Doctor Mansoor 8

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


    Na

_Jiddah S Mapi_


*Chapter 8*


                 ~Saida tayi kusan awa uku tana bacci, shi kuma time ɗin ya dawo daga masallaci, hannunshi rike da sallaya ya turo kofan bakinshi ɗauke da sallama, tana zaune a kasa ta taƙure cikin hijabi tana rarraba

manyan idanunta, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yana cigaba da karanta addu'anshi wanda yake saurara ta cikin earpiece ɗin dake maƙale a kunnenshi, zama yayi a saman kujara yana latsa waya bai kara ɗagowa ya kalleta ba, dan ya lura akwai ta da kunya sosai ga kuma tsoro, saida ta ɗan nutsu ta daina tsoron kafin ta mike a hankali ta fita, baice kala ba har ta dawo ta cire ɗankwalin kanta ta shimfiɗa ta tada salla, cikin nutsuwa take yin komai har ta idar ta ɗaga hannu sama tana addu'a idanunta suna zubar da hawaye, saida ta shafa addu'a ta juya tana kallonshi, hankalinshi akan waya tace "good evening"

murmushi kaɗan yayi kafin yace "evening how are you"

"am good" tayi maganan kanta a kasa, bai kara yimata magana ba saida ta kalmashe ɗankwalin ta ta rike a hannu, zama tayi a ƙasa inda yake zaune tayi shiru tana kallon kasa, bai ce komai ba sai latsa waya yake, saida ta kara kuka sosai kafin ta share hawayen tace "ko akwai aikin da zan iya yi a cikin wannan asibitin wanda zan iya kwana tareda marasa lafiya?"


ajiye wayan yayi yana kallonta da kyawawan idanunshi, lips nashi yake tauna a hankali kafin yace "ya sunanki?"


"Jahad"


Lumshe ido yayi kafin yace "jahad meke faruwa kuma yanzu?"

share hawaye tayi kafin tace "bayan an zubar da cikin na koma gida kanin Abba ya rinƙa zuwa yana gayawa Abba wai bana jin magana ina bin maza harma na zubda ciki, da Abba ya kirani bai tambayeni komai ba sai cewa yayi na zubda ciki ko ban zubar ba?

niko nayi duba da irin rashin lafiya da yake ciki nace banyi ba, shine yace nayi alwala na rantse da qur'ani, jin haka yasa nace na zubar, daganan Abba bai kara juyowa ya kalleni ba, hasalima cewa yayi ko muryata baison ji, ya tsane ni, Baba Bala kuma ya kwace kuɗaɗen hannuna yayimin duka, ka duba jikina.

ɗaga rigan jikinta tayi tana nuna mishi yadda shatin bulala ya fito sosai har yayi ciwo a jikinta, rufe ido yayi yana jin zafi sosai a cikin zuciyarshi, hannu ya ɗaga mata alaman ta sauke rigan, saukewa tayi tana hawaye sosai, fita yayi daga office ɗin, saida yayi kusan 30mins kafin ya dawo ya mika mata waya, a hankali tasa hannu ta karɓa, karawa tayi a kunne cikin sanyin murya tace "salamu alaikum"

Ammi ce ta amsa tana bata hakuri akan abinda yake faruwa, domin Man yayi mata bayani, abu ɗaya ya ɓoye shine zubar da cikin da sukayi, saida ta kwantar mata da hankali kafin tace "idan zai dawo zaku taho tare ɗa na kowa ne"


sauka kasa tayi daga kan kujeran tana mata godiya tana kuka, hakuri Ammi ta bata, ganin kukan yayi yawa ya amshe wayar yana cewa "sai munzo Ammi na"

kashewa yayi ya zauna a kujeranshi yana kallon yadda take zaune a kasa har yanzu bata daina kuka ba, kallon gashin dake kwance a gaban goshinta yayi, wanda yake kara mata kyau, ɗagowa tayi bai taɓa ganin wacce kuka yake mata kyau kamar wannan yarinyar ba, saide kukan yayi yawa da alama ta saba da hakan, hannu ya ɗaga mata alaman tayi shiru, murmushi ta sakar mishi kafin ta share hawayen tana sauke ajiyan zuciya.


