Gidan Aro 26


*26*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽

Rigar nata ta maida dikda cewa bai bushe ba, Allah ya gani bazata saka kayan da yace ta saka ba. Ta window take hangensa yana tsaye jikin motarsa waya mak’ale kunnensa. Tai tsuka a hankali tana tinanin ina zai kaita..

Allah yasa gajiya yai da zamanta a gidan, Allah yasa gida zai maidata wajen Ummanta. Wannan tinanin ne ya d’arsu a zuciyarta. Haka ta nufo waje sai rawan d’ari take dan harta hijab d’in ma da danshi jikinsa.


Da mugun mamaki yake kallonta, ya rasa wane irin taurin kunne take dashi, watau dai baza’a fad’a mata abu tai ba. Katse wayar yai yana dubanta yanda take k’ok’arin k’arasowa bakinta a ture tana kallon k’asa.


“Ke, Meye haka..?” Ya fad’i yana dubanta.


“Mene kenan..?” Ta tambaya tana d’an dubansa itama fuska a dame.


“Bance miki kar ki saka jik’akk’en kayan nan ba.. Do you want to fall sick.?”


Tab’e baki tai kad’an tace “Idan ma nayi rashin lafiyar ai jikina ne..”


Ya jinjina kai yana dubanta, a hankali ya furta “She’s so stubborn..” Ya d’ago yana dubanta kafin ya bud’e murya yace “And waye kike tinanin zai d’auki asaran saya miki magani.. Wuce kije ki canza kayan nan or else..”


“No I won’t change.. Kayana kenan..!” Ta fad’i tana mak’e kafad’a still tana rawar sanyi dan a lokacin ma hadari ne a garin iska na kad’awa.


Fuzar da huci yai kad’an kafin ya nufota, kafin ta ankara ya shiga janyo hannunta.. Tarjewa take tana fad’in “Malam ni ka sakeni.. Ni bazan saka wasu kaya ba bayan na jikina.. Bana so kuma bazan saka ba.”


Bakinta bai mutu ba haka nan shima Mu’azzam bai fasa janyota ba har suka shigo cikin d’akin. Tana gani ya bud’e wardrobe ya ciro wata Doguwar riga abaya kalan shud’i. Ta soma matsawa da baya ganin yana nufota.


Cikin rawar murya take furta “What are you doing.? Don’t come near me.. Dan Allah kayi hak’uri ka k’yaleni..” Ta k’arashe cikin rawar murya tana kuma matsawa baya.


Fuzgota yai ta fad’o cikin jikinsa fuskokinsu suka had’e waje guda.. Jikinta sosai ya soma rawa.. Ta shiga k’ok’arin turasa amma Ta kasa.. Kafin ta ankara taji hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa..


Kuka Ta soma tana girgiza masa kai “Please don’t.. Please..!” Tai maganar tana mai rintse idanunta jikinta bai daina rawa ba.


Mu’azzam kaw fuskarta yake duba musamman idanunta da ta rintse su da kuma bakinta da take motsawa a hankali tana rok’onsa ya k’yaleta.  

A ransa yace ga tsoro ga tsaurin ido.


Jin ya tsaya Cak ya dena abinda yake ya sanyata tattaro sauran k’arfinta tai k’ok’arin turasa.. Aiko nan yai losing balance saidai bai yarda ya fad’a kan gadon shi kad’ai ba fuzgo hannunta yai suka fad’o gadon tare k’irajensu suka had’e waje guda.

Su duka biyun suna iya jin bugun zuciyar junansu.. Jikin Sadiya yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata. Tai azaman mik’ewa amma sai taji ya rik’eta ya hanata tashi.


Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Stop acting like you’re new in the system.. Like I told you everything here is free of charge.. Ba sai kin biya da jikinki ba.. I’m not interested.. Get dressed now.. And don’t make me wait..!” Daga haka mik’ewa yai ya fice ya nufo k’asa.


