Gidan Aro 29

 


*29*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Feenah Ta dubi Meema data tsareta da idanu, sai kuma ta girgiza kai tace “I don’t know.. Ban Sani ba Meema.. I.. I’m feeling restless. Ina son sanin wani hali Mu’azzam ke ciki.”


Meema ta d’an rausayar da idanu tace “Idan dan wannan ne kar ki wani dami kanki, Kinsan halinsa ya iya bada mamaki yanzu zaki iya ganinsa a cikin gidan nan kaman babu wani abinda ya faru.. Com’on chill, ki daina damuwa Ya Mu’azzam fah ba yaro bane balle ace za’a saka masa ido dan bai dawo gida ba.. Magidanci dashi mutum da gidansa, na tabbata yana can gidan naku Kinsan ba’a sona zuba kaya a gida sannan a barshi haka nan babu kowa.. Balle ma kin sansa kinsan halinsa, Kinsan yada yake abubuwansa ba tareda ya saka kowa ciki ba ko ya fad’a ma wani.. Bari ma yanzu zamuje da Aunty Shemau wanka kawai zanyi zamu kai wasu kayayyakin.. And you’ll see zamu tadda Ya Mu’azzam can yana jiran isowarki..” Ta k’arashe cikin k’ok’arin kwantar da hankalin ‘yaruwar tata.


Feenah ta murmusa tana Ware idanu “Ok akwai wasu frames da zan baki a tafi dasu please..”


“Tau amaryar Yaya..” Meema tace tana kashe mata idanu.


Sauri sauri Meema ta wuce tai wanka tana fad’ima Kiki ta jirata su had’a hanya tinda lesson ne take zuwa ba latti zatai ba.


Hakan kuwa akai, breakfast ma sama sama Meema taci sai shirya sauran kayayyanki da za’a tafima Safeenah dasu take.


Aunty Shemau tace ta fara gaba tabi Kiki tinda Mu’azzam na gidan ba sai an tsaya neman key ba. Ita zata Zo da wasu kayan daga baya, yanzun akwai wani shirin da zataima Safeenah ne na musamman shisa.


Gidan Amarya mai Farin jini kowa San zuwa yake ko yaya ne. Kiki ta dubi Aunty Shemau tace “Aunty nima zuwa Zanyi..”


Aunty Shemau tace “Toh makarantar fah..?”


“Aunty dan Allah zanje ai bazanyi latti ba, lesson ne kawai kuma sai 10am ma a fara, idan yaso daga can na wuce.”

Kiki tace tana turo baki gaba.


Aunty Shemau tace “Toh shikenan sai ku tafi da Spices d’in nan..” Tai maganar tana mik’owa Kiki basket na spices da za’a Kai gidan Safeenar. Kiki ta saki baki tana duban tulin spices d’in.. Ta saci kallon Safeenah dake zaune parlo k’afafu mike tana shafa wayarta. Kwantar da murya tai tana kare bakinta kad’an alamun bataso Safeenah Ta jita “Chabd’in.! Aunty ma waye za’a kai spices d’in nan.. Toh wllhi saidai su gaji suyi K’warai dan dai Addah Feenah ba girki take ba..”

Muryar Safeenah suka sinkayo tana fad’in “I heard what you said Baby sis.. And yes Cooking is not my thing, Allah yasa akwai eateries a garin zamu saya..”


Kiki ta dubi Aunty Shemau tana tab’e baki alamun kinji dai da kunnenki..


Aunty Shemau tace “Shige maza kuje k’yaleni da Addarku zamuyi magana.”


Kiki ta d’au books d’inta da hannu guda d’aya hannun basket d’in spices d’in ne.

Nan suka fice driver ya tuk’asu.


**


A can gidan Mu’azzam kaw shirinsa ya ida cikin suit d’insa ruwan toka dan yau yake reporting back to work bayan dakatar dashi da akai na d’an lokaci.


Ya ida d’aura agogonsa k’irar Rolex, ya gyara zaman suit d’in kafin ya fito, k’amshin nan nasa sai tashi yake, ya dubi k’ofar d’akinta yana tina kalan draman da sukai a daren jiya kafin tai bacci, from nowhere yaji murmushi na kufce masa still idanunsa naga k’ofar d’akin. Stubbornness d’inta yake tinawa, zai iya cewa bai tab’a cin karo da stubborn person iri ta ba tsawon rayuwarsa.. 

Lokaci guda yasa kai zai wuce, Sai ya kuma duban k’ofar d’akin. A hankali ya furta “Should I tell her or not..?” Gajeren tsaki yai kafin yasa kai zai shige.


