Gidan Aro 14


*14*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Da tsananin mamaki Umma take duban Malam Liman “Malam Alhaji Isyaku fah kace.. Shine yace zai biya bashin idan za’a basa auren Sadiya.? Malam Sadiya fah k’awar d’iyarsa ce Aminiyarta ce Wanda sam baya k’aunar tarayyarsu shine zai zago yace yana sonta da aure.. Allah mai iko..”


Malam ya nusa kad’an yace “Ni kaina banji dad’in cewa da yayi har sai idan za’a basa auren Sadiya ne zai biya bashin, domin kuwa naso ya biya dan Allah Allah ya basa ladansa toh amma ya kawo sharad’i sharad’i kuma shine a basa auren Sadiya..”


Umma ta katse Malam Liman da fad’in “A’a Malam wannan ma bazai tab’a yuwa ba, Ko lokacin da nake ganiyan son kud’ina da abin duniya bazan tab’a bari Sadiya ta auri mutumin nan ba balle yanzu da duniyar da abindake cikinta suka fita kaina.. Yajesa mun gode da niyyan taimako Allah zai kawo mana wani hanyar amma banda auren Alhaji Isyaku..”


Liman ya nusa yace “Toh shikenan dama ni ga abinda na Fad’i idan na tuntub’eku zaiji ba’asi.. Allah Ubangiji ya huwace ya kawo wani hanyar..”


Umma ta amsa da Ameen Malam Liman yai mata sallama...


Ta rapka uban tagumi tana mamakin halin mutanen duniya.. Lallai kaga d’an mutum ka barsa, yanzu dik kushe Sadiya da hanata k’awance da mutumin nan keyi da d’iyarsa ashe idonsa nakan Sadiyar ce.. Ashe zai zago bayan ya rabata da d’iyarsa yace zai aureta.. Oh Lallai duniyar yau Ta zama abinda Ta zama.. Wai mutum bazaiyi taimako dan Allah ba sai idan zai sami wani abu in return.. Taimako dan Allah yayi k’arancin har sai idan kaima zaka sami wani abu. Ta yaya kuwa Allah Bazai barmu da halinmu ba idan har na sama bazai tallafi na k’asa ba.. Kai Allah ka kawo mana sauk’i a wannan duniyar tamu.. Ta k’arashe tinanin nata tana mai sauk’e nannauyan ajiyan zuciya.


A d’aki ta iske Sadiya ta gama lallashin Habib yayi bacci dan yaron tinda yaga yanda aka kad’e mahaifinsa akan idonsa Sai ya dinga wani irin firgita idan yana bacci yaita surutai, har sai sunyita masa addu’o’i kafin su samu ya d’anyi baccin.. 


Umma ta k’ura ma yaran nata idanu cikeda tausayinsu da k’aunarsu, ta k’udiri niyyan da zaran ta gama iddarta zata nemi Sana’a domin ta rufa ma kanta da iyalanta asiri.. Har kullum hannun da yake bayawar yafi hannun da yake karb’a, tayi kuskuren fahimtar rayuwa a baya da tayi tinanin Lallai sai ta hanyar namiji mace zata sami kud’i, yau da ace tanada sana’arta da zai rufa mata asiri da ba sai ta tsaya hangen abin hannun namiji ba balle har taje ta jefa rayuwar d’iyarta a tsaka mai wuya.. Juyowan da Sadiya zatai suka had’a idanu.. Murmushi suka sakar ma juna kafin Sadiya ta gyara ma Habib abin rufuwarsa ta mik’e ta nufo bayan Umma.


Yanayin da taga Umman ciki ya tabbatar abubuwa sunci gaba da tafiya babu dad’i, Ta taimaka ma Umman ta zauna da k’yar saman tabarma sakamakon ciwon dake k’afarta wanda Safeenah ta kuskureta da mota..


“Umma lafiya na ganki haka..? Umma ko wani abin ne ya faru..?” Sadiya Ta tambaya cikeda kulawa tana mai duban mahaifiyar tata..


Umma ta nusa tace “Sadiya wani magana zan fad’a miki amma bana so ki d’aga hankalinki, sannan Inaso ki sani dik abinda kike so, dik abinda zai faranta miki rai nima shi nake so kuma ki sani muddin Ina numfashi Ina tareda ke a Ko menene a matsayina na mahaifiyarki kinji koh...”


K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e Sadiya tai “Haba Umma ki daina magana haka dik sai kina sa naji wani iri haka nan.. Bazamu sake rasa kowa ba da yardar Allah kinji koh.. Sannan Tabawa Allah zai kawo mana yanda zamuyi da ita...”