Tai saurin tattaro rigarta ta tak’ure waje guda wasu hawayen na zubo mata. Har lokacin bata dawo daidai ba.. Rintse idanunta tai sosai tanaji kaman har lokacin cikin jikinsa take.. A hankali ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka wanke mata fuska. Ta Ware Doguwar rigar tana gani.. Ya zama dole ta bar wannan gidan, bazata iya ci gaba da zama ba, ba Karnuka ba ko kuraye ne zai sake mata zata gudu.. Bathroom ta koma ta d’auraye fuskarta ta goge da towel.. Dama sumarta tupke yake cikin ribbon. Ba don taso ba Ta zira rigar wanda yake daidai ita kaman an auna. Ta rufa mayafin rigar akanta tana duban kanta cikin mirror a nan toilet d’in.. Dikda bata shafa komai a fuskarta ba Ta fito tas Sady pretty d’inta saidai fuskarta da yake kaman Ta maras lafiya. Ta sadda idanunta k’asa kafin ta nufo k’ofa, nan taga takalmi flats mai kyau a bakin k’ofar da alama shi ya aje mata. Ta zira k’afafunta ciki a hankali kafin Ta nufo motar tasa.


Tai tsaye kaman bazata shiga ba har lokaci idanunta na k’asa bata d’ago ta dubesa ba.


“Ke shige mu tafi we don’t have the whole day..” Ya fad’i yana key ma motar.


Bai tsaya biye mata ba ya mik’o hannunsa ya bud’e mata front seat.. Ta d’an d’ago ta saci dubansa amma sai taga idanunsa naga wayarsa ko kallon yanda take baiyi ba. Tai k’wafa cikin zuciyarta kafin Ta shige motar. Kaman wanda yake jira nan yaja motar suka fita daga gidan.. Ya sauk’o ya rufe gate d’in gidan kafin suka d’au hanya..


Suna tafe babu mai cewa komai. Addu’a kurum take cikin zuciyarta Allah yasa ya maidata gidansu.. Bata ida addu’an ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “A ina kuka had’u keda Sagir.. ? Allah yasa ba club bane ko Hotel dan ni banyi miki kama da mutumin da za’a gansa a irin wad’ann wajajen ba..”


Ta dubesa da mamakin tambayar sai kuma ta girgiza kai tace “Wannan ba matsalarka bace koma a Ina muka had’u..”


Jinjina kai yai yana duban kwalta “Baki so ki koma gidanku ashe..” Ya fad’i ba tareda ya dubeta ba.


Jin abinda ya fad’i ya sanyata saurin fad’in “A park muka had’u..”


Ya tambayeta sunan park d’in nan ta sanar dashi.


Jinjina kansa yai a hankali yana mai maimaita sunan park d’in..Lokaci guda ya d’auki  direction d’in da zai kaisu Park d’in data fad’i masa.


Ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “Kina jina.. We are on a mission.. If you mess everything up delay d’in komawarki gidanku zaki ci gaba da ja ma kanki.. We’ll go to the  park, and we’ll act like a real couple.. Don’t mess up kinji abinda na fad’a miki koh.. Idan kika b’ata komai lokacin zama a GIDAN ARO kike k’ara ma kanki.. The sooner we are done with this mission, the sooner you get your freedom back. Did I make myself clear..?” Ya k’arashe yana dubanta da gefen ido.


A hankali ta jinjina kanta har lokacin fuskarta a hard’e.. Suna tafe tana jinsa yana waya wanda dagaji da abokin aikinsa yake wayar.. Har suka isa Park d’in waya yake.. Saida sukazo yanda zai parking kafin taga yaja jikin Seat d’insa ya ciro bindiga.. Ganin bindiga da tai ya sanyata ta razana “Na shiga uku.. Mai zakayi da bindiga..?” Bai amsata ba yaci gaba da shirya bindigar kafin ya d’aga jacket d’insa ya mak’alata ciki..


Ya d’ago yana dubanta har lokacin a tsorace take “Don’t mess up na fad’a miki.. We will act like a real couple.. Kinji abinda na fad’a miki ko bakiji ba..?” Tai saurin jinjina kai alamun taji.


Sauk’owa yai ya zagayo yanda take zaune ya bud’e mata.. Hannu ya mik’a mata alamun ta kama hannunsa ta fito..


Ta dubesa ta kuma dubi hannun nasa. Tsareta da idanu yai alamun ta rik’e hannunsa ta fito. Zuciyarta sai tsinkewa yake, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta mik’o masa hannun nata ya rik’o yana mai sakar mata murmushi.. 


