Gidan Aro 23


*23*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


K’ura masa idanu Mu’azzam yai yana duban yanda Alhaji Isyaku ke rarraba idanu kaman an jefa mage a tukunya.


“Alhaji, nasan ka gane ni, domin kuwa munje gidanka a satin da ya gabata Nida abokin aikina domin gudanar da bincike..”Ya k’arashe yana d’ago kai had’ida duban Assad dake tsaye saman kansa.


Alhaji Isyaku yai saurin jinjina kai yana duban Mu’azzam d’in harma da Assad “Eh K’warai Yallab’ai.. Na ganeku.”


Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Good, bazamu cutar dakai ba.. Hasalima mu Jami’an tsaro ne, inada Tabbacin ka fahimci cewa bazamu cutar dakai ba bayan  abokan aikina sun Kub’utar dakai daga hannun wad’anda sukai garkuwa dakai..”


Cikin sauri Alhaji Isyaku ke jinjina kai yana fad’in “Wannan haka ne Rankaidad’e, wllhi kud’in aurena suka sace nid’in sabon ango ne Yallab’ai..”


Fuzar da huci Mu’azzam yai cikeda takaici kafin yace “Wannan ba matsalata bace Alhaji, tambayoyin da zaka amsa mana yanzu sune damuwata.. And I suggest that you cooperate with us dan muji dad’in gudanar da aikinmu kuma kaima mu maidaka gida a mutunce.”


Alhaji Isyaku ya zuba masa idanu kafin yace “Maiyasa baku kaini police station ba kuka kawo ni nan wajen..?”


Mu’azzam dake murza hannayensa kad’an yana duban Alhaji Isyakun gajeren murmushi ya kumayi kafin yace “Kasan da cewa yarinyar dake yunk’urin aura ‘yantadda suna bibiyarta..?”


Alhaji Isyaku ya zaro idanu waje yana mai tuna kalan tashin hankali da iftila’in da ahalin Sadiya ke ciki dik dalilin tsohon saurayinta Sagir.. Idan ya fahimta Wato yarinyar suke hari shiyasa sukai yunk’urin d’aukesa. Yai saurin d’ago kai yana fad’in “Yallab’ai wllhi tsautsayi ne ya sanyani neman auren yarinyar nan.. Wllhi bansan komai ba.!”


Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Baka San komai ba..? Then Maiyasa ka firgita..?”


“Yallab’ai satan mutane ya zama ruwan dare a k’asar nan dole na firgita..!” Alhaji Isyaku ya fad’i jikinsa na rawa.


Mu’azzam ya jinjina kai yace “Wannan shine dalili...?” Shiru ya gifta gumi na tsartsafo ma Alhaji Isyaku yana kuma zaro idanu waje, lokaci guda yanajin babu abinda zai kuma had’asa da Sadiya balle yai tinanin aurenta..


Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Alhaji idan muka kaika ofishinmu dole sunanka ya shiga record sannan hakan ka iya shafan reputation d’inka harmada sana’arka.. And once you’re proven guilty  dole a maka ka a kotu akumayi shari’a dakai.. Amma ni na maka alk’awari idan ka sanar damu iyakacin gaskiyar abinda ka sani zamu sakeka tin daga nan basai mun tafi ofishinmu ba.. Just cooperate Alhaji and tell us how you’re connected to this man.!” Ya k’arashe yana mai aje masa hoton Danger saman hannunsa.


Da mamaki Alhaji Isyaku ke duban hoton kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam, lokaci guda ya girgiza kai yace “Rankaidad’e wllhi kaji na rantse maka bansan wannan mutumin ba.. Wllhi Allah shine shaidata ban sansa ba ban kuma tab’a ganinsa ba sai yanzu daka nuna min hotonsa.”


Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Amma kanada masaniyar mutumin nan sunanka ya soma ambata mana a lokacin da muke bincikensa.. Ta yaya zaka ce baka sanshi ba bayan shi d’in ya sanka..”