Muryarta ya sinkayo tana bugun k’ofar daga cikin d’akin tana fad’in “Please let me out.. I beg of you please.. Have mercy.. Just let me out please..!” 


Ya lumshe idanunsa a hankali kafin ya isa ya bud’e k’ofar d’akin.


Kuka take tana had’e hannayenta tana rok’onsa ya taimaka ya barta ta tafi.


Shiru yai yana dubanta, idanunta duk sun kumbura alamun taci kuka, ya d’an fuzar da fuci yana shafa sumarsa dake Ta faman shining “Look, honestly I don’t want to be seeing you like this.. You are forcing me to be hard on you..Idan kikabi abun da nace miki zamu zauna lafiya a gidan nan har ki gama mission d’inki  ki kama gabanki.. I told you gidan nan ba gidanki bane GIDAN ARO ne.. Anytime soon zaki tafi idan kikabi duk abubuwan da nake fad’a miki.. Amma taurin kunnenki da tsiwarki babu abinda zasu jawo miki face tsawon jimawarki a gidan nan.. It’s pretty dangerous out there.. Especially for you. Ki zauna a nan ni na fad’a miki we’ll save your family.. Just trust me on this one..”


Ya d’an duba agogon hannunsa kafin yace “Zan wuce aiki yanzu.. Ki tsaya a nan kar ki fita ko Ina kinji koh.. And make sure you eat something..” Daga haka Sa kai yai ya nufo k’asa.


Sadiya tabi bayansa da kallo hawaye na gangaro mata.. Ganin zai fice daga parlorn ya sanyata saurin nufosa k’asa itama.. Ta kamo suit d’insa daidai lokacin da ya bud’e k’ofar parlorn.


“Please kaje dani.. I want to look for them myself... They are all I have..” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya.


Saida ya d’ibi lokaci yana dubanta kafin ya gyara tsayuwarsa yace “Are you a Detective now..?” 

Shiru bata basa amsa ba sai hawayen da take 


Ya kuma furta “Do you want me to register you to the police academy..?” 


Nan ma shiru bata amsa sa ba..


Ya jinjina kai yace “Idan kika kuskura kika fita sai na miki register a makarantar ‘Yansanda.. Kuma ki gwada fita ki gani.. Kinsan tsaf zan aikata..”


Cikin kuka take furta “Dan Allah ka fahimceni .. Sud’in sukenan ahalina bani da kowa sai su..”


Cikin k’osawa ya rausayar da idanunsa. Lokaci guda ya finciki suit d’insa daga rik’on datai masa “You are so strong headed.. How do you want me to explain the situation you are in.. Da alama bakisan wani yanayi rayuwarki ke ciki ba. Do you want to get hurt..? Do you want to get killed..? Do you want to put your loved ones at risk...?”


Cikin tsananin kuka Ta katsesa da fad’in “They are already in danger.. And it’s all because of me.. Ni na janyo ma ahalina duk halinda suka tsinci kansu ciki domin kuwa kafin na had’u da Sagir cikin kwanciyar hankali muke.. Bamusan tashin hankali ba..”


Katseta yai da fad’in “You should know...!” Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubanta yanda Yai maganar a tsawace.


Lokaci guda yaci gaba da jinjina kai  yana furta “This is what you get when you approach life materialistically..!” 


Sai ta kwantar da kanta tana mai jin nauyi da kunyan kalamansa, domin kuwa abinda ya fad’i haka d’in ne. One shouldn’t approach life materialistically.. Garin son abun duniyarta ya kaita tayi tarayya da D’antadda irin Sagir wanda ba ita kad’ai abun ya tsaya ba har kan ahalinta.. Sun rasa kwanciyar hankali da Farin cikin ahali...


Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. A hankali taci gaba da furta “What if you couldn’t find them.. What if kafin ‘yansanda su cimmasu wani abin ya samesu.. Do you think I’d be able to bear it.. I know you don’t care about me or anyone else.. You only care about your mission.. Now you let me go and find my family.. Please..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin rab’awa ta gefensa.


Fincikota yai ta dawo cikin jikinsa.. Ya rik’eta da k’arfi tana k’ok’arin k’wacewa tana fad’in ya barta ta tafi.. Bai saketa ba saima dad’a matseta da yai..


Tana kuka nan cikin k’irjinsa.. Haka dan dole tai lak’was cikin k’irjinsa tana kuka mai tab’a zuciya.


