Gidan Aro 24


24*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Assad da fitowarsa kenan daga layin gidan Alhaji Isyaku bayan ya maidasa gida nan ya hango bayan motar Mu’azzam tana ficewa daga layin. Mamaki ya cika Assad mai ya kawo Mu’azzam nan kuma.? Shi zai iya cewa yama mance Wai Mu’azzam d’in ya auri Sadiya. Juyawa yai ya dubi lungun gidansu Sadiya nan ya hango Umma ta fito tana kuka tana ambato sunan Sadiyar.. Babu shiri Assad ya nufota.. 


Tambayarta ya soma abindake faruwa.


Cikin zuban hawaye Umma ke sanar dashi dik abinda ya faru tin daga zuwan Mu’azzam har d’auke Sadiyar da yai. Dan ta gane Assad shine abokin aikin Mu’azzam d’in da suka soma zuwa bincike gidansu tare.


Assad ya lumshe idanunsa a hankali yana girgiza kai “Mu’azzam! Mu’azzam.. Mu’azzam..!! Mai ka aikata kuma..” Yai maganar a hankali idanunsa a lumshe. Bai gama kashe wani wutan da Mu’azzam d’in ya kunna ba ga wani ya kuma tadawa.


Muryar Umma ya sinkayo tana fad’in “Yallab’ai dan Allah ka ceceni.. Kar abokin aikinka ya cutar min da d’iya.. Ka taimaka min ka nemo min d’iyata.. Wllhi batada laifin komai..”


Assad da zuciyarsa ta gama raunana ganin yanda matar ke zuban hawaye tana ambaton ya taimaka mata dik sai yaji zuciyarsa na kuma karaya. A hankali yake furta “Umma ki kwantar da hankalinki.. Nothing bad will happen to your daughter... Mu k’arasa gidan naku sai muyi magana.”


Umma ta share hawayen da suka wanke mata fuska kafin Ta girgiza kai tace “A’a bazan iya ba sai nasan Ina yakai mun d’iya.. I don’t want to lose another family member..  Na yarda ni yakaini ya rufeni amma kar ya cutar min da d’iya..”


Assad ya d’an kifa kansa kad’an kafin yace “Umma mu k’arasa gidan muyi magana a natse, na miki alk’awari babu abinda zai sami d’iyarki.”


Duban Assad tai da idanunta masu zuban ruwa kafin ta samu kanta tana mai bin umarnin Assad d’in lokaci guda Ta juya suka koma gida.


Sauk’in abun su Ashir dik suna bacci da batasan yanda zatai tama yaran bayanin abinda ke wakana ba.


A nan veranda d’in Umma tai nuni ma Assad da tabarmar dasu Malam Liman suka tashi kafin Ta k’arasa saman kujera irin wanda mata ke amfani dashi a kitchen ta zauna, har lokaci sharan hawaye take da hijabinta.


Tsananin tausayin bayin Allahn ya rufe Assad. A hankali ya soma furta “Umma da farko Ina mai baki hak’uri kan abinda abokina ya aikata.. K’warai Mu’azzam bai kyauta ba sannan bai biyo ta hanyar da ya dace ba.. Ina baki hak’uri Umma on his behalf kiyi hak’uri.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam is not a bad person, yanada kurakurensa  kaman ko wani d’an Adam, but I can assure you he’s not a bad person, and he’s not going to do any harm to your daughter.. Saidai ma ya d’auketa ne to give her protection daga mutanen da suke yunk’urin cutar da ita.. Mutanen da suke tunanin Sagir ya sanar da ita wani abu.”


Umma ta dubesa da mamaki wannan karon kafin tace “Amma ai mun sanar daku Jami’an tsaro Iyakacin abinda muka sani gameda Sagir.. Maiyasa abokin ka bazai k’yale d’iyata ba.. Na tabbata da wani dalili nasa da nufi ya aureta ya biya mana bashinmu.”


Assad ya jinjina kai kafin yace “Haka ne Umma, Kinyi gaskiya..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam ya auri Sadiya ne to keep her safe from danger, itace target d’in ‘yantaddan da muke nema muke kuma bincike kansu.. Nasan kinada masaniya akan irin mutuwar da mijinki kuma mahaifin Sadiya yayi..”


