Gidan Aro 21*21


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Rana ce mai tsayi ta kasance a gidansu Sadiya, wajen Sadiya da mahaifiyarta. Ga duk wanda ya sansu zai fahimci tashin hankalin da suke ciki ya ninka wanda suka shiga a lokacin da Sagir ya tafi ya bar Sadiya a ranan bikinsu. Aure ne da basu san Mecece makomar auren ba. Iyakacin abinda suka sani shine K’addarar su rubutacciya ce tuntuni. Kuma bazasu tab’a tsallake K’addarar da Ubangiji ya gindaya masu ba. ‘Rabbi yassir wala tu’assir’ shine kad’ai abinda bakin Umman Sadiya ke iya nanatawa a wannan rana mai matuk’ar tsawo a garesu.


Wai abin mamaki saiga Tabawa gidansu Sadiya harda d’ibo masu kid’an k’warya..


Da baya da baya ta shigo gidan tana tik’an rawa, tin daga lungun ma take tik’an rawa har suka iso gidan..


Baki sake Umma ke dubanta da tsananin mamaki. Tabawa kaw ko ajikinta, sai tik’an rawa take tana sabada harda k’awayenta ‘yan rakiya su Asabe mai kayan Koli.


Umma ta zuba tagumi tana duban Tabawa da k’awayenta daketa faman juya mazaunanai suna tik’an rawa. Masu kid’i da rawan da Tabawa ta kawo kaw tuni yaja hankalin mutane akai cincirindo a gidan.


Tabawa taci d’amara ta shiga rabon drinks da ruwa ma bak’i harda snacks danginsu cake da donuts Tabawa tazo dasu kwali kwali tana rabo wa mutane.


Umma ta k’arasa tana k’ok’arin janyo Tabawa amma Sai k’ok’arin janyota Tabawar ma take fad’i take “Yauwa Uwani dan Allah ki saki jiki ki tik’a rawarki na yau d’aya.. Mance kina takaba ai dai biki ne.. Bikin tilon d’iyarki mace.. Kaman yanda aka fasa wancan auren nata bamu fata wannan ma a fasa shisa muke nuna Farin cikinmu.. Yo dole ma na nuna Farin cikina za’a biya ni hakkina, zan yarda k’wallan mangoro na huta da k’uda “Anyiiirriiirii.. Ungun mai kid’a saka mana Sabada kinji..”


Hakan bai hana Umma janye Tabawa ba tana fad’in “Kiji tsoron Allah Tabawa gidan mata mai takaba kike.. Nasan kina Farin ciki za’a biyaki kud’ad’enki amma dik abubuwan da kikazo kinayi mu bama buk’ata..”


Dogon tsaki Tabawa taja tana mai kuma turo kallabi gaba “Aifa saidai kiyi Uwani, yau kwana da kwanaki ina bin sahun kud’ad’ena na samu yau za’a biyan ki wani ce kar na nuna Farin ciki.. Wllhi ko kece kika mutu ba mijinki ba sai na nuna Farin ciki da sauk’e nauyin bashin nan da za’a maku.. Kai Kai Kai aci gaba da gashi.. Aci gaba da kid’a aci gaba da juya mazaunai wacce batadashi haushi ya kasheta.. Ahayyee yiririri nanaye sama mataaa..!” Ta k’arashe tana mai juyi da baya.


Cikin zuban hawaye Sadiya ta fito zata janye mahaifiyarta aiko nan Tabawa ta fincikota ta jefata tsakiyar fili suna rawa suna zagayeta.. Duk’awa tai wajen tana kuka mai ban tausayi tana rok’onsu su fice masu daga Gida suji da abinda ke damunsu amma kaman cewa take su k’ara.


Umma ta isa ta janye d’iyarta suka koma gefe suka rungume juna suna hawaye, Azo har gidansu afi k’arfinsu sabida kawai basu dashi.


**


A can gidan Alhaji Isyaku kaw yaci uban wanka yasha gayu cikin sabuwar d’inkin babbar rigarsa, yadai zuba shiga irinta angwaye sai zuba k’amshi yake bakinsa har kunne sabida Farin ciki. A haka ya fito ya tadda Maman Sabeera da Sabeera a parlor sunyi jigum jigum hawaye saman fuskar Sabeera dake kwance cinyar Mamanta. Kallo guda ya masu ya wani d’auke kai irin ko a jikinsa.


Maman Sabeera ta mik’e ta nufesa “Alhaji Wai yanzu dan Allah bazaka fasa auren yarinyar nan ba..? Fisabilillahi yarinyar nan fah ‘yar cikinka ne..”


