Gidan Aro 10

 *10*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

FUFORE 

_Adamawa State, Nigeria_

Ta kasance ranace na cin kasuwar garin, mutane daga ko wacce lungu da sak’o sai tururuwan zuwa kasuwar suke domin saye da sayawarwan hajojinsu. Mutane da

rugagen da suke kusa dasu sukan shigo garin domin cin Kasuwa..


Wata kyakkyawar budurwa ce zaune k’asar Rumfar azara wacce bazata gaza shekaru 18 ba, ga tulin k’ulli k’ullin magunguna gabanta. tana karkad’a karan barankaci tana fad’i cikin wak’e irin yanda masu saida magani suke “Azo a sayi magani.. Sai an gwada ake sanin na k’warai. Magani ko wacce iri ce zaka samu wajenmu.. Azo a sayi maganin AJIDDE d’iyar Kyallu mai warka warka.. Ina saurayi mai shirin yin wasan shad’i Ina budurwa mai neman Farin jini.. Ina me neman lak’anin kariya daga mugun baki ko maita, toh ga Ajidde ta taho maku da warka warka...Azo a gwada maganin Ajidde d’iyar Kyallu mai Warka warka.. Dik garin nan babu wanda baisan amincin maganinmu ba.. Azo a gwada..!” Cikin harshen fillanci take tallan magungunan nata.. Kan kace mai an wawushe magungunanta..


Ajidde ta Washe baki tana k’irga cinikin da tai, ta kuma turo kallabinta gaba tana kuma k’irga kud’ad’en “Wo ni Ajidde wllhi Inna Kyallu yau dole ki saka mun albarka.. Kai jama’a watau dai idan kana so kayi kud’i nan take ka zamo macuci..” Ta shek’e da dariya tana tura kud’d’en cikin lalitarta “Ahab wawayen banza ku kuka sani idan maganin bai maku aiki ba.. Heheheh wllhi nidai babu ruwana Inna Kyallu ce ta d’auran talla..”


Tana ida fad’in haka ta mik’e daga Rumfar tata ta nufi gida tin kafin Kasuwa ta watse sabida ta gama saida kayyayakinta..


Tana isowa gida ta hangi d’akinda Kyallu take duba majinyata wata mata mai tsohon ciki Ta fito.. Kyallu na biyeda ita cikin shigarta ta bak’ar riga.. Wannan kakkauran bak’ar riga itace rigar Kyallu duk zafi duk sanyi. Ga uban daud’a da rigar tayi.. Ita kanta Kyallun idan ka dubeta sai ta baka k’yama sabida tsaban datti da daud’anta..


Hannayen mata mai cikin rik’eda guraye da layu Kyallu naci gaba da fad’in “Ki tabbata ki d’aura gurun nan dan shine maganin mugun baki harma da mayu.. Shi zai baki kariya Keda abin da ke cikinki daga duk mai nemanki da sharri bama kishiyoyinki da suka saka ido kan abin dake cikinki ba, zai baku kariya daga sharrin mugu... Shi kuma layan da zaran kin haihu a d’aura ma jaririn a wuyarsa shi zai zame masa kariya..”


Matar cikeda jin dad’I had’ida amincewa da abunda Kyallu ta fad’I mata take jinjina kai tana ma Kyallu godiya cikin tab’ewa da dulmuyewar basira.


Matar sukai sallama da Kyallu kafin Ajidde ta k’arasa wajen Kyallu.

“Inna Kyallu albishirinki.. Yau dai kaf na saida komai dole ki saka min albarka..”


Dariya mai sauti Kyallu tai da muryarta mai gwab’in gaske kana tace “Ai babu albarka tattareda ke Ajidde.. Ki daina mafarkin samun albarka daga wajena.. K’irgo kud’ad’ena ki mik’o mun..”


Jikin Ajidde ya d’anyi sanyi.. lokaci guda ta shiga fiddo kud’ad’en tana mik’a ma Kyallu..


Kyallu ta k’irgaga kud’ad’enta ta soke a hamnatarta.


“Yauwa kina jina..?”


Ajidde ta gyad’a kai a hankali 


Kyallu taci gaba da fad’in “Gobe zakije Gidan Gonar nan dake wajen gari ki kai maganin matar nan..”


