Gidan Aro 13




*13*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*






Inne tana ganinsa Ta soma masa lale kaman ta goyasa dan murna, Aunty Shemau ma na zaune wajen tai masa Barka da zuwa cikeda kulawa. Take ta tina wayan da sukaida Mommy, bazata tab’a bari Mu’azzam d’in ya fahimci wani abu ba.

Kakarsa sai nan nan dashi take dan Farin ciki, tuni ta soma masa tayin abinci daban daban harma tambayarsa take ko akwai abinda yake so a girka masa a gurguje. Mu’azzam yace “A’a Inne zanci duk abinda ya samu, amma zanyi wanka na duba Mamy first idan yaso sai muci dinner gaba d’aya..”


“Har dare bakaci komai ba, yammacin da saura fah..”


“No Inne babu komai ai ba wani yunwa nakeji ba ma.. Zan duba Mamy sai na d’an huta..”


Mik’ewa tai tana fad’in “Mutum yayi tafiya bai saka komai cikinsa ba inyi.. Badai a gidan nan ba..” Ta k’arashe tana mai kiran ma’aikatan.


Mu’azzam yabita da kallo murmushi saman fuskarsa zuciyarsa Cikeda k’aunar ahalinsa.


“You must be jet lagged.” Musaddiq ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana mai k’ok’arin k’arasowa cikin parlorn.


Juyowa Mu’azzam yai sanda Musaddiq d’in ya k’araso fuska fal fari’a sukai handshake suna d’an hugging juna.


“Wai dama kana tafe.. Kuma shine baka fad’a mun ba.. I would’ve arranged something for you. You know this place is boring and annoying..”


Da mamaki Mu’azzam ke duban Musaddiq dake sanye da uniform na ma’aikatan gidan gona“I can see you’re better off here.. And to be honest, naji dad’in ganinka haka da uniform kana aiki..”


Musaddiq ya fuzar da fuci kad’an yana ‘yan waige waige dan ya tabbatar Inne bata wajen “Ai ni kawai matar nan ta gama dani.. Wllhi wnn jarabbebbiyar tsohuwa Ta gama dani.. Musaddiq Marwan Gamji no longer exists.. I guess fate has decided for me.. Ni kuma kalan nawa K’addaran kenan..” Yai maganar sanda suka jera suna tafe hanyar d’akin Aunty Nuratu..


Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Haka shine da kyau Musaddiq, kaga one day you’ll takeover the family business. After all, Wannan shine mafarkin da a Kullum Daddy yake.. Wani daga cikinmu ya kula da kasuwancin Ahalin.. Saidai ni tuni Allah ya k’addari ba d’an kasuwa bane kaman yanda Daddy yaci min buri ni D’ansanda ne.. Naji dadi sosai da naga kai d’in zaka cika burin Daddy.. I’m so proud of you Musaddiq..”


“Kawai ka fito fili kaima kace kana Farin ciki da k’untata rayuwata da akai..” Musaddiq yace yana kuma b’ata fuska


Murmusawa wann karon Mu’azzam yai ya kaikaito yana duban Musadddiq sosai “Watarana zaka fahimci Inne gata ta maka Musaddiq.. We all love you, and we want what’s best for you..” Yai maganar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.


Gajeren murmushi Musaddiq d’in ma yai yace “Sai ka shafe watanni Abuja kaji bana nan sannan ne zakace a dawo maka dani and your Grandma bata kyauta ba data d’auke ni..”


Mu’azzam ya d’an daga fuskarsa suna ci gaba da takawa a hankali, ba tareda ya dubi Musaddiq d’in ba yace “At least zan d’an huta da rashin jinka..” 


“Au haka kace. Zamu gani ai.. I know rashina a gareka tamkar rashin police force ne..” Cewar Musaddiq daidai sanda yake tura k’ofan d’akin Aunty Nuratu sallama saman bakunansu.


