Doctor Mansoor 7


 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 7*



                 ~Fita yayi daga unguwar bai tsaya ko ina ba sai gidansu Man, sunyi waya yace yana gida shiyasa yabiyo ta nan, saida ya gaida Ammi kafin ya wuce part ɗin man, ganinshi kwance akan sofa yana latsa waya yasa ya harɗe hannu a kirji, da karfi yace "Maaan"

a firgice ya ɗago har wayan yana shirin kuɓucewa, kallon Ahmar yayi wanda yake ta dariya harda rike ciki, yatsine fuska yayi kafin ya cije lips saida ya bari ya zauna a gefenshi kafin ya ɗau wani wani katon trustpillow yana maka mishi a kai, da sauri ya kauce yana dariya

"kai kam Man akwai ka da tsoro kamar mace wallahi, daga kiran sunanka saika firgice kamar mai aikata abinda babu kyau"


"to ka sani ko abinda babu kyau nake aikatawa"

matsowa yayi kusa da shi kafin ya riko hannunshi duka biyu yana kallonshi cikin ido yace "na san halin kanina kuma abokina bazai taɓa aikata wani abinda babu kyau ba, domin shine yake mana hani da aikata abinda babu kyau, ina yimaka kyakkyawan shaida Man, kai ɗin mutumin kirki ne"


jikinshi ne yayi sanyi ganin yadda ƴan uwanshi suka yadda dashi, yasan ko da case na zubda ciki ake dashi ba zasu taɓa yadda ba, musamman Amminshi wacce ta bashi yadda hundred percent, tafa hannu Ahmar yayi ganin yadda man ɗin ya shiga duniyar tunani, ɗaga mishi gira yayi alaman meya faru yayi shiru, girgiza kai kawai yayi

"ba komai amma kamar naji kace min kaninka ko?"


da dariya yace "yes you're my little brother"

harara ya aika mishi "ka manta 5days kawai ka bani a duniya"

"koda one second ne ai na baka rata, kaga ni duk ba wannan ba, yanzu na tashi daga school ɗin su Kabir wallahi wata innocent beauty na gani, yarinyar tana da sanyi ga kyau ga hankali"


murmushi Man yayi wanda ya bayyana kyawawan fararen hakoranshi, lumshe ido yayi ya kuma buɗewa yana kallon Ahmar, "kaine yau da yabon mace? brother na ya faɗa love"


"kai nifa ba sonta nake ba, kawai de yarinyar ta bani tausayi ne, domin yadda na fuskance ta kamar tana cikin damuwa, kuma akwai talauci sosai a tare da ita"

yayi magana yana buɗe drowern dake gaban shi, ciro wani kwali yayi ya buɗe tare da gyara zama ya fara cin pizzan da yake kanshi sosai tun shigowarshi ya jiyo ƙamshin shi.


haɗa fuska Man yayi, ya ajiye wayar hannunshi da sauri ya mike yaje gaban Ahmar ɗin ya ɗauke kwalin kafin ya juya, janye kwalin Ahmar yayi nan suka fara faɗa akai, Ammi da tazo kiran Man tayi knocking badu amsa ba, buɗe kofan tayi ta gansu suna dambe kamar yara, hannu tasa ta dafe goshinta "ya Allah yaushe waɗannan zasu girma ne?"

ƙarasawa tayi wurinsu da karfi ta kwace kwalin pizzan tana kallonsu, dukar da kai Man yayi sai kuma Ahmar da ya matso wurin Ammi yana rike kafaɗarta, a hankali yace "Ammi na kinga wallahi Gara da kika zo, da baki shigo ba da yasa mun zubar da pizzan nan, tunda kinzo ki bani naci ko?"

hannu yasa zai karɓa da sauri ta mayar ɗayan gefenta tana murmushin baka isa kamin wayo ba, turo baki yayi "Please Ammi na ki bani"


kin bashi tayi ta juya zata fita, "idan kun gama faɗan ku sakko kasa muci abinci"

fita tayi, gwalo Man yayi mishi kafin ya buɗe kofa ya fita, shima binshi yayi suka sauka zuwa kasa, abinci aka jera akan dining ɗin cikin kuloli na alfarma, Noor tana ganin Ahmar ta zo da gudu ta rungumeshi, ɗagata yayi sama kafin ya sauketa da sauri yana yarfe hannunshi 

"me nayi ya Ahmar?"