Umma Ta kuma nusawa tace “Haka ne Sadiya.. Toh yanzu idan nace miki an samu hanyar rabuwa da tashin hankalin Tabawa amma bisa sharad’i shin zaki amince da sharad’i..?”


Wani irin Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Sadiya.. Ta fad’ad’a fari’ar ta tana jinjina kai take fad’in “Umma nasan sharad’in nan bazai tab’a mutuncinki ba sannan bazai tab’a nawa ba, nasan da ace zai shafi mutuncinmu ko sab’on Allah da baki Zo mun dashi ba, da kin watsar tin a inda kikaji.. Umma mecece sharad’in.? Aikatau ne zan masu babu biya ko kuwa wani aikin k’arfi zanyi.. Umma ki sanar dani ko menene zan k’ok’arta na aikata muddin Tabawa zata daina d’aga miki hankali..”


Sauk’e ajiyan zuciya Umma tai cikeda tausayin d’iyar tata, saida ta nusa kafin ta kirawo sunan Sadiya cikin wane irin siga da yanayi..


Sadiya ta d’ago fuska Jiki a sanyaye wann karon ta amsa “Na’am Umma..”


“Zaki iya auren mahaifin Aminiyarki..?”


Dummm! Haka k’irjin Sadiya ya buga, taji batun wani irin gantsagarau wanda zatace ba don daga bakin Umma ya fito ba zasu hau sama Su fad’o da dik wanda yazo mata da wannan batu.. Mahaifin Aminiyarta.. Wacece ma Aminiyarta ai ita tama mance tanada wata Aminiya.. Kai Aminiya fah k’awa mafi kusanci ake nufi.. Wacce kuka d’auki yarda kuka aza ma junanku.. Ita ko lokacin da take Sady pretty d’inta mai son dukiya da abin duniya Ai bazataso ta auri Baban Aminiyarta ba dan idan akwai abinda tafi tsana shine cin amana.. Ita bazata tab’a cin amanan K’awarta irin haka ba..


Muryar Umma ne ya katse mata tinanin nata.. Ta d’ago tana duban Umma tamkar mutum mutumi..


“Umma wacece Aminiyata.. Umma mai kike fad’i... Ban gane komai ba Umma..?” Ta k’arashe gaba d’aya a daburce take.


Umma ta jinjina kai tace “K’warai dole ki shiga rud’u amma ya zama dole na fayyace miki komai yanda mukai da Malam Liman..”


Cikin tsanaki tiryan tiryan Umma ta karanto mata dik yanda sukai da Liman.


Da tsananin mamaki Sadiya ke duban mahaifiyarta “Umma Abban Sabeera fah kikace, Sabeera dai Sabeera aminiyata.. Haba haba Umma.. Wllhi ni koda ace ban tsani mutumin nan ba bazan auresa ba Ko dan Sabeera.. Bana k’aunar ko ganin mutumin nan balle ace aure ya shiga tsakaninmu...Haba Umma ai akan bar halal dan kunya.. Balle ma mutumin nan Umma wllhi ayarsa yake shek’ewa cikin Abuja shisa yake tak’urawa ‘yarsa yake kaffa kaffa da ita dan kar a lalata masa ita kaman dai yanda yake lalata yaran mutane.. Saidai ya mance abinda yakeyi bashi ne kuma adashi ne da dik daren dad’ewa sai ya d’iba.. Ai dik Wanda ya faye kushe da aibata wasu shima d’in na aikatawa ne.. Bayan dik cin mutuncin da ya mana shine yanzu zai wani zago ko kunya babu yace ni zai aura.. Wllhi Allah ya sawak’e min Allah ya tsari gatari da saran shuka..”


Umma ta katseta da fad’in “Nima abinda na fad’iwa Malam Liman kenan, yaje can da taimakonsa bama so Allah zai kawo mana wani hanyar.. Allah yana jin addu’an bayinsa kuma bai mance damu ba, da sannu zai yassare mana kinji koh.. Kar ma Ki saka wannan abu a ranki balle ya dameki.. Kuma kar ki nunawa Sabeera komai dan yarinyar da mahaifiyarta sunada mutunci.”


A hankali Sadiya ta jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba dan har lokacin cikin Shock take, Wai Baban Sabeera Alhaji Isyaku Chanji ke sonta.. Ikon Allah kenan.. Kai jam’a sai kaga mutum ka barsa.. D’an Mutum sai Allah.