7:30pm


Saida ya idar da sallan Isha kafin yazo yana kallonta, bacci take cikin kwanciyar hankali ta rufa jikinta da hijabinta, kallonta yayi sosai tana da sihirtaccen kyau, ga skin nata yana shining sosai, kawar da tunanin yayi yaɗan buga kujeran da take kwance akai, bata farka ba hakan yasa ya kara bugawa tareda cewa "jahad?"

a hankali ta buɗe idonta ta sauke a kanshi, lumshewa tayi cikin sanyi ta saki murmushi kafin tace "gari ya waye ko?"

girgiza kai yayi kafin yabar wurin yana shirya kayan dake kan tebir ɗin, saida ya shirya yaɗau jakanshi yace "muje ko"

tashi tayi tana binshi a baya har suka isa Parking space, tafiya yake cikin kasaita da nuna shiɗin cikakken namiji ne, buɗe motar yayi yashiga, ta tsaya tana kallonshi, saida ya kalleta kafin ya nazarceta da alama ta saba a buɗe mata mota ne shiyasa ta tsaya, shiru yayi ya jingina kanshi da jikin motar ya kira number ɗin Bro Ahmar yana ɗagawa suka fara hira yadda suka saba, saida ta gaji kafin tasa hannu a jikin marfin motar ta buɗe cikin tsoro ta shiga, zama tayi tana aikin murza yatsun hannunta wanda ya zame mata jiki, kallo ɗaya yayi mata kafin ya watsar yaja motar suka bar cikin hospital ɗin, har suka yi nisa babu wanda yayiwa juna magana, shiru tayi tanajin cikinta yana wani irin juyawa alaman yunwa sosai takeji domin rabonta da abinci tun jiya, kofar makeken get nasu suka tsaya yayi horn kafin megadi ya buɗe, cusa hancin motar yayi zuwa ciki, kallon cikin gidan tayi ta cikin glass ɗin motar, gabanta ne ya faɗi, taji ranta yana wani irin tsinkewa, ta yaya zan iya rayuwa a wannan gidan? nashiga uku, kallonta yayi bayan yayi parking, murmushin ta me sanyi tayi mishi kafin ta buɗe motar ta fito, gaba ya shiga bayan ya rataya jakanshi ya yiwa Ahmar sallama, wayan a hannunshi yake takawa zuwa cikin gida, kallon bayanshi tayi, yana dakwarjini sosai ba kaɗan ba, hakan yasa ko tambaya takeso tayi mishi bata iyawa domin tsoronshi take sosai, binshi ta fara harda ɗan gudunta saida suka isa kofar babban palour kafin ya tsaya ya nuna mata hanya, shiga tayi tana tafiya a tsorace, da gudu Noor tazo ta rungumeta, tana dariya tace "welcome Unty Jahad"

murmushi tayi kafin ta shafa bayan Noor tace "nagode"

dama kafin yazo Ammi ta sanar musu cewar za suyi bakuwa, Jawad da yake saukowa daga up ya kalleta tareda cewa "welcome" bai jira ta amsa ba ya wuce abinshi, binshi Man yayi da kallo yana mamakin yadda bai wani sake mata fuska ba, lalle Jawad ya girma yakejin kanshi yanzu, Ammi ce ta sakko itama kyakkyawar fuskarta ɗauke da murmushi tasa shadda light blue wanda yaji zubi da red na zare, tana karasowa ta rungume Jahad tana murmushi tace "sannu da zuwa ƴata"

Man kam ya riga ya wuce tun ɗazu, dukar da kai tayi ƙasa tace "yawwa" durkusawa tayi kasa tace "ina wuni hajiya"

ɗagota Ammi tayi tace "no ba hajiya ba, ki kirani da Ammi kamar yadda yayanki da kannenki Noor da Jawad suke kirana"

a hankali tace "tom Ammi"

"Yawwa ƴar albarka, ga Noor ta kaiki ɗakinki sai kiyi wanka kici abinci ki huta ko?"

girgiza kai tayi hawaye yana sauka a idonta, sun tarbeta kamar dama sun santa, wannan shine abinda yake sata kuka, "no bamason kuka a gidannan" cewar Noor wacce take janyo hannunta, ɗakinta dake gefen na Noor ɗin ta kaita kafin ta nuna mata toilet da sauran kayan amfaninta, godiya tayi kafin ta shiga ciki tana share hawaye, saida tayi wanka tasa wani dogon abayan da aka ajiye mata akan bed, dark blue ne da mayafinshi ɗan karami, sawa tayi nan ta kalli jikinta ta cikin mirror, ba karamin kyau tayi ba, saide yaɗan kamata domin tanada hips sosai, hijabinta tasa kafin ta sakko zuwa kasa, dukka suna zaune akan kujeran dining suna cin abinci, Man ya maida hankali sosai akan daddaɗan abincin da Amminshi ta dafa mishi, Ammi ce ta mike ta rikota, hijabin jikinta ta cire tana cewa "kema ƴar gida ce" 