"bakiyi komai ba, nauyi kika kara kamar me cin abincin karfe"

dariya suka kwashe dashi harda Jawad wanda ya shigo yanzu jin zasuci abinci, zama sukayi kowa a kujera kafin akayi serving ɗinsu, Jawad ya cika plate ko ɗago kai baiyi ba yana cin coconut rice, wanda yaji kwakwa da kayan lambu, Noor ma tana cin nata, sai Ammi wacce ta ke faman shan zobon da ta haɗa, Man da Ahmar suma suna ci, wayar Man ce tayi kara yayinda take hannun Ahmar, a hankali ya juya zai duba, da sauri Man ya fizge wayan, ran Ahmar ne ya ɗan ɓaci, domin Man baison a turo mishi sako wayarshi a hannun mutum "kenan bai yadda dani ba?" yayi maganan a cikin zuciyarshi, saida ya duba sakon ya karanta kafin ya ajiye wayan a gabanshi, ɗago kai yayi yana kallon Ahmar wanda ya canja fuska alaman ranshi ya ɓaci, yadda man ya wafce wayar kaman bai yadda dashi bane sam-sam.


baiyi magana ba sai taɓe baki da yayi ya cigaba da cin abincinshi, saida ya gama kafin ya ɗau tissue ya goge bakinshi tareda cewa "alhamdulillah"

tashi yayi zai tafi saida yaje bakin kofa Ammi tace "wani sako aka turo maka yanzu?"

tsayawa yayi cak yana jin gabanshi yana faɗuwa, saida yayi 3mins a haka kafin ya juyo yana murmushi yace "Ammi sakon mtn ne kin sansu da son tura sako"

da mamakinshi yaji tace "ka bawa Ahmar ya duba kuma ya karanta da karfi, koda  point ne ban yadda ya tsallaka ba"


"Ammi? baki yadda dani bane?"


"na yadda dakai hasalima yadda da nayi da kai shine dalilin da yasa na faɗi hakan, ka bashi"

hannayenshi ne suka yi mishi nauyi, ji yayi zuciya da kirjinshi sun buga a tare, wani irin zufa ya fara ƙeto mishi, lips nashi na kasa ya tura cikin bakinshi, a hankali ya lumshe ido yana rike wayan sosai a kirjinshi, jin muryan Ammi ta kuma cewa "ka bashi nace"

ba zai iya jayayya da Ammi ba hakan yasa ya juyo yana kakalo murmushi, a hankali ya fara takawa zai mikawa Ahmar sallama suka ji, tsayawa yayi cak ganin Abba yana shigowa, manyan kaya ne a jikinshi wanda yake fari sol, bayanshi bodyguard ne rike da jaka da alama na Abba ne, da sauri duk suka mike suna yimishi sannu da zuwa, hannu ya ɗaga musu kafin ya karɓi jakanshi ya fara takawa har zuwa sama, saida ya kai karshe kafin yace "coffee"

Ammi da ta tsaya cak tana kallon su Ahmar wanda suke tsaye kowa yasha jinin jikinshi tayi murmushin yaƙe kafin tace "ku zauna kuci abincinku ina dawowa"

zama sukayi su duka, Man ganin haka ya silale ya bar ɗakin ba tareda ya bashi wayar ba,  yasan idan ya bashi asirinshi ya tonu, kuma babu shakka Ammi saita faɗawa Abba wanda hakan zai iya sawa Abba ya cireshi daga cikin ƴaƴanshi, da kanta ta shiga kitchen ta haɗa coffe mai sanyi, domin baison mai zafi, ice ta sa a cikin cup ɗin kafin ta ɗaura akan karamin plate ta kai mishi, knocking tayi kusan sau uku bai amsa ba, a hankali ta turo kofan ta shiga, yana zaune akan sofa ya ɗaura kafarshi kan centre table, jikinshi sanye da jallabiya hannunshi rike da remote yana canja station, zama tayi a gefenshi tace "sannu da dawowa"

"yawwa" ya faɗa tare da karɓan cup ɗin ya fara sha, saida ya shanye tass kafin yace "ina Man?"


