Gidan Aro 12


*12*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali yake takowa yana kuma k’arema wajen kallo, memories d’in baya suna dawo masa.. Daidai jikin wata bishiyar mangoro ya tsaya ya d’aga kai yana duban bishiyar, lokaci guda yake tuna zamanin yarintarsa, sukanyi wasa da mahaifinsa wasan Corps da Bad guys, dama tin yana k’arami yake mafarkin zama D’ansanda domin ya kama masu laifi.. Ya tina wasu lokutan yakan d’ale bishiyar yayi kwanton b’auna Babansa na k’asa yana nemansa.. Sai ya bari Babansa yazo daidai jikin bishiyar Sai ya d’ago bindigar robarsa ta wasa yana pointing Baban nasa dashi yana fad’in ‘Na kamaka.. Freeze or I’ll shoot..’ Ya saki murmushi yana tuna moments masu dad’i da suka kasance ciki shida mahaifinsa.. A hankali ya aje jakarsa jikin bishiyar kafin ya dafa bishiyar ya d’ale.. Sai yana ganin hoton abubuwan cikin idanunsa kaman yanzu suke faruwa, komai yana nan yanda yake babu abinda ya canza Sai rayuwarsu data canza..


Akwai wani d’an hole jikin bishiyar yanda yake b’oye k’aramar bindigar robar tasa dik sanda zasuyi wasan hide and seek da Dad d’insa, ai kuwa nan ya hangota ciki tana nan a wajen har wannan lokacin.. Mu’azzam ya saki murmushi mai bayyana hak’wara yasa hannu ya d’ago bindigar yana juyawa, lokaci guda yake kuma tuno abubuwa da dama murmushin bai bar saman fuskarsa ba.. Yana nan zaune saman bishiyar yana tinani rayuwar baya ya hango wata yarinya Ta nufo wajen.. Tana tafe tana cillo da jakan dake hannunta tana ‘yan wak’e wak’e.. _”Mangoro.. Mai Mangoro kawo musha.. Idan da kud’i ma zamu sha idan babu kud’i ma zamusha.. Balle ma mu na bati zamu sha..”_


Mu’azzam ya mik’e daga kishingid’en da yake nan saman bishiyar yana kuma duban yarinyar dake nufo bishiyar tana wak’e Mangoro..


Cak Ajidde ta tsaya sakamakon hango bak’in jaka da tai aje k’asan bishiya..


Ajidde ta shiga wage baki tana furta “Allah ya kashe ya baki Ajidde, tsuntsu daga sama gasasshe.. Wannan jaka da gani Kud’i ne a cikinki..Idan nayi nasaran bud’eki na d’ibi kud’in ciki na kaima Inna Kyallu ko shakka babu zata yabeni za kuma Ta saka mun albarka..” Taci gaba da Washe baki tana kuma nufo jakan...


Tana isowa ta soma ‘yan waige waige dan ta tabbatar babu mai ganinta.. Saida Ta tabbata babu kowa wajen kafin ta duk’a ta soma kiciniyar bud’e jakan...


Mamaki ya cika Mu’azzam Ganin k’amar yarinya na k’ok’arin sata.. 


Ajidde bata fasa kiciniyar bud’e jakar ba tana fad’in “Dik taurin kanki sai na bud’eki jaka..!” Ta k’arashe tana mai daddage k’arfinta tana kiciniyar bud’ewa harda wani bada balance tai..


Tana kiciniyar bud’e jakan taji mangoro guda ya fad’o mata akai timm.. 

“Kai Kai Kai..” Ta fad’i tana dafe kanta.. Ta d’auki mangoron da ya fad’o ta shiga nunasa da yatsa tana fad’in “Tind kika buga min Kai zan miki shan azaba Alk’ur’an.” 

Lokaci guda kuma ta saki Tsaki tana mai furta “Ke mangoro yau bata taki nake ba.. Ki bari na samu abinda zan samu cikin jakan nan kafin na dawo kanki, nidake akwai amana ai..”  Ta k’arashe tana mai kuma janyo jakan..

Fad’owar wani mangoron ne data kumaji ya sanyata tsagaitawa.. Ta soma k’ok’arin mik’ewa tana tinanin kodai mai jakan na saman bishiyar ne..


A hankali ta soma k’ok’arin d’ago kanta.. Ai a zabure ta saki wani irin k’ara sakamon hango mutumin datai saman bishiyar rik’eda bindiga “Bindiga.. Bindiga..” Kalman data iya furtawa kenan jikinta na k’yarma.