“My lady..!” Ya fad’i yana sakale hannunta tsakankanin arms d’insa da k’irjinsa. Lokaci guda ya d’an janyota cikin jikinsa da k’arfin gaske yai k’asa da kansa saitin kunnenta yana fad’in “Remember this is all acting.. So you better cooperate.!”


Tai murmushin yak’e tana dubansa “Of course My Detective..!” Ta k’arashe tana d’aure fuska kaman ba itace mai fake smile d’in ba.


Sunata wuce mutane a haka sai ka rantse wasu masoya ne.. Saman grass carpet suka k’arasa suka zauna gefen wasu furanni..  Nan wayarsa ta soma ringing.. Assad ne mai kira..


Lokaci guda ya mik’e yana mai amsa wayar idanunsa akan Sadiya.


Daga d’aya b’angaren Assad yace “Kana nufin kaida Sadiya..? Toh mai kuke a park.?”


“We’re on a mission..” Ya basa amsa kai tsaye.


“Mission kuma.. Wane irin mission..?” Assad ya tambaya.


“Dama da nace maka aurenta da nayi mission ne baka yarda bane.. Well yanzu sai ka yarda.. Abun shine itada Sagir a nan suka had’u so kaga definitely ta iya yuwa shida accomplices d’insa suna zuwa nan.. Idan har suna hunting d’inta zasu making move”


Assad ya girgiza kai dan ya dena mamakin abokin nasa “You’ve got to be kidding me Mu’azzam.. What if she gets hurt.. What if suka mata wani abu bakada backup bakada komai..”


Katsesa Muazzma yai da fad’in “They’ll have to pass through me before they lay a finger on her..! Kaidai kawai stay alerted zan iya neman backup daga wajenka.”


Assad ya jinjina kai yace “Shieknan.. Be careful Mu’azzam.. Allah ya tsare.”


Mu’azzam ya amsa da Ameen kafin sukai sallama.. Yana dubanta yanda take ta wasa ma wani yaro shida mamansa sunzo sun zauna a wajen.


Yanata kallonta yanda take wasa ma yaron har dai suka mik’e zasu wuce shida mamansa yaron har waving yake mata itama tana masa kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Sosai Mu’azzam ya shagala da duban yanda take murmushi. Yana nan tsaye wayar Safeenah ya shigo masa.. 


Ya d’aga cikeda kulawa, saidai yana d’agawa da kuka Safeenah ta fara masa tana fad’in taji ciwo ya tafi ko sallama basuyi ba gashi nan taji ciwo kuma mai gyaran k’afan yace zata iya kaiwa sati guda kafin Ta fara taka k’afar.. Sai kukan shagwab’a Safeenah take masa.. Lallashinta ya soma idanunsa na kan Sadiya yana kuma matsowa kusan Sadiyar yanda zataji wayar da yake da matarsa.


Abin ya mugun dad’i ma Safeenah ya kuma bata mamaki Wai Mu’azzam ne ke lallashinta irin haka ba tareda ya gwaleta ba ikon Allah.. Lallai ta yarda yanzu kam tana da matsayi mai girma cikin zuciyarsa..  Ta fara Mitan ita ta gaji Abuja take son dawowa su tattara su koma gidansu.


Mu’azzam yace “I had to attend to some urgent matters ne shiyasa na dawo cikin gaggawa but Kar ki damu soon zamu koma.. I promise you kina dawowa zamu koma gidanmu.. But for now kiyi abinda mai gyaran yace kar azo a sami matsala..”


Sadiya kaw d’auke kanta tai kaman bata a wajen.. Yanda kasan tafiyarsu ba d’aya bane haka tayi.. A ranta tana fad’in ita tausayin matar tasa ma take dan wllhi sam batai dacen miji ba.


Wasu samari ne guda biyu suka dosota d’ayan yana wani fad’ad’a murmushinsa ya k’araso yanda take zaune “Miss Beautiful are you alone..?” Ya fad’i yana mai k’ok’arin duk’awa. Ai kafin yakai k’asa Mu’azzam yai ma Safeenah sallama a gurguje yana sanar da ita zai koma bakin aiki.. Lokaci guda ya k’araso yanda Sadiya ke zaune.. Ya sakalota cikin jikinsa yana fad’in “Sorry Wife na barki ke kad’ai..”