Harga Allah sosai zuciyarsa ke masa zafi.  Ya sani he doesn’t give a Damn about how she feels. Amma Sai ya kwantar da murya yana lallashinta wanda zaice baima San yana yin hakan ba. Shi kukan nata ne baison ji bai masa dad’i, haushi kukan nata ke basa musamman idan ya tina biye biyen mazan da tai duk akan abin duniya.. Balle Sagir da aka tsinci gawarsa da k’anwarsa Allah kad’Ai yasan sau nawa ta bada kanta ma D’antaddan nan tinda gashi har aure zasuyi.

Ya rintse idanunsa yana jin zuciyarsa na masa wani irin k’una. Fuzar da fuci mai zafi yai kafin ya soma shafa gadon bayanta a hankali irin yanda ake ma yara idan suna kuka. 


Cikin kwantar da murya yake  fad’in “Everything will be alright I promise you.. Hush now.!” 

Idanunta a lumshe tana hawaye yayinda shima idanun nasa a lumshe suke, su duka biyun suna jin bugun zuciyar junansu.



A can gate kuwa su Meema ne sai fama da D’ansandan dake bakin gate suke dan Mu’azzam ya kawo police guda d’aya ya saka a gate, ko Sadiya dake cikin gidan ma bata San da Police d’in ba dan a yammacin Jiya Mu’azzam ya kawosa.


D’ansandan ya d’anyi gyaran murya yana duban Meema “I was interested not to let anyone in.. Miss kuyi hak’uri nayita kiran wayar oga bai d’aga ba balle na sanar dashi zuwanku.. He must be busy at the moment..”


Harara Meema ta aika masa tace “Do you want to lose your job.. Ka kuwa San su waye mu.. We are his sisters.. You must let us in ka fahimta..”


Zai sake magana Meema ta bangajesa tana fad’in “Dalla kaucewa mutane a hanya we are not scared  of your gun.. Kiki shige muje..”

Ta k’arashe tana janyo  k’anwarta.


Kiki ta juyo ta masa gwalo kafin suka nufi cikin gidan Meema tana fad’in “Karnuka sun daina masa Gadi kenan ya d’auko mutum D’anuwansa D’ansanda.. Ai wllhi shegun karnukan nan dama nace Addah Feenah tana tarewa zamu sakawa shegu poison duk suci su mutu.” 


Birki tai tana hango k’ofan parlorn bud’e ya mutane tsaye rungume cikin juna idanunsu a lumshe.


Tai saurin rik’o Kiki dake k’ok’arin tura kai, ta tareta tana nuna mata abinda ta gani hannunta har rawa yake.


Kiki ta saki baki tana gyara medicated glass na k’ara k’arfin gani dake mak’ale idanunta.


A hankali take furta “Meema.. Ya Mu’azzam ne rungume da wata.. But Who’s she..?”


Meema ma ta kwantar da murya tace “How would I know.. Yanzu fah muka Zo tare dake..”


Kiki ta soma k’ok’arin jada baya tana fad’in “We didn’t see anything Zo mu tafi before he sees us.. I’m sure idan ya ganmu harbemu zaiyi.. Let’s leave now Meema.” Ta k’arashe cikin tsananin tsoro tana janyo Meemar.


Meema tai saurin jinjina kai tana fad’in “Yeah.. Let’s go now..!”


Juyawan da zasuyi Karnukan dake rufe cikin d’akunansu suka soma haushi alamun sunji mutane.. Wanda hakan shi ya janyo hankalin Mu’azzam ya ware idanunsa.. A guje su Meema suka fice dan bayansu kawai ya hango suna gudu sun nufi gate.


Ya k’arasa ya zaunar da Sadiya saman kujera, rik’eda arms  d’inta yake fad’in “Don’t go anywhere kinji koh.. Idan kika fita kuma Allah yana ganinki kuma kin sab’a dokan mijinki..” Yai maganar yana d’an duban sama da idanunsa.


Bata iya ce masa komai ba Sai sadda kanta k’asa da tai.


Lokaci guda ya janyo k’ofar parlorn ya rufe kafin ya nufi gate d’in.. Nan police d’in dake tsaye gate d’in ya soma tuba yana fad’in “Sir I did everything I could to stop them, but they wouldn’t listen.. I’m sorry Sir.”


Mu’azzam ya jinjina kai a hankali hannayensa saman kunkumi “It’s alright.. Kar ka bar wani ya shiga sannan kar ka barta ta fice ita kad’ai..”

Har ya soma tafiya ya kuma juyowa yace “Don’t go anywhere..”


Jinina Kai yai yana sara masa “Yes, Sir. A dawo lafiya Sir.” Yai maganar sanda Mu’azzam ya nufi motarsa.