kame jikinta ta fara da hannunta tana kallonsu da manyan idanunta, ɗan ɗago kai yayi ya kalli yadda rigan yake kwanciya a jikinta, idanunshi yakai kan hips nata wanda ya bayyana ta cikin abayan da yayi matukar fito da kyawunta, ɗauke kai yayi da sauri ya kara cin abincinshi yana faɗin "ya Allah"

a gefenshi ta zauna tana kallon Jawad wanda ya ɗauke kai yana shan drink, a hankali tayi murmushi cikin zazzakar muryanta tace "kanina?"

wani irin kololon bakin cikine ya cika zuciyar Jawad, wai kaninta, murmushin dole yayi mata kafin yace "ina wuni"


"Lafiya kalau" ta faɗa, a hankali ta fara cin abincin da Ammi ta zuba mata, lumshe ido tayi domin yayi daɗi, kuma rabonta da cin irin wannan tun lokacin da Dady yakeda kuɗinshi, ji tayi wasu hawaye suna sauko mata daga idanu, ji tayi abincin ya koma mata kamar maɗaci, turawa kawai take domin yunwa Ammi tana kallonta tanaci tana kuka, Noor tayi shiru kalan tausayi domin duk wanda ya kallo Jahad yasan tana cikin damuwa, Abba ne yayi gyaran murya ya shigo, amsa sallaman sukayi kowa yana gyara zamanshi, Jahad ganin haka ta sauko daga kujaran tana aika mishi gaisuwa, amsawa yayi fuska a ɗan sake, "Jahad ko?"

giɗa kai tayi, murmushi yayi "to sannu jahad naji duk labarinki hasalima ni nace Man ya kawoki gida, ki saki jiki nan kamar gidanku ne komai zaiyi daidai insha Allah" yana gama magana ya juya yayi tafiyarshi ba tareda yaji godiyan da zatayi mishi ba, hawayene ya taru a idon jahad hakika wannan family sunyi mata gata, babu abinda zata iya saka musu dashi, komawa tayi kan dining tana kallon yadda suke cin abinci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ido Jawad ya zuba mata yana kallon yadda take kallonsu Ammi, tashi yayi a wurin yana kiran waya, bin bayanshi Man yayi da kallo, kafin ya sa hannu a suman kanshi ya shafa yanajin cikinshi ya koshi.


              "Unty Hamida?" da mamaki ta kalli Ra'eefa wacce ta durkusa da hijabi dogo a jikinta tana tayata wanke wanke, shiru tayi domin abin ya mugun bata mamaki, murmushi ra'eefa tayi sai a lokacin naga tsananin kama da sukayi itada Hamida, hakika uwarsu suka biyo saide Hamida ta fisu farin fata da kyaun jiki, saida suka gama wankewa kafin tace "kina lafiya?"

Ra'eefa shiru tayi jikinta duk a mace, abin ya kara bawa Hamida mamaki, gyara karamin hijabin jikinta tayi kafin ta mike ta riko hannun Ra'eefa suka shiga cikin ɗaki, zaunar da ita tayi tana cewa "ki faɗamin menene yake damunki?"

kin magana tayi sai kuka harda jan majina, saida Hamida taga abin yayi yawa kafin ta mike ta ɗibo ruwa a cup ta bata, karɓa tayi ta sha kafin ta kwanta a gefe idanunta suna cigaba da zubda hawaye, jikin hamida yayi sanyi, bata taɓa ganin Ra'eefa cikin wannan halin ba sai yau, ta lura tun jiya jikinta ba'a sake ba, bacci ne ya ɗauke ta ba tareda tayi mata bayanin komai ba, fita tayi ta gama girki kafin ya girka mata ruwan zafi, tashinta tayi domin time ɗin sallan Azahar yayi, mikewa tayi da idanunta wanda suka kumbura sukayi luhu-luhu, murmushi Hamida tayi tace "je kiyi wanka sai kici abinci ko?"

giɗa kai tayi ta mike, saida tayi wanka taci abinci kaɗan kafin Hmaida ta kuma tambayarta meke damunta, bata amsa mata ba sai kuka da take cigaba dayi, zuwa yanzu Hamida ta fara tsorata saide kawai ta share taci gaba da aikin gabanta, tun daga ranan Ra'eefa ta fara shiga ɗakin Hamida suna kwana tare, biyayya da ladabi tanayi mata kamar ba gobe, duk abinda Hamida takeso Ra'eefa tanayi mata, hakan yayi wa umma daɗi domin yanzu Hamida ta fara sakewa a cikin gidan, Samha abin yana bata haushi tayi kokarin rabasu amma ta kasa hakan yasa ta kyalesu tana kallonsu, faɗan Baba ya ragu tunda Ra'eefa ta fara shiri da Hamida.