Umma ta d’ago tana dubansa wannan karon sai kuma ta katsesa da fad’in “Mijina had’arin mota yayi.. Mota ce ta bigesa.. Sannan tsautsayi ne kuma k’addara ne da bazai tab’a tsallakewa ba..” Tai maganar cikin tsananin rauni.


Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “K’warai haka ne Umma, Tabbas tsautsayi ne da bazai shige ranansa ba.. But mu jami’an tsaro hasashenmu da bincikenmu sun tabbatar mana accident d’in shiryayye ne.. Shiryawa akai Umma and  Sadiya suke hari sai suka fara daga kan Wanda yake sama da kowa a family d’inta which’s her father.. Sun kawar da mahaifinta sabida shine mutum na farko da zai bata protection ya zamto garkuwa a gareta. Zaman Sadiya a taredaku had’ari ne a gareta da kuma gareku baki d’aya.. Na tabbata bazaki so wani abu ya sake samun wani cikin ahalinku ba.. Inada tabbacin wannan dalili shiyasa Abokina ya d’auketa sabida ‘yantaddan Ita suke hari they believe Sagir ya sanar da Ita wani abu wanda zai iya exposing nasu..”


Umma tai shiru tamkar mai nazari sai kuma tace “Idan na fahimceka Abokinka ya d’auke d’iyata ne domin yaja hankalin mutanen da yake nema.. Ba don ya bata kariya ba..”


Assad ya d’an shafi kansa kad’an yana mai sadda Kai k’asa “Umma bazan so kiyi ma abokina mummunan fahimta ba Dikda cewa kinada cikakken damar da zaki masa irin wannan fahimtar... Wato Umma Mu’azzam mutum ne da ya had’u da tarin iftila’i na rayuwa.. Dikda cewa ansan musulmi da d’aukan k’addara.” Ya d’an kuma nusawa kafin yaci gaba da fad’in “Ya rasa mahaifinsa tin yana k’arami sannan a daidai wannan lokacin jinya mai tsanani ya sami mahaifiyarsa.. Bayan wannan yazo ya rasa tilon k’anwarsa wacce aka kasheta aka kuma tsinta gawarsu tareda Sagir.. Kinji dalilin da yasa bincikenmu ya gangaro har kanku.. Sabida tarayyar Sadiya da Sagir... Amma kawai abinda nake so ki yarda dashi kuma ki amince shine Mu’azzam is never going to do any harm to your daughter.. And He’ll protect her with his life.. Ki kwantar da hankalinki Umma ki natsa zuciyarki kuma ki saka a ranki d’iyarki tana safer place.. Kiyi takabarki cikin kwanciyar hankali ki kuma rungumi yaranki.. I’ll be checking on you time to time in sha Allah.. Allah ya gafarta wa Abba yasa yana Aljannah..”


Jiki a sanyaye Umma ta amsa da Ameen tana mamakin tarayyar Assad da Mu’azzam, yanda wannan yakeda mutunci da sanin yakamata ba kaman abokin nasa ba. 


“Ina mahaifiyar tasa take..?” Umma ta tambaya tana d’an dubansa kad’an.


Assad ya d’an risina kafin yace “Tana can garinsu ana mata magani. Shekaru goma sha biyar kenan tana kwance tana jinya..”


Jiki a matuk’ar sanyaye wann karon Umma tace “Allah sarki Allah ubangiji ya bata lafiya.” 


Assad ya amsa da Ameen. Daga haka Assad sallama yai ma Umma kafin ya fito ya nufi bakin Babban kwalta..


Yana tafe yana  dialing layin Mu’azzam. 


Mu’azzam na driving yaga kiran Assad na shigo masa, yana d’agawa Assad ya soma fad’i daga d’aya b’angaren 


“Do I always have to remind you that you are a big jerk..”


Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Say what you want to say quickly, I’m busy right now.”


“Who do you think you are Mu’azzam Gamji.! Ta yaya zakazo har gidan mutane ka d’auke masu d’iya.. Are you out of your mind.”


“No you’re out of your mind Assad, for as far as I know I didn’t do anything wrong. Matata na d’auko tareda ni.. Did I commit a sin..?”