Alhaji Isyaku ya girgiza kai yace “Wllhi wllhi Allah d’aya ne ban sanshi ba, bansan yaya akai ya sanni ba.. Koda yake ba abun mamaki bane dan ya sanni dan ni mutum ne mai huld’a da mutane da dama. Sannan Allah ya rufa mun asiri a unguwarmu inada tabbacin idan ka shigo layin gidana na d’aya daga cikin gidajen da ake kwatance dasu.. So ba abun mamaki bane dan ya kama sunana Rankaidad’e..”


Mu’azzam ya tsaresa da idanunsa da suka gama kad’awa sukai jazir “Alhaji zan sake tambayarka nicely ka sanar dani abinda ke tsakaninka da mutumin nan.!”


Jin zai fice a giya yasa Assad saurin kamosa suka fice daga wajen.


Dukan garu Mu’azzam d’in yai da hannunsa yana duban Assad “What now..! Mai kuma na aikata..? I was only questioning the man..”


Fuzar da huci Assad yai yace “Baka aikata komai ba Mu’azzam, amma kana shirin aikatawa, ka d’auko mutumin nan ba bisa k’aida ba kana interrogating nasa, and not only that. you’re forcing him to admit to the crime he’s not committed. Bayan cewa koda ya aikata laifin yanada damar da zai k’i yin magana har sai an barsa ya gana da lawyer d’insa..Anya Mu’azzam ka d’auko hanyar da zai b’ulle.. Don’t allow your anger to consume you.. Kabi komai a sannu.. I’m positive mutumin nan Iyakacin gaskiyarsa yake fad’i babu abinda ya Sani. Kaman yanda na fad’a maka he’s caught in the middle ne sabida auren yarinyar da ya tassama yi, Toh haka d’in ne.. Instead mu tsaya muna b’ata lokacinka kan tuhumarsa da neman mutanen da suka tassama kidnapping d’insa mukai.. Dan na tabbata babu abinda zamu samu wajen mutumin nan..”


Mu’azzam ya d’ago fuskarsa data rine zuwa ja sabida tsananin tashin hankali, lokaci guda ya shafi goshinsa da hannunsa guda kafin yace “Kai baka tunanin mutumin nan had’a baki sukai da mutanen da suka tassama sacesa.. Baka tunanin hakan na iya kasancewa cikin plan d’in Danger.. Danger is a very dangerous person Assad, he’s capable of everything.”


Assad ya jinjina kai yace “Na sani Danger is Dangerous, amma tambayar da zan maka a nan shine idan bakinsa d’aya da Danger Maiyasa zai sacesa.. Sannan idan bakinsa d’aya da Danger bazasu amshe kud’ad’en dake hannunsa ba..”


Mu’azzam ya zuba masa idanu kaman mai nazarin sai kuma ya murmusa yace “Kana magana  as if you can’t read criminal minds  and how smart they can act.. Yanzu dashi da Danger duk zasu iya shirya haka dan su karkatar da hankalin jami’an tsaro dan kawai abun yayi kaman Su d’in suna bibiyar Alhaji Isyaku ne sabida Auren Sadiya da yake yunk’urin yi.. I believe ka amince zasu aikata fiyeda haka.”


Assad ya nusa yace “Everything is possible in a situation like this saidai hanyar da ka d’auko zai iya sakamu cikin matsala gaba d’aya.. Maimakon muyi solving case d’in zamu iya b’ata komai da wannan hanyar daka biyo ba bisa k’a’ida ba..” Shiru Assad ya d’anyi yana mai tsaresa da idanu kafin yace “But wait, idan har kana tinanin Danger da mutumin nan bakinsu d’aya ne Maiyasa ka hana mutumin auren yarinyar..? Sannan Maiyasa kai ka aureta.. Kana tunanin zasu iya cutar da ita ne..?”


Shiru Mu’azzam bai basa amsa ba sai mugun kallon da yake aika masa. Lokaci guda Assad yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Now I get it.. Ka aureta ne to give her protection..!”