*Monday 28may 7:30pm*


Iska ake a garin sosai sakamakon hadari daya haɗu a sararin samaniya, gefe guda Hamida ce ke gudu tana kiran sunan Ra'eefa wacce tunda safe basu ganta ba, babu inda bataje ba domin duba ta amma bata ganta ba, dawowarta daga school kenan ta tarar da Umma da Samha suna kukan nemanta, fita tayi domin ta tsorata Ra'eefa ta jima da daina yawo koda ta fita tana dawowa da wuri, ruwa ne ya kece kamar da bakin kwarya, hijabin jikinta yanada tsayi domin riga da wando ne a jikinta wanda ya ɗan kamata, takalmin kafarta me sulɓi ne hakan yasa ta cire ta rike a hannu, gudu take ruwa yana jiƙata tana kiran Ra'eefa da karfi, ta area ɗinsu ta fara bi tana dube-dube, hawayene ya fara bin kumatunta yana haɗuwa da ruwan sama wanda ya jika mata fuska, tsoro takeji batason wani abu mara kyau ya kara faruwa da ƴar uwarta, so take ya tsaya akan adda Amrah, gudu take tana duba duk wani inda zata ganta saide shiru har yanzu, umma kam sun koma gida da Samha domin Samha tace ta gaji, a cikin wani kwalbati ta hango kamar hijabi ruwan lemo, gabanta ne ya faɗi ga ruwa yana gudu sosai a cikin ramin, da gudu ta karasa tana kara hango hijabin wanda tasan Ra'eefa tana color ɗinshi, tsayawa tayi cak tana kallon takalmi a gefen ramin, tabbas wannan takalmin Ra'eefa ne, ɗagawa tayi taga ya tsinke, a tsorace ta karasa wurin ramin jikinta yana ɓari, ihu ta kwala ganin hannu acikin ruwa yana motsi kaɗan kaɗan, babu me jinta domin ruwa ake sosai ga tsawa da walkiya duk a lokaci guda, daurewa tayi a ranta tana cewa "ba Ra'eefa bace"

janyo hannun tayi saida ta janyeta daga ramin taga yadda taji ciwo a fuska da gangar jikinta, ihu ta kwala tana kiran sunanta tareda jijjigata, ganin bata motsi ta mike zatayi gudu ta kira mutane, hannunta Ra'eefa ta rike bakinta yana motsi a hankali, dawowa tayi time ɗin hijabin jikinta ya sauka daga kanta, kunnenta ta kai wurin bakinta taji kamar tana magana, da karfi tace "menene? meya sameki?"


"un..un...unty.. Ha..ha.ha.hamidaa, Bashir yamin ci...ci.."

jikinta ne ya fara ɓari ganin Ra'eefa na shirin mutuwa da karfin da batasan tana dashi ba ta danne cikinta ruwa yana fita ta bakinta, "meya miki?"

kai kunnenta tayi zuwa wurin bakinta, tanaji tace "Bashir yamin ciki, nace kada...kada..kada ya zubar zan haifa..yace saiya zubar..shine..shine..ya kaini, wurin... doctor..... doctor... doctor....."

shaƙuwa ta fara, da karfi Hamida ta mari fuskarta tana cewa "kada ki mutu dan Allah, kada ki barni kamar yadda Amrah ta barni, ki taimakeni ki rufamin asiri zan kaiki asibiti, kiyi hakuri kada ki mutu, waye ya zubar da cikin"

ganin bakinta yana motsi sai cewa take "doctor doctor"

bata kumajin komai ba sai R.


"Doctor waye?"

hannunta Ra'eefa ta damke da nata, a take idanunta suka juya bakinta yana furta kalmar la'ila ha illah Muhammadan Rasulullah, Saw, har jikinta ya sake, kallon hannunta Hamida tayi da karfi ta daki wani ihun da batasan tayishi ba, saida mutanen dake cikin wani shago suka fito suna kallonta, ruwa ne ya tsaya cak babu ko Alaman yayyafi.


*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.