Saurayin ya d’an sha jinin jikinsa ya mik’e yana basu hak’uri yana fad’in baisan matar aure bace.


Mu’azzam baice komai ba Sai aika ma Sadiya mugun kallo da yake.. Suna shigewa ta cire jikinta daga nasa su duka biyun suna sakin huci


“So abinda kika saba zuwa yi park kenan.. Dan kiyi new catch masu kud’i koh.. Kina wani zaune wancan d’aniskan yaron mai suma kaman na shed’an yana k’ok’arin zama kusa dake.. Kuma ko a jikinki koh.. Da kin bari ya zauna da na had’eku duka biyu na harbe..”


Rausayar da idanunta tai cikeda k’osawa take k’ok’arin mik’ewa “Mr Inspector da alama babu wani abinda zaka samu a nan.. Kaga ruwa zai iya sauk’owa any moment.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata tinda nayi abinda ka umarceni..”


“Ank’i a maidake d’in..!” Ya fad’i yana tsareta da idanu dan zuciyarsa tafarfasa take tin lokacin da yaga samarin nan sun nufota.


Fuzar da fuci tai kad’an kafin tasa kai kaman zata shige.. Saidai tuni taji ya janyota ta dawo da baya.. Hakan yai daidai da soma zuban ruwan sama.. Mu’azzam ya mak’aleta cikin jikinsa yana mai kallon yanda ruwa ke zubowa.. Dubansa take da idanunta da sukai rau rau hawaye gauraye da ruwa cikinsu.. Drops d’in ruwa saman fuskokinsu su duka biyu.. Wani mutumi ne mai tallan lema ya k’araso yana fad’in “Rankaidad’e saura d’aya ce ta rage ya kamata ka siya.. Kar Amarya tayi mura..”


Mu’azzam ya dubi mutumi mai saida leman yace masa “Nawa ne..?”


Mutumin ya fad’i masa kud’in leman.. Zaro kud’ad’en yai cikin pocket d’insa ya mik’a wa mutumin yana fad’in “Keep the change.” Mutumin ya masa godiya had’ida mik’a masa lemar.. Saida ya bud’e masu ma kafin ya mik’awa Mu’azzam d’in..


Lokaci guda ya kuma janyota cikin jikinsa sannan ya rufa masu lemar akansu.. Ta dubi hannunsa yanda ya rungumota ya rik’eta, zafin kalamansa akanta kurum take tunawa da wulak’ancin Sa take tunawa.. Lokaci guda taji wani irin k’arfi yazo mata.. Tai k’ok’arin turasa dashi da lemar tasa.. Saidai sam bai saketa ba saima dad’a matseta da yai.. Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Don’t get wrong ideas dik cikin acting ne..!”


Lumshe idanunta tai hawaye na gangaro mata.


Ganin tana rawar d’ari ya sanyasa zame jacket d’insa ya rufa mata.. Still saida ya sake tina mata cewa a cikin acting ne.


Ruwan na k’aruwa dole suka nufi mota, ya bud’e ya shigar da ita.. Nan wani mutumi mai hoto ya tsallako a guje yana tare Mu’azzam d’in.. Envelope ya mik’o masa yana fad’in “Yallab’ai hoto aka maku d’azu kaida Madam baku Sani ba.. Yayi kyau sosai bud’e ka gani..”


A hankali Mu’azzam yasa hannu ya amshi envelope d’in.. Lokaci guda ya soma zaro hoton kaman mai tsoron ganin hoton.. Fuskokinsu ya gani su duka biyun suna murmushi sanda yake ce mata ta nastu tayi acting d’inta da kyau idan tana son komawa gidansu..

Sunyi kyau sosai like a real couple.. Kud’in hoton ya zaro ya mik’a wa mutumin kafin ya saki tsaki a hankali ya tura hoton cikin aljihunsa.. Ya kaindubansa ga Sadiya dake zaune cikin Mota ta kifa kanta da alamun kuka take. Ya d’auke kansa yana sakin gajeren tsaki.. Lokaci guda ya shige cikin motar ya tada suka tafi.. Sam baiji dad’I ba dan babu wani abinda suka samu gameda Su Danger ko masu bibiyan Sadiya.


