Gidan Aro 20



*20*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

O




Ikon Allah, wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan kowa na mamakin haukar yarinyar. Inne Ta k’arasa ta rik’eta tana fad’in “Ke Ajidde.. K’alau kike..? Lafiya kiketa zunduma ihu haka..? Ko wani abu ne ya faru..?”


Ajidde ta Ware idanu tana kallon mutanen da sukai cincirindo a parlorn Kowa ya zuba mata idanu. Ta kai dubanta ga Mu’azzam wanda yakai mak’ura wajen had’e rai kafin ta maidoda da dubanta ga Safeenah wacce ke tsaye tana aika mata mugun kallo ko ba’a ce ba kasan shak’e take da ita.


Inne ta dubi Mutanen da Ajidde ke duba Wato Safeenah da Mu’azzam, sai kuma ta maidoda dubanta ga Ajidden “Ajidde lafiya kike.. Wani abu ya faru ne..?” Ta tambaya tana mai tsareta da idanu.


Cikin sauri Ajidde ta jinjina kai alamun Eh.. Inne tace “Mai ya faru.. Ko wani abin ne ya sami Nuratu..?” 


Ta girgiza kai a hankali tana duban Safeenah da har lokacin huci take tana aika mata mugun kallo ga Mu’azzam dake gefe shima yana aika mata razanannen kallo hannayensa hard’e ta baya.


Matsawa bayan Inne tai cikeda tsoro still idanunta naga Mu’azzam da Safeenah take fad’i a hankali “Inne Allah ne ya toni asirinsu..”


Inne ta kuma dubanta da mamaki “Asirin Su Wanene ya tonu..?”


Ajidde tai saurin shigewa bayan Inne tana lek’en Mu’azzam da Safeenah wanda kallon mutanen parlorn ya dawo kansu.


Mamaki ya mugun cika Mu’azzam ganin yanda yarinyar nan ta tara masa jama’a sunata kallansa babu gaira babu dalili.


Aunty Shemau baki sake take duban Ajidde Cikeda takaici tace “Da sukayi mai..?”

Ajidde Ta dubi Inne sai ta kuma dubansu, lokaci guda take girgiza kai..


A kufule Safeenah tayo kanta tana fad’in “Ke yarinyar nan na kula kanki rawa yake.. Tin zuwanta gidan nan kike shiga hurumina.. Cikinmu wanene sa’anki da zaki tara mana jama’a.. Zo nan ki fad’a Uban mai mukai..”


Inne Ta tare Ajidde tana fad’in koda wasa kar Safeenah ta tab’ata..


Lokaci guda Ajidde dake tsalle bayan Inne take fad’in “ Inne wllhi Allah ne ya toni asirinsu, ni ba lek’ensu nayi ba k’ofa suka mance bud’e shine na gansu suna abinda ‘yaniskan turawa suke a tv.. Wllhi Inne Shi naga sunayi bari ma kiga..” Ta juya Ta manna ma garu kiss tace “Wllhi Inne haka naga sunayi...”Tai maganar cikeda gadara irin ita ga mai gaskiya. Cikin zuciyarta kaw duban Mu’azzam take tana ayyana dama dik wannan famkam famkam d’in nasa na K’arya ne da bogi iskancinsa yake a b’oye.


Meema baki sake take dubansu ta kuma dubi Ajidde ga wani irin dariya dake taso mata Wai abinda ‘yaniskan Turawa keyi a tv.. Kai wann yarinya anyi shashasha Ta bugawa a jarida. Babu hali Meema tai dariya ganin yanda Mu’azzam ya gumun had’e rai yana aikawa yarinyar razanannen kallo.. Sad’af sad’af Meema ta shige tana kuma k’unshe bakinta da dariya keta k’ok’arin kufcewa.


Uncle Salman ya girgiza kai kafin ya dubi Mu’azzam dake tsaye kaman wanda aka dasa idanunsa sunyi jazir, ya maido da dubarsaga matarsa Shemau yace “Ni na wuce Office.”


Musaddiq ya dafe goshinsa cikeda takaici kafin Shima ya juya d’aki dan yanzu kam ya gama yarda haukar Ajidde yafi k’arfinsa. Haka aka dinga barin parlorn cikeda takaici da kunyar abinda Ajidde tai.


