Gurbin Ido 17


 *17*


         "Ni ai tuni na samarwa ja'afar matar aure"anni ta fada kanta tsaye,ba tare data jira komai ba ta dora


"Ire irensu unaisa ba daya ba ba biyu ba......amma sun kasa jumuri da juriya da kuma samar mana da abinda mukeso" anni ta fada cikin cikakkiyar nutsuwa da bawa zancan muhimmanci,har yanzu ita dr marwan yake kalla,ganin haka ya sanyata ta dora


"Eh,hakan yasa na sauya shawara bisa hasashen ramatu" nan ta ware masa komai kan hasashen yuuma,da yadda ta gamsu da maganarta,da kuma yadda ya zamana tashin farko maimunatu ce ta fara zuwa mata zuciya da ranta,mizani da ma'aunai masu yawa da maimunatun ta hau taga kuma tabbas ta dave da matsayin matar ja'afar.


         Cikin nuna gamsuwa dr marwan yake gyada kai,dukka hasashen annin dama abinda ta aikata yayi dai dai da nasa ra'ayin


"Saidai duk wanda keson naka yakeson hada jini da kai ba qaramin masoyinki bane,sa'an nan wannan ba shine karon farko da ya nuna sha'awarsa kan hakan ba,to bai kamata mu watsa masa qasa a ido ba,kuma namiji mijin mace  hudu ne ai,fatanmu shine Allah yasa a dace,yasa qarshen matsalar kenan" kai abbi ya gyada


"Gaskiya ne anni,Allah ya saka da alkhairi,ya qara girma"


"Banga abun godiya ba marwan,wajibi na nayi,babu abinda bazanyi ba saboda rayuwar ahalina matuqar bai sabawa shari'a ba,yanzu abu daya ya rage,ja'afar ya dawo cikinmu,koda zai koma sai komai ya dai daita,don ban gamsu mu bashi yaran mutane ya tafi dasu har wata uwa duniya ba"


"Gaskiya ne anni,hakan yayi"


"Shikenan,zan sa a kiramin jabirun ko zuwa anjima ne".


           Dai dai lokacin maimunatu ke fitowa daga dakinta zuwa falon,tayi wankanta ta shirya tsaf bayan baba tabawa ta leqa da safen sun gaisa,ta kuma umarceta da yin wankan,mamaki ne yaketa kasheta,duka duka yaushe tayi wankan jiya?awa nawa ne a tsakani?,duk da hakan bata musa ba tayi kamar yadda baba tabawa ta umarceta,ta kuma shirya kamar jiya,saidai yau din haskenta ya sake fitowa fiye da jiya.


         Da murmushi anni ke kallonta sanda take isowa wajen,daga nesa dasu ta zube har qasa tana gaidasu,abbi baisan wace ba,amma ya amsa mata cikin kulawa kafin ya maida kansa ga labaran qasa da ake gabatarwa a tashar NTA da ya dauki hankalinsa.


          Cikin kulawa anni itama ta amsa


"Ya kwanan baqunta?" Ta tambayeta cikin salon jan mutum a jiki da kuma son ya sake,murmushi kawai tayi mata tana sad da kanta qasa


"Kinsan kitchen ai,leqa kice aishatu tazo,ta taho da qarin plates"


"Toh" maimunatun ta amsa tana miqewa a nutse tayi kitchen din.


        Kafin ta qarasa tadan dinga jiyo hirarraki da alama akwai mutane a kitchen din,ta saka kanta a hankali bakinta dauke da sallama,abinda yaja hankalin amma dake tsaye suna magana da baaba tabawa,hannunta dauke da wata roba tana duba rubutun jiki.


          Waiwayowa tayi,sai suka hada idanu da maimunatu,dan zubawa maimunatun idanu tayi,tana mamakin jin irin muryar data sani daga gareta,amma kuma batasan fuskar ba,bata taba ganinta ba.


          Gaisuwar da take mata ta amsa cikin kulawa,sannan ta maida dubanta ga robar hannun nata,saidai kuma hankalinta naga muryar tata sanda take gayawa baaba tabawa anni ce ta aikota ta kira wata,kasa fadar sunan tayi kai tsaye,saboda suna ne dake da girma da kima a idanunta


"Yanzun bansan wa anni ke nema cikin madafa ba,kin kuma kasa fadi,hala sunan yana da nauyi a wajenki maimunatu" murmushi tayi a takure gami da jin nauyinsu su duka,musamman amma da hakanan taji tayi mata kwarjini.