Suna isowa gida tai shigewarta tana matsan k’walla.


“My jacket.” Ya fad’i yana dubanta.


Babu musu ta cire ta mik’a masa abunsa kafin tai shigewarta. Shima shigewar yai nasa d’akin dan yin wanka dan duk a jik’e suke.


Yana cikin rage kayan jikinsa yaga hoton da akai masu a park.. Ya jima yana duban hoton, lokaci guda ya k’arasa dustbin zai disposing sai kuma ya tsaya kaman wanda ya tina wani abu.. Drawer ya janyo ya jefa hoton ciki kafin yai shigewarsa bathroom.. 


Yana fitowa daga wanka yaga kiran Assad na shigo masa.


Daga d’aya b’angaren Assad ke sanar dashi Sun sami wani clue regarding the search for Danger..


“Are you serious Assad.. Did you find his whereabout..?”


“No not really... But mun samu abinda zai iya  leading namu to his hideout..” Assad yace yana juya flash drive d’in dake hannunsa. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “I’ll tell you about the details idan muka had’u.. Yanzu dai ya kamata muyi aiki akaine.. Ina zamu had’u..?”


“Let’s meet up here at my place..” Mu’azzam yace yana k’arasa shiryawa.


Assad yace “Alright zamu taho tareda Yusuf dan d’aya location d’in shi yaje yai spying mana..”


“Alright sai Kun k’araso..” Daga haka sallama sukai kafin ya ida shiri a gurguje ya fito ya nufi masallaci dan kiraye kirayen sallar magrib ake.


Yana dawowa daga masallaci d’akinta ya nufa ya tadda Ta ida sallah kenan tana k’ok’arin linke darduman.


Bata ko dubi yanda yake ba taci gaba da abinda take.


“My friends are coming over tonight, kar ki damu ba masu kud’i bane balle kice zaki samu wani attajirin cikinsu.. ‘Yansanda ne irina masu fafutuka.. So karki kuskura ki sauk’o downstairs har sai Sun bar gidan nan...” Daga haka Sa kai yai ya juya ya fice a d’akin..


Ta girgiza kai ba tareda tace komai ba. Zama tai nan saman carpet tana tinanin abinyi.. Take taji ya kamata Ta karanta Alk’ur’ani dan zuciya da karatun alk’urani ne kawai take samun nastuwa.. A hankali cikin tsanaki ta soma rero karatun ta cikin suratu Maryam daka dan dama ta haddace suran.Bayan su Assad da Yusuf sun iso tuni sukai connecting na’urar aikinsu a nan parlorn gidan. Mu’azzam yai masu offering coffee da tea Assad yace “Tab Inaa wannan ai sai ku turawa.. ni wllhi yunwa nakeji.. Idan zan samu something solid I’ll be glad..” Bai kai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “The kitchen is right there Sai ka shiga ka girka dan dai nikam k’asan ban iya girki ba.”


“Toh matar gidan fah.. Haba Malam Officer gidan Amarya fah muka zo.. Ni wllhi kafin a fara aikin nan sai an bani abinci idan ba haka ba bazaku tab’a gane kaina ba..”


Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yasan da gangan Assad yai maganar nan kawai dan dai ya had’asa magana da yarinyar ne..


Car keys d’insa ya d’auka yana fad’in “Barin sayo maka a nearby eatery..”


“A’a wllhi.. No gaskiya bazanci na restaurant ba na Amarya nake so idan kuma ba rowar abincin gidanka zaka mana ba.. Ko ya kace Yusuf..?” Ya k’arashe yana duban Yusuf wanda tinda suka fara tattaunawar murmushi kurum yake yana k’ok’arin connecting computer.


Fuzar da huci yai kad’an yana aikama Assad mugun kallo “Damn you..!”Ya fad’i yana hayewa upstairs.