**


Ita kad’ai sai zagaya d’akin take tana kuma duban wayarta ta rasa yama akai Barr Ameer ya kuma samun sabon layinta, layin data canza tin lokacin mutuwar Ikram.. Ta masa kashedi ya daina kiranta it’s over between them amma yak’i daina kiranta, ta kula so yake ya kashe mata aure tako ta halin k’ak’a bacin haka mai yasa zai damu da kiranta a waya har yana ce mata yasan bata tare a gidan Mu’azzam ba.. What if Barr Ameer yanada masaniya kan sak’on da aka turo mata a daren da ya gabata kafin safiyar da aka tsinci gawan Ikram.. K’irjin Safeenah yai wani irin yankewa ya fad’i.. Idan kuwa Barr Ameer yasan wani abu tabbas tasan zai dik yanda zai ya tabbata aurenta ya k’are kafin tariyarta da Mu’azzam.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ya zama dole ta tabbata Barr baisan wani abu akan wannan sak’on da ya shigo wayarta ba.. A fili ta furta “Enough Feenah.! You can’t get convicted.. After all, you’re innocent.. You didn’t kill her.. Shegen san sanin k’wak’waf d’inta shi yayi ajalinta..” Ta k’arashe tana mai cusa yatsu cikin sumarta..


Fuzar da fuci tai tana tinanin toh yanzu mai zatayi, ta Ina zata soma b’ullowa Al’amarin.. Idan Mu’azzam ya soma zarginta shikenan itakam tasan tata ta k’are.. Gaba d’aya Safeenah Ta fice a hayyacinta ko Dairy Company d’insu da take aiki a nan bata iya zuwa.. Ita yanzu babban damuwarta shine ta tabbata Barr Ameer baisan komai kan alak’arta da mutuwar Ikram ba sannan ya fice daga rayuwarta ta har abada..


Lokaci guda ta yanke shawarin kiran Barr.


Bugu biyu ya d’aga kaman wanda yake jira “Mrs Mu’azzam Gamji. Matar Officer.. To what do I owe this pleasure..”


Cikin tsananin huci Safeenah ke furta “Enough with your games Ameer.. Na gaji da kiran wayata da kake.. At first ka kirani ka min murnan aure na fad’a maka kar ka sake kirana amma bakaji ba.. And now ka kirani ka tayani jajen rashin tarewata gidan mijina.. Wannan ba matsalarka bace Ameer.. Na tare ko ban tare ba duk bai shafeka ba.. Mu’azzam is still my Husband and I’m his wife.. Idan munga dama zamu iya zama cikin gidanmu basai munje wani wajen ba. After all, Gidanmu gidansu Mu’azzam ne.. Kar ka mance Nida shi are first cousins so ka daina b’ata ma kanka lokaci da har kake cewa kanada sauran hope akaina.. I was never yours and I’ll never be.. Ka fahimta..?! And Remember you’re messing with the Corps wife.. You don’t want to get arrested. Do you..?”


A hasale ya katseta da fad’in “Don’t you dare threaten me..!” Ya murmusa kad’an kafin yaci gaba da fad’in “And remember, I’m a lawyer. I can defend myself and easily incriminate you.. Kar ki damu ina k’aunarki Safeenah.. And I’ll never give up on you..” Yana ida fad’in haka ya fashe da dariya had’ida katse kiran..


Bibbiyu Safeenah ke gani.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa.. Da dafe dafe ta zauna saman gado, wani irin rawa jikinta keyi.. Ta kuma duban wayarta jikinta naci gaba da rawa.. Tama nemi kukan Ta rasa sai tsananin rawa da illahirin jikinta ke mata.. Har ji take Tamkar zazzab’i ke shirin sauk’o mata.. Ashe kuka ma rahama ne dan ta nemi kukan ta rasa.. Tsoro take kar Ameer ya zamto silan mutuwar aurenta.. Ya zama dole ta kare aurenta at any cost. She needs to be with her husband idan har tana so ta gyara aurenta. Amma mijinta baya nan yana can Fufore dan saida tayi waya da Assad taji Ba’asin abinda ya sami Mu’azzam ya tafi yai abandoning aikinsa tinda Ta sansa kan batun aikinsa.. Sanin cewa Safeenah matar Mu’azzam ce da kuma magiyar data tayiwa Assad d’in ya kuma san halin Mu’azzam d’in ba lallai ya sanar da ita an dakatar dashi na wani d’an lokaci ba yasa shi sanar da Ita suspending nasa da akai..


Tai zaune saman gado tana juya wayar cikin hannunta “What do I do now.. It’s too bad he got suspended.. But he sure had it coming da wannan zafin zuciyar tasa.. Yanzu idan inaso na kasance dashi saidai na bisa cen kenan.. Oh shitt.. I don’t like it there gaskiya bazanje ba.”