“Is that how you take your wife..” Kafin Assad yakai aya ya katsesa da fad’in 


“We talk tomorrow. I’ll send you some numbers.. Tracking nasu nake so ayi since you’ve access to the tracking room..” 


Daga haka katse kiran yai yana k’ok’arin forwarding lambobin da aka turo masa sak’on BAD dasu..


Birki yai sakamon motar da bai kula wanda ke gabansa ba. Aiko nan Sadiya Ta hantsalo daga saman seat ta buga kanta.. A hankali ta soma k’ok’arin bud’e idanunta tana dafe goshinta dake mata zogi yanda Ta buga. Nan ta Ware idanu ta ganta cikin mota.. A firgice ta mik’e tana k’ok’arin bud’e k’ofar motar saidai tuni ya danna motar a central lock.


Sadiya ta dubesa yanda yake driving hankali kwance lokaci guda Take furta “Malam ina zaka kaini..? Ka maidani yanda ka d’auko ni ko na maka ihun b’arawo.!”


Shiru idan steering da hannayensa ke bisa ya amsa shima zai amsa.


Hawaye suka cika idanunta, cikin rawar murya take furta “Please ka maidani yanda ka d’aukoni.. I promise ban aikata komai ba.. Please don’t hurt me.. Ka maidani wajen Umma..!”


Nan ma shiru bai amsata ba. Lokaci guda Ta soma sakin huci tana dubansa, kaman wacce akanjefota haka ta tsallako ta dawo frontseat d’in.. Steering wheel ta shiga k’ok’arin janyowa tana fad’in “Either you take me back home ko kuma na jefamu a rami gaba d’aya.”


Ya juyo ya dubeta da mamaki ganin yanda take ta kokawa da steering.


Nan ma bai kulata ba bai sakar mata kan motar ba. 

Idanunta na hawaye take dubansa “You’re merciless.. This is police brutality, Mr Inspector. Idan baka maidani ba wllhi zan maka ihun b’arawo.”

 

Ba tareda ya dubeta ba idanunsa naga street yake d’an rage girmansu, kafin ya saki murmushi kad’an yace “Go ahead and shout. Shout at the top of your voice.. Let’s see idan akwai wanda zai taimakeki..”


Hango check point na ‘yansanda da tai ya sanyata sakin murmushi tana hamdala, kafin ta juyo ta aika masa mugun kallo “You won’t get away with this.. I promise you..!”


Suna k’arasowa aiko yana zuge glass ta dubi ‘yansanda  masu patrol d’in “Officers dan Allah ku taimakeni.. He’s a kidnapper, wllhi satoni yayi.. I know my Mum must be worried.. Dan Allah ku taimaka min.”


Mu’azzam ne ya katse zancen da fad’in “Officer all is well, I just found  out my wife is pregnant. And you know how pregnant women are like..” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa 


Daskarewa tai tana dubansa, for the first time da taga murmushinsa, sai kuma ta shiga girgiza kai tana fad’in 

“K’arya yake Rankidad’e wllhi satoni yayi.. You need to arrest him please..”


Bata Kai aya ba taga ‘yansandan sun k’ame suna sara masa had’ida clearing masa hanya “SIR.!” Suka fad’i a tare suna masu nuna masa hanya.


D’ayan har yana fad’in “Congratulations Sir.!” Yana wani Washe baki yana k’anwata Cak ta tsaya da bayanan nata kafin ta juyo tana duban Mu’azzam dake maida wallet d’insa cikin aljihu wanda ko shakka batayi ID d’insa masu patrol d’in nan suka gani.


Tabi ‘yansandan da kallo baki sake yanda Suka k’ame masa har motar Ta shige.. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in  


“Do you think zanyi asaran wad’annan kud’ad’en kanki a banza ne,.. I’ll only dispose you when I’m done with you..” Yai maganan tamkar dai bashi yake maganar ba dan ko duban yanda take baya yi.


Cikin tsananin huci da zafin rai take dubansa, kalaman nasa masu zafi suna mata Yawo a dodon kunnuwarta. Wai zai disposing d’inta when he’s done with her saikace wata shara. Take kuma tsoro ya bayyana sosai saman fuskarta.. Ko lokacin da take Sady Pretty d’inta  bata tab’a tsintar kanta da tsoron wulak’ancin d’a namiji irin wannan karon ba.. Tsoro take kar wannan mutumin ya mata babban wulak’anci.. Hijabin dake jikinta ta shiga duk’unkunewa ciki tana girgiza kai wasu hawayen na kwaranyo mata.