“Oho dai naji koma menene..” Assad yace yana darawa kad’an.Mu’azzam na hayewa ya tadda karatu take. Ya d’an tsaya jikin k’ofa yana sauraronta. K’amshin nan nasa da taji ya tabbatar mata yana tsaye wajen. Ta dasa aya ma k’aratun nata kafin ta juyo a hankali. Cikin zuciyarta tai tsaki tace mutum kaman goyon maguzawa Sai ya ringa shiga waje babu sallama.


“Abokaina suna jin yunwa.. I told them ba’a dafa abinci a gidan nan amma sunk’i amincewa.. Can you cook something simple for them..?”


Jin bata amsasa ba ya sanyasa fad’in “Nasan kin San matsayin girman miji a wajen matarsa. So idan har kinada karatun addini kaman dai yanda naji kina karatun nan zakiyi abinda mijinki ya umarceki.. Idan kuma Bakiyi ba Kinsan mai hakan yake nufi.. And please do not embarrass me.”


Daga haka ficewa yai ya barta nan zaune ba tareda ta tankasa ba. Watau yanzu kuma da Ubangijinta zai had’ata bayan ya gama mata barazana da mission. Taji wasu k’walla masu zafi suna zuwa mata... Tasha jin ana cewa ko Wanne gidan Aure da nasa k’alubalen wata nata dangin miji ne wata uwar miji ne nata k’alubalen wata kuwa shi mijin kansa ne k’alubalen kaman dai yanda nata ya kasance dikda kuwa Auren nata ba mai d’aurewa bane. Tina cewa da tai  koda auren na d’an lokaci ne shid’in mijinta ne kuma umarni yake bata ya sanyata mik’ewa ba dan taso ba. Ta nufo wardrobe d’in tana duba mai zata rufa akanta.. Wani shud’in mayafi ta d’auko yalwatacce ta rufa akanta kafin ta nufo k’asa ta shige kitchen d’in.. Tana jin hayaniyar su shida abokan nasa har tana mamaki ashe dama ana jin muryar sa haka.. Wata zuciya tace ai indai bincike yake kam tsaf zakiji muryarsa.. Ta tab’e baki kad’an kafin Ta nufi kitchen d’in.


Store ta soma dubawa taga store d’in shak’e da kayan abinci. Ga dangin su pasta da couscous.. Tai tinanin dafa masu abinci mai sauk’i kaman yanda yace. Couscous d’in ta d’auko ta dawo kitchen d’in ta bud’e fridge ta duba groceries nan taga gasu veggies sealed cikin leda irin yanda ake saidawa a super markets harda minced meat dasu sausage dik Suma sealed... Minced meat d’in ta d’auko kafin ta dafa white couscous tai garnishing d’insa da veggies sannan tai soma had’a masu sauce d’in minced meat d’in wanda za’aci white couscous d’in dashi..Suna zaune parlor suna aikinsu k’amshi ke dakan k’ofofin hancinsu. Assad yace “Kai wannan k’amshi ai sai ya cika mana ciki kafin muci.. Gaskiya da alama Amarya ta iya girki..”


Gajeren tsaki Mu’azzam yai ya kuma duban Yusuf dake k’ok’arin saka flash jikin computer yace “Ina sauraranka Yusuf go ahead.”


Yusuf yaci gaba da fad’in “Kaman yanda na fad’a maku shi wannan footage d’in wajen security d’in da suke kula da restaurant d’in na samu bayan na shafe kwana biyu ina bincike ina tambaya people around the area ko sun tab’a ganin mai kama da Danger wajen.. Toh shine na samu har mutum uku suka ce Sun tab’a ganinsa sau kusan uku yana zuwa wannan restaurant d’in yana sayan abinci.. Da alama Danger yana son abincin wannan restaurant d’in.. Toh sai na tambayi CCTV Footage daga wajen securities bayan na sanar dasu matsayina da binciken da nake.. Bari mu gani gaba d’aya mu tabbatar..”


Suka jinjina kai a tare sanda Yusuf ya soma playin videos d’in har kashi Uku wanda yake tabbatar da cewa Danger ne yake zuwa Restaurant d’in sayan abinci dikda yana saka rigar sanyi mai hood dan kar a ganesa.


Sanda akazo daidai fuskar mutumin Mu’azzam yace “Stop. Yi zooming muga.” Yusuf yai kaman yanda yace d’in.