**


Cikin tsanaki Sabeera take parking kayanta dan Washe gari suke tafiya Dutse. Lokaci guda tana tina tattaunawarsu da Sadiya a yau d’in.. Tai gajeren tsaki tana tina sanda Sadiyar ke sanar da ita irin auren da tai “‘Yar rainin hankali ta bata auri wannan D’ansandan ba da yanzu tana gidan nan tareda Babana..” Aya tai ma kalaman nata sakamakon abinda taji hannunta ya tab’a cikin drawer d’in nata.. Lokaci guda taci gaba da lalumen abun har ta ciro shi.. Waya ce k’aramar Nokia.. K’irjinta yai wani irin bugawa tana mai kame bakinta da duka hannayenta biyu.. Take ta soma tino abinda ya faru.. Ranan da Sagir da Sadiya sukai firan k’arshe a gidansu Sagir ya mance k’aramar wayarsa a gidansu Sabeeran yanda sukai zance shida Sadiya.. Sabeera ta d’aga ta ajiye da k’udirin Washe gari zata dank’awa Sadiya.. Tabbas ta mance har dai tashin hankalin rashin Sagir ya riskesu..


Sabeera ta kame bakinta tana kuma juya wayar.. Tinani ta somayi kodai ta jefa wayar cikin toilet ne tai flushing d’inta.. Bata fatan abinda zai had’ata da wannan jarababben d’antadda wanda har bayan mutuwarsa duk wanda suka rab’esa basu tsira ba.. Tayi imani idan Jami’an tsaro suka samu wayar hannunta zata iya jefa kanta cikin matsala.. Take taji zuciyarta tafi aminta da ta jefar da wayar koma ta farfasa kar ta kaiwa jami’an tsaro ta jefa kanta da ahalinta cikin matsala kaman yanda Sadiya Ta fad’a matsala duk a dalilin tarayyarta da Sagir. Da wannan tunani Sabeera ta mak’ale wayar bakin skirt d’inta tana mai ci gaba da tattare kayanta.


**


Gaba d’aya gidan anyi carko carko babu mai iya zuwa kan Safeenah sabida buge buge da take ta famanyi.


Kuka take tana fad’in “Mommy wllhi sai na kasheta.. Whoever she is Sai nayi ajalinta.. Mommy mace ya d’auka yakai gidan aurena yana cin amanata da ita..? Mommy wllhi yau ko wacece ita sai tayi datasanin zuwanta duniya.. Sai ta tsinewa uwar data haifota duniya har ta d’aura ido kan mijina..!”


.. Ala dole Musaddiq ya rik’e Safeenah daketa faman buge buge tana hauka tana fad’in sai ta kashe Karuwar da Mu’azzam ya kai mata gida tin kafin ta tare.. Dan ma daga bacci yake hayaniyar ya tadashi.


Fad’i yake “Ke Feenah get your act together ki daina wa mutane wannan haukan..!”


Safeenah Ta fincike tana mai ci gaba da fad’in “Na rantse da Allah Mommy ko wacece ita sai tayi danasani.. Idan kuma ba haka ba wllhi Sunana  ba Safeenah Gamji ba..!”


Mommy fad’i take ba ita kad’ai zaki kar ba harda shi babban minafikin Mu’azzam.. Bayan duk abinda na masa shida uwarsa a rayuwa babban butulcin da zai saka mana dashi kenan.. Bari Daddyn naku ya shigo yau sai muga bayan waye zai bi..!”


Cikin tsananin b’acin rai Musaddiq da aka barsa shi kad’ai tsakiyan mata ya daka masu tsawa gaba d’aya “That’s enough Mommy..! Bai kamata wad’ann yaran suzo Su fad’i magana ku d’auka ba Sai abi komai sannu a hankali a jira Mu’azzam yazo ba wai ku taru kuyita hauka ba..”


Katsesa Mommy tai cikin tsananin fushi “Kamin shiru kaima babban minafikin ne waya sani ko kana sane ma da abinda yake baka tab’a sanar da kowa ba.. Meema da Kiki ba k’Arya zasu masa ba.. Bak’in azzalumi maci amana.. Ni ko a labarai ban tab’a jin irin wannan cin amanar ba ka d’auki Karuwa ka tare da ita a cikin gidan matarka wacce ko tarewa batai ba.. Da kayan d’akin Safeenah ya tare da Karuwa sabida shi ya cika babban tantiri babu mai saka sa babu mai hanasa.”


Meema dake lab’e gefe tai tsulum tace “Mommy wllhi wllhi na rantse da Allah rungume da mace muka kamasa cikin gidan kuma harda police ya saka a gate babu mai shiga. Da muka tambayi Police d’in dake gate d’in ma ce mana yai Wai Oga yana Busy baiso a damesa..”