"yana ɗakinshi" tayi magana a ɗan tsorace domin Abba yana da kwarjini sosai, kana ganinshi sai ka tsorata tun kafin yayi magana balle kuma ace ya buɗe baki yayi magana, "kirashi tareda Ahmar"

tashi tayi ta fita bayan ta amsa da tom.


a hankali take taka stair ɗin tanaji a ranta kodai wani laifi Man yayi wanda ya fusata Abba sosai? yanayinshi dama bai fiye dariya da sakin fuska ba amma yau abin yayi yawa, ta sauka lokacin da Man ya fito yayi shiri cikin riga da wando jins, Ahmar yana rike da car key da alama fita za suyi, kallon agogo tayi taga 9pm yayi, "ina zakuje?"


"Ammi zanje gidansu Ahmar na manta watch ɗina jiya"

harara ta aika mishi dan tasan wannan yana neman excuse na fita ne kawai "Abbanku na kiranku"

baiso haka ba yafison ya gudu kafin su haɗu da Abba, turo baki yayi kafin ya wuce gaba Ahmar yana biye dashi,

Jawad yana jingine da kofa bayan yaji abinda suke faɗa ya silale ya gudu, murmushi Ammi tayi dan tasan baison a kirashi ne shima.



             "Ra'eefa kinga ke karama ce har yanzu, bakisan me rayuwa take ciki ba, wannan rayuwar da kika ɗauka bazai kaiki ko ina ba sai halaka"

Hamida ke magana yayinda take tsaye tana kallon Ra'eefa wacce ta shafa powder Kamar ba gobe, dama gata fara sol, hakan yasa tayi pau sosai, Hamida tada riga da siket na atamfa ta ɗaura kanta da ɗankwali tayi kyau sosai, Ra'eefa kuma wando papulos da riga bodyhug tasa wanda ya ɗameta ya fito da surarta sosai.


kallon Hamida tayi ta ɗanja tsaki "gaskiya Unty Hamida kinada sa ido, duk time ɗin da zan fita dai kizo ki tsayamin aka, kibarni mana nima fa inada wayo nasan me nakeyi, idan tsoron kada nabi maza kike bazan bi ba, nifa kawai na fita yawo naci abu me daɗi shine damuwata amma bana biye biyen maza gaskiya"

ta karashe magana tana murguɗa baki, bata kuma yi mata magana ba kawai ta wuce ta ɗau abinda zata ɗauka kafin ta fita, a zuciya take addu'a ubangiji yasa kada Ra'eefa tayi abinda zatazo tana dana sani, badan tasan ba zatayi tsawon rai ba da ta janyota jiki kota yaya, amma tasan itada rayuwa me tsayi sai ikon Allah, duk lokacin da ta haɗu da wanda yayi sanadiyyan mutuwar Amrah wallahi saita kashe shi, kuma tasan itama dolene a kasheta, ta sadaukar da rayuwarta hakan yasa bata tsoron abinda zaije ya kuma dawo.


bubbugata Umma tayi, ganin yadda ta faɗa duniyar tunani, ɗago kai tayi tana kallon Umma da idanunta wanda suka cika da hawaye, girgiza mata kai umma tayi tana mata alama da kada tayi kuka, share wayane tayi ta ɗau taliya tana karyawa a cikin ruwan dake tafasa akan wuta, saida ya fara dahuwa ta ɗau cokali tana juyawa, rufewa tayi ya cigaba da dahuwa, saida yayi kafin ta juye tana kallon Umma wacce tayi tagumi tana kallonta, saida ta soya manja ta ajiye a gefe ta kashe wutan kafin ta mike taje gaban Umma ta zauna, kallon meya faru tayi mata, a hankali umma tayi murmushi "Hamida yaushe rabonki da kitso?"