“O C’mon just shut up Assad..!”


Assad yaci gaba da fad’in “Yes gaskiya ne Mu’azzam dan ka bata kariya daga sharrin su Danger ka aureta.. Because she’s there target.. Ko baka fahimci hakan yanzu ba I’m positive gaba zaka fahimci haka.”


Da mugun mamaki Mu’azzam ke kallonsa yanaji yanda yake k’ok’arin k’irk’iro wani zance, kan mai zai bama wannan yarinyar protection Iyakacin abinda ya Sani shine he still needs her for his mission ne. Gajeren tsaki yai yana mai girgiza kai yake furta “You are not serious Assad. Bansan ya akai kake aiki k’ark’ashin NPF ba. You should be a clown and not a police officer..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya koma cikin building d’in yanda Alhaji Isyaku ke zaune.

Assad ya take masa baya yana mai girgiza kai kad’an.


Suna k’arasowa Mu’azzam ya dubi Alhaji Isyaku yace “Alhaji zamu k’yaleka ka tafi.. Zamu maidaka Gida.. Motarka tana nan a waje wad’annan abokan aikin nawa sun taho maka da Ita nan.. Amma still idan kanaso zaka iya reporting ‘yanta’addan nan da suka tasamma saceka suka kuma sace maka kud’ad’enka.”


Alhaji Iskyaku Yai saurin girgiza kai yana mai zaro idanu yace “Ni wllhi bana fatan abinda zai had’ani da ‘‘yanta’addan nan, yo a k’asa irin wannan da aka maida satan mutum kaman an d’auke ‘ya’yan kaji ai abun na gode ma Allah ne da bai k’addari zan sha wahala hannun mutanen nan ba.. Kuma tinda na tsira Alhamdulillah.. Sannan wannan yarinya ko a k’afa aka d’aura mun ita zan kwance na gudu dan na kula tsautsayi da bala’i ke bibiyarsu.. Ban tab’a jin k’aran harbe harbe ba saida nace zan aureta.. Na gode maku matuk’a da ceton rayuwata da kukai..”


Assad ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Kar ka damu Alhaji, hakan aikinmu ne.. Kula da al’umman k’asa tsare masu rayuwarsu lafiyarsu harmada dukiyarsu.. Kuma kar ka damu da izinin Allah zamu gano mutanen da suka maka wannan aika aika and they will answer to the law. Ku daina karyar ma jami’an tsaron k’asar nan da fad’in cewa sun gaza Gwabnati ma sun gaza.. NPF tana iya k’ok’arinta a kullum domin taga Ta kawo k’arshen ta’addanci da rashin tsaron da ya addabi k’asar nan..A koda yaushe ku saka a ranku cewa mu ‘yansanda abokanku ne ba mak’iyanku ba.. Dukda cewa da yawa sun mana shaida cewa akasarin mu gurb’atattu ne ba haka abin yake ba domin kuwa akwai na k’warai a cikinmu.. Kaman dai ko wacce irin Sana’a akwai gurb’atattu akwai na K’warai..”


Alhaji Isyaku ya jinjina kai a hankali yana duban matashin D’ansandan. Lokaci guda ya kuma masu godiya kafin suka nufo waje gaba d’aya.


Suna fitowa waje Alhaji Isyaku ya kasa key ma Mota, jikinsa dik sai rawa yake.. Gani yake kaman ‘yantaddan zasu kuma dawowa.


Ya lek’o da kansa ta glass yana fad’in “Rankaidad’e ko zaku taimaka min dan Allah.. Wllhi ban iya tuk’a motar.”


Assad ya dubesa kafin ya dubi su Mu’azzam sai kuma yace da Alhaji Isyaku “I’ll drive you home Alhaji.”


Alhaji Isyaku  cikeda jin dad’i yake godiya wa Assad “Na gode matuk’a yallab’ai, aikam bazan iya tuk’a mota ba dan har yanzu tsoro bai sakeni ba.. Gani nake kaman idan ina tafiya ‘Yantaddan nan zasu dawo.. Na gode na gode k’warai.”