“Don’t hurt me please.!” Ta fad’i cikin tsananin rawar tana mai rintse idanunta.


Ko kallo bata isheshi ba saima bada mahimmanci da yai sosai ga tuk’in motar.


Suna isowa k’ofar gidan taga ya bud’e motar ya fito kafin ya zagayo ta yanda take zaune. Bud’ewa yai yace “Fito.”


Da rinannun idanunta take dubansa “No I won’t.!” Ta basa amsa kai tsaye.


Gajeren tsaki yai kafin ya fincikota ya fito da Ita ya soma k’ok’arin janyota tana tarjewa. Bai fasa janyota ba har saida suka shiga gidan. Saidai suna shiga taji haushin wasu irin k’artan karnuka irin breed d’in turawan nan. Ai bata San sanda tai tsalle Ta mak’ale cikin jikinsa ba.


Cikin tsananin rawar jiki take furta “Na shiga uku mai zaka mun.!”


Kai tsaye ya bata amsa “Zaki gani..!” Yai maganar yana mai tsare fuskarta da kallo wanda cike yake tab da tsoro.. Sai rawa jikinta yake ta kasa sakinsa.


Saitin kunnenta ya rad’a mata “Sakeni kafin ki Shafa min wani cutan zamani..”


Dubansa tai zuciyarta naci gaba da yankewa sai kuma taga ashe shid’in ta rik’e tsananin firgicin haushin karnukan wanda bama tasan tayi hakan ba. Cikin tsananin huci da zafin nama ta turasa da iya k’arfinta wanda saida ta kusan kaisa k’asa “Idan kana tsoron na shafa maka cutan zamani Maiyasa ka sato ni daga gidanmu ka kawo ni nan.. Bari kaji na fad’a maka Allah bazai tab’a baka nasara akaina ba.. Nafi k’arfinka nafi k’arfin wulak’ancinka..!” Ta k’arashe tana mai kuma janye hijabinta tana sauk’ar sa sosai tana mai kuma rufe jikinta.


Dubanta yake daga sama zuwa k’asa cikeda mamaki kafin yace “Ke.! Cut this nonsense. No one wants a trash like you..!” Yana ida fad’in haka yaci gaba da janyota.


Ga tsananin mamakinta wani d’an d’aki mai kaman store taga ya k’arasa ya bud’e gefen na Karnukan nan daketa faman haushi. Tsoro ya soma cikata sosai, kardai da gaske ya kawota ne ma karnuka su cinyeta. Jikinta yaci gaba da rawa.


Yana ida bud’e d’akin ya turata ciki. Sadiya na hawaye ta d’ago hannu tana rok’onsa “Please don’t.. Don’t leave me here please.. Na rok’eka.. If you have any good in your heart dan Allah kar ka barni a nan.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata..Wllhi tsoro nake..”


“Ina tsaurin idon naki da courage d’in suka tafi.? Maima kika ce..?” Ya kannare idanu yana dubanta kafin ya jinjina kai yace “Yauwa kika ce A cheap low life police Officer wanda baida komai bai dogara da komai ba face karb’an bribe baida kud’ad’en  da zai sauk’e miki bashinki..? Ko ba haka kika fad’a ba..”


Ta shiga girgiza kai still tana hawaye.


Jinjina kai ya kuma kafin yace “Dama na fad’a miki Zaki maimaita. Well, wannan Matsiyacin D’ansanda ya biya bashin kuma harda sadakinki.. And yau zan tabbatar miki cewa ke d’in Low life ce. Wannan d’akin shi ya kamaci low life irinki.. You’ll spend the night here, tareda Karnukan nan dan na tabbata kema d’in Kariyace.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofar ya rufe yai ficewarsa.