taɓa kanta tayi tana ɗan huro iskan bakinta, dariya tayi "umma wallahi mantawa nayi"

kwanciya tayi a cinyar umma bayan ta cire ɗankwalin kanta, fara tsefe mata tayi saida ta gama ta taje tana kallon yadda gashin Hamida yake da yawa da tsantsi ga kuma baki kirin, ya kwanta a kan fatar kanta wanda yake fari sol kamar baturiya.


"Meyasa jiya kika dawo daga school da wuri?"

umma ta jefo mata tambayar, shiru tayi tunawa da yadda kadangare ya shige mata riga, bataso ta tuna wannan abin amma ya matukar tsaya mata a rai, Kabir, sunan da ya faɗo mata a rai kenan, yaron da yayi mata abinda bazata taɓa mantawa ba, cire hijabinta da kokarin zama tsirara a cikin mutane shine abinda yake cimata rai idan ta tuna, ji tayi zuciyarta yana zafi kirjinta yana bugawa, sai kuma taji sanyi a lokaci guda tunawa da yadda wannan ya taimaka mata bai bari ta kwaɓe hijabin ba, murmushin daya karawa fuskarta kyau da kwarjini tayi, a hankali ta kalli Umma tace "wallahi umma kaina ke ciwo kuma babu malamai sosai kinsan karshen sati"


"A,a Hamida banson karya, nasan bakya wasa da school amma yanzu akwai wani matsala ne, ki faɗamin idan akwai damuwa koda bazan taimaka miki da komai ba, zan taimaka miki da shawara da kuma addu'a ko?"

girgiza kai tayi kafin tace "wallahi umma na babu komai, idan akwai ai zan faɗa miki"

tashi tayi ta ɗauko mai ta shafa a kanta, hijabi tasa ta kalli umma "bari naje kitso"

"saikin dawo"

fita tayi daga gidan tana nufan gidan kitson, zuciyarta cike da tunani kamar kullum.



            "Wani labari nakeji a gidan jaridan hamony? me idanuna suke nunamin? Man? magana nake maka"

Abba ne zaune akan sofa ya haɗa giran sama dana ƙasa fuskarnan babu alaman wasa ko dariya, Man na zaune akasa ya harɗe kafarshi kanshi a kasa yana girgiza kai, Ahmar kuma ya tsaya daga waje domin Abba yace maganan bai shafeshi ba.

zufa ne ya fara ƙeto mishi wanda yasa kyakkyawar fuskarshi jikewa, a hankali yace "Abba ka yadda dani bansan da wannan labarin ba"


Kallonshi Abba yayi yana nazarin wani abu a fuskarshi, saida ya kare mishi kallo tass kafin yace "ka tabbata bakada laifi? baka taɓa zubar da ciki ba?"

girgiza kai yayi "kwarai Abba na tabbata ban taɓa yi ba, kuma bazan taɓa yiba da yaddan Allah"


"shikenan tashi kaje zan ɗau mataki akan gidan jaridan, nema suke su ɓatamin suna, dama haka mutane suke basaso suga kaci gaba ko kuma ka fisu sai su nemo hanyan ɓata maka suna, amma kada ka damu na yadda da kai man, nasan koda bana raye zaka kula da kannenka da yaran yayana wanda nafi sonshi fiye da komai, tashi kaje Allah yamaka albarka"


tashi yayi yace "ameen Abba na gode"

saida yaje bakin kofa zai fita Abba yace "dakata" cak ya tsaya hannunshi har yana rawa 

