Gurbin Ido 13

 


*13*



       Tunda gari ya waye take zaune tangaram tana duban qofa zuwa window,tana lissafa wucewar mintuna da awanni da yatsun hannunta,wucewar kowacce daqiqa bugun zuciyarta ne ke daduwa,ta kalli qullin

kayanta da ba komai bane a ciki illa fararen kayan saqinta,wadanda su daya ne abinda ta mallaka take kuma ji dasu,Sallamar da taji da baqin murya ya tabbatar mata ranar barinta rugar yayi,karon farko da zata fita daga rugar tun sanda suka shigo ita da mahaifiyarta.


        Laulo ne ya leqo yayi kiranta,sai ta miqe riqe da qullinta tabiyo bayansa,saboda tasan cewa abinne yazo wai inji mai tsoron wanka.


         Laila da yuuma ne tsaye a tsakar gidan,lailan cikin ado take dake nuni da zallar ilimi dukiya da kuma wayewa,ta qaraso a hankali ta gaida yuuma dama lailan,dukka suka amsa mata da sakakkiyar murya.


          Sosai inna furera ta kama kunnuwanta,har data dafe gefen fuskarta saboda tsananin zafi


"Banda dauke dauke,banda mugun hali,iya abinda aka kaiki shi zakiyi,kada ki yarda a kawomin qararki,idan haka ta kasance kuwa kashinki ya bushe" kai take gyadawa da sauri don ta samu ta saketa,duka yuuma da laila sai da zuciyarsu ta motsu,saidai kowannensu da sauqi,saboda sunsan taqi kadan ya rage ta rabu da wannan rayuwar .


          Sanda suka qaraso gaban motar tsaye tayi kawai tana qarewa motar kallo,tana qissima yadda zata tsinci kanta a ciki,wai yau itace zata shiga wannan abar?.


"Ki shiga maimunatu,anni na jiranmu" laila ta daga kai daga danna wayar da take ta yiwa maimunatu magana,ajiyar zuciya ta sauke sanda ta shiga motar,saidai gaba daya a takure take saboda rashin sabo,sai da suka koma ta gidan yuuma suka dauko anni sannan suka juya suka nufi hanyar barin rugar gaba daya.


        Duk inda suka gifta sai maimunatu tabi wajen da idanu,tana jin wata kewa tana ratsata tun yanzu,tana jin wani yanayi mara dadi cikin zuciyarta,tana qissima yaushe zata dawo?,yau ko gobe?,ko kuma ta tafi kenan tafiya ta har abada?.


"Ki saki jikinki maimunatu,ki sanya a ranki zaki je kiyi rayuwa ne irin ta kowanne yaro dake gaban mahaifiyarsa" anni ta fada bayan ta karanci damuwa da tunani daya cika kwanya da zuciyar maimunatu,qas tayi da kanta tana jinjinashi,sannan tasa hannu a fakaice ta goge qwallar dake shirin sauko mata,babu abinda yake dawo mata sai wani lokaci can baya da suka baro garinsu na gembu ita da daadarta shatu zuwa wannan rugar,a zahiri rayuwar sam mara dadi ce,to a yanzun gata ra cira daga nan din zuwa wani wajen,an mata bushara da kyautatuwar rayuwarta,to amma kuma sanin haqiqanin yadda zata kaya din sai ubangiji,sanin gaibu sai Allah,ko wacce irin qaddara ce cikin wannan tafiyar kuma?.


_ku biyo alqalamin 'yar mutan huguma_



        Sosai maimunatu ta bude idanunta tana kallon hanya,a wancan lokacin da suka shigo garin akwai qarancin shekaru,shekarunta basu kai haka ba,don haka ta dinga kallon hanya abinta,tun daga cikin rugarsu har suka fito suka dauki hanya dodar.


         Bayan 'yan hirarraki motar ta dauki shiru,bacci yayi gaba da anni,haka ma yahaya,sai ita sai driver,sai laila data nutsu ta tattara hankalinta kan waya,ta karanci yadda laila ke son waya,daga dan qaramin sanin data yi mata,ta saci kallonta kadan sai kuma ta sake maida hankalinta ga titi,tana kallon yadda ubangiji ya shimfida qasarsa.


         Wani sashe na ranta kuma cike yake da mamaki,gashi dai tafiya suke,amma kamar a tsaye suke a waje daya,banda tana ganin yadda suke wuce dazuka da bishiyu tabbas da zata ce ba tafiya suke ba.