Katseta yai da fad’in “Kar ki sake cewa ‘yar cikita ce balle ki haramta min matata.. Ni ban haifeta ba bani ne ubanta ba kin fahimta..”


Maman Sabeera ta goge hawayen da suka gangaro mata “Amma ko baka haifeta ba ka haifi Aminiyarta, Kai yanzu ko gudun maganan mutane bakayi kawai ka tashi ka auro mana k’awar d’iyarka aminiyarta.”


“Gudun magana.? Toh waye yake sauraron maganganun mutane.. Ai bari kiji Rahina Idan kika ce zaki tsaya sauraren abinda mutanen duniya zasu fad’i akanki ne kina tareda babban aiki.. Ke bari kiji na fad’a miki babu uban da ya isa ya hanani Auren Sadiya.. Ko Ubanta ne ya taso daga kabari bai isa ya hana auren nan ba.. Matsa ki ban waje kar Malam Liman suyita jirana an had’a mutane a masallaci.. Shirirtar banza da wofi.” Ya k’arashe yana bangajeta gefe.


Maman Sabeera ta fad’i nan k’asa wajen tana mai sakin kuka tana kiran mijinta ko kulata baiba ya sunkumi bak’ar leda wanda kud’ad’en da zai biya bashin Sadiya da mahaifiyarta ke ciki..


Sabeera tuni ta K’araso ta duk’a ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna masu sakin kuka mai ban tausai.


Yana fitowa daga gidan nasa ya shiga aza babbar rigarsa shi kad’ai ya nufi motarsa dan dama a waje hai parking d’inta, Baba Mai gadi yace dashi a dawo lafiya..


Baban Sabeera yana shiga Mota sai gani yai wasu k’artan maza guda uku fuskoki rufe da bak’ak’en masks sun bud’e motar suma sun shigo..


Cikin tsananin firgici da tsoro Baban Sabeera ke fad’in “A’a.. A’ah su waye ku.. Mai nai maku..? Dan Allah kar ku cutar dani.. Wllhi nid’in Sabon ango ne yau ake Bikin aurena.. Dan Allah Kuji tausayi na kar ku cutar dani..!” Yai maganar hularsa tana karkacewa hannayensa rok’onsu dasu sai rawa suke.


Wanda yake zaune a backseat ya buga ma Alhaji Isyaku k’asar bindiga a k’eyarsa yana fad’in “Shut up.! Rufe mana baki and keep on driving..!”


Jiki na matuk’ar rawa Alhaji Isyaku ke tuk’a motar, a haka har suka fice daga layin.


Sun d’auki hanyar barin gari kenan motar dake bayansu tasha gabansu, lokaci guda suka firfito daga cikin motar  suna pointing d’insu da bindigogi suke fad’in “This is the police, freeze..!”


Tuni suka soma bata kashi da mutanen da suka kira kansu ‘yansanda wanda suma ba kayan ‘yansandan bane jikinsu da kuma mutanen da sukai abducting Alhaji Isyaku.


D’aya gardin ya finciki ledar kud’in Alhaji Isyaku suka ci gaba da harbi tsakaninsu da ‘Yansandan kafin suka nufi daji a guje.. D’aya D’ansandan yai k’ok’arin bin bayansu yayinda d’ayan ya k’arasa wajen Alhaji Isyaku dake duk’e hannayensa ta bayan kansa ya kifa Kan nasa Sai b’ari jikinsa yake sabida tsaban tsoro da hargitsin Bindiga da yaji ya kuma gani.


D’aya daga ‘yanta’addan ya harbi D’asandan da yabi bayansu a hannu wanda hakan yasa dole ya dakata da bin ‘yanta’addan ya dafe hannunsa dake fitar da jini yana cije baki. A haka ya dawo wajen d’aya D’anuwan nasa da Alhaji Isyaku dake duk’e wajen.


Alhaji Isyaku ya d’ago yana dubansu yana fad’in “Na gode na gode maku.. Kun ceceni hannun ‘yanta’addan nan.. Wllhi nid’in sabon ango ne yau ake d’aura aurena. Muyi sauri Mu k’arasa Amaryata da Malam Liman suna jirana, dikda B’arayin nan sun sace kud’ad’en zansan yanda zan nemo wasu kud’ad’en..”