Ajidde batai wata wata bata ta suri takalmanta da jakan maganinta a hannu ta soma gudu.


Mu’azzam dake rik’e da bindigarsa tin na yarinta dirk’owa yai daga saman bishiyar ya soma k’ok’arin bin bayan b’arauniyar yarinya wacce bai tab’a ganin ko mai kamanninta a Gidan gonar ba dik zuwansa..


Gudu take tana waige waige tana hango alamun mutumin na nufota.. Rumbun da ake aje abincin dababbobin tai wuf ta shige had’ida turo k’ofar..


Musaddiq dake cikin d’akin aje abincin an basa aikin gyaran d’akin yanayi yana turb’une fuska kaman daga sama yaji an turo k’ofa an shigo.. Ya dakata da abinda yake yana dubanta da mamaki yanda take lek’en mutumin dake casing d’inta..


Motsin da taji bayanta ya sanyata juyawa babu shiri.. Razana tai da ganin yanda fuskar Musaddiq ya b’aci da k’ura shima ya razana da kwalliyar dake fuskarta da yanda duk ta dame kwalliyar ya b’ata mata fuska sakamakon gudun famfalak’i da tai.. Suka saki k’ara a tare kowa na tsoron juna.. Kowa gani yake gamo yayi..


Sai kuma Ajidde ta soma matsowa kusansa tana kuma zuru zuru da idanu, Musaddiq bai daina binta da kallon tsoro da mamaki ba.. Kan ya ankara ta duk’a ta soma k’ok’arin janye boot d’in da k’afafunsa ke rufe ciki.. Musaddiq yana janye k’afarsa yake furta “Hey what are you doing.. Who are you.. Ke ki sakar min k’afata..”


Ajidde bata fasa janye takalmin cikin k’afar Musaddiq ba, harga Allah tsoro ya kamasa sosai ganin yanda wannan halittar ke janye masa k’afa.. Bata fasa janye Boot d’in ba har saida ta cireta gaba d’aya.. K’afar Musaddiq ya bayyana.. Ajidde na ganin k’afar Musaddiq ta sauk’e ajiyan zuciya hannu a k’irji tana fad’in “Wai Allah na.. Ashe mutum ne..!”


Mamaki bai saki Musaddiq ba ganin itace ya kamata yace ashe mutum ce amma shine take masa zaton ba mutum bane.. Ya kafe yarinyar da idanu cike da mamaki yana mai kuma turb’une fuska..


Ajidde ta d’ago idanu daga duk’en da take tana duban Fuskarsa da dust ya b’ata masa yayi fusufusu.. Lokaci guda ta tintsire da dariya tana nuna fuskarsa take fad’in “Wllhi saikace Kuran tashe..”  Tana maganar tana nunasa tana dariya..


Yanda ta wage hak’waranta tana dariya ga janbaki har kumatunta ya mugun bawa Musaddiq dariya, Ai take shima ya b’ige da dariya yana nunata yana dariyar.. Itama bata fasa nunasa tana ci gaba da dariya ba..


Cak ta tsaya da dariyar da take sakamon jiyo motsi da tai daga waje kaman wani na zuwa, tasan bazai wuce mutumin da taso b’alla jakarsa bane.. Fit ta had’iye dariyar tai saurin yin alama wa Musaddiq da hannu kan yayi Shiru.. 

Musaddiq ya daina dariyar da yake, yai shiru yana dubanta, lokaci guda take masa alama a hannu kan ya duk’a ya b’oye shima..


Babu musu ya duk’a ya d’an b’oye shima.. Sunajin motsin na kuma matsowa yanda suke.. Sukai likimau suna sauraron tafiyan.. Har kaman an tab’a k’ofar sai kuma sukaji an koma ba’a shigo ba.. Saida suka tabbata sun bar jin tafiyar kafin Ajidde ta sauk’e ajiyan zuciya tana furta “Allah ya ceceki Jidde yau da kin sha harsashi..”


Musaddiq yace a fili “Ke Wai gudun me kike ne..? Wacece ke ma Wai..?”


Ajidde ta mik’e tana fad’in “B’arawo ne ya biyoni.. Da k’yar nasha harda bindiga hannunsa..”


Musaddiq yace “B’arawo kuma a nan.. Bayan duka masu gadin dake tsaron babban k’ofa..?”