Nan fah Ajidde Ta soma Washe baki dan sau d’aya kawai da sukaje gidan gonar nan taji tana son wajen.. Ga shukoki koraye gwanin ban sha’awa ga kuma dabbobi masu yawan gaske kama daga shanunmu na gida har zuwa irin na turawan nan iyaka ganinka dan yawansu.. Kai gaskiya a cikin noma da kiwo akwai albarka mai tarin yawa..


Tuni Ajidde Ta soma murna ta mance fushin da take na rashin saka mata albarka da Kyallu batayi.


**


ABUJA 


Kaman yanda sukai tsammani basu tadda Danger ba, majalisar k’ofar shagonsa ma babu kowa babu komai kaman anyi shara.. 

Shiru Mu’azzam yai yana nazari sanda suka keb’e su biyu shida Assad.


“I told you so.. Mutumin nan must be in hiding, an sanar dashi muna nemansa.. Idan bai fice a gari ba Toh kuwa shakka babu yana b’oye wani wajen. Idan ba Chief Jaja bane ya sanar dashi waye zai sanar dashi.. Who could be his informer Assad.?!” Ya k’arashe yana sakin huci a hankali.


Assad ya nusa yace “Ba Lallai ya zama Chief Jaja ba, sabida Chief ma bai san da hakan ba har saida abin ya kasance.. And it could be anyone from our Department.. Kasan yanda Al’amara suke a wajenmu..”


D’an jim Mu’azzam yayi kafin ya girgiza kai yace “No way.. Binciken nan is classified, there’s no how wani daga department d’inmu zai zama snitch... The only Rat here is Chief Jaja.. And don’t forget a aiki irin namu wanda ya d’auraka kan bincike zai iya maka zagon k’asa domin ya b’afar da basirarka..”


Girgiza kai Assad yai yace “I don’t think Chief Jaja zai aikata wani abu mai kama da haka  sabida idan baka mance ba kafin Chief yasan da labarin anyi sketching fuskar Danger a matsayin Uncle d’in Sagir saida ka nufi Office d’insa ka sanar dashi.. Da ace  yau ne Danger yasan da labarin an zana fuskarsa a matsayin Uncle d’in Sagir da mun samu wani trace ko alamun cewa yau ne ya gudu.. At least da mun samu mutane a majalisar.. Amma bamu samu trace ko wani alama na hakan ba.. It’s possible Danger yana cikin shirinsa tintini.. Ba Lallai ya kasance yanada agent a CID ba..”


K’urama waje guda idanu Mu’azzam yai yana nazari.. A hankali ya soma girgiza kai “No Assad.. Those people are smart, ‘Yanta’adda k’wararru bazasu bar wani trace ko alama ba.. I’m positive akwai snitch a department d’inmu..”


Assad ya d’an nusa kafin yace “Who do you have in mind..?”


“Mutum d’aya ne kuma ba kowa bane face Chief Jaja.” Ya fad’i yana duban Assad d’in.


“Be careful who you’re up against.. Kabi komai a sannu Mu’azzam har ka gano bakin zaren komai.. Ba komai bane da ya bayyana maka zai zamto gaskiya.. Nasan kasan da hakan..” Assad ya fad’i yana duban abokin nasa..


Fuzar da huci Mu’azzam yayi kafin yace “I trust my team members, you’re my best friend, Yusuf ma amintaccenmu ne.. Sannan Maleeka..”


Assad ya ida maganar da fad’in “Maleeka you’re her all time crush.. Muna tare da ita tin a police Academy.. And I guarantee you wannan yarinyar babu abinda take buri face taga Tayi abinda zai burgeka Ta samu karb’uwa wajenka.. She’ll never betray you. Inada guarantee akanta. She loves you so much..”


Mu’azzam ya d’an fuzar da fuci kad’an yana duban Yusuf da Maleeka daketa k’ok’arin neman trace na Danger dik yanda ya shiga ya fita.. A hankali yace “We’ve one option idan munaso mu kamo Danger da accomplices d’insa..”


Assad ya dubesa yace “Wani option kenan..?”


“The girl..” Ya fad’i yana duban Assad kafin yaci gaba da fad’in “Through her muka San cewa Danger nada saka hannu a crime d’in nan.. I believe through her zamu samo yanda Danger yake..”


“Kaman yaya.? According to her statement ita kanta da family d’inta basusan waye Danger ba.. Ta yaya zata samo mana yanda yake..?” Assad yace yana duban Mu’azzam d’in.