Assad ya dubi Mu’azzam yai masa alama da hannu kan cewa zai kai Alhaji Isyaku gida. Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin suka soma fitowa tareda su Yusuf suka nufi motocinsu suna basa update abinda ke faruwa a CID.


Shiru Mu’azzam yai yana nazarin abducting Alhaji Isyaku da aka tasamma Yi wanda baida haufi idan har Alhaji Isyaku baida wani connection da Danger Toh ko shakka babu masu bibiyan yarinyar ne suka kuskuresa. A fili ya furta “Danger..! Zan kamaka dik yanda ka shiga ka fita.. Da k’udurar Ubangiji.!”


K’aran shigowar sak’o cikin wayarsa da yaji ne ya sanyasa ciro wayar aljihu yana dubawa. Lamba ce Babu suna, sannan abinda kawai aka rubuta jikin sak’on shine _BAD_


Ya nanata alphabets d’in a hankali “BAD” sai kuma ya fad’a in word “Bad..!” Ya nanata yafi sau UKU. Lokaci guda ya yanke shawarin kiran lambar.. Kafin yakai ga kiran lambar wani sak’on ya sake shigo masa. Wannan karon ga abinda aka rubuta.


_BAD is your enemy_ 


A hankali ya kuma furtawa “Bad is your enemy”. Yai shiru yana kuma duba. What does this mean.?


Saurin sake danna kira yai amma wayar bata shiga, a kashe take.


Take wata sak’on Ta kuma shigo masa da wata lamba ta daban 


_BAD is ruining your home._


Dafe kansa yai kad’an yana duban lambobin da aka turo masa wad’annan sak’on dasu wanda ko shakka babu wasa da hankalinsa mai turo sak’on yake shiyasa yake turo masa da lambobi barkatai dan kar yayi tunanin tracing lambobin.


Bai ida tinanin ba wani sak’on ya kuma shigowa da wani lamba daban duk dai akan BAD.


_BAD is very BAD_


A hankali ya fuzar da fuci yana duban lambobin kusan guda uku.


Cikin natsuwa ya nufi motarsa lokacin ana kiraye kirayen sallar magrib. Tinanin Bad bai daina Yawo a kwanyarsa ba. Yana driving yana nanata kalmar Bad. 


Wata sak’on ta sake shigo masa da wata lamba daban duk dai akan bad


_You need to find BAD_


A fili Mu’azzam ya furta “Who are you BAD..?!”


**


A gidansu Sadiya kaw tana k’udundune a d’aki cikin bargo sai rawa jikinta yake alamun zazzab’i ya kuma rufeta, ko kukan ma ta kasa yi yanzu kam. Tabbas da ace zatai kukan da taji sa’ida cikin zuciyarta. Tana nan kwance tana kar karkarwa tana iya sauraro muryoyinsu daga tsakar gidan yanda yanda Malam Liman da Ummanta da shaidu guda uku suka had’u suna warware bashin da Tabawa ke binsu Wanda Wai mutumin da ya aureta ya biya masu.. Kuma Wai ba kowa bane wannan mutumin face d’asandan nan da Ta tabbata da zai iya samun daman harbeta da zai aikata hakan.. Ta yaya za’ace wannan mutumin shine mijinta.. Ta yaya za’ace an mata aure haka bagatatan saikace wata ‘yar tsana.. Shin talauci hauka ne kokuwa dai rashin mahaifinta ne yasa akai mata haka.. Allah sarki yau Ta kuma yarda cewa mahaifi Katanga ne mai k’arfi kan iyalansa duk talaucinsa da babunsa kuwa.. Ta tabbata da ace Abba yana nan sam bazai zuba idanu ai mata irin wannan auren ba.. Tabbas maraici akwai ciwo cikinsa.. Tabbas wanda bai d’and’ani d’acin maraici ba baisan rashi a rayuwa ba.. Yau taga ranan mahaifinta sannan taji ciwon rashin sa a gareta.. Gashi nan a aurar da ita saikace wata taguwar da aka ciwo a yak’i wacce batada wani daraja.. Wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo mata. Tana jin sanda Tabawa ke gud’a tana fad’in ta yarda k’wallan mangoro ta huta da k’uda.


