Doctor Mansoor 3
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DOCTOR MANSOOR*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 3*
~Da kyar ta iya daurewa har aka tashi, bayan sun taso ta samu wata wacce suke shiri da Amrah tana tambayarta shin da gaske kan adda Amrah ciwo yake kodai kawai ta faɗa ne? Amrah duk ƴan class ɗinsu suna so su kulla abota, batada surutu gata da hakuri ga kyau da ilimi,
yarinyan ta nuna alamu Amrah tana lafiya sannan ta kara da cewa ai tana yawan zama shiru a class yanzu, kuma bata wani karatu sai yawan tunani, daga karshe ma uncle ɗinsu yace zai bata hutun kwana biyu taje ta huta kafin ta dawo, jijjiga kai tayi jikinta har yana rawa, ta rasa meke damun yayarta da ba haka take ba, a hankali ta juya kafin ta kama hanya zuwa gida, a ranta sai addu'a take Allah yasa lafiya, tana isa gida ta tarar da Umma na girki, a hankali tace "ina Amrah ita da bazata shigo ba?"
da mamaki tace "ba ta dawo gida ba? wai kanta yana ciwo"
"tun yaushe?"
"muna isa school ta dawo ai"
da mamaki umma ta daina girkin tana kallon hamidan wacce ta tsaya tana kallon umma,
shiga ciki tayi ta sanarwa Baba abinda yake faruwa, shima ya fito yana tambayan Hamida "mamana ba tare kuka tafi ba?"
jijjiga kai tayi "eh Baba amma ancemin ta dawo ai"
fita sukayi da mama suka fara duba ta a duk inda suka san zasu sameta, sun san batada yawo batada tarin kawaye gara Hamida tana yawo, har yamma basu ganta ba, Hamida tun safe bataci komai ba har yanzu tana nan a haka babu komai a cikinta, gashi ta gaji sosai, umma tace ta koma gida ta huta ita zata duba ta saide tace a,a baza ta iya zama ba idan ta koma, haka har mangrib babu ita babu dalilinta.
saida suka koma kowa ya zauna jigum a tsakar gida, sai bayan isha tayi sallama da murya kasa-kasa, da gudu Hamida ta tashi tana kiran sunanta, ganin itace yasa tace "ina kikaje muketa nemanki adda Amrah? kin samu cikin tashin hankali, bazan iya zama babu ke ba koda na minti ɗaya ne"
jakan hannunta ta sake ya faɗi akan varanda dake shimfiɗe a ƙasa, har yanzu uniform ne a jikinta, tana lumshe ido bakinta ya bushe sosai, idonta ya shiga ciki ciki, umma ganin tayi shiru ta karaso da zafinta, babu ɓata lokaci ta rinka gaure fuskarta da mari tana tambayar ina taje?
ganin ta tsaya kamar gunki taji haushi ya daɗa kamata, muciyan da take tuƙa tuwo da shi ta ɗauko, maƙa mata ta fara a gadon baya tana huci, da kyar Hamida ta janyeta ganin yadda ran umma ya matukar ɓaci, abinda yake daɗa tunzura ta shine yadda Amrah take yin shiru tana kallonsu idan suna tambayan, sallama Baba yayi bayan ya dawo daga masallaci ganin Hamida ta janyeta yace Amrah ta zo, tana zuwa ta zauna tana kallon kasa, ɗago ki kalleni banson munafurci"
kin ɗagowa tayi cikin zafin rai ya ɗago casbin hannunshi ya watsa mata, taji zafi sosai hannu ta sa awurin tana sosawa, "tashi ki bani wuri kafin nayi miki dukan da sai an kaiki asibiti, ina kika kai hankalinki amrah? meke faruwa dake?"
a hankali ta mike, Hamida na tsaye a jikin labule ta rike gefen ta damke sosai tanajin zafin abinda yake faruwa da yayarta.
ganin Amrah ta shiga ɗaki itama ta bita, cire hijabi Amrah tayi tana zama a gefen gado, yatsunta take murzawa inda Umma ta maka mata muciya tabbas taji zafi rabon umma ta daketa har ta manta, Hamida ce take shan duka kullum amma sai gashi yau ta ɓatawa iyayenta rai har ya kai ga duka, saide zafin da yake zuciyarta yafi wannan, batayi magana ba ta zauna a gefenta, ganin tana murza hannu ta mike ta ɗibo ruwan zafi a flask cikin wani karamin roba, ɗan karamin tsumma ta ɗauko ta jiƙa, hannun ta kamo ba tareda ta kalleta ba, fara matsewa tayi, a hankali Amrah take cizan leɓe domin ba karamin zafi take ji ba, saida ta gama ta shafa rub, kallonta take amma Hamida bata ɗago kai ba, saida taga zata fita tace "kiyi hakuri"
"bakimin komai ba"
shiru kawai tayi tasan ranta ya ɓaci dajin wannan kalaman, haka har dare babu wanda ya yiwa wani magana, Amrah sai kukan zuci take, ita kuma Hamida tana lura da duk wani motsinta, saida ta kwanta akan katifa itama amrah ta kwanta, bacci suke su duka, har ɗakinsu umma sun rufe sun fara bacci.