Murmusawa kad’an yayi kafin yace “Kana magana kaman ba ma’aikacin bincike ba.. Ai yanzu na tabbata Danger bazai bar family d’inta ba muddin yasan ansan wani abu akansa.. Nasan dole zai hanasu magana ma ‘yansanda ta ko wacce hanya.. Sannan zai saka masu ido idan yaga jami’an tsaro na zarya wajensu.. Zai making move d’insa.. Mu kuma zamu buga wasan idan yayi losing.. Caraf sai kama wuyarsa..”


Assad ya jinjina kai yace alamun gamsuwa sai kuma yace “But don’t you think rayuwar yarinyar da ahalinta zai zamto yana cikin garari..?”


Mu’azzam ya jinina Kai yace “Already cikin had’ari suke tinda sukai involving kansu da wannan criminal d’in.. They are in this mess already..” 


Assad ya d’an nusa kafin Mu’azzam yace su tafi gidansu yarinyar.


Assad ne yai alama masu Maleeka da Yusuf yace Su k’araso su tafi..


**


Har lokacin Sadiya kife kanta yake kan gawan mahaifinta da tuni an gama shiryasa cikin suturarsa na gidan gaskiya.. kuka take da duka zuciyarta, cikin kuka take furta “Abba Maiyasa zasu maka haka.? Su waye suka maka haka..? Abba Dan Allah ka tashi.. Kar ka tafi ka barmu.. Abbbaaaa..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka


Tinda suka doso layin ya tsaya yana duban cincirindon mutanen dake tsartsaye k’ofar gidan nasu ana jajanta lamarin..


Wani mutumi da hatsarin ya faru gabansa yaci gaba da bama sauran labari “Ai mai mashin ne ya fara bugesa, kansa na rufe cikin rawani.. Malam Ibrahim tareda yaransa guda biyu yake tafiya sai mai mashin d’in ya bigesa ya cillasa wani gefen.. Yana cillasa gefe guda mai mota yabi kansa.. Wllhi abun abin tashin hankali kaidai..”


Mu’azzam kam bai iya sauraron tattaunawarsu ba Yusuf da Assad ne sukai sallama kafin suka ja mutumin gefe suna tambayarsa yai masu bayani dalla dalla yanda had’arin ya kasance.. Shikam Mu’azzam tuni ya kutsa Kai cikin gidan Dan tabbatar ma idanunsa abinda ke faruwa..


Cak ya tsaya yana dubanta yanda ta kifa kanta saman k’irjin mahaifinta tana kuka mai ban tausayi ga mahaifiyarta gefe rungume da k’annenta suma duk kukan suke.


Cikin sautin kuka Sady taci gaba da fad’in “Abba Dan Allah ka tashi kace ka yafe mun.. Nasan nayi maka laifuka da dama Abba, Abba dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barmu bazamu iya ba.. Maiyasa suka kad’e mun kai Abba na..”


Muryarsa ne ya katseta da da fad’in “Because they believe your father knows something shiyasa suka kashe shi Dan kar ya tona masu asiri..!”


Cak Ta tsaya da kukan nata sakamako sinkayo muryarsa da Tai... Ta d’ago rinannun idanunta ta sauk’esu tsaf akansa, zuciyarta na mata wani irin zogi take dubansa.. Take tsanansa ya ninku cikin zuciyarta..


Cikin kuka ta mik’e tana furta “This is all your fault.. Ku kuka jawo aka kashe mana Abbanmu.. Maiyasa bazaku k’yalemu ba.. Bamu San mutumin da kuke nema ba, bamu San komai akansa ba.. Mun sanar daku Iyakacin abinda muka sani.. Mahaifina Bai cancanci a kashesa mercilessly irin haka ba... Just leave us alone already.. Ka tafi Dan Allah.. Kuje can ku nemi criminals d’in da kuke nema.. And leave us in peace..!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o had’ida zubewa saman gwiwoyinta..


Dubanta kurum yake yana jin zuciyarsa na masa wani irin k’una.. Yana duban yanda hawayenta ke zubowa da sautin kukanta had’ida rok’onsa da takeyi ya tafi ya k’yalesu suji da rashin mahaifinsu da sukai.. A hankali ya soma jada baya still idanunsa akanta..