Muryar Meema ce ya katseta “You have to.. Ya zama dole kije Adda Feenah and be with your Husband idan har kinaso ki sami kusanci da mijinki.. If not you’ll end up losing him..”


A zabure Safeenah ke duban Meema. Nunata take da tsananin mamaki “How long have you been standing there.. Did you hear everything I said..?” Tai tambayar idanunta na firfitowa waje..


Meema taci gaba da takowa cikin d’akin murmushi saman fuskarta “Why.. Did you say something that I shouldn’t hear..?”


Murmushin yak’e Safeenah tai tace “Sabida na sanki da shegen gulma ne da shiga abinda babu ruwanki shiyasa.”


Meema ta murmusa tace “That’s my personality I guess. And I’m sure you’re used to it.. Addah Feenah you need to follow your husband.. Shawari nake baki..”


Hararata Feenah tai tace “Last time I check komai lalacewa yai da nabi shawarinki..”


D’an tab’e baki Meema tai tace “I’ve done my part tinda na baki shawari, it’s up to you Ki d’auka ko kar ki d’auka..” Ta k’arashe tana duban Safeenar murmushi saman fuskarta. Lokaci guda tasa kai zata fice. 

Feenah ta dakatar da ita da fad’in “We are going together Meema.”


Meema ta zaro ido waje tace “Wa ni. Spare me Adda Feenah.. Wann mijin naki lamba d’aya ne a rashin mutunci. Bansan mai zai aikata mana ba wann karon. Chabd’i. Who knows what he might do to us.. Inaga kuraye zai kwance mana wann karon.”


Feenah tace “Kar ki damu we’ll act smart wann karon. Yanzu mai zamuce wa Mommy ga Daddy ma yau na hanya.. Nasan definitely Mommy bazata barmu mu tafi ba..”


Meema ta murmusa tace “Haba Adda Feenah kar ki badani mana, Keda kike da dalilin zuwa k’wakk’wara. Kawai cewa zakiyi mijinki ne yace yana so kije can ki samesa and yana jin kunya bazai iya kiran Daddy ko Mommy ya fad’I ba.. He wants you to have your first honeymoon a garinku..” Ta k’arashe tana kashe mata ido..


Pillow Feenah ta jifa mata tana fad’in “Zaki sani ne.. Well shawarinki yayi, zan fad’awa Mommy Mu’azzam yana so naje Fufore and inaso ke kuma ki rakani.. Ita kuma Mommy tasan mai zata cewa Daddy.. Nasan bazata yarda muje ba amma sai mun fama arranging komai mu sanar da ita.. Ke sai mun isa ma mu sanar mata dan Nasan babu yanda ta iya idan taji Muna cen dole kawai tasan abinda zata nemo ta fad’awa Daddy..”


Meema ta murmusa had’ida mata jinjina da babbar yatsa “You’re genius Adda Feenah.” 


Ita kaw Feenah sai murmusawa take tana jin yau d’in ta tsara zance ya tafi daidai.


**


Koda Malam Liman ya samu Baban Sabeer da batun cewa Sadiya da mahaifiyarta basu amince da buk’atarsa ba huci ya dingayi cikin zuciyarsa yana ayyana bai tab’a neman abu ya rasa ba balle ma mace, bazai fara akan Sadiya ba.. Dik yanda zai Sai ya tabbata ya aureta.. Koda ita da mahaifiyarta basa so..


Tabawa ce ta fad’o masa ransa, ya saki wata irin muguwar murmushi kafin yai sallama da Liman yace idan sun canza shawarinsu shi dai yana nan akan bakansa, zai sauk’e masu nauyin bashi a matsayin Sadakin Sadiya..


Baban Sabeera yana ficewa daga Zauren Malam Liman bai zarce ko ina ba sai gidan Tabawa. Tabawa taji mamakin jin Alhaji Isyaku na sallama da ita.


Ta fito mamaki fal saman fuskarta, bayan Ta masa gaisuwan mutunci irin wanda ake ma masu abin duniya.. Ta kuma risinawa tana fad’in “Alhaji inji dai lafiya koh, ko wani abin ne ya faru..?”


Alhaji Isyaku ya gyara babbar rigarsa yana fad’in “Toh lafiya ne ya kawo haka kuma babu komai sai alkhairi..”


Tabawa ta Washe baki dan a tinaninta Alhaji Isyaku zaice yana sonta ne bayan tsawon shekarun data kwashe a unguwar tana zaman kanta. Tabawa ta shiga sanne kai tana mad’e.


Alhaji Isyaku yai gyaran murya yace “Nasan kina so a biyaki kud’ad’en da kike bi bashi.. Musamman wanda kike bin iyalan Malam Ibrahim mai rasuwa..”


