba tare da yaje ba,abune me muhimmanci cikin rayuwarsa,yana daya daga cikin ababen tarihin da shaheeda ta barwa rayuwarsa,ita ta koya masa hakan,ita ta sanar dashi wanzuwar wajen,sai ya miqe da hanzarinsa dake nuna zallar lafiya da kuma cikar kuzari,ya dauki wayarsa da kuma agogon hannunsa dake saman table ya nufi dakinsa,dai dai lokaci jabir ya dawo falon,yabi hanyar da kallo,sai kawai ya rufa masa baya.


        Goye yarinyar take a bayan maimunatu,suna takowa. Ahankali daga sassan amma zuwa wajen anni,tun sanda ta fuskanci anni waya zatayi ta zame daga dakin,ta kuma fake da dauko amna,hakan tafi nutsuwa da hakan,ko babu komai annin zata sake tayi wayarta yadda ya kamata,tun annin tana qorafi harta saba,indai wannan ne halin maimunatu ne.


       Dariya yarinyar keta yi abinta,hankali kwancw tana jin dadin labarin da maimunatu ke bata.


      Kusan minti goma kenan da dawowarsa cikin gidan,amma bai shiga ciki ba,ya tsaya daga bakin motarsa yana amsa waya,hannunsa dauke da briefcase dinsa da kuma lab coat,harda qarin baqar leda.


         Siririyar muryarta dake cike da wani irin taushi ce ta ratso ta inda yake tsaye,abinda yaja hankalinsa kenan,ya daga kansa a hankali yana dubansu daga inda suke takowa.


       Sanye take da skert high waisted wanda ya kama qugunta ya kuma baje sosai daga qasa,sai wadatacciyar rigarsa me hannu wanda ya tsaya mata iya gwiwar hannunta,kanta lullube yake da mini hijab wanda shima ya taimaka wajen suturce jikinta,saidai kuma yayi matuqar haskata kasancewarsa peach color.


      Samun kansa yayi da binta da kallo,dan qaramin bakinta me siraran tausasan labba suna motsawa,tana da wani irin kyau me sanyi da fusgar hankali,tun ranar da ya fara ganinta ya tantance hakan,ta dauki hankalinsa ta kuma burge shi qwarai,duk da kasancewarsa mutum da ba kasafai mata ke burgeshi ba,bama shi kadai ba,kusan duk haka mazan gidansu suke,dalili da ya sanya ake musu kallon masu jin kai kenan


"La la la,kika yarda kike goyata a bayanki saita karya miki baya?" Maganar haisam ya ratsa kunnenta sanda take shirin giftashi ba tare data kula da tsaiwarsa a wajen ba,hada idanu sukayi,ya bita da murmushi,sai tayi maza ta janye idanunta tana sakin wani qaramin murmushin ba tare da tace komai ba.


      Gyara tsaiwarsa yayi,yana maida wayarsa gaban aljihun rigarsa tare da sake cewa


"Baki gani ta kusa kamoki a qiba?,amna bakisan yanzun kin girma ba,saura kadan ki cika 4years fa" kafada ta noqe tana buya bayan maimunatu sanda yake shirin karbarta,a dole ya haqura da amsar nata,maimunatu ta wuce da ita bayan ta gaidashi,ya amsa yana binta da kallo har sanda ta bacewa ganinsa.


      Cikin jikinta takejin wani iri a duk sanda haisam yake mata irin wannan kallon,batasan ma:anarsa ba,ba kuma tasan dalilinsa ba,ya mata shige da kallon da himunta yake mata,amma dai tana jin nauyi da kunya sosai.


        A dining area suka tadda khadim,shi ya karba amna daga wajenta,ta bashi ba don ta gaji ba,sai don khadim din shima mutumin amna ne na gaske,saidai tun bata isa dakin anni ba sai ga amnan ta sake biyota,ta kama hannuwanta tana dariyar meya hadota da khadim din taga ta bata rai,bata amsa mata ba suka wuce.


      A hankali anni ta ajjiye wayar gefanta tana fidda ajiyar zuciya,dai dai lokacin maimunatu ta shigo dakin,goye da amna a bayanta,kusan wannan al'adarta ce,mtuqar zasu tattaka zuwa wane waje kamar haka sai ta dauketa ta aza a bayanta,dukkaninsu fuskokinsu dauke suke da dariya,da alama wani labarin suke baiwa junansu.


          Idanun anni a kansu,wani abu ya darsu a ranta,kusan tafi kowa jin dadin qulluwar wannan kyakkyawar mu'amalar tsakanin amna da maimunatu,taci gaba da kallonsu a fakaice,farinciki ne shimfide saman fuskarsu,wanda abune da ba kasafai ake ganinsa akan fuskar amna ba,tun daga sanda ta rasa mahaifiyar da 'yar uwarta da suka kwanta ciki daya.