            Awa biyu cur sukayi suna tafiya kafin anni ta farka,ta sanya drivern ya shiga dasu cikin wani gari,sukayi sallah,kafin su idar kuma saiga yahaya nan ya shigo musu da takeaway,wanda suka wuce dashi mota,suka dora tafiyarsu.


        Tunda ta karba ledar abincin take hannunta a riqe ba tare da ta ci ba,abinci ne data jima rabonta da irinsa,tama manta lokacin,tun a zamanin da suke muhallinsu ita da mahaifiyarta,cikin ranta take tantamar anya abincinta ne?,bata sake budawa ba saida laila wadda ta gama cin nata ta kalleta


"Ki buda mana maimunatu kici?,ko bakison irinsa?" Dan qaramin murmushi ta saki ta girgiza kai,sai ta buda ledar a hankali,laila ta bita da kallo,wani irin kyau fuskarta ke fitarwa fiye da wanda take dashi duk sa'ad da tayi murmushi,janye idanunta tayi,tana gyara zamanta yadda zataji dadin ci gaba da danne dannenta,zuwa lokacin maimunatu ta fara kaiwa cikinta abincin.


          Yawan wanda yaci sai yasa ta dinga jin kunyar suga ledar,ita kanta tayi mamaki qwarai,amma kuma daga bisani da taga laila sabgarta take a tab dinta,anni kuma ta koma baccinta sai ta sake itama.


         Duk yadda taci burin ganin hanya tun daga adamawa zuwa gombe amma sai da bacci yayi mata tsiya,tana gama cin abincin jikinta ya mutu murus,tsohuwar yunwar data jima a jikinta ta kwanta,tsohuwar gajiya kuma ta shekara da shekaru,basussuka baccin da batasan adadin yawansu ba suka taso mata haiqan,bata shirya ba baccin yayi awon gaba da ita.


*GOMBE STATE*


 *_G R A GOMBE_*

_DR SULAIMAN KUMO ROAD_



_Dr marwan khalid akko residence_



        Katafaren gida ne wanda ya amsa sunansa ta kowacce fuska,irin ginin da aka yishi ba don alfahari fariya ko taqama gami da almubazzaranci ba,gini ne na ma'ana da sanin rayuwa da kuma abinda duniya ke ciki,duba daya zaka yiwa gidan kasan cewa daga zubi da tsarinsa ginin ya zaunu matuqar zaunuwa,hakanan yakan dauki hankalin mafiya yawan jama'a,tun baka ma shiga cikinsa ba.


         Gidane dake dauke da sassa guda hudu,biyu na matan gidan,daya kuma mallakin me gidan,yayin da daya bangaren ya zama mallaki ga mahaifiyar me gidan wato haj maryam Farooq kumo.


       Gaba daya gidan mallakin dr marwan khalid akko ne,babban limamin gombe gaba daya,shararre kuma sanannen dan kasuwa,wanda Allah ya yiwa baiwar arziqi dama dukiya gaba daya,gami da tarin ilimin addinin islama wanda shi ya kaishi ga zama cikakken dr,hakanan ta fannin boko din ma ba'a barshi a baya ba.


        Wani irin mutum ne da Allah ya yiwa baiwar kwarjini da kuma farinjini,mutum ne me amfani da ilimin addininsa ainun,mai yawan taimako sadaka da kuma kyauta ma gaba daya,dukka sirrin nasararsa ya ta'allaqa ne ga mahaifiyarsa,jajirtacciyar uwa da bata daukan raini ko kuma wargi komai qanqani,tsayayya akan 'ya'ya da kuma jikokinta.


           Marwan shine babban d'a a wajen haj maryam anni,hakan ya sanya yayi mata matsuguni cikin gidansa tun bayan rasuwar mahaifinsu,kuma dama shi din mutum ne mai matuqar qaunar mahaifiyarsa


        da kuma qawa zuci,hakan ya sanya itama haj maryam anni ko cikin yaranta tafi ji dashi,duk da cewa dan fari ne ba auta ba,autansu alhj sagir yaso daukarta ganin kamar shi yafi dacewa,amma gaba daya ya hanasu hakan,yace shi yafi cancanta tunda shine babba.