“Auho baka yarda ba amma ka biye mun ka b’uya.. Na fad’a maka har bindiga nadashi Allah ne ya kare bai ganmu ba da ya had’a da kai..”


Musaddiq ya d’anyi tsaki a hankali sanda Ajidde taci gaba da nuna fuskarsa tana dariya tana fad’in “Yauwa ashe dariya nake ya kaste min..”


Girgiza kai Musaddiq yai yace “Ke are you crazy.? Wait waima mai kike a nan ne..?”


Sai sannan Ajidde ta tina bada magani tazoyi.. 


“Jaka na..!” Ta furta tana shafa bayanta.. Lokaci guda taci gaba da furta “Na shiga uku.. Na zubar da maganin.. Shikenan yau Inna Kyallu halak’ani zatayi.. Wayyo Na shiga uku na mutu na lalace..!” Tana maganar tana kuka tana kuma lalumen maganin.. Dariyar da Ajidde take ya koma kuka..


Harga Allah yanda dariyarta ya bawa Musaddiq dariya kukanta ma dariyar ya basa.. Hannayenta biyu ta saka aka tana kukanta.


Tin yana dariyar kukan nata har kuma ta fara basa tausayi. Yai k’ok’arin saita kansa yace “Ki nastu ki fad’a mun meke faruwa..”


Ajidde ta kuma fashewa da kuka tana fad’in ta zubar da maganin.


Musaddiq yace “Wani magani.?”


“Maganin masu Gidan da Innata ta aikoni na kawo.”


Sai sannan Musaddiq ya fahimci d’iyar mai maganin Aunty Nuratu ce.


“Toh yanzu ya kike so ayi..?” Musaddiq ya tambaya.


Ajidde naci gaba da kukanta take fad’in “Ni wllhi ban Sani ba.. Abu d’aya na sani shine yau zan yabawa Aya zak’i hannun Inna Kyallu..?”


“Wacece Inna Kyallu..?”


“Inna ta ce.” Ta bashi amsa kai tsaye


“Toh yanzu mai zakice wa mutanen gidan da kika zubar masu da maganin.?”


“Nima ban Sani ba.. Kai zaka ce masu..” Ta fad’i hakan abinta.


“Ni kuma.. Ta ina na sansu da zan shiga na sanar dasu kin zubar masu da magani..” Cewar Musaddiq yana dubanta


“Toh ba Kai kana masu aiki ba Ai ka sansu..”


“A’a ni aiki kawai nake masu.. Kuma masu gidan basuda kirki balle na shiga na miki cover.. Nima aikin da ya shafe ni kawai nake ko shiga gidan banayi..”


Ajidde tai zururu da ido tace “Toh yanzu ya zanyi..? Dan Allah ka taimakeni ka shiga ka tsara masu zance ni naje naji da Inna Kyallu.. Dan Allah Kuran Tashe ka taimakeni..”


Sunan data kirasa dashi ya sanyasa dubanta kad’an yace “Ke mai kikace..?”


Tai saurin kama bakinta tace “Toh bansan sunanka ba..”


“Ba Lallai ki sani ba.. Makeup abuser..”


“Sunanka kenan..?” Ta tambaya tana dubansa..


“A’a naki dai..” Ya bata amsa kai tsaye..


“Ni sunana Ajidde Jidde Jiddodo d’iyar Kyallu mai Warka warka.. Ka fahimta..”


Musaddiq ya zuba mata idanu ya da take jero sunaye.


“Toh ai sunayen naki da yawa wanne zan d’auka.?”


“Duk wanda ka d’auka ma yayi.” Ta basa amsa kai tsaye.


Musaddiq ya murmusa kad’an sai kuma yace “Toh yanzu ya za’ayi ki fice B’arawon nan na nemanki..”


Ajidde ta zaro idanu tace “Bazan fice ba sai ka min alk’awari zaka shiga gidan nan ka kareni kafin gobe Inna ta nik’o gari tazo da kanta..”


Ya girgiza kai yace “Bana alk’awari.”


“Toh ka taimakeni kaman yanda Allah ya taimakeka..” Tai maganan tana mai k’ok’arin duk’awa..


“Ke tashi basai kin durk’usa ba.. Naji zanyi magana ma abokin aikina shi yana shiga gidan.. Toh amma mai zance masu..? Nace masu b’arawo ya biyo mai maganin..”


Baikai aya ba tai saurin dakatar dashi da fad’in “A’a kar kace haka..”