Aunty Shemau suka tadda ta gama kintsa Mamy ta d’aurata saman wheelchair.. Ta fad’ad’a murmushinta tana duban Mu’azzam d’in “A a Mu’azzam ka shigo, Aiko har na gama shiryata zan kawota wajenka.. Sai gashi ka shigo ma..”


Cikeda jin dad’in yanda Aunty Shemau ke kulada mahaifiyarsa yace “A’a dama zan shigo Aunty.. Sannu da d’awainiya fah..”


Aunty Shamau tai saurin katsesa da fad’in “A’a Haba dai Mu’azzam wani d’awainiya kuma.. Kawai na d’aura daga yanda ‘yar uwata Aunty Hajara ta tsaya ne. Aunty Nuratu ai ‘yaruwa ce a garemu.. Ka daina mana godiya kaman wani hidiman muke.. Ciwo ai na kan kowa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad’unta..”


Gaba d’aya suka amsa da Ameen daidai sanda Mu’azzam ya k’araso gaban wheelchair d’in ya duk’a Aunty Shemau na kuma gyara mata kanta da ya tank’washe a karkace.


Mu’azzam ya zuba mata idanu zuciyarsa fal k’aunarta gauraye da tsananin tausayinta, Allah sarki inama wani na iya yaye ma wani cuta da ya bada duk abinda ya mallaka koda rayuwarsa ce dan mahaifiyarsa Ta sami lafiya.. Saidai ba haka abin yake ba. Allah shine yake jarabtan bayinsa da cuta ba Don ya k’isu ba saidai dan ya jarabci imaninsu da wannan cutan sannan ta kuma zame ma bayinsa na k’warai kankarewar zunubi..


Inne ce ta shigo tana tambayar ko mai maganin ta iso.?


K’irjin Musaddiq ya buga dan sai yanzu ya tina da Ajidde da yanda sukai.. 


Inne taci gaba da fad’in “Shemau ki kirata muji ko lafiya bata iso ba har yanzu.. Ni bana son ana sako shiririta cikin lamarin jinyar nan..”


Aunty Shemau ta d’an daburce tana fad’in “Ai Inne tace tana tafe.. Inaga abin hawa ne bata samu ba..”


Musaddiq yayi caraf yace “Wait. Wai mai maganin Mamy.. Ai kuwa tazo amma saidai akwai maganin data mance bata taho dashi ba wanda za’a bata yau d’in.. So sai ta koma, and I don’t think zata iya dawowa yau dan wajen da take zuwa akwai nisa daga nan.. And kaman hadari ne a garin..”


Duk suka juyo suna dubansa kafin Inne tace “Wannan ai shirita kenan..” Inne ta fad’i tana duban Musaddiq. Taci gaba da fad’in “Kuma sai ta rasa nawa zatai bayani sai kai..”


“Toh ai ni ta samu Inne shisa ta fad’a mun..” Baikai aya ba tace “Kai rufe min baki..” Ta dubi Aunty Shamau tace “Shemau ki kira matar nan kiji bayani daga bakinta dan ban yarda da zancen Gidado ba.”


Aunty Shemau ta jinijina kai tana fad’in “Toh Inne zan kirata..”


Shidai Mu’azzam bai bi tankasu ba hannun mahaifiyarsa rik’e cikin nasa har lokacin..

A haka har d’akin ya rage saura shi da mahaifiyarsa.. Addu’o’i ya dinga mata har Shemau ta shigo ta taddasa. Nan take sanar dashi mai magani tace ko zuwa gobe za’a iya bata idan Allah yakai rai dan lokacin ma ruwa ake tsulawa..


Ta kuma k’arasowa tana fad’in “Kaje ka huta kaci abinci Mu’azzam gani nan ga Hindu zamu kula da ita...”


Gajeren murmushi ya d’anyi had’ida mik’ewa yana ma Aunty Shemau godiya..


Yana ficewa Shemau ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da fuci a hankali.