      Murmushi amma tayi

"Falon zan koma,muje naji wanda ake kira....tabawa qarasa aikinki,idan kin gama ki sameni keda bara'atu a sassana,zaku yimin gyaran wardrobe"


"To in sha Allah" haka suka jero,amma tana gaba maimunatu tana binta a baya,har suka qaraso falon


"Baquwar taki ta kasa faden wanda kk nema anni" amma ta fada tana zama daura da dr cikin shirin serving dinsu abincin data kawo musun,murmushi anni tayi


"Ke na aika ta kiramin,hala kasa fadin sunan tayi" gyada kai amma tayi


"Eh wallahi,anni ina kika samo mana bafullatar usul"


"Daga garinsu ramatu,gata nan don Allah aishatu,inaso a kulamin da ita da kyau,so nake ta zama 'yar gida tamkar su salma"


"In sha Allah"amma ta fada tana dan sake kallon maimunatu kadan,wadda kanta yake qasa har lokacin,sai kuma ta miqe,don a takure take,ba zata iya zama cikinsu ba.


           

          Anni na shirin tsaidata don taci abinci a cikinsu tabawa ta fito ta kirayeta zuwa kitchen,abinda yasa anni ta qyalesu,ta maida kanta ga surukuwarta da danta.


          Cikin yanayi na shaquwa da kuma fahimtar juna suke cin abincin,suna kuma tattaunawa kan lamuran rayuwa wanda suka shafesu,amma na gefe ba tare data sanya musu baki ba,wannan daha daga cikin halayyarta kenan.


        Gab da zasu gama akayi sallama cikin falon,kyakkyawan matashine,yana da white skin hakanan giant ne shi sosai,kamanninsa na zahiri shi da dr Marwan sun bayyana.


        Yayi dressing very neat cike da tsafta kamun kai nutsuwa gami da zallar ilimi,hannunsa daya riqe da lab coat dake bayyana cewa shi din tabbas likita ne,a nutsensa sannan cikin girmamawa ya tube takalman qafarsa ya qaraso falon,ya duqa ya fara gaida anni sannan dr sai amma.


           Kansa yadan shafa kadan da yasha saisaye me kyau


"Anni,zan samu sauran abinci kuwa?" Kai tsaye anni ta kalla amma


"Bakuyi girki ba yau aishatu?"


"Munyi anni,sanda zan fito ma na leqasu suna gab da gamawa,zuwa yanzu nasan sun gama" qaramin tsaki taja


"Shine wannan qaton gardin zaizo ya sani gaba da tambayar abinci?....kaga idan zaka wuce gwara ka wuce,kuci a waje kamar yadda kuka saba,tunda haka kuka zabarwa kanku" dama yasan za'a rina,tsautsayi yasa yayi mata maganar,tun kafin ta tafi adamawa dama taketa rikici dasu,aure kawai takeso wai kowannensu yayi,wani lokaci sai yaji gwara ma dasu JJ suka basa nan,sun huta da ciwon bakinta.


          Idanun dr marwan dake a wajen ya sanyashi miqewa yana sake shafa qeyarsa hadi da cewa


"Allah ya baki haquri"


"O'o'o'o,na kusa yiwa tufkar hanci ai"


"Fitarmin da briefcase din nan,ka cewa muslimu ya tada motar gani nan fitowa" cewar dr marwan,sai haisam ya qarasa ya dauka jakar ya musu sallama ya fice,amma tana masa addu'ar Allah ya tsare.


            Kusan idan da sabo amma ta saba raka dr koda a gaban anni ne,idan ma bata je ba zata ce ita ta tashi taje,don haka yanzun ma ta tako masa har zuwa farfajiyar dake sassan annin


"Da gaske wannan karon anni ta tada wannan rigimar kan yaran nan,gaba dayansu so take a kauda su" rausayar da aki amma tayi


"Eh banga laifinta ba,tunda abinda ya kamata kenan dama ayi,kowannensu ya kamata zuwa yanxu ace bashi kadai bane"


"Musamman ja'afar da yake da buqatuwa ta kowanne bangare" dr ya fada don yasan daya daga cikin abubuwan da amma ke kwana dashi ta tashi dashi ne a cikin ranta,amma kuma yakana da kara ya sanya bata nunawa ko a fuska,amma shi din sau tari yasha jinta cikin tsakiyar dare tana kaiwa Allah kukanta akan matsalar yaron nasu,ya sani dole abun zai tabata sosai ya kuma dameta kamar kowacce irin uwa.