Saida su Malam Liman da shaidu suka fara ficewa kafin Tabawa ta mak’ale kud’ad’enta ta fice.


A zauren gidan Tabawa Malam Liman da D’an Rakiyarsa Munkaila kuka tsaya suna jiran Tabawar.


Tabawa tana shigowa tai wani birki tana bada balance dan bataga alamun mutane ba da shike dare ne.

Rawanin Malam Liman ta hango ta gane sune.


“Ahh Haba Malam yo ai sai ka razanen.!”


Malam Liman ya Washe baki yace “Yo banda abinki Tabawa ai su kud’i ‘yan sirri ne..”


Tabawa tace “Haka ne..” Lokaci guda ta juya ta basu baya Liman sai nad’e carbi yake cikin hannunsa yana gyara rawani yana ‘yan lek’e lek’e irinta marassa gaskiya.


Tabawa ta k’irgo dubu biyar ta mik’awa Malam Liman.


Malam Liman ya amsa yana juya kud’ad’en “Haba Tabawa. Haba Tabawa dubu biyar fah nake gani.. Dik wa’azin dana dingayi ina d’aga jijiyan wuya duba fah ki gani jijiyoyin wuyata da mak’oshi na har ciwo suke.. Ace duk a dubu biyar zasu tsaya.”


Tabawa ta karkace tana dubansa “Toh Malam kazarka ce ta kama..? Kaga idan bazaka amsa dubu biyar d’inba kana iya dawo da ita dan wllhi dama da k’yar na baka.. Ni Tabawa kud’i basa fita hannuna idan bazan sami k’ari ba.!”


Malam Liman ya girgiza kai yace “Ai shikenan kuma.. Dama idan da kwad’ayi da wulak’anci.. Allah amfan.. Kai Munkaila Shige muje..!” Ya tasa k’eyar Munkaila suka shige Tabawa na rakasu da bak’ak’en magana.. “Kaji min rashin kunya saikace da guminsa cikin kud’ad’en..”


Tana nan tsaye tana sababi su Over suka shigo rungume da ledar kud’i suna ‘yan lek’e lek’e.


Over sai bin bayan Su Liman da ficewarsu kenan daga lungun da kallo yake, yana wani duk’awa yana d’aura hannunsa saman gira irin idan haske ya maka yawa kana so ka tantance abu kai kace ba dare bane haka Over ke kannare idanu yana fad’in “Kaiiiii!  wa nake gani a nan..! Kai bara’uba ashe Malam ma yana d’an capcapkewa kenan..!” Suka fashe da dariya shida abokansa suna fad’i cikin muryarsu Ta ‘yan maye “Wllhi mutumin nan yama raina mana hankali yake taramu yana mana wa’azi ashe yana zagayowa idan dare ya raba..! Toh wlllhi ya sake cewa zai mana wa’azi zamu fasa k’wai.. Fayaaa zamu masa harsashi d’aya ta mar..!”


Tabawa tai saurin tura k’ofar tana fad’in “Kai Kai ya isa.. Wannan ba matsala Ta bace ku ta Shafa.. Ina labarin aikin da na sakaku..? ya ta kasance tsakaninsu da Alhaji Isyaku.


Over ya d’ago mata ledar kud’i yana nuna mata kafin yace “Tin yaushe muka cika aiki.. Amma saidai ‘yansanda sun biyomu sanda muka d’aukesa..”


Tabawa Ta zaro idanu waje tana dafe k’irji “Ince baku sakamu cikin matsala ba.. Allah yasa babu wanda yaga fuskokinku..”