Hamida da tunani ta kwanta ta rasa meke damun yayarta meyasa take ɓoye mata abubuwan da suka shafi rayuwarta? dama asali amrah akwai zurfin ciki, ta manta cewar ciki ɗaya suka fito?
da wannan tunani tayi bacci, kudurin ta gobe saide ayi yadda za'ayi koda ta karfi ne saita sa amrah ta faɗa mata damuwanta.
*Washe gari*
Hamida ce ta tashi sallan asuba, bubbuga Amrah tayi tana cewa "tashi kiyi salla" ganin bata ko motsa ba tace may be har yanzu fushi take da dukan umma, Baba bayan ya dawo yace kowa yayi salla? Hamida tace "adda amrah batayi ba"
"tasheta maza tayi ita da take tashin mu shine yau zata gagara tashi"
bubbugata ta kuma yi tana kiran sunanta, jin tayi shiru ta koma ta kwanta, saida gari yayi haske sosai kafin ta tashi, har yanzu Amrah na bacci, tashinta tayi shiru kakeji, abin ya fara bata tsoro, da fari tayi tsammanin bata salla ne, saide ta tuna bata period a ƴan kwanakin, fitowa cikin gida tayi kanta babu ɗankwali, gashinta a tsefe domin yau Amrah zatayi mata kitso kowani asabar haka take kamata tayi mata kitso koda bata so, Umma? umma? Umma?
"Lafiya kike kwalamin kira haka?"
"Umma adda Amrah fa bata tashi ba har yanzu ko lafiya?"
"batayi salla ba kenan?"
jijjiga kai tayi, da sauri suka koma ɗakin, umma ta fara bugunta kaɗan tana kiran sunanta, ganin bata tashi ba tace "zan ɗibo ruwan sanyi na watsa miki fa, keda kike tashin mutane salla shine yau zaki ki tashi?"
a rayuwa idan Amrah taji zasu watsa mata ruwan sanyi tashi take da sauri, saide yau shiru, hannunta umma ta ɗaga tana cewa "ki tashi" sakin hannun tayi taga ya saki, kara ɗagawa tayi ta sake, ganin hannun ya koma yasa umma ta zaro ido tana jin gabanta yana faɗuwa sosai, kallon Hamida tayi "kawo ruwa a buta"
fita tayi ta kawo ruwa, da bakin butan umma ta fara zubawa, ganin bata farka ba, Hamida ta saki ihu tafita a guje tana kiran Baba, fitowa yayi daga ɗaki yana cewa "menene?"
"Baba adda Amrah"
ta faɗa tana nuna mishi hanya, shiga ɗakin sukayi a tare, ganin sun jiƙata da ruwa bata farka ba ya matso, ɗaga hannunta yayi ya matse, jin bata motsi yace kalli umma wacce tayi shiru tana jin bugun zuciya, kallon Hamida yayi yace "bamu wuri"
fita tayi daga ɗakin jikinta a sanyaye, maida hankali yayi kan umma "Allah ya karɓi ajiyanshi"
daga bakin kofa sukaji faɗuwan mutum, Baba yana dubawa yaga Hamida ce ta faɗi da alama taji abinda ya faɗa, umma idonta ya kafe neman hawaye take ta rasa, bushewa tayi a wurin jikinta yana ɓari, bata iya ɗaga koda ɗan yatsanta ne, ganin haka Baba ya ɗaga Hamida ya kaita ɗaki, fita yayi daga gidan ya yiwa makota magana kafin suka shigo su dayawa, kan kace kobo an cika gidan da mutane, wata ce Inna tsohuwa ce suna shiri da Amrah tana cemata Mamana domin asalin sunan shine Fatima, itama sunan mamanta Fatima, shiga wankan sukayi na gawa, tana ganin gawan Amrah ta gane komai, saida aka gama wanka Baba ya watsawa Hamida ruwa ta farfaɗo, ganin mutane da yawa a kanta ta fara rarraba ido tana cewa "mafarki nake?"
Umma da take gefe tasamu hawaye yana saukowa a hankali tace "Amrah ta tafi ta barmu"
fito da gawan akayi sukace kowa yazo yayi sallama da ita, Hamida babu ɗankwali babu nutsuwa ga gashinta a tsefe ta fito kamar zararriya tana kallon mutane ɗaya bayan ɗaya tana murmushi, saida aka riketa domin tana shirin fita waje, zaunar da ita akayi a wajen gawa sukace tayi mata addu'a, hannu kawai ta haɗa yadda taga masu addu'a sunayi, babu abinda bakinta yake faɗa sai murmushi da dariya, Baba jikinshi ya fara rawa ganin abinda yake shirin faruwa da Hamidan, ɗaukan gawa sukayi zasu kaita makonci, da wani irin gudu da karfin tsiya Hamida ta rike, sai a lokacin ta fara ihu tana kuka, umma ma kuka take da kyar aka zame Hamida aka fita da makaran,
faɗuwa tayi a wajen mutane suna ta salati, umma ma ta kusa faɗuwa saida aka riketa.