         Kamar yadda ya zata din kuwa fuskarta ta dan sauya daga yadda take a daxun,hakan yasa cikin kulawa ya bata dukka hankalinsa


"A wannan lokaci muna saka rai da fatan samun warwarewar komai,bake daya ba bani kadai ba,kusan duk wanda ke cikin gidan nan ya damu da lamarin,amma kuma addu'ar bawa mumini bata faduwa qasa banza" kai amma ta gyada cike da gamsuwa,koda yaushe shi din mutun ne da yake da qoqarin ganin ya kwantar mata da hankali kan dukkan wani lamari,bawai iya na ja'afar kadai bama


"Idan na dawo akwai maganar da xamu tattauna,duk da ban sani ba wala'alla anni ta shaida miki kafin na dawo din"


"Allah ya tsare hanya,a adawo lafiya"


"Ameen een,zan samu dambun nan kuwa?" Ya fada yana murmushi,cikin nata murmushin ta amsa masa


"Ka cika cikakken bafulatani kai din,zaka samu in sha Allah" da haka yana dariya ya juya ya fice,ita kuma ta koma ciki tana murmushin itama,wani sashen na zuciyarta kuma ya lula ga tunanin dan nata,wanda ta kwashe wasu kwanaki bataji muryarsa ba,abinda a shekarun baya bata saba da hakan daga gareshi ba,komai cunkushewar aiki baya iya tsallake wuni guda baiyi kiranta ba,qaddarar data afkawa rayuwarsa tasa komai ya canza.


****************


         Cikin sati guda rak maimunatu ta gama fahimtar abubuwa masu dama tattare da family din anni kuma familyn dr marwan khalid akko,ba shakka duk tubalin iyalin da nagartaccen uba ma'abocin ilimin addini da kuma aiki dashi ya samar dashi zaka sameshi ya banbamta da sauran ahali ta fuskoki da dama,kowanne mutum cikin gidan yana rayuwa bisa kyakkyawar tarbiyya da suka samu daga mahaifansu,mutane ne masu fahimta gami da sauqin kai da daukar kansu ba komai ba,duk da tarin dukiya da kuma arziqi da Allah ya yiwa mahaifinsu,akwai haduwar jini tsakanin maimunatu da 'yammatan,babu wanda ke nuna mata qyamata ko wani mummunan hali da zai sanya taji babu dadi cikin ranta.


         Gida ne da baya rabo da baqi 'yan uwa family kuma jinin marigayi khalid akko mahaifi gasu dr marwan,mutanen gidan suna da son baqi da son ganin wani baquwar fuska yazo musu,abinda yasa suka kasance masu son jama'a.


          Kusan dukka jama'ar gidan ba mazauna bane,idan ka cire matan gidan da anni,kusan zamansu a gidan kadanne ne idan ba weekends ba,hakan yasa ta fara sabawa da anni sosai da kuma amma,duk da cewa har yanzun bata sake sosai dasu ba,musamman amma da hakanan take jin nauyinta,tafi sakewa dasu laila.


          Bisa shawarar tabawa anni ta daga qafa,ta kuma fasa kiran ja'afar kamar yadda ta tsara,abinda ya karkatar da hankalin annin tasa aka maida maimunatu islamiyya cikin satin,tabawa kuma ta qara da cewa


"Ina ganin haj anni,me zai hana a maidata boko ma?,tunda rannan naji suna hira da laila,da alama meson karatu ce,kuma hakan shine dai dai,ta yadda babu yadda za'ayi babban mutum ya raina zabinki" murmushi anni tayi


"Haka maganarki take,amma kuma tabawa,inaso ne yayi mata hidima da kansa,ya  raineta da kansa,ya kuma san ciwonta,ta yadda kome zaije yazo bazaiyi wasarere da ita ba,banqi shawararki ba,amma zan samar mata wanda zai dinga zuwa gida yana dora mata karatun bokon,har zuwa lokacin da zan fara aiwatar da abubuwan dana tsara,idan yaso shi da kansa ya samar mata duk makarantar da yaga dama,ya kuma cire kudinsa ya biya,hakan nakega sai yafi" kai tabawa ya gyada,lallai ta hangi dabaru masu yawa kan wannan shirin na anni,fatansu dai shine Allah ya tabbatar da alkhairi,ya shige gaba akan dukka lamarin.