Ta maidoda dubanta ga Aunty Nuratu tana aika mata mugun kallo 


“Nakasasshiyar banza.!” Ta fad’i tana mai hankad’a wheelchair d’in da Aunty Nuratu ke kai..

**


A b’angaren Ajidde kuwa koda ta koma gida ma Kyallu ba taro ba Sisi jibaganta tai Ta jefata d’akin Tumakai tace ta Kwana dasu, D’akin da Kyallu ke aje dabobbinta harda turke tayi ma Ajidde Wanda idan tai mata laifi take d’aureta a nan itama Ta Kwana tareda dabbobin.. Haka tayi lamo jikin turken da Kyallu ta d’aure mata k’afafu tana rungume da hular da ma’aikacin Gidan Gonar  ya bata wanda bata San koda sunansa ba. Saidai tuni Ta masa lak’abi da Kuran Tashe.. 


Dikda azaban da take ciki hakan Bai hanata sakin murmushi ba sanda ta tina had’uwarta da mutumin wanda ko sunansa bata sani ba.. Tanaji can k’asar zuciyarta tana son ta sake ganin wannan fuskar tasa mai lullub’e da hazon k’ura wanda ya sanyata dariya da nishad’i har ya mantar da Ita ukuban da Inna Kyallu ke mata..



Washe gari bata aiki Ajidde ba da kanta tai shiri Ta nufi gidan dan bama Majinyaciyar maganinta..


Kyallu tana fita Ajidde ta samu ta k’ok’arta ta tsinke Turken data d’aureta. Gefe da Gidansu akwai wata mata wacce malama ce kuma har matan aure tana koyarwa, wasu lokutan idan Kyallu Ta fice tsiddabarunta da bokancinta gidan Malama Hafsatu take zuwa domin ta taimaka mata da abinci..


Yau d’inma hakance ta kasance da Ajidde..


Malama Hafsah na aji tana ma matan aure karatu Ajidde ta shigo da k’yar da k’yar kaman zata kifa k’asa..


‘Yan aji suna ganin Ajidde suka soma k’ok’arin mik’ewa kowacce tana neman hanyar gudu dan an canfa ance tanada Farin k’afa dik yanda taje Sai bala’i ya auku wajen.. Malama ta tsawatar masu da fad’in “Shin ba yanzu muka gama karatu kan yarda da canfi ba.. Canfi haramun ne a musulunci.”


Wata mata Ta d’aga hannu tace “Malama inada tambaya”


Malama Ta jinjina mata kai tace “Ina sauraronki..”


“Amma malama ai akwai Kambun baka.. Shin shi ba canfi bane..?”


Malama ta jinjina kai tace “K’warai Al’ainu haqqun. Akwai Kambun baka, harta a musulunci an yarda akwai Kambun baka, yazo kuma a sunna cewa akwai Kambun baka har an bamu addu’a da zamu dinga yi domin neman tsari daga sharrin Ido wanda ake cema kambun baka.. D’aura laya ko wani abu mai kama da haka da sunan neman kariya daga sharrin ido haramun ne a musulunci.. Yin hakan shirka ne inji Manzon Allah SAW, hadisin yana nan a cikin Musnad Ahmad 16969.” Malama ta d’an tsagaita kafin taci gaba da fad’in “Wacce dik take neman kariya daga sharrin ido ko Kambun baka ga abinda zatace ‘A’uthzu bi kalimatillahit taammaati min kulli shaid’anin wa haammaa wa min kulli ainin laammaa.’ Wannan addu’a ce ingantacciya datazo a sunna sannan zaki iya karanta ma yaranki ko wacce safiya da maraice domin nema masu kariya daga sharrin ido dama duk wani shed’ani ko abin sharri.. Babban darasin da nake so mu d’auka a nan shine wani baya tab’a sauk’ar maka da bala’i sai idan Allah yaso haka wani baya tab’a kawo maka nasara sai idan Allah yaso Kun fahimta..”


Gaba d’aya suka amsa da “Na’am Malama mun gane..”