Daskarewa Sadiya tai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam ya mata. Rufeta yayi a wannan k’aramin d’akin dake jikin d’akin Karnuka wanda motsi kad’an sukai zataji balle suyi haushi. A hankali taji k’afafunta suna silalewa. Ta tak’ure waje guda tana duban d’akin mai tsananin duhuwa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai take iya ambata.. Bata tab’a jin ta tsani wani mutum a rayuwarta irin Mu’azzam ba. Ta rintse idanunta tana fad’in “Allah na tuba.. Na tuba ka yafe mun.. Abba ka yafe min.. Umma kizo ki cecen.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Na shiga uku ni Sadiya..!” Tana jin sanda Mu’azzam ya fice daga gidan ya rufe gate. Da gaske barinta yai a gidan Ta kwana tareda Karnuka.. Wani wawan haushin da karnukan suka saki saida taji har tsakiyar k’wak’walwarta.. Ta saki k’ara dan tsoro tana mai duk’awa had’ida toshe kunnuwanta da duka hannayenta biyu, ta rintse idanunta dikda tsananin duhuwa dake cikin d’akin wanda ko tafin hannu baka iya gani.


**


A can Fufore kaw anyi carko carko akan Safeenah wacce mai gyaran k’afa yazo ya yana d’aure mata k’afar tata. Sai kuka take tana fad’in ta shiga uku gashi sam batasan yanda Mu’azzam yake ba tin jiya basu had’u ba sannan bata isa ta tink’ari Inne ta tambayeta Ina Mu’azzam yake ba. Ga wayarsa sam ta kasa samu.. Safeenah sai kuka take tana fad’in zafi k’afar take mata.


Inne na zaune saman kujera mai gyara na kuma jan k’afar Safeenah na ihu. Inne tace “Ki rufe mana baki.. Uban da yasa kika zuba ma yarinyar tsantsi a hanya.. Gashi nan da yake batada hakkinki ta tafi gida lafiya ke kuma kin taka abinda kika zuba mata kinji ciwo.”


Safeenah tace “Inne amma ke Wai bakiga abinda yarinyar nan tayi bane.. Wllhi na tabbata akan abinda tayi Mu’azzam zai iya b’ace mana b’att a dena ganinsa a gidan nan.. Ai dai Kinsan halinsa Kinsan yanda yake abubuwa.. Wllhi Allah na tabbata kan abinda yarinyar nan tai zai iya barin gidan nan without informing anyone... Wayyo Allah Malam mai d’auri Kaja a hankali..!” Ta kuma fad’a tana k’ok’arin janye k’afarta.


“Ki rufe wa mutane baki.. Allah k’ara. Gobe ma dan Allah ki k’ara..!” 


Musaddiq ya tina sanda Ajidde zata tafi tace masa anyi babu shi bayi kallon birgiman bijimi a k’asa ba.. Dik a tinaninsa D’aya daga cikin shanun gidan ne ya fad’i k’asa yana birgima ashe fad’uwar da Safeenah tai ne take son sanar dashi kenan.. Ya girgiza kai kurum yana ba tareda ya ce komai ba. Sai kuma ya dubi Safeenah dake ture turen baki tana motsa k’afar da k’yar yace “Next time sai a kiyaye.. Allah ya kara sauk’i..”


Bata amsa ba ta rakasa da harara ga hawaye saman fuskarta.


Bayan kowa ya mata sannu an watse Meema ta matso kusanta tace “Sannu Adda Feenah..”


Harara Safeenah Ta aika mata kafin tace “This is all your fault you know.. Saida nace miki kar mu saka mata ruwan tsantsi ba lallai ta taka ba Kikace mahaukaciya ce bata tafiya a natse dole zata taka gashi nan ita bata taka ba ni na taka..”


Meema Ta tab’e baki tace “Addah Feenah ni fa da nace ki zuba mata ai bance kibi bayanta ki duba ko ta taka ko bata taka ba, ke da kanki kiyi wannan shawarin naki.. Toh ki fad’a mun how am I at fault..?”


D’an gyara zama Meema tai tana kuma fito da idanu waje had’i da kwantar da murya tace “Addah Feenah.. What if this is your Karma..! Kin tuna matar nan da kika taka mata k’afa da Mota ranan a k’ofan Police Headquarters.. Karma is backfiring you Addah Feenah..” Tai maganar tana mai d’aga gira sama had’ida jinjina kai alamun tabbatarwa.