Musaddiq ya tsareta da idanu yace “Toh k’arya kika mun kenan..”


Ajidde ta shiga raba idanu tana twisting ‘yanyatsunta.. Murmushin yak’e tai yellow teeth d’inta da basu ganin brush suka bayyana kafin tace “Dama ai k’arya na maka.. Barin fad’a maka gaskiyar.. Kanaji tsinkar mangoro zanyi shine ya biyo ni a guje harda bindiga..”


Musaddiq yace “Toh kece b’arauniyar kenan..”


Ajidde ta fito da harshenta ta dangwala da yatsarta manuniya tace “Aradun Allah ban d’auki mangoron ba.. Ai kai shaida ne da ka ganni da ita..”


Sosai ta basa dariya musamman rantsuwar tata..


Ya jinjina kai yace “Shikenan yanzu kije ni nasan mai zance ma abokin nawa Sai ya fad’a masu..”


Ajidde ta jinjina kai tana masa godiya.


Har zata fice yace tsaya..


Ta dawo da baya tana dubansa.


“Idan kika fita haka mutumin da yake chasing d’inki zai ganeki.. Bari na miki dabara yanda bazai ganeki ba..” Ya k’arashe yana mai cire malfar kansa.. Lokaci guda ya d’aura mata akai yace “Yauwa he won’t be able to recognize you now.. Kina iya tafiya..” Ya k’arashe yana mai sakar mata murmushi..


Murmushin itama ta sakar masa tana mai furta ta gode.. 


Yanda take murmushi tana sanne ido ya mugun bawa Musaddiq dariya, Aiko nan ya tintsire da dariya.. Take Ajidde ma ta tintsire da dariya tana kuma duban fuskarsa mai lullub’e da hazon k’ura.. A haka ta fice tana dariyarsa yana dariyarta.. 


A b’angaren Mu’azzam kuwa tinda yabi bayan yarinyar bai cimmata ba Sai ya yanke shawarin tambayan securities na gidan gonan Ko sunga yarinyar da yake nema.. Saidai kafin ya isa wajen securities ya hango Daddy da Uncle Salman sun fito daga wani babban Office suna tattaunawa Uncle Salman d’in na nuna ma Daddy wasu documents.. Ko ba’a ce ba Business suke tattaunawa..


Suna hangosa fari’ar Daddy ya k’aru, yama daina sauraren Uncle Salman wanda shima tuni ya tsaya da bud’e takardun yana duban D’an d’anuwan nasa wanda sam inuwansu Bai jituwa..


Mu’azzam na K’arasowa Daddy ya tafi ya d’an basa light hug yana fad’in “A’a Inspector sauk’an Yaushe..?” 


Mu’azzam na murmushi ya d’an sadda kai yana gaida Daddy.. Su duka biyun annuri ne saman fuskokinsu..


Uncle Salman ya d’anyi gyaran murya yace “Sirki na rungumar Sirki nan dai ba Abuja bane..”


Murmushi bai bar saman fuskar Daddy ba yake fad’in “Mu’azzam D’ah na ne ba Sirki na ba..” 


Mu’azzam ya d’an kaikaito yana duban Uncle Salman, irin duban da yake masa tin yana yaro shine dai saman fuskar tasa.. Ya gaishesa cikeda girmamawa yana tambayan ya samesu lafiya..


Uncle Salman yace “Lafiya lou Mr Officer.. Saima bautan dukiyar ka da nake Kanyi wanda Yayana ya hana a cire maku Shares d’inku tun kafin rashin ‘yaruwarka..”


Take annurin fuskar Daddy ya d’auke cak.. Ya dubi Uncle Salman yace “Salman ya isa haka..”


Uncle Salman ya d’an tab’e baki kad’an yana maida hannayensa baya..


“Ni zan shige Meat Factory aiki na jirana..” Uncle Salman ya fad’i yana mai k’ok’arin shigewa.. Lokaci guda kuma ya kaikaito ya dubi Mu’azzam yace “Ina maka Barka da zuwa D’ah na Mu’azzam..!” Yai maganar murmushi saman fuskarsa.


Murmushin Mu’azzam ma ya sakar masa yana mai jinjina kai ba tareda yace komai ba..


Uncle Salman na shigewa Daddy ya kamo kafad’an Mu’azzam guda yana fad’in “Mu k’arasa ciki Inspector..”


No comments

Powered by Blogger.