Malama ta jinjina kai tace “Monita ki bud’e shafin da muka k’ara jiya ayi bitarsa kafin na dawo muyi k’ari.. Ku d’an ara min lokaci naji da Ajidde..”


Gaba d’aya suka jinjina kai suna amsa mata..


Malama ta janyo Ajidde suka fice zuwa tsakar gidanta..


Dik karatun kore shirka da aikata tauhidi da malama tai tsaf Ajidde ta saurareta, gaba d’aya jikin Ajidde yayi sanyi domin kuwa abinda Inna Kyallu ta d’aurata Kai kenan..


Malama ta nufi kitchen ta d’auko ma Ajidde abinci Ta bata tace ta zauna taci..


Saidai yau gaba d’aya jikin Ajidden a sanyaye yake babu sokancin data saba yima Malama.. Tak’i zama taci abincin ta fice sai waige waige take tana kuma duban Malamar rungume da kwanon abincin. Sauri sauri ta fice dan kar Inna Kyallu ta dawo ta tadda bata nan..

Malama Ta bita da kallo cikeda tausayawa har Ta b’ace ma ganinta.. Allah ya gani rayuwar yarinyar sosai yake bata tausayi..


**


Koda Kyallu ta isa gidan gonar sassafe tasa aka rufesu a d’aki daga ita sai Aunty Nurah, tai mata hayak’i da surace na magani.. Ta ciro wasu layu guda biyu ta bama Aunty Shemau tace a saka cikin matashin da Aunty Nuratu ke kwanciya..


Shemau Ta amsa tanai mata godiya.. Nan take sanar da Aunty Shemaun idan bata sami zuwa Washe gari ba zata turo d’iyarta ta bata maganin dan ita kusan ko yaushe fama take da masu karb’an magani..


Aunty Shemau tace babu damuwa za’ayi dik abinda Kyallu tace d’in..


Koda suka fito Daddy na parlor yana jira ya shiga yayi sallama da matarsa dan a yau d’in zai koma Abuja..


Koda Daddy yaga Kyallu tsareta da idanu yayi dan haka kurum yaji mata mai maganin bata wani kwanta masa ba amma yasan ba daga appearance na mutum bane kyaun magani.. Kuma basu san a Ina maganin Nuratu yake ba.. Idan aka dace sai maganin wannan matan yayi mata aiki..


Shemau dikda tasha jinin jikinta da ganin Daddy zaune yana jira a parlor hakan bai  hanata wayancewa ta risina tana gaida Daddy had’ida introducing Kyallu mai magani.. 

Daddy ya amsa masu da sakin fuska ya kumayi ma Kyallu godiya..


Har zasu shige Daddy ya tsaida Shemau, ya ciro kud’ad’e da dama yace a k’ara wa mai maganin..


Kyallu ta kanne idanu tana duban tulin kud’in da aka bata.. Tuni ta Washe baki ta shiga yima Daddy godiya da addu’an girma.. Lokaci guda tana kuma gwad’a maganinta da fad’in nan da k’ank’amin lokaci zasuga canji jikin Nuratu..


Daddy yace Allah yasa haka kafin ya nufi d’akin..


Kwance take fuskarta Ta kuma yin fayau Sai hancinta da d’an bakinta kake hangowa, Ya k’ura mata idanu k’walla fal idanunsa.. A hankali ya duk’a ya d’aura hannunsa guda saman nata. Cikin rawar murya yake furta “Bansan ko na cika alk’awarin da na d’aukar ma d’anuwana ba cewa zan kula da bayansa.. I don’t know why I’m feeling this way.. Like I failed somehow.. Ban cika alk’awarin dana d’aukar ma d’anuwana cewa zan kula da bayansa ba.. It’s been 15 long years kina kwance cikin jinya ba tareda Kinsan a Ina kike ba.. And.. And Ikram..” Kuka ya hana Daddy ci gaba da magana, kansa kife gefen Nuratun, yake furtawa cikin murya irinta mai kuka “I failed to protect his family.. Na kasa kula dasu as I promised to.. Na kasa..!” 