Musaddiq ya nufota a kufule ya kasheta da wani wawan mari “Ke waye sa’anki a nan zan b’abb’allaki na karerayaki naga k’arshen rashin kunyarki..” 


Meema ta saki ihu tana kame fuskarta.. 


Mommy ta finciko Musaddiq tana fad’in “Kar ka sake dukar mun yarinya.. Gaskiya take fad’i.. Idan ma babu mai yarda da zancen Meema ai Kiki bazatayi k’arya ba tinda kowa ya mata shaida a gidan nan.. Kai kake rufa masa asiri waya sani ma ko tare kukeyi..”


Da tsananin mamaki kurum Musaddiq yake duban Mommy wacce Ta rufe idanu gaba d’aya ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.


Aunty Shemau tace “Toh Wai ni uban mi ake jira da baza’a tafi gidan Safeenar ba a fidda yarinyar ko a mik’ata ma hukumar ‘yansanda.”


Mommy tace “Kin mance shi shafeffe da mai d’in gadaransa kenan shi ga D’ansanda.. Maras mutunci butulu..! Wllhi yau ko Headquarters za’a d’aga sai anbi mun hakkin d’iyata.’”


Daidai nan Daddy ya shigo ana tsaka da hatsaniyar.


Safeenah ta nufi Daddy tana kuka cikin yanayin tausayi tana kuma d’ingile k’afarta mai ciwo yanda za’aji tausayinta sosai “Daddy mutuwa zanyi.. Zan mutu Daddy Mu’azzam ya cuceni yaci amanata Daddy.. Daddy karuwai yake kaiwa Gidana shiyasa yak’i na tare..”


“Safeenah..?” Daddy ya kira sunanta da mamaki kafin ya k’arada “ Mai kike fad’i haka.. Mai Kike fad’i kenan.. Lafiyarki.?” Daddy yace cikin d’an tsawatarwa.


Mommy tai karaf tace “Abinda kaji gaskiya ne.. D’an D’anuwanka D’an matarka azzalumi ne kuma maha’inci ne.. Gidan Safeenah da ko tarewa cikinsa batai ba yake d’iban karuwai yana kaiwa ba dole yace kar a kai masa Safeenah ba tinda yanada wad’anda zaike kaiwa.. Wllhi wllhi sai anbi ma d’iyata hakkinta.. Wllhi idan ta kama mu makasa a kotu ne zamu tafi.. K’aryar Kakin Dansanda yake..!” 


“Ina Mu’azzam d’in..?” Daddy yace yana duban Safeenah.


“Yana can tare da ita Daddy.. Tare suka kwana a gidan Daddy kuma wllhi tare suke kwana.. Nasan wannan Police Woman d’in ce dama budurwarsa ce..”


Meema da zafin marin da aka mata ko d’aukuwa baiba ta kuma bud’e baki tace “Wllhi wannan watace daban ba police woman d’in bace..” Ta k’arashe maganar tana ci gaba da kukan marinta..


Musaddiq ya kuma yiwa kanta yana fad’in idan bata daina saka baki ana magana ba Sai ya karyata.


“Toh sannu makaryi sai ka karyata mu gani..!” Mommy ta katsesa da fad’in haka.


Musaddiq ya dubi Meema yace “Ke bar nan kafin na takaki..!” 


Mommy Ta janyota tana fad’in “Babu yanda zataje ko kotu akaje akwai shaida kuma Meema ce shaida ehe..! Bazai yuwu na nik’a gari na tafi har Dubai naima Safeenah sayyan kayan d’aki wata ‘yar iska can Ta rigata kwana saman gadonta ba ehe..!”


Daddy ya girgiza kai yana duban Musaddiq “Kira mun D’anuwanka a waya..” Daddy yace yana duban Musaddiq d’in.


“Alright Daddy.” Musaddiq ya amsa kafin ya soma dialing layin Mu’azzam yana aikawa mutanen dake parlorn mugun kallo idan ka cire Daddy.



Aunty Shemau ta kamo Safeenah da k’yar ta zaunarta saman kujera tana fad’in ta zauna ta huta duba da yanayin ciwon dake k’afarta.


Ana haka Mu’azzam ya shigo yana takunsa cikin nastuwa kaman babu abindake faruwa.

Duk suka zuba masa idanu suna dubansa. 


Wani zabura Safeenah tai tana mai kuma fashewa da wani irin kuka.




SameenaAleeyou📚

No comments

Powered by Blogger.