        Matan Dr marwan akko biyu,akwai haj Aishatu,wadda take da yara bakwai dashi,diyarta ta farko macace mai sunan anni wato maryam suna ce mata maama,sai ja'afar d'a na biyu a wajenta,wanda ya zamto halitta mafi soyuwa a wajensu,duka sauran mata ne,salma,hafsa,nadiya,safina,sai autansu namiji khadim,daya dakin kuwa dakin amarya umamatu tana da yara hudu ne,suma din mata ne,fa'iza ce babba,sai khadija,zahra'u,sai mai sunan yuuma rahama suna ce mata baby.


         Tsakanin aishatu da suke kira da amma da kuma umamatu da suke kira da ammy zama ne na fahimtar juna da kuma zaman lafiya dai dai gwargwado,yadda Allah ya dorawa kowa son ja'afar haka ammy ke qaunarsa,shi din dan gidanta ne tun farkon zuwanta gidan,amma kuma ta tattara ta miqa mata shi,shima kuma ya dauketa kamar uwa a gareta.


        *_Ja'afar marwan khalid akko_*



matashin saurayi kuma matuqin jirgin sama,mai jini a jika,wanda Allah ya yiwa baiwar qira ta jiki,bashi sahun dogaye ko kuma gajerun maza, moderate ne,yana da murjajjen jiki mai siffar qarfi dake nuna shi din ma'abocin gym ne,kalar fatarsa ruwan tarwada ce,wadda ta samu kulawa ta gasken gaske take bada wani irin launi mai daukan hankali matuqa,baya tara suma kamar yadda shi din ba ma'abocin yin aski bane,saidai yadda yake barin sumar kansa zuwa habarsa da kuncinsa abun yana da matuqar qayatarwa da kuma daukar hankali,Allah ya zuba masa wani irin mugun kwarjini wanda yake qara masa kyau haiba da kuma cikar kamala,yana da wani irin farinjini na musamman,bawai a wajen mata kawai ba,a'ah.....hatta a wajen al'ummar gari gaba daya.


            Dan gayu ne na gasken gaske,gayu wanda ake kira gayu bawai muna gayu ba,mai tsananin tsafta ne daya tsani qazanta dama qazami,yana da tsari da kuma dokoki da ya sanya ba kowa ke iya mu'amala dashi ba,kamar yadda shima bada kowa yake iya mu'amala ba.


           Miskili ne ajin farko,irin miskilancin da zakayi tunani bebe ne ko kuma kurma,magana ko hira bata daga cikin abubuwan dake burgeshi,abu ne mai wuya ka zauna dashi kaji wata doguwar magana a bakinsa,sau tari yafi ganewa amfani da body language,kamar wani me ciwon baki ko kuma mara lafiya,yana da tsananin kamewa da kuma tsare gida,akwai jinin sarauta sosai cikin jikinsa,hakan ya sanya yake da izza da kuma rashin daukan raini,bai yarda da qasqanci ba,yana da neman na kansa sosai,mahaifiyarsa diya ce ga turakin akko,yana da matuqar girmama na gaba dashi,komai qanqantar shekarun daka bashi,duk da mutane da yawa sun masa shaidar wulaqanci da kuma girman kai.


            Mutum ne mai tsanani ta fannin so ko qi,bai iya so ba,hakanan bai iya qiyayya ba,idan jininku bai hadu ba ka fita a hanyarsa kawai shi yafi maka alkhairi,yana tsananin son mahaifiyarsa fiye da kowacce halitta a duniya,mahaifinsa da kuma anninsa suke da gurbi na biyu,don yakan kasa tantance cikinsu wa yafi so?,sannan gwaggwo sadiya qanwa ga anni,akwai mutanen da yake ganin kima sosai cikin rayuwarsa da zamantakewarsa.


            Jabir shine qawa kuma amini ga ja'afar,d'a ne ga qanin mahaifin ja'afar,mahaifiyarsa ta rasu ta barshi sanda ta haifeshi ko juyawa taga abinda ta haifa bata yi ba,akwai aminci sosai tsakaninta da mahaifiyar jaafar,kuma rana daya aka haifesu,don haka ta dauka jabir ta hada jaafar ta riqesu gaba daya,duk da taso qwarai ta shayar dashi kamar yadda ta shayar da jaafar amma anni ta hana,tace tayi haquri,yasha madara,saboda gudun samun matsala anan gaba,idan hakan ta faru zata haramta masa duk wata 'ya da ita din zata haifa jaafar yace yanaso,ko kuma wata daga cikin 'ya'yan 'yan uwanta,ba'asan kuma me Allah zaiyi ba,dukkansu sun gamsu sun kuma fahimta,taci gaba da bashi madarar,madarar kuma ta amsheshi sosai,ya tashi tubarkall,dashi da jaafar me shan nono babu bambamci,sun tashi tamkar 'yan biyu,don haka ma ake ce musu,akwai matuqar shaquwa da fahimtar juna a tsakaninsu,kowannensu bashi da kamar dan uwansa,dashi yake shawara,shi yake gayawa sirrinsa.