Hindu ta janyo Ajidde tana fad’in “Zo muje Ajidde lokacin maganin Aunty Nuratu yayi..”


Ajidde ta saki baki tana duban yanda babu wanda ya kuma tankata a parlorn, ta dubi Mu’azzam da idanunsa suka kad’a sukai jajir yana aika mata razannan kallo.. Safeenah kaw ta Kasa yarda haukan yarinyar ya kai har wannan matakin.


Hindu ta janye Ajidde  parlorn ya rage saura Inne Mu’azzam da kuma Safeenah.


Mugun kallo kurum Inne ke aika masu “Banaso naji wani ba’asi daga wajenku, ya maku kyau.. Ni bazan zuba maku idanu haka nan ba.. Na riga na gama magana, yau d’in nan zanyi magana da Salman a soma gyara maku b’angaren can gefen. Abin ya isheni haka..” Ta dube Safeenah dake ture turen baki tace “Tashi ki bamu waje kije ki saka sitira jikinki zanzo naji dake idan na gama dashi..”


Baki a ture Safeenah ta tashi ta bar parlorn tana kuma gyara zaman rigar baccinta ta nufi yanda takeda tabbacin Zata cimma shegiyar Ajidden nan.


Mu’azzam daketa faman murza zoben hannunsa yana sakin huci yana hango fuskar Ajidde sanda take nunasu tana fad’in asirinsu ya tonu, saurin d’agowa yai yana duban Inne data tasa sa gaba “Inne Yarinyar nan is a complete lunatic.. Mahaukaciya ce Inne. Bai kamata a barta ta kusanci Mamy ba in the first place, wayasan mai zata aikata mata idan haukarta ya tashi.. Gaskiya Inne lokaci yayi da za’a kori yarinyar nan daga gidan.”


Katsesa Inne tai da fad’in “Kai tafi can ka rufe mun baki dama tin can kana son kasancewa da matarka kak’i a Kai maka ita.. Kaketa wani hanya hanya.. Ai gaskiyar Ajidden ne da tace Allah ya toni asirinka..”


Mu’azzam ya shafa kansa kad’an yana kuma sakin huci “Inne, nifa bance Safeenah bazata tare ba, kawai banso a raba mun hankali ne a halin yanzu.. And Inne gaskiya yarinyar nan zata daina zuwa gidan nan daga yau ni ban ma yarda da maganin nata ba.. Idan har tana bada magani ma kanta ya kamata Ta fara yi.. Because she’s sick in the head.!”


Inne Ta kuma katsesa da fad’in “Kanka farau.? Nace Kanka farau..? Wane D’ansanda ne Aure ya hanasa bincike.. Kuma bari kaji da kyau na Fad’a maka Ajidde lafiyarta lau ehe, tanada hankalinta yarinta ce kawai ke d’awainiya da ita.. Sannan jikina na bani cewa maganin Nuratu na tattare da ita da izinin Allah..Babu wanda ya isa yasa a sallami Ajidde ko a hanata zuwa.. Ai Kai da matar taka kune manyan mahaukata da zaku shige d’aki ku bar k’ofa bud’e, ku ya kamata ayima magani ba Ajidde ba.”


Da mamaki Mu’azzam yake duban Inne yanda ta dage tana kare yarinyar nan da k’arfin gaske, ga gaskiya amma tana kaucewa.


 Inne Ta mik’e tana ci gaba da sababi ta shige ta barsa nan zaune kaman an dasa sa .. Lallai zai karya yarinyar nan, zai mata horon da bazata sake gangancin shiga huruminsa ba. Idan ma wauta ne ko hauka duk sai ya cire mata Su. Ya mik’e a fusace ya fice daga parlorn. Banda iskanci gaban kowa da kowa harda ma’aikatan gidan zata dubesa tace ta kamasu suna aikata abinda ‘yaniskan turawa suke aikatawa a tv, wai Ta gansu suna  suna kiss shida Safeenah harda manna bakinta jikin garu tana nuna yanda sukai Wato.. Lallai ma yarinyar nan Ta samu waje, kuma dik Inne ce ta sakar mata da yawa har wannan raini yake yunk’urin shiga tsakaninsu, yarinyar da yakeda tabbacin ko hak’orinsa k’wara d’aya bata tab’a gani ba..Aiko kafin ya bar gidan Sai ya cire mata haukar nan nata. Ji yake gaba d’aya ransa a jagule, ya kuma tsanar yarinyar fiyeda misali.