Jikin Tabawa ya d’anyi sanyi, ta dubi Alhaji Isyaku tace “Toooh zaka biya masu ne Alhaji..?”


“K’warai kuwa zan biya masu amma fah inada sharad’i..”


Tabawa ta dubesa da mamaki wannan karon “Alhaji sharad’i kuma ni da hakkina.. Hakkin d’imbin jama’a dake kaina ace sai an gindaya min sharad’i a biyani.. Wannan batu ma ai hankali bai kama ba.. Haba haba dai jama’a.. Wllhi Alhaji ina ganin mutuncinka a layin nan dan rufin asirin da Allah yayi maka, kar kasa na daina gani.. Ka gode ma Allah wannan maganar da dare kazo min da ita dan da ace da rana tsage tsage kazo min da ita da na daina ganinka da wannan mayafi na mutunci da nake ganinka da Ita ehe..” Ta k’arashe tana jijjiga had’ida huci..


Alhaji Isyaku ya murmusa cikeda jin dad’in halin rashin mutunci da Tabawa keda shi yasan bazai sami matsala daga wajenta ba.


“Hajiya Tabawa kenan.” Hannu ya zira cikin aljihunsa ya ciro kud’i bandir ‘yand’ari bibbiyu ya mik’a mata “Ungo karb’i wannan..”


Tabawa ta k’yalla idanunta akan kud’i sai kuma tai wani murmushin rainin hankali tace “Haba Alhaji nice za’a min biyan ‘yan tasha a bani kud’ina gutsiri gutsiri..  Ko kasan kullum k’Arya nake wa mutane masu kaya cewa Kaya yana saman ruwa bai iso ba.. Ni fa na gaji da k’anan Murya. Wllhi bazan karb’i kud’i kad’an kad’an ba.. Dubu ashirin fah kake mik’o min..”


Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Wataran ma Daloli za’a mik’o miki.. Yanzu ki amshi wannan kiji na Menene..”


Tabawa ta dubesa a yatsine sanda yaci gaba da fad’in “Wnn kud’ad’e da kike gani ba bashin da kike bi bane.. Sune mabud’an hanyar da zaki bi Ki sami kud’ad’enki..”


Tabawa ta dubesa da mamaki, hanu har na rawa Ta amshi kud’ad’en.


Alhaji Isyaku yaci gaba da fad’in “So nake ki saka masu pressure.. Ki matsa masu ki tak’ura masu.. Idan ta kama kice zaki d’ebo masu ‘yansanda kuma zaki maka Su a kotu. Dik yanda kud’ad’enki suka shiga suka fita su nemo su baki. Ni kuma na miki alk’awarin baki wasu kud’ad’en bayan bashinki da za’a biya..”


Mamaki ya cika Tabawa Ta shiga Washe baki tana fad’in “Idan dan wannan ne kar kaji komai Alhaji.. Wllhi rashin mutunci yanzu zan soma masu irin wanda ma ban masu a baya ba.. Kuma babu ubanda ya isa ya dakatar dani..!”


Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Da kyau Tabawa.. Sai naga sakamako..” Daga haka sallama sukai shida Tabawa ya wuce yanda ya aje motarsa..


**


Kyallu ta gyara tsayuwarta sosai tace “Kina jina..”


Ajidde dake duk’e gabanta Ta jinjina kai a hankali alamun eh.


“Zakije wannan gidan kuma zaki rufe kanki a d’aki da wannan nakasesshiyar matar, idan ta kama ki shige har cikin drawer kin binciko mana ‘yankunnayen zinari da a warwaro ne zakiyi.. Wannan karon kar ki dawo min gidan nan babu komai Ajidde.. Ke idan ta kama ki saci jiki ki shiga sauran d’akuna nan ne toh fa sai kin shiga kin sato mana abin duniya da ‘yankud’ad’e kinji koh..”


Ta ciro wani laya cikin bujenta Ta mik’a ma Ajidde “Ungo nan amsa.”


Ajidde Ta mik’a hannu Ta amsa da k’yar.. 


“Layar zana ce da zaran kinga za’a kamaki kafin su shigo cikin d’akin sai ki matsata da k’arfin gaske yanda bazasu ganki ba..”


Nan ma Ajidde jinjina kai tai kafin Kyallu Ta shureta da k’afa tace “Tashi ki daina kallona da wannan zuru zuru idanun naki..”


Ajidde Ta mik’e da k’yar rataye da jakan maganinta Ta fice..


Tana tafe tazo dai dai k’ofan gidan Malama Hafsah, tai tsaye tana duban k’ofar gidan..


No comments

Powered by Blogger.