"idan na gano wani abin tashin gaskiya akan asibitinka zan iya ɗaukan mummunan mataki a kanka"

jijjiga kai yayi, kafin ya fita, saida ya ganshi a waje kafin ya sauke ajiyan zuciya me karfi, Ahmar ya gani da sauri ya faɗa jikinshi ya rungumeshi da karfi yana cigaba da sauke ajiyan zuciya, bayanshi ya buga a hankali kafin yace "lafiya?"

sai a time ɗin ya sakeshi kafin ya girgiza kai "ba komai dude muje ko?"

sauka sukayi Ahmar yana kula da yanayinshi, parking space sukaje nan suka shiga motar Ahmar, shi ya zauna a mazaunin driver domin Man yace ba zaiyi tuki ba, horn yayi me gadi ya buɗe musu kofa nan suka fita, hira suke a motar sosai, Man yace "meya kaika school ɗin su Kabir?"


"wallahi naje karɓan wani document nashi ne, kasan Dady baison yana school anan nigeria amma na rasa dalilin da yasa Kabir ya nace sai anan zaiyi"


"to indai yafi son nan ɗin ku barshi mana"

"mun barshi ma"


saida sukaje kofan Dady kafin Ahmar ya fita ya baiwa Man motar dama yace mishi akwai inda zashi, karɓa yayi yace "ka gaidamin Laila ta"

"bazan gaishar ba sai kazo da kanka"

shiga gida yayi, man yaja motar da gudu yabar layin, saida ya hau titi kafin ya ciro waya ya danna call, kira ɗaya aka ɗaga yasa a handsfree, "barka da warhaka yallaɓai"

murya a dake yace "ba wannan na kira naji ba, wanene ya shigar da labarin a gidan jaridan hamony?"


"wallahi yallaɓai ban sani ba nima nayi iya bakin kokarina domin samun meshi amma na rasa"


"idan ka samomin wanda ya shigar da labarin kanada miliyan 5"

Yana faɗan haka ya kashe wayan, hannu yasa a kwantaccen sajen fuskarshi yana shafawa, a hankali yace "Allah ya taimakeni Abba bai yadda ba, da yau nashiga uku"

lumshe ido yayi yana cewa "ai taimako nake badan haka ba da mutane dayawa sunji kunya"


bai tsaya ko ina ba sai kofan hospital nashi, saida yayi parking ya fito yana kallon ciki, da mamaki ya kalli yarinyar da take zaune a gefe ta taƙure jikinta yana ɓari har bakinta bai daina rawa ba, ga idanunta da suka firfito waje alaman tana cikin storo sosai  da mamaki ya nunata da makullin hannunshi tareda cewa "lafiya?"

jin muryanshi ta tashi a firgice rungumeshi tayi da karfi jikinta yana ɓari, kokarin cireta yake daga jikinshi amma taki yadda, domin ba karamin riko tayi mishi ba, da yaga bazata sakeshi ba ya kyaleta tana kukanta, saida tayi me isanta kafin ta fara sakin ajiyan zuciya tana lumshe ido, a hankali yaji tayi nauyi a jikinshi, dubata yayi yaga bacci ya ɗauketa, ɗagata yayi sama tana manne da jikinshi ya kaita office  ɗinshi, kwantar da ita yayi akan doguwar kujera kafin ya janyo hijabinta wanda yake da tsayi ya rufata dashi, sakamakon sanyi da ake.


kare mata kallo yayi, da alama yarinyar tana cikin tashin hankali da kuma tsoro, bakinta har rawa yake, tashi yayi zai matsa daga wurinta da sauri ta rike hannunshi cikin bacci ta janyoshi jikinta tana sakin ajiyan zuciya, da kyar ya janye jikinshi bayan bacci me nauyi ya ɗauke ta, zama yayi a kan kujaranshi yana kare mata kallo, baisan me ya sameta ba kuma yanzu, amma yasan kanin mahaifinta shine sanadi, bayan ta zubda cikin har yanzu bai daina bibiyarta ba? wannan wace irin miserable life yarinyar nan taƙeyi?





*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.