A can d’akin Aunty Nuratu kaw Safeenah ce keta kokawan kamo Ajidde Hindu na raba tsakaninsu “Yau sai na koya miki manners dan ubanki.. Sai na cire maki wannan k’auyancin naki..” Safeenah ta kuma fad’i tana kuma yowa kan Ajidde da tuni ta daka tsalle ta b’oye bayan gadon Aunty Nuratu. Hannayen Aunty Nuratu ta kama tana fad’in “Dan Allah kar ki bari ta daken kinji dan Allah.. Nice dai Ajidde mai baki magani.” Yanda take maganar kace Aunty Nuratu na sauraronta ne.


Hindu kaw Sai k’ok’arin dannar Safeenar take.. Daidai nan Inne ta shigo.. Ba tareda tace komai ba ta janye Safeenah tana fad’in “Shige muje kece ya kamata ki fara koyan manners d’in kafin ki koya mata.”


Inne tana janye Safeenah Ajidde ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana furta “Wai Allah na tsira..”


Hindu ta dubi Ajidde tace “Ajidde Maiyasa kika aikata hakan.. Kan mai kika kunyata Safeenah da Baban Hajiya a gaban jama’an gidan nan..”


Ajidde ta dubeta da mamaki irin ita batayi laifi ba sune masu laifi “Ah Toh ni mai nayi.? wayace su aikata tinda sunsan babu kyau.. Naga dai wannan jiya jiya tazo gidan nan.. Dodanniya.”


Hindu ta girgiza kai tana mai jinjina shashancin Ajidde “Toh ke baki San matarsa bace, bakisan sud’in sunyi aure bane..” 


Baki sake Ajidde ke dubanta tana nanata kalman aure cikin zuciyarta.. Tinani take Meye ma auren.. Sai kuma ta kame baki ta rufe da duka hannayenta biyu tana zaro ido waje. 


Hindu ta girgiza kai tace “Ai dai nasan a shekarunki Kinsan mai kalmar aure yake nufi.. Ajidde ke macece ya kamata ki rage wannan wautan naki Kinga kefa budurwa ce da wanann sakarcin naki babu wanda zaice yana sonki, nan gaba kad’an Kema auren nan zakiyi ya kamata kike natsuwa kinji koh..”


Baki sake Ajidde ke kallonta “Chabb kujita Wai nima aure zanyi.. Wllhi har kin bani kunya.. Tabb ni koda nake ce ma Inna Kyallu zata sami surki k’arya nake, ni wllhi kunya ma nake ji.. Ni dik kinsa inata jin kunyarki.. Ni yau Allah bazan iya duban fuskarki ba.. Na shiga uku.. Kujita Wai aure..” Ta k’arashe tana tura kanta tsakankanin cinyarta Wai kunya takeji..


Hindu ta girgiza kai kurum tana mai gauraya maganin kafin ta isa ta tallafo Aunty Nuratu tana fad’in “Kizo ki bata ko itama kunyarta kikeji yau..”


Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai kunyar Hindu take. Ta Kasa d’agowa ta tallafi maganin “Toh ni dan Allah ki daina kallo na wllhi kunya kika bani..”


Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai ita kunyar Hindu take, d’agowar da zatai kaw ta hangesa bak’in k’ofa fuskar nan tasa tamau kaman ma yafi na ko yaushe.. Wani irin tsalle Ajidde tai ta haye bayan gado jikinta sai rawa yake.

“Na shiga uku na mutu na lalace, shikenan harbeni zai.!” Tana maganan tana duk’e lungun Gado jikinta sai rawa yake idanunta a rintse.


Hindu Ta rik’e baki tana fad’in “Oh yau naga ikon Allah ni Hindu.. Wai meye yanzu kuma kika gani..?”


K’ofa Ajidde ke nuna mata tana fad’in “Gashi can a k’ofa Mama Hindu wllhi harbeni zai.. Ki ceceni..”