Cikin sauri Mu’azzam ya juya ya fice daga gidan gaba d’aya yana duban yanda Sadiya ta zube saman gwiwoyinta tana kuka mai tab’a zuciya..


Har ya shige su Assad dake faman tattare bayanai daga wajen mutanen unguwa basu lura dashi ba.. Sautin tashin motarsu kurum sukaji.. Assad ya saki baki yana dubansa.. Maleeka dake faman rubuce rubuce itama baki sake take duban Mu’azzam d’in..


A yanda sukaga ya kwashi motar sunsan komai ka iya faruwa..


Assad ya girgiza kai yana mai furta “Oh no..! Mu’azzam mai kake shirin aikatawa..?”


**


Ko parking mai kyau bai ida ba ya nufi ofishin Chief Inspector Jaja... A lobby ya iske Chief tareda wasu abokan aikinsu ‘yansanda suna tatauna wani matsalan.. Mu’azzam duban Chief kurum yake yana kuma sinkayo kukan yarinyar da yanda take fad’in an kashe mata mahaifi ba tareda ya aikata laifin komai ba.. Fuskar yarinyar yake hangowa cikin idanunsa yanda Ta duk’a tana zuban hawaye.. Baiyi wata wata ba yana isowa ya dunk’ule hannunsa yakai ma Chief naushi maiji da lafiya a Hanci wanda saida takai Chief har k’asa..


Ba Chief da yaji sauk’an naushin kaman a mafarki ba harta sauran ‘yansandan saida suka tsaya suna duban Mu’azzam cikin tsananin Shock Dan kaf d’insu babu wanda yaga zuwan Mu’azzam sauk’an naushin kawai suka gani..


Mu’azzam ya cakumo wuyan Chief yana fad’in “Lets end it now.. You better tell me waye kake karewa.. Ka sanar dani Manzo Jaja.. Waye kake karewa.. Do you know how many innocent lives are stake here.. Shin kasan rayuka nawa ka jefa cikin garari da gurb’atacciyan zuciyarka.. Tell me.. Tell me Chief Manzo Jaja..!!” Yanda yake jijjiga Chief dole ya baka tsoro..


Wane irin fincika Chief yai yana tsananin huci yayinda sauran ‘yansandan suka janye Mu’azzam daga jikin Chief..


Huci kurum Chief yake yana nuna Mu’azzam da ‘yar yatsa ga bakinsa dake fidda jini sabida naushin da Mu’azzam d’in yai masa “You’ll pay.. You’ll pay for this..!” Ya k’arashe yana mai shigewa ofishinsa cikin tsananin b’acin rai..


Daidai lokacin su Assad suka k’araso duk a birkice suke..


Yanda Assad ya hango Mu’azzam yasan mai aukuwa ya auku.. Saurin k’arasawa yai wajen abokin nasa dake faman yarfe hannuna wanda ya naushi Chief dashi.. Hannun Mu’azzam d’in kawai Assad ya duba da yanda yake yarfe hannun nasa ya fahimci cewa mai aukuwa ta auku..


Assad ya k’araso yana duban yanayin mutanen dake wajen yanda kowa yasha jinin jikinsa..


Dafa Mu’azzam d’in dake zaune saman kujera ya kifa kansa k’asa yai.. Ko baa ce kasan zuciyarsa ce ke tafarfasa


“Can you tell me now.. What really happened here..?” Baikai ga basa amsa ba sukaga ana mik’owa Mu’azzam d’in Doguwar takarda cikin envelop.. Saida ya dubi mai mik’o masa takardan kafin yasa hannu ya amsa takardan ba tareda ya amsa tambayar Assad ba..

Lokaci guda ya shiga warwareta.. A hankali ya lumshe idanunsa Dan yasan za’a rina haka.. Suspending d’insa akayi har na tsawon makonni biyu... Cikin sauri Assad ya amshi takardan yana karantawa..

Dafe kansa kurum Assad yai yana mai fuzar da fuci..


Cikin tsananin b’acin rai Assad ya soma fad’in “You see.. Kaga abinda nake fad’a maka Mu’azzam.. You never listen.. You’re so stubborn Mu’azzam.. Yanzu ga irinta nan kaja an dakatar dakai..”


Bai k’arasa sauraron Assad ba ya mik’e yai ficewarsa waje.. Assad ya biyo bayansa yana ci gaba da magana cikin tsananin b’acin rai..