Jinjina kai yai yace “It’s him.. Danger ne.. So Ta tabbata yana zuwa wannan restaurant d’in tinda har yaje sau uku..”


Yusuf ya jinjina kai kafin Assad y ciro wani flash drive d’in yace “Wannan kuma wani super market ne da aka ga wani  mai kama dashi once.. But nima I’m not sure idan shi d’in ne domin wannan kaman yafi Danger girman jiki saidai kuma idan camera ce ta k’ara masa girman jikin.. Footage d’in na k’ofar super market d’in ne wanda fuskarsa ta d’an fito amma is not that clear..”


Mu’azzam ya jinjina kai yace “Saka mu gani..”


Lokaci guda Assad ya saka ya soma playing.. 


“Wait.” Mu’azzam ya dakatar dashi yace masa yai zooming.. Lokaci guda ya k’ura ma lambar motar da mutumin zai shiga idanu a nan k’ofar super market d’in..Lambar motar tayi daidai da motar da aka basu bayanan cewa itace motar data buge Baban Sadiya.


Mu’azzam ya shiga jinjina kai yana fad’in “That Scumbag.! Shi ne.. Shine ya kad’e Babanta.. Danger ne ya kad’e mahaifin Sadiya..!”


Ya shafa sumarsa a hankali yana jin zuciyarsa na masa zogi.. Cikin sauri Yusuf ya shiga d’aukan plate number d’in motar dan suyi comparing da wancan...


Assad yace “Yanzu ya tabbata Danger yana nan cikin garin nan yana  hunting dik wani wanda yakeda alak’a da case d’in nan.. By all means yake so ya rufe bakin kowa.”


Ya dubi Mu’azzam yace “Surely Danger will come after your wife..!”


Mu’azzam ya jinjina kai yace “I’ll kill him if he attacks her..” Yai maganar yana murza hannunsa a hankali.


“What’s plan now.?” Assad ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in.


Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya soma fad’in “Yanzu dole mu rabu muje wuraren da muke tsammanin Danger na zuwa. Kunga ni bazai yuwu na tafi aiki under NPF ba since I’m still on my suspension.. Naji ASUU sunyi calling off warning strike d’in da suka tafi.. So Sadiya zataje makaranta gobe.. Ni zan kaita dan nasan Maybe Danger yai tinanin attacking nata idan ta fita makaranta.. Kai kuma Assad kaje wannan Super market d’in.. Kai kuma Yusuf ka tafi wannan location d’in.. Restaurant d’in sai muga ina danger zai fara zuwa.. We should all stay alerted wanda dik ya soma ganin Danger cikinmu Sai muyi alerting juna mu nemi backup..”


Gaba d’aya suka jinjina masa kai suna fad’in “Yes sir..!” 


Daidai nan Sadiya ta fito daga kitchen rik’eda plates ta nufi dining table.. Tin daga nesa Assad ke zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi.Mu’azzam sai satan kallanta yake cikin zuciyarsa yana addu’an Allah yasa kar Ta basa kunya.


Saidai ganinta da yai sanye da tufafin da ya zuba mata a wardrobe yasa hankalinsa d’an kwanciya. K’ila bazata basa kunya ba.


Daga can yanda take tsaye ta d’an duk’a ta gaidasu Assad gajeren murmushi saman fuskarta jin yanda Assad ke Zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi had’ida yi mata godiya.


Ko duban yanda Mu’azzam ke zaune bataiba tai juyawarta kitchen ta kawo masu sauran abincin. Harda pineapple drink Ta had’a masu.. Sai dubanta yake cikeda mamaki. Ita kaw yi tai kaman batasan yana parlorn ba, tana gama jera komai tai hayewarta sama. Yabi bayanta da kallo har Ta b’ace ma ganinsa.. Muryar Assad da tuni ya nufi dining area ya soma bud’e warmers d’in shi ya dawo da hankalin Mu’azzam. 


Assad yai ma Yusuf tai baibi takan Mu’azzam ba. Suka soma cin abincin yayinda Mu’azzam ke ci gaba da duba footage d’in dikda kuwa sosai k’amshin ya cika masa ciki.


No comments

Powered by Blogger.