Kafin yai shiru d’aya mutumin cikin wanda sukai acting kaman ‘yansanda suka kuma taimakesa ya murmusa yace masa “Not too fast Alhaji..!” Yana ida fad’in haka ya buga ma Alhaji Isyaku k’otar bindiga a k’eyarsa. Tuni Alhaji Isyaku ya fad’i sumamme. Nan take suka jefasa cikin motarsu sukai tafiyarsu.

**


Tun su Malam Liman suna jira har dai suka gaji da jira, Tun ana k’irga mintoci hardai aka koma k’irga awanni, babu Alhaji Isyaku babu dalilinsa, su Tabawa kaw ana can gidansu Sadiya ana tik’an rawa. 


K’arshe Malam Liman ya dubi ‘yan committee na masallaci yana basu hak’uri kan rashin zuwan Alhaji Isyaku da ya tarasu a wajen nan ya kuma sab’a alk’awari.. Malam Liman yaci gaba da fad’in “Mai yuwa ya canza shawari ne bazai iya biya masu wannan tsugugun kud’ad’en matsayin bashi ba.. Yanzu bansan mai zance wa yarinyar nan da mahaifiyarta ba.. Bansan mai zan sanar dasu ba domin kaw mahaifiyarta ta damk’a min ragamar auren yarinyar a hannuna matsayin awalinta.. Bayin Allah Kuji tausayin wad’annan bayin Allah ku biya masu wannan bashi zaku sama lada wajen Ubangijin..”


Shiru babu wanda yakeda wad’ann tsugugun kud’ad’e, babu wanda zai iya biyan wad’annan kud’ad’e.. Kud’i ba naira dubu ba wuri na gugan wuri har Naira Miliyan d’aya da rabi..


Nan fah mutane suka soma k’ok’arin watsawa daga masallaci Liman na k’ok’arin dakatar dasu ko Allah zaisa Alhaji Isyaku ya canza shawari yazo ya biya masu bashin nan..


Ana tsaka da watsewa Malam Liman ya mik’e yana fad’in “Bayin Allah ku dakata.. Ku dakata Kuji tausayin na k’asa daku idan akwai mai kud’ad’en nan ya taimaka ya biya bashin nan.. Shin babu wanda zai iya sauk’e nauyin bashin nan..?”


Kaman daga sama Malam Liman yaji wata murya “Akwai wanda zai biya bashin..!”


A tare Liman da ‘yan tsirarun da suka rage a masallacin suka juyo suna duban mutanen da suka shigo cikin masallacin.


Wani matashi ne sanye da  bak’ak’en kaya suit fuskarsa rufe da bak’in glasses saidai suna shigowa harabar masallacin saurayin ya zame glasses d’in dake mak’ale idanunsa fuskarsa Ta bayyana, taredashi wani mutumi ne   wanda shi ya d’an manyanta sannan manya kaya ne sanye jikinsa shi.


Cikeda tsananin mamaki Assad dake zaune wani b’angare a harabar  masallacin ya b’adda kama yana monitoring duk abindake faruwa cikin masallacin gameda auren Sadiya da Alhaji Isyaku kaman dai yanda Mu’azzam ya saka sa, ya mik’e in a shock yana duban Mu’azzam da sam baisan yaushe ya iso garin ba.

Assad ji kawai yai bakinsa na furta “Unbelievable.!! You.. Are.. Unbelievable.. Mu’azzam Gamji..!”


Mu’azzam da Uncle Salman suka ci gaba da takowa cikin masallacin a natse, suna K’arasowa suka mik’a ma Malam Liman hannu sukai masabaha.


Malaman Liman ya koma ya zauna yana nuna masu waje cewa su zauna suma. 


Uncle Salman a Mu’azzam suka zauna daga gefe. Fari’an Malam Liman ya k’aru, lokaci guda yake furta “Allahu Akbar, nasan na kirki bazasu k’are ba.. Dikda cewa taimako dan Allah yayi wuya a duniyar nan tamu na k’warai bazasu k’are ba.. Bayin Allah yanda kukayi niyyan taimakon nan Ubangiji ya biyaku da Aljannah, Allah ya saka maku da mafificin Alheri. Yanda kuka yayewa wad’annan bayin Allah damuwarsu Ta Gidan Duniya Ubangiji ya yaye maku damuwarku ta lahira..”


Uncle Salman yaji addu’o’i tuni ya d’aga hannunsa biyu yana amsawa da “Ameen Malam..!”


Mu’azzam ne ya d’anyi gyaran murya yana mai matso da bakinsa kusan kunnen Uncle Salman, cikin sigan rad’a yake furta “Uncle let’s finish the deal.”