Idan jacket d’in dake jikinsa ya amsa shima zai amsa.. Yanda motarsa ke ajiye ya isa ya shige, har lokacin Assad na masa magana yana k’ok’arin dakatar dashi suje dubawa Chief hak’uri ko rage masa tsawon wa’adin suspension d’in ne ayi amma ko ranka Assad baiba..


Tuni ya shige Mota ya fuzgeta.. Yana driving amma kukan yarinyar da rok’onsa da take su fice masu a rayuwa bai daina Yawo a kwanyarsa da dodon kunnuwarsa ba.. An kashe mata mahaifi dik akan binciken da yake na neman gaskiyar mutuwar ‘yaruwarsa.. A hankali ya lumshe idanunsa yana mai jin motar bayansa na danna masa horn.. Cikin sauri ya ware idanun nasa yana k’ok’arin saita kansa Dan k’iris ya rage baiyi causing accident ba..


Traffic ne ya tsaidasu, a daidai k’ofar wani kanti yake hango k’aton takardan Sanitary pad irin na advert d’in nan.. Lokaci guda ya tuna sanda Ta jefe shi da gidan abin.. Nan yake tina farkon had’uwarsu.. Yayi nisa duniyar tunani yaji ana masa horn motar bayansu alamun traffic light ya basu koren wuta..


Lokaci guda ya soma tafiya cikin tsanaki.. Bai zarce ko Ina ba Sai gidansa.. Saida ya iso gidan ya tina ashe su Safeenah na gidan ya kwance masu karnuka..


Ya ida shigo da motarsa yai parking a gefe Karnukan har sun koma gefe, suna ganinsa suka taso suna shinshina k’afarsa.. Yakai dubansa ga motar Safeenah, a hankali ya janyo chain d’in dake d’aure wuyan karnukan ya maidasu d’akinsu.. Lokaci guda ya isa jikin motar Safeenah..


Ta cikin glass yake dubansu yanda sukai laushi, d’an kad’an suka zube glass d’in ta d’an sama kad’an yanda iska zaike d’an shigo masu kad’an..Safeenah kam kamar ma bacci tai dan azaba, tana tak’ure jikin seat ga bushesshen hawaye kwance saman fuskarta..


Meema ce batai bacci ba amma har lokacin hawaye ne cikin idanunta.. Tana ganinsa ta mik’e wani kukan na zuwa mata.. Saman gwiwoyinta ta duk’a nan kan seat d’in, Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana fad’in “Ya Mu’azzam dan Allah kayi hak’uri.. Wllhi na tuba bazan sake ba.. Dan Allah ka k’yaleni na tafi gida na rok’eka...” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka..


Cikin ransa yace ashe k’aryar rashin kunya kike.. A fili kuwa bai furta komai ba.. Kukan Meema ya tada Safeenah.. Tana ganin Mu’azzam ta wani zabura ta mik’e zaune.. Take ta fashe masa da wani irin kuka ba tareda tace komai ba.. Saida tai mai isarta kafin ta tsagaita, cikin rawar murya take fad’in “please take us home..”. Ta fad’i tamkar zata kuma kurma wani ihun..


Basu baya yai kafin ya ciro wayarsa cikin aljihu.. Dialing layin driver d’in gidan yai ya sanar dashi ya shigo Cab yazo ya samesa..


Jim kad’an kuwa driver d’in ya iso da shike gidan nasu babu wani tafiya sosai tsakani..


Car keys d’in motar Safeenah ya mik’a masa bayan ya iso yace ya kaisu gida. Driver d’in ya amsa cikeda girmamawa kafin ya bud’e motar ya shige mazaunin driver.


Abin sosai ya sosa ran Safeenah watau bazai kaisu gida ba dikda yanda ya basu azaban nan sukai Laushi saidai ya kirawo driver ya kaisu.. Tana fama da kanta bazata iya tanka masa sannan wani sabon shakkarsa ne ya d’arsu a zuciyarta hakan yasa batace komai ba Sai mutsuke ragowar hawayen idanunta da take.. Ita dai Meema bata damu ko uban waye zai maidasu gida ba. Burinta kawai ta fice daga gidan ta ganta a gidan mahaifinta..