a ɗaki aka kwantar da ita, batasan inda take ba, sai dariya take tana kallon mutane idan ta farka, sai kuma ta fara kuka tana baza gashin kanta, hakika ta fara zarewa, addu'o'i Baba yake mata bayan sun kai Amrah makoncinta, tofa mata addu'a yake yana bata a ruwa tana sha, da kyar aka samu ta dawo hayyacinta, bacci ne me nauyi ya ɗauke ta.
Bayan kwana uku mutane sun watse ciki harda kanin mahaifinsu da matarshi, Inna ta shigo gidan tayi sallama, amsawa sukayi duk jikinsu babu kwari, kallon Hamida tayi taga duk ta rame tayi haske sai idanunta da suka kara girma, ga kuma bakinta da yayi jaa alaman tana cikin yunwa sosai, tabarma umma ta shinfiɗa mata, zama tayi tace "ƴar nan ki rage tunani da damuwa, kiga yadda kika lalace keda kike babu rama amma duk kin zama kamar tsinken tsire?"
murmushi kawai tayi
"Ina malam?"
umma tace "yana cikin ɗaki kirjinshi ke ɗan ciwo"
"Okay may be ulcer ne, kiramin shi"
tashi tayi ta kira Baba, fitowa yayi yana yiwa Inna sannu da zuwa, zama yayi a gefenta, ta kalleshi tace "inason muyi magana amma so nake naji ta bakinka zan iya faɗa a gaban iyalanka ko na bari sai munyi gefe?"
da mamaki yace "babu komai ki faɗa Inna"
gyara zama tayi "nikam wani rashin lafiya Amrah tayi ne kafin ta mutu?"
girgiza kai yayi, shiru tayi kafin daga bisani tace "ba zakuji daɗin abinda zan faɗa ba, amma dan Allah kuyi hakuri hakan ya zama dolene domin mu kiyaye gaba"
shiru sukayi jikinsu yayi sanyi sosai.
"Mamana ta zubar da ciki kafin mutuwarta watakila hakan shine dalilin mutuwar"
zaro idanu Baba yayi "ciki?"
"Kwarai ta zubar da ciki kuma a daren ranan ne ta zubar, lokacin wankan gawa na gane hakan"
shiru umma tayi domin ta so ta fahimci hakan lokacin da Amrah ta fara canja yanayi a cikin gidan, a hankali Baba yace "a,a Inna badai ciki ba, Amrah bazata iya yin hakan ba, kowa yasan halinta tana da nutsuwa da kamun kai, da Hamida ce kika cemin haka watakila zan ɗan yi shakku amma Amrah bazan taɓa yadda da hakan ba"
kallonshi umma tayi "hakan ne ya faru domin jiyan ranan naga jini a jikin riganta saide an wanke shatin kawai na kula dashi, sannan yanayin Amrah ya canja tun daga ranan da bata dawo school da wuri ba"
jinjina kai Baba yayi kafin ya kara magana Umma ta fara kuka me cin zuciya, domin ranan da Amrah ta dawo tana dukanta batayi kuka ba kamar tana cikin damuwa, yarinya me hakuri da sanin ya kamata batayi dogon tunani ta tambaye ta damuwarta ba tayi ta dukanta.
Hamida shiru tayi dama ga damuwa a ranta gashi an kara mata wani, ji take kamar zuciyar zata fashe dan nauyi, a hankali ta mike ta shiga ɗaki, makwancin amrah ta kalla ta kife kanta jikin gadon ta fara raira kuka, hannu ta sa a pillow ta ɗaga da karfi tace "meyasa? meyasa kina cikin damuwa zaki ɓoyemin? nifa kanwar ki ce, Amrah waye ya miki wannan cikin? koma wanene nasan fyaɗe ya miki, bazaki taɓa aikata hakan da saninki ba, nayi miki kyakkyawan shaida badan ke yayata ba saidan ke ɗin kawata ce, aminiya ta, meyasa kika ɓoyemin wannan babban al'amarin har saida ya ɗau ranki kafin zan sani?"
kife kanta tayi akan pillow tana kuka, hannu ta cusa cikin zanin gadon tana yamutsawa, a hankali ta janyo wani takadda, share hawayenta tayi ta maida hankali kai tana dubawa, babban takadda ne wanda akayi rubutu akai.
zama tayi a kasa dirshan tana karewa rubutun kallo, ko shakka batayi wannan Amrah ce ta rubuta domin handwriting ɗinta ne, buɗe wa tayi a hankali tana share hawayen dake cikin idonta wanda yake hanata kallon rubutun da kyawu, ganin tayi anyi rubutu kamar haka.
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*
Leave a Comment