          Cikin satin maimunatu ta zama cikakkiyar daliba ta kuma saje da iyalan gidan dr marwan,islamiyya dake layi na biyu dake bayan gidansu,ranar da zata fara zuwa din laila natsaye falon anni hanunta dauke da qur'aninta tana tisa haddar da zata bayar a yau din,maimunatun ta fito sanye da Egyptian hijab dinta har qasa dinkin kalar blue black.


"Wow....ma sha Allah" laila ta fada tana murmushi,idanunta bisa fuskar bafulatana maimunatu,fuskar da zuwa yanzu ta sake washewa,ta fara fresh da ita saboda samun canjin weather da kuma zama waje daya gami da sauyin cima dama makwanci


"Kinga yadda kayan sukayi matuqar karbarki kuwa maimunatu?,kamar don ke aka zaba kalar?" Murmushin nan nata me sanyi ta sakarwa laila,wanda kusan shi ta fiyi yi fiye data yi magana.


           Sai data leqa anni dake dakinta tayi mata sallama,sannan suka fito suka rankaya ita da hafsa da laila din da nadiya,fa'iza da rahama sun rigasu yin gaba,don dama ba kasafai suke jerawa dasu ba.


        Abinda ke bata mamaki yadda duk sanda zasu islamiyyan da qafa suke takawa,duk da cewa idan da sunso jikinsu zasu iya bin motar gidan ya qarasa dasu,amma sam basu damu ba tafiyarsu suke,babu wani girman kai ko jin cewa ubansu wani ne,ko kuma sun fito ne daga babban gida.


*************


        Zaune take cikin qawataccen falon anni,wanda ya wadata da tsafta da kuma qamshi ta ko ina,falon da a yanzu yake qarqashin kulawar maimunatu da bata bari koda tsinke ya sauka a kansa,ita daya ce qwal a falon,sanye take da wani milk high waist skirt na material mai santsi,sai rigarsa ta chiffon material milk color mai torches na brown,fatarta ta sake wani irin haske da kyau,ta kuma yi luwai luwai,duba daya zaka yi mata kasan cews tabbas ta samu nutsuwar zuciya da kuma ruhi a watanni ukun data shafe cikin gidan,saman kanta baby hijab ne da bata rabo dashi ruwan madara kalar skert din jikinta,wanda ya zame daga gaban kanta,ya bayyana lallausar sumar dake kwance daga gaba,kai baka ce akanta akwai manya kalba data roqi laila tayi mata ba,wansa lailan taso taqi matan,saboda sunyi sunyi ta bisu suje saloon da suka tsara zuwa a ranar saboda shirye shiryen bikin da suke a dangin ammi amaryar dr marwan kenan amma maimunatun ta qiya,ba kasafai take zarmewa da kuma zaqewa cikin lamuransu ba,don har yanzu bata saki jiki dasu yadda suke so ba,bawai don tans musu mummunar fahimta ko kuma zato ba,a'ah.....saidai ita din a koda yaushe tafi ganewa tsaiwa iya matsayinta,kada rayuwar ta rudeta ta kuma sanyata mantawa wacece ita.


          Komai dake tattare da maimunatu ya sauya,saidai har yanzun bata bar wasu dabi'u nata ba,saboda gudun manta asali da tushe,kamar yadda bata zubda ko cire duwatsun hannunta ba,hakanan kayan saqinta suna nan,tayi musu kyakkyawar ajiya,kamar yadda lokaci zuwa lokaci idan taji kewar gida ko dabbobinta,take sanyasu a jikinta ta wuni da abinta,su laila suyita tsokanarta,saidai ta bisu da murmushi kawai,kasancewar shine fiye da rabin amsar maganarta.


           Yau din gidan babu yawaitar jama'a sosai,kusan dukka kowa ya fita sha'aninsa,'yan mata matan sun fita wankin kai,anni kuma yau tana daki a kwance,don kwanaki biyu kenan bata da dan jin dadi tana fama da mura,masu aikin dake sassanta kuwa suna kitchen,wasu kuma suna bangarensu suna hutawa,ammi ta fita unguwa itama,sunata shirye shirye da hidimar biki,acan sassan nasu sai amma kawai.


