Doctor Mansoor 24

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    Na

_Jiddah S Mapi_*Chapter 24*                 ~Suman zaune yayi sai kallonta yake kamar zai maida idonshi kanta, dariya tayi sosai tace "yanzu baka da gida baka da aiki gashi baka da Jahad, kowa baya sonka kuma baka da mutunci"


riko hannun Jalal tayi "muje Baby"

tafiya suka fara a bakin kofa ta tsaya ta ciro zoben dake hannunta ta juyo, takawa ta fara har zuwa gabanshi ta wurga mishi zoben a fuska "ga wannan mushen zoben naka banso, Jahan ɗina tafimin komai a rayuwa, na tsaneka Man na tsani ganin fuskarka, a duk lokacin da nake tare da kai ji nake kamar na kasheka na huta, idan ka taɓa ni zafi nake ji kamar an samin wuta a kirjina, wukan hannunta ta riko ta kamo hannunshi ta zana J a jiki, ko runtse ido baiyi ba, dan zafin da yake ji a hannu bai kai na zuciya ba, saida ta gama zana J sannan tace "banso ka manta ni da wuri, so nake koda yaushe kaga wannan harafin ka tuna da Jahad da Jahan wacce kayi sanadin rayuwarta, ko yanzu zanyi bacci cikin jin daɗi dan na ganka cikin masifa, mugu azzalumi jarirai basu fara damunka a bacci ba sai zuwa gaba, sannan kawu Bala ba kanin mahaifina bane, shine mutumin daya taimaka min lokacin dana rasa iyaye, ya bani duk wani kulawa da uba ya kamata ya baiwa ƴarshi, kuma ina alfahari dashi, na barka lafiya Dr Mansoor"


tare suka fita hannunsu rike dana juna itada Jalal, mota me lafiya suka hau suka bar unguwan ba tareda kowa ya sani ba.


yana kallonsu har suka fita a hankali yace "Jahad? Jahad"

gani yake kamar mafarki yakeyi, so yake ya tashi daga wannan baccin, Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, da ihu yace "Jahaaaaaaad"


Ammi dake bacci a cikin ɗaki taji kamar ihu, kasa kunne tayi domin jiyo kode kunnenta ne? da karfi ya kuma cewa "Jahaaaaaaad"

a firgice ta fito daga ɗaki ta fara tafiya, time ɗin Hamida ma ta fito dan itama taji ihun, ganin Ammi tayi sauri ta gyara lifayan jikinta, a tare suka tsaya bakin kofa kowa yana tsoron buɗewa domin tsakanin mata da miji basu san meke faruwa ba, tura kofan Ammi tayi jin ya kuma kiran sunan Jahad da karfi, Hamida ma ta bi bayan Ammi, ganinshi ɗaure a jikin gado suka karasa da gudu, Ammi ta fara kwnaceshi Hamida tana taya ta, saida suka kwanceshi Ammi ta fara tambayar "meya faru Man?"

da karfi ya rungumeta jikinshi yana ɓari, gabanata ne ya faɗi, tasa hannu a bayanshi "Man meya faru?"

kankameta yayi da karfi, baiyi magana ba sai kara kankameta yake, ba karamin tsorata tayi ba, domin bai taɓa razana irin na yau ba.


"Ina Jahad?"

jin ta kira sunan Jahad ya kara riketa da karfi, kuka Ammi ta fara tana cewa "meya faru? kada zuciyata ta buga Man ku kaɗai kuka ragemin, kaine karfin gwiwa ta dan Allah ka faɗa min meya faru"


"Ammi ki lulluɓani sanyi nakeji"

jikinshi har ɓari yake, tareda hakoranshi suna haɗuwa tsabar rawan ɗari, blanket ta janyo ta rufashi dashi, har yanzu yaki sakinta, kuka take tana tofa mishi addu'a cikin kunne, a hankali ya fara samun nutsuwa jikinshi ya daina ɓari, kwantar dashi tayi akan pillow ta karo blanket ya zama guda uku ta rufashi, zama tayi a gefenshi hannunta a kanshi tana shafa suman dake kwance lub, runtse ido yayi hannunshi rike da ƙafan Ammi baison ta matsa a kusa dashi.


"ki duba mana Jahad Kaka"

gida kai Hamida tayi, wacce ta tsorata da ganin yanayin Man, duba Jahad ta fara a cikin ɗakin bata ganta ba, har toilet ta leka babu Jahad, dawowa tayi "hajiya babu ita fa"

da mamaki Ammi tace "mu duba ta kasa"

fita sukayi daga ɗakin suna dube-dube, bata nan, da sauri suka nufi ɗakin Jalal, abin mamaki suna buɗewa babu shi babu dalilinshi, cikin tashin hankali Ammi ta kalli Hamida "Mama babu su fa meke faruwa?"