“Shi wane..Ni banga kowa ba..”


Sai sannan Ajidde ta bud’e idanunta a hankali sai kuma ta dubi k’ofar taga baya nan.. Toh kodai gizo ya fara mata ne.. Sabon tsoro ya bayyana a fuskarta.. Itakam tak’i jinin mutumin Allah ya gani tsoro yake bata.


A b’angaren Mu’azzam kaw tinda yaga ganinsa kawai da tai ya firgitata ya bata tsoro Sai ya shige d’akinsa dan yayi shirin tafiya masallacin Juma’a da shike ranan Juma’a ne babban Rana. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Ashe k’aryar rashin kunya da k’auyanci kike.. Tinda kika shiga gonar muazzma kin b’ata yarinya.’


Yana cikin shirin ne wayarsa ta soma ringing Assad ne mai kira..



Cikin sauri ya janyo wayar ya d’aga dan yasan update Assad zai basa gameda bincikensu.


Saidai baisan sanda cufflinks d’in dake rik’e hannunsa yana k’ok’arin mak’alawa hannun rigarsa ta fad’i ba.. Cikin rarrabewar kalma yake furta “What do you mean she’s getting married Assad..? I mean.. She can’t get married now.. We still need her for our mission..!”


Ya mik’e babu shiri yana mai zagaya cikin d’akin sanda Assad yaci gaba da fad’in “And that’s not the case Muazzma.. Mutumin nan idan ya aureta d’auketa zai daga garin nan, idan ma Danger bibiyarta da ahalinta yake kaga shikenan bazamu cimmasa cikin sauk’i ba..”


Muazzma ya fuzar da wani fuci yana girgiza kai alamun a’a “No Assad.. We can’t let this happen...  Danger is still on the loose.. Hakan na nufin bazamu samesa nan kusa ba..” Ya d’anyi fasali kafin yace “Wai ma tsaya waye mutumin da zai aureta d’in..?”


Assad ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Bazaka yarda da abinda zan fad’a maka ba.. Amma bari na baka labarin komai in details..”


Mu’azzam ya k’urama window idanu yana sauraren Assad dake labarta masa yanda auren Sadiya da Alhaji Isyaku zai kasance a gobe Asabar..


Wani irin gumi ne ke tsartsafowa Mu’azzam, Wai gobe auren yarinyar da Alhaji Isyaku “Wait Assad mutumin nan ba shine ya dinga sanar damu munanan halayyar yarinyar na kwad’ayin abin duniya da bin maza masu abin duniya ba.. Ba shine ya sanar damu irin shaidar da akai ma yarinyar na rashin kamun kai a unguwar ba.. Ba shine ya rabata da d’iyarsa ba..? Idan duka yayi wad’anann abubuwan Maiyasa zai zago yace zai biya mata d’inbin bashin dake kansu idan za’a bashi aurenta.. Ni fah ban yarda da mutumin nan ba Assad, idan baka mance ba bincikenmu ta Kansa ya fara biyowa kafin mu isa ga yarinyar domin kuwa Danger sunansa ya soma mentioning mana.. Assad I won’t let this happen.. I’ll stop this marriage from happening no matter the cost.”


Assad ya nusa yace “Bashin zaka biya masu kokuwa d’auke yarinyar zakai..? Muazzma kar fa ka mance You’re still on your suspension, you’re not allowed to go to work ko kuma Kai wani abu ba tareda umarnin NPF ba.. Nasanka Mu’azzam, I know exactly how your mind works.. Don’t get yourself into another trouble.. Mubi hanyar da ya kamata musan yanda zamu b’ullo wa al’amarin..”


Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Idan bazan Yi  da yarda da amincewan NPF ba then I’ll have to do it my way..”


Daga haka katse kiran yai ya k’arasa shiryawa a gurguje yana tina Wai auren gobe gobe ne.. Baisan mai zai aikata ba, baisan mai zai iya faruwa ba. Ya San yayi nisa da garin. Hakan na nufin baisan ko zai iya dakatar da wannan aure ba.. 


Yana ficewa bai zarce ko Ina ba sai Factory.. Nan ya nemi ganin Uncle d’insa Salman.  Sectary d’insa ya ma Mu’azzam iso..