Suna isowa gida kai tsaye upstairs suka haye a jikace dan dama gidan ba kowa daga ma’aikata sai Mommy da Kiki. Su Daddy da Musaddiq da Inne harmada Aunty Nurah sun tafi Fufore a jiya..  Mommy ce kawai ma a gidan Sai ma’aikata dan Kiki tana WAEC Lesson zatayi trial a SS2.. Meema kuma dama jiran admission d’inta take ya fito a UK amma bayan Mommy taji yanda Safeenah ta watse da mazan turawa ta fara shakkun Barin Meema ta fita karatu waje. 


Ummati Dattijuwa cikin ma’aikatan gidan ne ta had’u dasu zasu haura sama a jigace. Tana tambayansu lafiya suke ko iya amsata basayi Meema kam ma da rarrafe take k’ok’arin shigewa d’aki..


Ummati ta girgiza kai kad’an ta shige sanar da mahaifiyarsu.. Domin kuwa babu lafiya tinda har Meema da Safeenah ne zata masu magana basu darara mata tsawa ba.


Koda Mommy ta taddasu Safeenah ke labarta mata duk abinda ya faru.. Tamkar ta rufe Safeenan da duka dan takaici haka Mommy taji.. Ta rasa wace irin wauta ne kan Safeenah.. Wai har Meema ce zata bata shawari ta d’auka.


Mommy tai k’wafa tana duban Safeenar cikeda takaici “Ya miki kyau ai.. Ki godema Allah da bai baki takardanki tin a titi kafin ki tare gidansa ba.. Banda shashanci da dolanci irin naki ta yaya zaki bisa har wajen aikinsa kici masa mutunci kici ma abokiyar aikinsa mutunci without any solid evidence..”


Cikin kuka Safeenah ta katseta da fad’in “Mommy I’ve proof... Sanitary pad d’in is enough evidence.. And Mommy you should have seen her face sanda nake cin mutuncinta ita karuwar.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba cin amanata yake da Ita...”


Dak’uwa Mommy ta dunk’ula mata tana fad’in “Kimin shiru kafin na tashi na tattakaki a wajen nan.. Banda ke shashasha ce sokuwa, idan ma da gaske cin amanar naki yake ta haka ne zaki samu gaskiyan lamarin..? Ta haka ne zaki kare auren naki..? Wannan dolancin da kikayi bashi zai hana ya fasa abinda yake ba idan ma yanayi d’in..Kusanci ma zaki K’ara masa da ita.. Yanzu haka zaije ya lalasheta bayan ya gama cin k’aniyarki.. Kinga wa gari ta waya..”


Safeenah tai shiru tana duban mahaifiyarta tana jin zuciyarta na mata k’una. “Mommy yanzu ya zanyi..?”


“Ya kuwa zakiyi banda ki k’yaleshi har ya sauk’o kafin ki basa hak’uri kan abinda kikai..”


A zabure take duban Mommy “Mommy shi fa ya mun laifi amma kike cewa na basa hak’uri..” Ta shiga bubbuga k’afafu tana turo baki tana kuka take fad’in “Wllhi dama an jima ana nuna wariya gidan nan.. Daga ke har Daddy bakwa tab’a ganin laifin Mu’azzam, dik abinda yayi daidai ne wajenku.. Wllhi Mommy this is not fair..!” Tana maganganun tana kuka ta shige bathroom..


Tsaki Mommy tai cikeda takaicin ‘yar nata.. Ita batasan ba dan komai take so Ta auri Mu’azzam ba sai dan watarana Fortune d’in Mu’azzam d’in wanda Mahaifinsa ya mutu ya bar masu ya dawo hannunsu.. Mahaifin Mu’azzam shike Babba cikin yaran mahaifinsa.. Su Uku ne yaran Jauro Gamji, Abubakar wanda shine Babba kuma shine mahaifin Mu’azzam da marigayiya Ikram, sai Marwan Wanda shine mahaifin Safeenah Musaddiq Maryam(Meema) da kuma Karimatu (Kiki). Sai Salman wanda shine autan Inne kuma shine cikon na ukunsu.. Shi yana zaune ne a can Fufore dan kula da gidan gonar su dake Fufore d’in da kuma Kampaninsu na GAMJI MEAT FACTORY dake Adamawa.. Kaman yanda Daddy ke kula da Kampaninsu na GAMJI DIARY DISTRIBUTION FACTORY dake a birnin tarayya Abuja.. Gidan Gonar da kakansu Jauro Gamji ya mutu ya bar masu shine yake samar da nama da kuma madaran da companies d’insu ke producing.. A halin yanzu Uncle Salman shike kulada Gamji Meat Factory dake Adamawa wanda a baya mahaifin Mu’azzam shike kula dashi. Sannan shi Uncle Salman d’in shi ke kula da Babban gidan gonar nasu dake garin Fufore. A can gidan gonar suke zaune gaba d’aya dan mahaifinsu saida ya k’era gini maiji da lafiya a cikin gidan Gonar wanda tafiya mai d’an nisa zakai kafin ka isa ginin sabida tsaban girman da gidan gonar kedashi bama zakai tunanin a gidan gona kake ba idan ka shige cikin Mansion d’in.. Shuka da shanu suna cen gefe yanda ake kula dasu..