Hamida taji duk abinda ya faru so take Man ya yiwa Ammi bayani da kanshi, tana ganinsu Jahad har suka gudu ta kyalesu ne saboda maganar da Jahad tayi na cewar Man shine ya kashe mata yar uwa, abinda ya faru da ita ta tuna hakan yasa ta bar Jahad ta gudu, itama tasan zafin rabuwa da ƴar uwa, taji zafi akan Amrah kuma taji zafi akan Ra'eefa, hakika Man ya cancanci wannan hukuncin, koba komai itama taji daɗi a ranta.Su Jawad ne suka fito suna tambayar meya faru? baya Ammi tayi musu bayani da gudu Ahmar ya shiga ɗakin yana duba man, kwance yake ya rungume Pillow cikin bacci sai zufa yake sosai, shafa goshinshi yayi "Dude meya sameka?"

Tashin hankali kowace rana sai mun ganshi a wannan gidan? me mukayi?

Ahmar yayi magana yana dafe kai.


haka suka kwana ido biyu babu wanda ya runtsa cikinsu.


*Asuba ta gari*


Bayan kowa ya idar da sallah shiru suka zauna suna jiran Man ya tashi, a plaour suke zaune kowa yayi tagumi, a hankali ya fara taka matattakalar yana saukowa, wando daidai gwiwa da riga armless ne a jikinshi, har jiri yake ji kamar zai faɗi, da gudu Ahmar ya rikeshi tareda cewa "easy"

saida ya sauka ya zauna ya kalli Ahmar "cikin 5hrs nakeso mu nemo Kabir"

da mamaki kowa yake kallonshi "Kabir kuma? meyasa kace haka?"


"Jahad ce ta saceshi kuma tace cikin 5hrs idan bamu nemoshi bazai mutu"

tashi sukayi a tare "yana ina?"


"Ban sani ba, Ammi Jahad ta cuceni, itace ta kashe Shaira da Sabir, Ammi ki taimaka min kada Kabir ya mutu ta dalilina, ta kashesu ta dalilina ne Ammi"


girgiza shi Ahmar yayi cikin kiɗima yace "ina Kabir yake?"


"ban sani ba mu nemoshi"

fita sukayi su gaba ɗaya suka fara tafiya, kowa yana addu'a cikin ranshi Allah ya bayyana Kabir, Ammi ta kalli Hamida cikin tausayi tace "ki koma gida kaka wannan tafiyan ba naki bane"


"a,a tare zamu je, bazan iya zama ba"


Man da kyar yake tafiya amma dolene su nemo Kabir, ko wani kango sai sun leka duk wani inda basu yadda dashi ba lekawa suke, tun basu gaji ba har suka fara gajiya.


saida suka gaji sosai kafin suka juya zuwa gida ba karamin gajiya sukayi ba, komawa gida sukayi jiki a mace kowa ya zauna jigum-jigum, saida suka ɗan huta, suka kiyo karan tafiya daga kan up, a tare suka ɗago suna kallon inda sautin tafiyan ke tashi, da gudu man ya haura sama yana cewa "Kabir?"

faɗuwa Kabir yayi a jikinshi yana haki, jikinshi duk jini ga kafarshi da kyar yake takawa, ɗagashi yayi sama ya sauko kasa dashi, kwantar dashi yayi akan Sofa yace "Kabir ka buɗe ido"


a hankali ya buɗe baki yace "Jahad....Jahad.."


"me tayi maka?"


"Itace take so ta kasheni, bansan me nayi mata ba"


cikin damuwa Man ya riko fuskarshi yana cewa "ka yafemin ta dalilina hakan ya faru....."

tureshi Ahmar yayi yana aika mishi mugun kallo, nunashi yayi da yatsa "stay away from my brother"


"Ahmar ka san me kake faɗa?"


"Na sani kada ka sake ka taɓa min Kani, da wannan ƙazamin hannun naka"


ɗaga Kabir yayi ya wuce ɗakinshi dashi, fara treatment nashi yayi, Man yana kallonsu har suka wuce, su Ammi suka bi bayanshi dasu Noor da Jawad, ya rage daga shi sai Hamida, satan kallonshi tayi "hakan yayi daidai"
*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.