Mu’azzam yana zaune yana k’are ma Factory d’in kallo, yana kallan workers sai shige da fice suke, yakai dubansa ga office d’in Uncle Salman wanda Office d’in Mahaifinsa kenan a baya.. Ya tina sanda yake k’arami mahaifinsa na zuwa dashi Factory d’in wasu lokuta, lokaci guda kuma ya tuna a wannan wajen ya rasa Mahaifinsa.. Ya tina sanda aka kawo masu gawan mahaifinsa a daskare ya k’ank’are bayan yayi jamming kansa a D’akin K’ank’ara da ake aje nama.. Lokaci guda yaji wani irin rauni na ziyartar zuciyarsa.. Sam sai yaji baison kasancewa cikin Factory d’in.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa kenan Sectary d’in Uncle Salman ya k’araso yai masa iso yace ya shiga.


Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin ya nufi office d’in.


Can saman kujerar mahaifinsa ya hango Uncle Salman yana zaune yana juyi cikin kujerar.. Wannan murmushin tasa saman fuskarsa.


“To what do I owe the honor..?My dear Nephew..” Ya k’arashe yana mai daidaita zaman nasa saman kujerar lokaci guda ya nunawa Mu’azzam d’in kujera mai duban table d’insa.


Mu’azzam ya k’araso ya zauna “Uncle, Barka da rana..” Ya fad’i yana mik’a masa hannu alamun musabaha.


Babu musu Uncle Salman ya mik’a masa hannu suka gaisa kafin yace “Har ka gama da commotion d’in da ka tayar a gidan..?”


Mu’azzam ya fahimci mai Uncle Salman yake nufi amma Sai ya kawar da zancen da fad’in “Uncle ever since my father passed away, ban tab’a tambayar wani alfarma daga wajenka ba..  Wannan karon nazo na tambayeka alfarma If I’m really your nephew..”


Gyara zama Uncle Salman yai yana duban Mu’azzam d’in wanda ga dukkan alamu magana ce mai girma yazo masa da Ita. Sannan babu tsoro ko kad’an cikin idanunsa wanda kusan ko yaushe idan ya dubi idanun yaron abinda yake iya hangowa kenan.. Rashin tsoro.


Ya kuma gyara zamansa kafin yace “Allah yasa ba Kud’i kazo nema ba dan idan kud’i ne zan iya cewa wanda Sirkinka ke tara maka yayi yawan da har zai iya fin nawa. You know you’re lucky Mu’azzam, dikda ka zab’i career wanda ba wani kud’in arziki zaka tara da wannan career d’in Naka  irin D’ansanda, You still have your inheritance a wajen Baban matarka.. Saidai kuma idan kaima baka yarda dashi bane..”


Mu’azzam ya d’an murmusa kad’an kafin yace “I trust Daddy with my life.. Ko mai zaiyi da dukiyata na yarda dashi d’ari bisa d’ari kuma na yarda bazai tab’a yin abinda zai cutar dani ba.. Kar ka mance Wannan shine karo na farko da zan tambayi alfarma daga wajenka, Uncle Salman. And inaso ya tsaya between us.. Juts the two of us.. Let’s call it uncle to nephew gift tax..” Ya k’arashe idanunsa akan Uncle Salman d’in, gajeriyar murmushi wacce yake yinta da gefen bakinsa saman fuskarsa.


Lokaci guda ya kuma gyara zamansa cikin kujerar kafin yaci gaba da fad’in 

“If you consider me your Blood, Uncle.. Zaka min wannan alfarmar.. Just this once..!” Wannan karon gumi ne ke gangarowa daga cikin gashin sa zuwa goshinsa sanda yai maganar.. Kana gani zaka fahimci har cikin zuciyarsa yake maganar.


A hankali Uncle Salman yake jinjina kai tamkar wanda ya tina wani abu yana duban Mu’azzam d’in wanda shima dubansa yake. 


“Alright fine.. Yes.. Zan maka wannan alfarmar my dear nephew, and you have my word it will stay between us.. Babu wanda zaiji, not my mother, not my brother, not even my wife..”