Mu’azzam yai tsaye bakin k’ofa yana duban yanda Daddy ke kuka kan mahaifiyarsa yana fad’in ya kasa kula dasu.. A hankali yake takowa cikin d’akin har ya k’araso yanda Daddy ke duk’e.. Yakai hannu ya dafasa.


Daddy na d’agowa da yaga Mu’azzam d’in sai ya kuma jin rauni can k’asar zuciyarsa..


A hankali Mu’azzam ya duk’a ya rik’o hannayen Daddy cikin nasa “Baka gaza ba Daddy.. What was meant to happen happened. Kuma Ka kula da bayan mahaifina kaman yanda kayi alk’awari.. Daidai da rana guda baka fasa cika alk’awarinka ba.. You’re true definition of a good brother Daddy... You’ve been taking care of us ever since my father passed.. You’ve become a father to his children and a husband to his wife wacce tin sanda ka aureta Allah ya jarabceta da jinya.. I’ve seen a lot of men wad’anda idan matansu Sun kamu da cuta irin haka har gida suke maidasu suje suyi jinya wasu ma auren ya k’are.. But bakayi haka ba Daddy.. Kai d’in ka d’auki d’awainiyar jinyarta kuma ka kula da ita daidai da rana guda baka gaza ba..”


Saurin girgiza kai Daddy yai yana mai duban Mu’azzam d’in “Don’t say those words Mu’azzam dik abinda nayi nauyi ne da ya rataya a wuyana and it’s not a favor kaji koh.. Come here..” Ya k’arashe yana rungumar Mu’azzam d’in.


Uncle Salman dake tsaye jikin k’ofa da ido ya tsaresu, lokaci guda ya koma da baya ba tareda ya bari sun gansa ba.


**



SULEJA



Tashin hankali goma da ashirin shine abinda Sadiya da ahalinta ke fuskanta, a yayinda mahaifinsu ko rufa kwanaki uku  baiyi ba da mutuwa Tabawa ta kuma sakosu gaba da maganan biyan kud’inta.. Babu yanda Umma batai ba ta bari ko takaba ne ta gama idan yaso sai ta fita ta nemo mata kud’ad’enta ko wani aikin ne sai tayi ta samo mata kud’ad’enta.. 

Tabawa tace atafau ita bataji ba bata gani ba. Yo wani irin aiki ne ma zatayi ta samo mata kud’ad’enta idan ba Sana’ar bin maza data d’aura ‘yarta akai zasuyi Su biyata kud’ad’enta ba.. Wanann magana na Tabawa sosai ya tab’a Zuciyar Umman Sadiya.. Abinda batayi tin k’uruciya ba shine Tabawa take jifanta da munanan kalamai irin haka.. Ya zama dole Ta nemo wa Tabawa kud’ad’enta dan abin ya zama akwai tab’a mutunci da tozarci bazata bari Ta kuma traumatizing yaranta ba bayan tashin hankalin rashin mahaifinsu da suke ciki already.. Hakan yasa Umma yanke shawarin tink’aran Committee na masallacin unguwa ko da akwai irin taimakon da zasu masu su rabu da Tabawa.. Malam Liman ya gyara zama had’ida nusawa kad’an yace “Da farko nasiha zan fara maki da ita.. Ita wannan rayuwar da kuke gani duka ba yawa bace da ita, sannan dik halinda bawa zai tsinci kansa ciki jarabawa ake masa.. Bazai yuwu ace koda Yaushe mun samu abinda muke so ba.. Sannan Ko yatsunmu muka duba ba daidai bane wani yafi wani toh haka Ubangiji ya tsara mana rayuwarmu.. Wani yafika kaima kafi wani.. Kai wani arzikin lafiya ma kawai yake nema dikda d’imbin tarin dukiyar da yake dashi wanda zai iya kashe ko nawa ne domin ya samu wannan lafiyar amma bai samu ba.. Ga dukiyar Allah ya basa amma babu lafiya da zaiji dad’in dukiyar.. Kaikuma idan ka dubi kanka kaga Allah ya huwace maka wannan lafiyan sai kayi tunanin ya gama baka babban arziki.. Har kullum idan zamuke duba rayuwar na sama damu toh fah bazamu tab’a gode ma Allah da tarin ni’imomin da ya mana ba.. Amma idan muka dubi na k’asa damu sai muyi masa godiya da ni’imominsa garemu.. Shi kuma Sai ya k’ara mana domin fad’insa da yace _’Idan kuka gode Mun Ni kuma Zan k’ara maku_.’ “