Uncle Salman ya jinjina kai kafin ya tura hannu cikin babbar rigarsa ya ciro kud’ad’e cikin leda ‘yan dubu dubu.. Lokaci guda ya ajiyesu gaban Malam Liman “Wannan Naira miliyan D’aya ne da dubu d’ari biyar bashin da ake bin iyalan marigayi Malam Ibrahim.”


Malam Liman ya jinjina kai cikeda jin dad’i, harda sujudu shukur yai yana d’aga hannaye sama yana Godiya wa Ubangiji “Alhamdulillahi Allah yayi yau an cire ma wad’ann bayin Allah k’angin bashi.”


Baikai aya ba Uncle Salman ya kuma ciro wasu kud’ad’en cikin aljihunsa, wannan karon rapan ‘yan dubu dubu ne bunch d’aya wato hundred thousand Kenan.. Ya kuma ajewa gaban Malaman Liman.


Baki sake da mamaki Malam Liman ke dubansa wannan karon “Alhaji wannan kuma na menene.?


Uncle Salman ya gyara zaman babbar rigarsa kafin ya soma fad’in “Sunana Alhaji Salman Gamji.. Wannan d’an D’anuwana ne Mai suna Mu’azzam Gamji.. Bakada dogon binciken da zakai akanmu domin ahalinmu sananne a fad’in garin Abuja da kewaye..”


Ya d’aura hannunsa guda saman kud’ad’en da ake bin Su Sadiya bashi yace “Wannan bashin da ake bin Sadiya da mahaifiyarta ce.” Ya kuma d’aura d’aya hannunsa kan Naira dubu d’arin yace “Wannan muma Naira dubu D’ari ce Sadakin D’ah na Mu’azzam ga d’iyar da aka mik’a maka jagorancin ragamar aurenta Wato Sadiya..”


Kafin Malam Liman ya kuma wani magana Uncle Salman ya zaro Doguwar takarda ya mik’awa Malam Liman “Wannan takarda ce kuma shaida ce dake tabbatar da cewa d’ah na Mu’azzam lafiyayye ne baida wata cuta da zata hanasa aure, sannan genotype d’insa AA ne wanda a k’a’ida zai iya auren mace mai ko wane irin genotype koda kuwa SS ce domin na sani a akasarin masalattanmu ana ci gaba da wayar da kai cewa idan za’ayi aure a auna jini asan wani irin jini mutum ke d’auke dashi domin guje ma tsautsayi na samun yara da za’a Zo aita faman jinya suna shan wahala iyayen na shan wahala wanda ansan akwai k’addara amma idan akwai hanyar da za’a iya bi a kiyaye faruwar hakan yin hakan shi yafi alfanu dan ko a musulunci akwai rigakafi kuma an amince da hakan..”


Tinda Uncle Salman ya soma magana Malam Liman ke dubansa, ya d’an girgiza kai yace “Alhaji idan na fahimceka kaima ka biya bashin ne domin ka amsar wa d’anka auren Ita Sadiya..?”


Uncle Salman ya jinjina kai yace “K’warai kaw Malam Liman, ai idan ban b’ata ba dama aurarta zakayi ma Alhaji Isyaku ko ba haka ba..”Malam Liman ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Amma Ai da yardar ita yarinyar da mahaifiyarta mukai za’a bada aurenta ga Alhaji Isyaku amma bamuyi dasu za’a aurarta ma d’anka ba.. Alhaji Aure ai ba abun wasa bane..”


Uncle Salman ya murmusa yace “K’warai kuwa aure ba abin wasa bane shiyasa na gabatar maka da komai tin kafin ka tambaya.. Sannan na tabbata Ita yarinyar dama auren sadaukarwa zatai dan a biya masu bashi da don soyayya ba.. Bana ko haufi yarinyar bata son Alhaji Isyaku.. Amma fah idan bazaka bamu auren ba muma zamu tattara i namu i namu.. Allah bamu Alheri..” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin janyo kud’ad’en..


Liman ya tsunduma tunanin alk’awarin taimaka masu Sadiya da yayi, yana tsoron kar wannan itace damarsu ta k’arshe kuma ta kufce masu.. Idan yarinyar da mahaifiyarta suka tafi gidan yari baijin zai tab’a yafe ma kansa bayan alk’awarin taimaka masu da yayi.. Sannan mahaifin yarinyar marigayi yana d’aya daga cikin members na committee na masallacin, bazaiso Hakan Ta faru ga ahalin marigayi ba.. Toh amma idan ya aurarta ga wannan matashi ba tareda saninsu ba shin yayi daidai..? Gaba d’aya kan Malam Liman ya cunkushe ganin dama na k’arshe na k’ok’arin kufce masa.. Take yaji b’angare mafi girma na zuciyarsa tana fad’in Kar ka bari mutanen nan su fice daga masallacin nan bakada Sauran zab’I, zaka jima kana jin ciwo idan Tabawa ta kai iyalan marigayi gidan kasu..