Mu’azzam ya sakar masa murmushi da gefen bakinsa su duka biyun suna duban juna “Thank you.. Uncle..” Ya fad’i still yana dubansa.


A hankali Uncle Salman ya jinjina masa kai shima murmushin ne saman fuskarsa.


**


Aunty Shemau ta d’an girgiza kai tana mai saita zaman wayar a kunnenta “Wai dama Aunty Hajara kinaso kice min Safeenah da Meema basu sanar daku zuwan nasu ba.. Toh mai Daddy yace.?”


Mommy ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Wllhi nasan bazai wuce shawarin Meema ba dan Safeenah dai bata amfani da k’wak’walwarta sai abinda Meema tace shi takeyi.. Tin jiya Daddy ke fad’a Maiyasa ba’a sanar dashi ba sai bayan Sun tafi. Nadai samu nace munyi ta neman wayar Office d’insa ance yana meeting nasa wayar kuma bata shiga.. Sannan da nace Mu’azzam ne yace saidai Safeenah taje can ta samesa sai baice komai ba, Kinsan wannan d’aniskan yaron yacce kika San ya lashe zuciyar Alhaji ne.. Duk abinda za’a ce indai Mu’azzam ne bai cewa komai.. Sami’ina wa’ad’a’ana ne. yanda kika San ya masa asiri wllhi.. Wani irin so yake ma Mu’azzam  wanda tuni ya rufe masa idanu baya ganin laifinsa duk kalan laifin da zai..”


Aunty Shemau Ta nusa tace “Yanzu dai Kakar tasu zata masu section a nan, jarabebbiyar tsohuwa.. Kuma sanin kanki ne Aunty Hajara zaman Mu’azzam a nan ka iya kawo mana cikas..”


Mommy ta share gumin dake goshinta tace “Dik Safeenah ce da jarabar tsiyarta ta ja mana, amma inada tabbacin zaman Mu’azzam a Fufore bazai yuwu ba domin kuwa bazai tab’a barin aikinsa ya tare can ba.. Kafin ya ankare sai mun Kai uwarsa rami..”


Aunty Shemau tace “Bakida wannan matsalar Aunty Hajara.. Aiko maganin Kyallu zai mata aiki mahaukaciyar yarinyar dake tareda Nuratu  Itace zatayi ajalinta..”


Suka shek’e dariya a tare kafin Aunty Nuratu taima Mommy sallama, Mommyn na cewa Ta saka mata idanu akan yaranta.


**


SULEJA 



A daren ranan ma iya cewa Sadiya kwana zaune sukai daga ita har mahaifiyarta, Umma na saman sallaya tana kai ma Ubangiji kukansu yayinda Sadiyar ta kasa tab’uka komai dan tuni zazzab’I mai zafi ya rufeta tsaban kuka da tsananin tashin hankalin da take ciki.. Muassman idan Ta tina Washe gari Wai Ita d’in Ta zama Matar Alhaji Isyaku Baban Aminiyarta Sabeera.. Haka ta tak’ure cikin bargo tana rawar d’ari dikda tasha pcm amma kaman bata sha komai ba.. Tak’i daina Kukan tak’i taci komai.. Kallo guda zakai mata ta baka tausayi. Lallashin duniya Umma tayi amma abu yaci tura haka dole ta hak’ura ta fawalla wa Ubangiji lamarinsu dan shi kad’ai ne zai iya kawo masu d’auki a halin da suke ciki..


Washe gari sallar asuba ma da k’yar Sadiya ta tashi tai, ko k’wakk’waran tsayuwa bata iya yi sabida yanda take jin jikinta babu k’arfi.. Haka ta jima saman sallaya tana kai ma Ubangijinta kukanta..  


Wasu almajirai ne sukai sallama rik’eda manya manyan kwalayan juice da dangin ruwan gora da dai abubuwan tab’awa irin na tarban biki.. Dikda Umma ta hanasu shigowa da kayan hakan bai Sa Almajiran sun fasa dire masu kayayyakin ba.. 


Sadiya tana jiyo yanda Umma ke fama da almajiran kukanta ya k’aru.. Shikenan da gaske yau ne aurenta da Alhaji Iskyaku.



SameenaAleeyou📚


No comments

Powered by Blogger.