Over ya dara irinta basawa yace “Haba Over da yaransa ai ba na wasa bane. Mun cika aiki yanda ya kamata. Mun amshe miki kud’ad’en Uwar Daba.. Amma Uwar Daba ina kika samo bindigar da kika bamu ne..? Kodai safaran makamai kike ne.!”


Tabawa Ta buge bakinsa tana fad’in “Kai over koda wasa kar na sake ji ka fad’I kalaman nan.. Bani bindigar ta k’arashe tana fuzge bindigar ta nad’eta cikin bak’in k’yalle.


Lokaci guda kuma idanunta suka sauk’a kan hannun over dake rungume da ledar kud’in ta dara cikeda jin dad’I tana mai amshe kud’ad’en hannun Over,  ta d’an tsakuro wani abu Ta basu tace su fara somin tab’i da wannan “Aikinku yayi kyau Over.. Sai mun had’e sauran bayanin.” Ta k’arashe tana rungume kud’ad’en.


Over yace “Baji uwarmu Ta daba.. zamu had’e ai.. Ya toh Baabaa mu Ware mana..!” Ya k’arashe yana duban abokan nasa. Lokaci guda suka fice suna tangad’i irin yanda ‘yan maye suke.


Suna ficewa Tabawa ta murmusa hannayenta biyu rik’eda kud’ad’en da ta dafe a ranan, d’aya hannun bashin Ta ne da Angon Sadiya ya biya, d’aya hannun kuwa kud’in Alhaji Isyaku ne data tura su Over suka sato mata.


A fili take furta “Alhaji Isyaku kenan abokin k’ullawa da warwarewa.. Da Tabawa kake zancen.. Wanda baiyi sharan masallaci  ba dama zaiyi na Kasuwa. Baka auri yarinyar ba kuma naci kud’inka naci banza.! Na jefi tsuntsu biyu da Dutse guda.” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya.


**

Umma da Sadiya na zaune Umma tana mata fad’an ta tashi taci wani abu idan ba kashe kanta take son yi ba, Su rungumi k’addara Su fawwala wa Ubangiji lamarinsu. Yana sane dasu yake aiko masu jarabawa daki daki.. Tai k’ok’arin cin jarabawar kar tai ma rahamarsa butulci.


Da k’yar Sadiya ta mik’e ta zauna Umma ta zuba mata paten dankalin hausar ta d’an soma tsakura kenan suka jiyo ana kwankwasa k’ofar gidan.


Suka dubi juna a tare itada Umma suna kuma duban lokaci, agogo ya nuna k’arfe 8:30 na dare.


Umma ce ta d’an soma k’ok’arin mik’ewa da dafe dafe dan itama k’afar nata bai warke ba. Sadiya ta dubeta taga yanda take k’ok’arin tashi da k’yar.


Lokaci guda ta girgiza kai tace “A’a Umma zan duba.”


Umma tace “Anya zaki iya kuwa.? Kiga fah kaman jiri zai kifaki.”


Sadiya ta mik’e da k’yar tana fad’in “Babu komai Umma zan iya.”


A haka ta nufo tsakar gidan tana tafe da k’yar tana dafa bango dan mugun juwa ke k’ok’arin kaita k’asa.


koda Ta bud’e k’ofar da tsananin mamaki take duban wanda ke bugun k’ofar.


“You.!!” Ta furta zuciyarta na wane irin tsinkewa idanunta suna kuma firfitowa waje.


Lokaci guda kalaman Malam Liman ya soma dawo mata, sunan mutumin da aka aura masa ita.. Rawar da jikinta yake ya k’aru.. Babu shiri cikin tsananin tsoro da firgici ta soma k’ok’arin maida k’ofar zata rufe saidai kafin tai wani aune ya saka hannunsa guda ya tare k’ofar. D’aya hannun nasa yai amfani da ya damk’o arms d’inta yana fad’in “Don’t you dare try that.!”