             Farinjinin ja'afar ya sanya yake da tarin 'yammata dake hauka a kanshi,saidai ko sau daya bai taba sha'awar bata lokacinsa akan kowacce yarinya ba,a haka kwarjininsa ya sanya mata da yawa sun hadiye kwadayinsu,don basa iya tunkararsa da zancan soyayya kansu tsaye,masu tsaurin idanu ke biyo ta hannun jabir,to shima jabir din yasan waye ja'afar,kuma dabi'un nasu suna dan kamanceceniya,duk da jabir bashi da miskilanci,saidai yana ararsa a duk sanda yaso,hakan yasa sau tari wasunsu baya ko gayawa ja'afar ma yake barin batun yabi iska.


          A sannan babban burin ja'afar a duniya shine ya zama pilot,dukka hankali nutsuwa da kuma rayuwarsa ya tattarata ne kan karatunsa gaba daya,sanda yake gab da zama pilot,a lokacin da suke komawa gida hutu daga qasar da yake karatu,a filin jirgin sama shaheeda ta fara ganinsa,d'iya ga shugaban malamai na qasa gaba daya,kuma babban limamin masallacin shugaban qasa dake abuja,yarinyar data bala'in mato masa,saidai tasirin tarbiyya data samu ya hanata bayyana masa,tana da kunya da kuma tsananin kamun kai,amma duk da haka ta kasa kanta sakat,sai data gano waye ja'afar din.


         Ta shiga tsananin tashin hankali sanda aka gama karanto mata waye ja'afar?,ta yaya zata shawo kansa?,da wannan tunanin ta dinga rayuwa,haka ta dinga ramewa.


           Kwanaki qalilan da ya rage musu su koma gida daga hutunsu suka giwa dr marwan rakiya abuja shi da jabir zuwa taron musabaqa na kasa da ake gudanarwa acan,a ture yaje bawai don yana so ba,don bai shirya zuwan ba.


         Cikin hall din kansa yana qasa yanata danne danne a wayarsa,yana jin jabir sunata hira da wasu matasa biyu da suka hadu a can,har zuwa sanda aka fara gabatar da musabaqar,bai daga kansa ko sau daya ba,saidai duk wanda yahau zaiyi karatu har ya sauka yana bibiyarsa a zuciyarsa,yana taya alqalan cin gyaransu,don shima Allah ya bashi haddar qur'ani izifi arba'in cif,sauran kuma biye ne da qur'ani.


            Kiran sunan wata daliba da akayi yaji daya daga cikin abokan hirar jabir din yace


"Alhamdlh......ga sister dita din" baiyi niyyar dago da kansa ba,amma jin ana sake maimaita kiran sunanta ganin bata fito ba,sabanin sauran dalibai da kowa ake kiransa sau daya.....shi ya sanyashi daga kansa sanda yaji me kiran sunan ya ajjiye abun maganar alamun ta taso.


            Daga rukunin kujerin dake opposite dinsu ta taso,sanye cikin yalwataccen dogon hijabi har qasa,qafarta da hannunta duka safar hannu ne,baka ganin komai nata sai kyakkyawar fuskarta wanda nutsuwa ke kwance samanta.


         Kansa ya dauke ya maida ga wayarsa,amma sai ya samu kansa da dakon jin nata karatun,ta daidaita zamanta aka tambayeta wacce qira'a take amfani da ita,ta fada,mai jan karatun ya janyo mata sannan aka bata damar ci gaba.


               Gaba daya hall din sai daya dauki shuru sanda tayi bismillah,zazzaqar muryarta ta karade hall din cikin kyakkyawan sauti da qira'a,wanda tunda aka fara ba'ayi mata gyara har ta dire,kabarbarin mutane da yawa data burge suka dinga fitowa daga bakunan jama'a


No comments

Powered by Blogger.