Uncle Salman da iyalansa harma da Inne a nan gidan Gonar suke zaune.. Uncle Salman yanada mata guda d’aya mai suna Shema’u tareda yaransu guda uku duka mata. Babbar zatai tsara da Meema sai sauran k’annenta guda biyu wanda Twins ne...

A lokacin da mahaifinsu Mu’azzam ya rasu Uncle Salman yaso a cire kason Su  Mu’azzam da k’anwarsa Ikram a basu tinda dole sunada kaso a both companies d’in.. Kason mahaifinsu.. Ya zaman babu sauran kason mahaifinsu cikin dukiyar.. Babu yanda Uncle Salman baiba  Daddy yak’i amincewa da hakan.. Yace wannan kasuwanci ta ahalinsu bazai tab’a yuwa a cire kason Su Mu’azzam a basu ba dole za’a ci gaba da juya musu dukiyarsu ba tareda an bari dukiyar ta salwanta ba, idan shi Salman bazai iya kulada dukiyar ‘ya’yan d’anuwansu ba Wato Mu’azzam da Ikram shi Daddy zai kular masu dashi  zaici gaba da juya masu har lokacin da zasu buk’ata.. Koda Mu’azzam ya girma Uncle Salman baisan Ina Daddy ke kai  kud’ad’en Mu’azzam d’in ba amma yasan duk budget da za’ai sai an cire nasu.. Yasan har wannan lokacin Mu’azzam da ‘yaruwarsa harma da mahaifiyarsu sunada kaso cikin dukiyarsu.. Wannan kenan..


**

A b’angaren Mu’azzam kusan kwana yai yana tinanin Abinda ya samu mahaifin Sadiya. Baisan dalili ba amma tinanin nasa mahaifin ne ya fad’o masa..Mahaifinsa da ya rasa a Meat cold Room wanda ya shiga inspecting freezer d’in tsautsayi da ajali ya ritsa dashi a can Meat Distribution Factory d’insu dake Adamawa.. Mahaifinsa yayi stucking a cikin meat cold room wanda har yayi ahalinsa sai gawarsa aka cire.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna irin mutuwar da mahaifinsa yayi, lokaci guda ya tina jarabawa na cuta da mahaifiyarsa ta had’u dashi ya kuma tuna rasa ‘yaruwarsa Ikram da yayi... A hankali ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa biyu.. Babu abinda yake so a halin yanzu kaman ya kasance da mahaifiyarsa.. Sosai yaji yana so ya tafi Fufore.

Bazai mance sanda aka ciro gawan mahaifinsa da ya sandare da k’ank’ara ba, kwanciya yai saman gawan mahaifin nasa yana kuka kaman dai yanda Sadiya ta kwanta bisa gawan mahaifin nata itama tana kuka..


Bazai tab’a mance kalaman lallashi da mahaifiyarsa ta fara furta masa ba ‘Kai hak’uri Mu’azzam, Duniya GIDAN ARO ce yanda mukazo cikinta kaman bak’i haka wataran zamu tafi mu barta.. Kayi hak’uri kayima Daddynka addu’a muma duka ma tafiya ne idan lokaci yayi’


A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kafin ya mik’e ya nufi motarsa..


Wajajen k’arfe shabiyu da rabi na dare ya shigo gidan. Baibi takan kowa ba ya nufi side d’insa ya soma shirya kayansa jirgin Washe gari yake so yabi zuwa Adamawa.


No comments

Powered by Blogger.