Safeenah ta aika mata harara tace “Don’t even start Meema..”


Meema ta murmusa tace “Wllhi Addah Feenah it’s possible hakkin matar nan ne ya kamaki.. Gashi irin abinda kika mata ya sameki.. Now we have no option dole mu k’ara kwanaki a garin nan har ki warke.. Who knows mai rikiceccen mijin nan naki zai tareda budurwarsa yanzu da kika gurgunce a nan..”


Pillow dake gefenta ta d’auka ta jifawa Meema tana fad’in “Get out before I kill you Meema..!” Tai maganar tana huci zuciyata na tafarfasa. Fuskar Maleeka kurum take hangowa tareda mijinta. Lokaci guda Ta saki k’ara tana mai jifa da pillow d’in. Dik shegiyar Ajidden nan ne ta jawo mata.. Wllhi babu abinda zai hanata cin uwar yarinyar nan..


Meema Ta k’unshe bakinta ta fice tana dariya.


**


Misalin k’arfe 11:00pm ya shigo gidan, Kai tsaye sashen Daddy ya wuce dan ya hango wutan parlor a kunne alamun  Daddyn bai kwanta ba kenan.


Da sallama ya shigo saman bakinsa. 

Daddy dake zaune daga center d’aukeda wasu documents yana sorting. A hankali ya soma zame k’aramar gilashin dake mak’ale idanunsa yana mai amsa sallamar Mu’azzam d’in. Nan fari’arsa ta k’aru.


“A’a Officer sauk’ar yaushe.” Daddy ya fad’I yana mai fad’ad’a murmushinsa.


Murmushin ne saman fuskar Mu’azzam d’inma sanda ya k’araso saman carpet d’in. Gaban kujeran da Daddy ke zaune ya duk’a ya zauna yana mai gaida Daddyn. 


Da sauri Daddy ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Yanzu ne zuwan Naka kokuwa ka jima da shigowa garin..”


Mu’azzam ya d’an girgiza kai yace “No Daddy tin da yamma na shigo na biya na kula da wasu al’amran ne..”


“Oh toh toh Allah sarki.. Kun taho tareda iyalin taka ce...?”


Tambayan da Daddy yai masa saida ya sanya k’irjinsa bugawa sannan sosai yaji nauyin Daddyn dan har cikin ransa ji yake abinda yake yima Safeenah bai kyautawa. Iyayenta sunada mutunci musamman Daddy. Gaba d’aya sai yaji bai kyauta ba. K’ok’arin saita kansa ya d’anyi yana mai girgiza kai “No Daddy.. Fitowar gaggawa nayi shiyasa na taho ni kad’ai..”


Daddy yace “Allah sarki.. Toh yayi kyau Allah dai ya taimaka yai maka jagora..”


Muazzma ya amsa da “Ameen Daddy.”


“Ya ka baro mutan gidan Inne da ‘yanuwanka.. Ya jikin Mamyn naka kuma.. Ana samun progress..?”


“Kowa lafiya Daddy.. Jikin Mamy Alhamdulillah da sauk’i sosai.. Mun sameku kafiya..”


Daddy yace “Toh Alhamdulillahi... Lafiya lou an gode Allah.. Gashi ka shigo ka samu ina duba takardu..”


Mu’azzam ya soma k’ok’arin mik’ewa yana fad’in “Barin Barka kayi aikinka Daddy..”


Daddy yace “No zauna abinka.. dama akwai maganar da nake so muyi amma yanzu naga dare yayi so zamuyi maganar gobe idan Allah ya kaimu.. And akwai yanda nake so muje dani dakai..”


Mu’azzam ya jinjina kai cikeda risinawa yace “Okay Daddy Allah ya kaimu.. Mommy ta kwanta koh..”


Daddy yace “Eh kasan Mamar taku kaman kasa ce nan da nan tayi bacci..” Ya k’arashe cikeda barkwanci irin tasu ta manya kafin Muazzma ya mik’e yana d’an Murmusawa. Saida safe yaima Daddyn kafin ya fice ya nufi side d’insa. Saidai tinda ya shiga d’akin tinanin yarinyar ya addabesa. K’ok’arin kauda tinanin yai kafin ya fad’a shower.


No comments

Powered by Blogger.