Umma na matsan k’walla cikin hijabinta take jinjina kai “Haka ne Malam.. Kuma in sha Allahu mun d’auki darasi.. Ina kuma fatan masu halin kwad’ayi irin nawa abinda ya faru dani da d’iyata ya zamto izna garesu..” Kuka ya hanata ci gaba da magana


Malam Liman yace “Ki daina kuka in sha Allah Committee na masallaci zatayi iya k’ok’arinta ta had’o abinda za’a iya samu a baku ku rage bashin.. Ubangiji ya dafa mana gaba d’aya..”Ya k’arashe yana mai mik’ewa ya kuma yima Umma  ta’aziya kafin ya fice.


Sadiya tai tagumi tana duban mahaifiyarta, ga k’annenta dake gefe har lokacin kuka suke. Hawaye suka kuma gangaro mata tana tina mahaifinta da k’alubale na rayuwa da suka fuskanta.. Inama mahaifinta zai dawo gareta da ta kasance irin d’iyar da yake so ta zama.. Amma saidai shi lokaci baya jira, idan ya wuce ya wuce kenan har abada..


Koda Malam Liman yaje ma Committee na masallaci da wannan batu suma sun tausaya ma Sadiya da mahaifiyarta dukda a baya basa k’aunar kasancewarsu a Layin.. Amma saidai kaf kud’ad’en dake asusun masallaci bai kai ko kwatan kud’ad’en da ake bin Umma da Sadiya ba.. Bazasu isa ba balle a biya masu dashi Sabida falalar dake cikin biyan bashi ga musulmi.. Haka Liman ya tara jama’a ya masu wa’azi kan falala da ladar da mutum zai samu idan har ya cire d’anuwansa musulmi daga k’unci na bashin da ake binsa ya biya masa wannan bashi.. Saidai ba’a samu wanda yace zai iya biyan bashin ba..


Ana haka saiga Alhaji Isyaku Dancanji mahaifin Sabeera Aminiyar Sadiya ya shigo, ya nemi ganawa da Malam Liman.. Bayan sun keb’e ne ya dubi Malam Liman yace “Malam naji sanarwan da kake na neman kud’i da yarinyar nan Sadiya da mahaifiyarta suke.. Zan biya masu bashin amma fah da sharad’i..


Liman ya fad’ad’a murmushi yana fad’in “Alhamdulillah.. Masha Allah.. Allah dai ya biyaka da gidan Aljannah Alhaji.. Taimakon da kake a layin nan Allah ya dad’a bud’e maka k’ofofin arziki.. Inaji mecece sharad’in naka..?”


Alhaji Isyaku yace “Zan biya masu bashin da ake binsu amma fah saidai idan za’a bani auren ita yarinyar Sadiya..”


Liman yai shiru yana dubansa “Alhaji kana nufi Sai za’a baka auren yarinyar ka biya masu bashin..?”


“K’warai kuwa Malam Liman yanda dai kaji haka ne.. Ai dama bashin na shagulgulan Bikin yarinyar ne.. Kaga Shagali bai tashi a banza ba Malam Liman shikenan sai a d’aura aure dani..”





SameenaAleeyou📚


No comments

Powered by Blogger.