          Yankam farce takeyi abinta da nail cutter,ta bada hankalinta sosai ga yankan,yayin da wani sashe na zuciyarta yayi nisa cikin zurfin tunani,yadda rayuwa ke gara mata,babu mahaifiya bakuma tasan inda mahaifinta yake ba,takan kalli su laila a matsayin 'yan gata gaba da baya,bawai gata na dukiya da daular da suke ciki ba,a'ah,gata na kasantuwarsu suna rayuwa gaban mahaifi mahaifiya kaka harma sa danginsu,sukan burgeta a yawancin lokuta,takanji inama ace tana da wannan gatan.


          Takun tafiya da sauri da asauri da kuma sautin kukan qaramar yarinya cike da rigima ya sanyata daga kanta daga abinda takeyi,ta kuma maida dubanta ga qofar shigowa falon duk da labulayen alfarmar da suka kangeshi daga ganin wanda ke tahowa daga waje,jim kadan me kukan ta bayyana,ta bankada labulen tana shigowa da sauri kamar yadda ta taho.


         Kyakkyawar yarinya ce ta gaske,wankan tarwada,kalar da dukka gidan mutum daya taga yana da ita,sanye da wata irin short sleeve gown mai azabar kyau,qafarta sanye da rufaffen takalmi na mata daya dace da kayan jikinta,kanta mai cike da suma me santsi da laushi kuma an masa wani irin gyara mai kyau da daukar hankali,an qawata shi da ribbons,hannunta daya dauke da wata qatuwar teddy da suka kusa yin kai daya,kai tsaye taci gaba da takowa cikin falon tana kuma kukanta,tare da rarraba idanu da alama akwai wanda take nema.


           Da idanu maimunatu ta bita,kuka take yarinyar da gaske,hawaye shabe shabe kan fuskarta,hakanan kawai tausayinta ya tsirga mata,duk da batasan wacece ba,batasab me akayi mata ba,saita miqa hannu a tausashe ta riqo hannun yarinyar,abinda ya ankarar da ita kenan da wani a falon,ta waiwaya a hankali tana duban maimunatu.


         Murmushi ta sakarwa yarinyar,duk da yadda taji idanun yarinyar har tsakiyar kanta,wasu irin idanu ne da uta masu kyau da daukan idanu,a hankali ta buda bakinta


"yaki,zoki gayamin wane ne?,me akayi miki" ta fadi da taushi cikin sigar lallashi,kai tsaye kuwa yarinyar ta soma takowa zuwa wajen maimuntun,batayi qasa a gwiwa ba ta dorata saman cinyarta kana ta jinginata da jikinta,take yarinyar ta narke jikin nata.


         Dumin jikin yarinyar yasa maimunatun taba wuyata,da alama zazzabi kenan take,saita zagayo da kanta gefan fuskarta


"Waye ya tabaki?,waye ya sakaki kuka?" Ta sake tambayarta kanta tsaye,salon tambayar da alama ya taba zuciyar yarinyar,sai ta saki kuka sosai cikin sheshsheqa tana cewa


"Uncle hisham ne......." 

"Ya isa,yi shuru,indai shine sai mun hukuntashi,ki daina kukan haka,kinji akwai dumi a jikinki kada ya sake qaruwa" maimunatu ta fada tana jin tausayinta ba tare da tasan dalilin hakan ba.


              Qanqameta yarinyar tayi


"Ba za'a yimin allura ba?" Ta tambayi maimunatu tana duban idanunta,murmushi ta sakar mata tana shafa tattausan gashinta


"Babu wanda zai miki allura kinji" ta qarashe maganar tana jan yarinyar cikin jikinta sosai ta rungumeta,sai ta narke itama tana sassauta kukan gami da sakin ajiyar zuciya me qarfi,da alama abinda take buqata dama kenan,tunanin maimunatu yadan cilla wani waje jin yadda yarinyar tayi luf a jikinta tana sauke ajiyar zuciya,kamar tasan fuskar yarinyar a wayoyin al'ummar gidan,kamar tana ganin fuskarta a wajensu.        Tsakiyar tunanin da take aka daga labulen akayi sallama wadda ke cakude da sauti na dariya a tausashe,ta daga kanta a hakali tana amsa sallamar,idanunsu suka sarqe waje guda dame sallamar.


No comments

Powered by Blogger.