        Kwarin gwiwa gami da yaqini taji yana shigarta,zuciyarta na bata shawarar tunkarar maimunatu,gwara tun yanzun tasan da maganar,tana ganin kamar hakan zaifi dacewa,akan ta samu zanca lokaci daya,amma kuma idan ta aikata hakan maimunatu zata ci gaba da walwalarta da sakewa dasu yadda take a da?,babu gamsashen tabbaci akan hakan,abinda yasa hankalinta yafi karkata da barin maganar a cikinta,har zuwa sanda zata gama magana da ja'afar kan ainihin lokacin da zai dawo cikin ahalinsa.        Ta baya jabir ke kallon ja'afar kadan kadan,cikin ransa yana juya maganar da suka fara yi da anni a kansa.


         Yana tsaye ne yana shirya kansa cikin wasu lafiyayyun suit saqar qasar Italy kamfanin kiton k-50 wine color masu dan haske kadan,agogon hannunsa gold color ne na companyn lange and sohne mai asalin tsada da kyau.


      Bayan ya feshe jikinsa da mayen tattausan turaren bad boy,ya zauna baya a hankali yana saka socks dinsa,sai a sannan jabir yayi magana,ganin cewa tunda ya shigo shi din bai ce masa komai ba


"Ina zaka ne haka a wannan lokacin?" Sai daya daga kai ya dubeshi sannan ya sauke yana ci gaba da sanya safar


"Ka manta yau wacce rana ce?" Dan tunani kadan jabir yayi sannan ya amsashi


"Oh,yeah,amma kamata yayi ka jirani mu fita tare"


"I finished bazan iya jiranka ba,saidai ka sameni a mint garden"


"Alright,ba case" ya fada yana miqewa ya nufi toilet,shi daya ne keda wannan alfarmar a wajen ja'afar din,banda shi din yasan bazai tsaya jiransa ba.


        Kamar yadda yace din kuwa,ya cimmashi a mint garden cafe and bistro,saman table din shi daya ne,yana kurbar coffee din me zafi a hankali yana duban wani sashe na daban, joining dinsa jabir yin yayi,idanunsa kan fuskar ja'afar din kafin ya sauke cup din yana dubansa.


"lokaci yayi fa,daya kamata ace ka sake ajjiye wasu family din da zasu zame maka makwafin wadanda ka rasa" tsaf ja'afar ya daga kai ya kalli jabir,tsahon wasu sakanni kamar bazai amsa ba kafin yace


"Kai ka taba ganin inda GURBIN IDO ya zama idanu?" Tambayar data sanya jabir zuba masa idanu,yana hasashen irin dagar da za'a diba nan gaba kadan,shi da kansa ya qarashe amsar tambayar bayan ya miqe tsaye ya zuba hannayensa a aljihun wandonsa


"Banajin har kawo yau an haifi macen da zata mayemin gurbin shaheeda,ita kadai ce,kuma ta tafi da dukkan abinda zai burgeni daga diya mace" daga haka ya fara takawa sannu a hankali.


         Tabbas jabir ya sani,ba abune mai sauqi ja'afar yaso wata diya mace ba,koda a nesa ne balle nan kusa,ko kafin shigowar shaheeda rayuwarsa,shi din ba irin mutanen nan ne da ake samun soyayyarsu da sauqi ba,bare kuma wannan babban al'amari yazo ya yiwa rayuwarsa karan tsaye.


         A wajen jiran jirgin qasa me tafiya da lantarki ya sameshi,tsaye yana kallon gefensa guda,hannunsa cikin aljihun wandon nasa,duk da yaji takunsa amma bai waiwayo ba,matsawa gaba kadan yayi ya daidaita tsahonsa da nashi,kusan kansu daya,amma ja'afar din ya darashi


"Dole dole ja'afar ka dai daita rayuwarka zuwa yadda take a baya,koda komai bai dawo ba,shekaru uku ba wasa bane,kana tunanin shaheeda zataji dadin wannan halin da ka sanya kanka?,wanda ya mutu ya riga da ya mutu,bazai taba dawowa ba,indai bakayi qoqarin saita kanka ba tabbas nan da lokaci qalilan zaka ji sanarwa daura maka aure,confirm" wani kallo ya juyo ya watsawa jabir,daidai lokacin da jirgin ya tsaya,sai ya taka zuwa gaba sannan yace


"Mafaashi" qaramin murmushi jabir din yayi,sannan yabi bayansa a hankali shima yana amsa masa


"Zaka gani kuwa"

No comments

Powered by Blogger.