Lokaci guda Malam Liman ya dakatar dasu.. Mu’azzam ya saki murmushi da gefen bakinsa.


Take Malam Liman yace ya amince idan zasu sauk’e masu Sadiya nauyin bashin nan.. 


Uncle Salman ya juya ya dubi sauran tsirarun mutanen dake haraban  masallacin dan dama ba cikin masallaci suke ba zaune suke haraba yace “Bayin Allah ku zama shaidu..!”


Nan take cika cikan aure suka had’u, aka samu waliyi, Wakili, Siga da kuma Sadaki da shaidu nan aka d’aura auren Mu’azzam Marwan Gamji da amaryarsa Sadiya Ibrahim kan sadaki Naira dubu d’ari lakadan ba ajalan ba.


Assad Daskarewa kurum yai dan ya kasa yarda da abinda Mu’azzam ya aikata kawai dan ya cimma burin bincikensa.

“You.. Are a Savage Mu’azzam Gamji.!” Assad yace yana mai girgiza kai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam d’in ya aikata.


Ana haka Wasu matasa ne suka shigo masallaci a hargitse.. Gaba d’aya su Malam Liman suka mik’e harmadasu Mu’azzam suna duban matasan daketa faman haki.. Malam Liman ya soma tambayarsu “Kai lafiya.. Lafiya kuka shigo masallaci haka nan.. Subhanallahi..!”


D’aya daga cikin samarin ya duk’a yana haki “Malam Alhaji Isyaku Chanji ne..!”


Malam Liman ya juyo ya dubi su Mu’azzam kafin ya dubi saurayin yace  “Subhanallahi.. Mai ya sami Alhaji, taron nan fah isowarsa muke jira Allah baiyi za’ayi auren dashi ba.. Dan dik munyi zaton janyewa yayi..”


“Malam wllhi wasu mutane ne mukaga Sun sakasa a mota sunyi wancan hanyar dashi.” D’ayan ya fad’i yana haki.Malam Liman dasu Mu’azzam  suka dubi juna cikin kad’uwa, Sai kuma Liman ya dubi Matashin yace “Wasu mutane ne kenan suka d’aukesa.”


“Malam ina tunanin ‘yan Garkuwa ne domin duk sun rufe fuskokinsu da bak’ak’en yadi babu wanda yake iya ganin fuskokinsu..”


“Subhanallahi..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!” Abinda Su Liman ke iya fad’i kenan..


Wannan karon Assad ne ya k’araso yana tambayar saurayin ta Ina Su Alhaji Isyaku sukai..


Malam Liman yace “Ai kuwa kafin a watse daga taron nan ya zama dole a sanar da ‘yansanda.”


Mu’azzam ya dubi Malam Liman yace “Kar ka damu Malam ni d’ansanda ne zamu kula da wannan..!” Lokaci guda ya ciro wayarsa yana neman backup dan dama yasan masu bibiyan Su Sadiya ba lallai Su k’yale Alhaji Isyaku ba muddin sukaji zai aureta tinda yarinyar da ahalinta suke targeting.. Lokaci guda ya fice a harabar masallacin waya manne kunnensa.


A can gidan Alhaji Isyaku kaw labari ya isa masu cewa anga wasu mutane fuskokinsu rufe da bak’ak’en masks sun sace Alhaji Isyaku hankalin Maman Sabeera da Sabeera ya kuma tashi.. Babu shiri Sabeera ta fice ta taho gidansu Sadiya.


Masu kid’an Tabawa suna tsaka da kid’a su Tabawa na rawa Sabeera ta shigo a birkice, tayo kan Sadiya Ta cakumota tana jijjigata take fad’in “Ina mahaifina Sadiya..? Ki fad’a mun su wanene suka sace Babana.. Ki fad’a mun Sadiya..!”


Toh fah Wannan shine ana wata ga wata Wai an sace Alhaji Isyaku Ango. Cak sautin kid’an k’waryar ya daina tashi, su Tabawa kaman wad’anda aka zare masu battery tuni suma suka dakata da rawar da suke.. Kowa ya juyo yana duban Sabeera dake jijjiga Sadiya tana fad’in ina Takai mata mahaifi.
No comments

Powered by Blogger.