Su duka biyun huci suke suna duban juna, fuskokinsu dab da juna suna iya jin fucin numfashin junansu babu kaman Sadiya da take ji zafin jikinta na k’aruwa tin sanda ya kamota.


Lokaci guda Mu’azzam yaci gaba da fad’in “You’re coming with me, wether you like it or not.!”


Cikin tsananin huci itama take dubansa, lokaci guda taji Ta tattaro duk strength d’in da ya rage mata “I’m not going anywhere with you.. Kai baka isa ka tilasta min ba.. I’m not your wife and I’ll never be..!” Ta fad’i tana kiciniyar k’wace jikinta daga rik’on da yai mata.


Da k’arfi take k’ok’arin turasa tana fad’in “Let go.. let me go.. Ka sake ni nace ko kuma na kira maka ‘Yansanda.!”


Murmushi wannan karon ya sakar mata yana kallon yanda take kokawan k’wace kanta daga rik’on da yai mata wanda da hannu guda kurum yai hakan “Go ahead and call the police.. Let’s see waye yakeda bayanan da zaima ‘Yansanda.. For as far as I know ban aikata wani abu illegal ba.. On the contrary..” Wannan karon matso da fuskar yake sosai kusan nata kafin ya manna bakinsa saitin kunnenta guda yace “Don’t you think I should report you instead.? Sabida nayi wasting kud’ad’en da a garbage like you bata cancanta ba.!” 


Wannan karon sosai bugun zuciyarta ya k’aru k’walla masu zafi suka ciko idanunta.. Batasan sanda wani irin k’arfi yazo mata ba, ta turasa baya da duka k’arfinta.. Hawaye ne ke gangaro mata sanda ta shiga nunasa da yatsa “You stay away from me.. Kar ka sake zuwa nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.


Daidai lokacin Umma Ta k’araso dan taji shirun Sadiyar yayi yawa.


Da mamaki Umma ke duban Mu’azzam dake tsaye cikin tsananin tsimewa yana duban Sadiya dake kuka.. Umma tana k’arasowa Sadiya ta k’arasa ta rungumeta tana kuka “Umma kice ya tafi dan Allah.. Umma kar ki bari ya d’aukeni..”


“Unfortunately, I’m not leaving this place without my wife..!” Suka sinkayo muryar Mu’azzam na fad’in haka cikin dakewa.


Jikin Umma yai sanyi, musamman da ta tina cewa shid’in Wai mijin Sadiya ne sannan a shari’ance yanada cikakken iko akanta.


Umma na hawaye take dubansa “Dan Allah kayi hak’uri abi komai a sannu.. Dan Allah na rok’eka..”


Gyara tsayuwarsa yana duban Umma wannan karon “Tell your Daughter to come with me willingly.. Or else..”


Katsesa Sadiya tai cikin huci “Or else what.. What are you going to do Mr Inspector.? Zaka janyoni da k’arfi ne ko zaka sanyani tafiya gidanka da k’arfi ne..!”


Wannan karon bai kuma tsayawa sauraronta ba ya k’arasa ya shiga janyota, Umma tana kuka tana rok’onsa yai hak’uri ayi magana cikin natsuwa amma kaman cewa take yaci gaba da janye Sadiyar.. Sadiya na kuka tak’i sakin Ummanta Mu’azzam bai fasa janyeta ba. Kuka take tana fad’in “Umma dan Allah karki barshi ya tafi dani.. Umma ki taimakeni.. Kar ki barshi ya d’aukeni...!” Muryarta ne ya katse sakamakon sakewa da jikinta yai ta zube cikin hannunsa sumammiya..


Umma ta rarrafo da k’yar tana jijjiga ‘yarta tana ambato sunanta shiru bata tashi ba.. Babu shiri ta mik’e da k’yar ta tafi kawo ruwa dan ta zuba mata.. Saidai Umma na mik’ewa Mu’azzam ya sunkumeta cikin hannunsa...Daga haka Sa kai yai ya fice daga gidan d’aukeda Sadiyar cikin hannunsa.

No comments

Powered by Blogger.