Doctor Mansoor 2

*Chapter 2*



         


       ~Yanka kayan miyan take tana kuka, zuciyarta yana suya, hawaye ya cika idon nata bata ganin komai, yanka hannunta tayi tsabar zafin zuciya bataji zafin hannunta ba, saida Umma ta gani tace "Innalillahi Hamida kin yanka hannunki"

kallon hannun tayi taga yana zub da jini sosai, a ranta tace "gara wannan zafin da wanda nakeji a raina Umma"

kamo hannun tayi ta fara wanke mata, daga nan ta karɓi yanka kayan miyan, ita kuma Hamida ta zauna daga gefe tana kallon Umma, turo kofan akayi da sauri ta janyo hijabin tasa, jikinta yana rawa ta mike taje gabanshi ta karɓi ledan dake hannunshi, wani mutum ne baki yana da kiɓa fuskarshi babu annuri ko kaɗan, ajiye ledan tayi a gaban Umma jiki na rawa ta ɗibo ruwa a buta ta kai mishi, karɓa yayi, ya shiga banɗaki, saida ya jima sosai kafin ya fito, Hamida na zaune ta taƙure cikin hijabin tana kallon ƙasa, gyaran murya yayi da sauri ta mike taje ta amshi butan hannunshi, ajiye tayi a gefe ta ɗau tabarma ta shimfiɗa mishi, saida ya zauna ta kawo ruwa a Cup na silver ta ajiye, komawa wani ɗan karamin ɗaki da yake dab bakin kofa ta shiga, katifa shimfiɗe a ƙasa babu wani faɗi ko tsayi a tare da katifan, yadda kasan tabarma haka yake, zama tayi bayan ta saki labulen dake kofan ta taƙure wuri guda, jikinta ne ya fara zufa domin ba karamin zafi ake ba, hakan baisa ta cire hijabin ba, sai zufa take har fuskarta, kara dukunkunewa tayi tana kallon cikin gidan ta cikin labulen ɗakin, tasan idan ta cire hijabin nan yana kiranta ta ɓata lokaci saita gane kuskuren ta, tana cikin tunanin ta jiyo muryanshi yana kiran sunanta, da sauri ta fita taje gabanshi ta durkusa.


fuskarnan ba dariya yace "keda suwaye kuka tsaya a titi ɗazu kina ɗaga murya?"

baki na ɓari cikin siririn muryanta tace "wallahi ban ɗaga murya ba, sune sukayi kamar zasu bigeni saida na faɗi, nace Allah ya isa"


a fusace ya fara magana "zakice Allah ya isa kinsan su ɗin su waye ne? to shi wannan Kabir ɗin mahaifinshi yana neman takaran kujeran governor akan wani dalili zaki jawo min matsala? idan kikaje school gobe ki durkusa har kasa ki basu hakuri idan ba haka ba wallahi saina koreki keda uwarki kuje can ku nemawa kanku masifa badai ni ba, kin taɓa ganin Ra'eefa ta kawomin matsala a cikin gida? ko kin taɓa jin Samha tana faɗa da maza? ki kiyayeni fa, zan saɓa miki wallahi"


shiru tayi kanta a kasa saida ya gama kafin tayi godiya ta mike, Umma na zaune a wurin da take har yanzu, ta gama miya jikinta har rawa yake idan taji ana yiwa Hamida faɗa, saida taga ya gama kafin taje ta dire abincin a gabanshi, ranta ya ɓaci sosai, meyasa bazai ji ta bakinta ba? sai ya hau yimata faɗa?"


harara ya aika mata "to to an yiwa gimbiya faɗa dole ranki ya ɓaci ko? to bari jiki bazan zuba ido yarinya tana aikata abinda taga dama a gari inyi shiru ba, wannan sheɗaniyar bakisan ta'asar da take tabkawa bane shiyasa, kina ganin wannan kyawun nata shine yake jan hankalinta"

shiru kawai tayi mishi ta shiga ɗakinta, itama kuka ta fara tana tausayin ƴarta, kwata-kwata rayuwa baya yimata daɗi, yarinya ta taso cikin taƙura da musugunawa bata da sakat, ko motsin kirki bata yi a gidannan sai sun zageta, me tayi musu?

saida taci kukanta kafin ta godewa Allah tare da nemawa ƴarta sauki a wajen Allah.


tana shiga ɗaki ta haɗa kai da gwiwa ta fara kuka, hakika ba'a sabo da wahala ne da zatace ta saba, ɗago kanta tayi idonta har ya koma jaa sosai, fuskar kamar ta shafa jan hoda, murza idon tayi bayan ta sauke nannauyan ajiyan zuciya, tuna yadda zatayi ta basu hakuri gobe take, yaran basu da kunya sam, amma zatayi kokarin yin hakan.


*Washe gari*


tunda tayi sallan asuba take aikin girki saida ta gama breakfast ta girka ruwan wankansu Samha da Ra'eefa ta juye a flask bayan ya tafasa, ruwanta ta girka yana yin zafi ta  juye a roba me faɗi, ɗagawa tayi ta kai toilet, omo da soso ta fara goga jikinta dashi, saida ta gama kafin ta ɗaura zani a kirji tasa dogon hijabi ta fito, hannunta rike da soson, ɗakinta ta shiga ta shafa mai, kayanta me ɗan kyau tasa, material ne pink da zanen baƙi a jiki, hijabinta ta ciro baki tasa, takalminta da ta ɓoyeshi domin zuwa school shima ta ciro tasa, jakanta ta rataya daga gefe kafin ta fito ko cin abincin batayi ba, bataso tayi laiti koda na rana ɗaya ne.


lokacin yake dawowa daga masallaci, har kasa ta durkusa tana gaisheshi, amsa yayi a dake kafin ya nunata da casbi "idan naji baki bawa yaran nan hakuri ba saina karya ki"

jijjiga kai tayi, saida ya wuce kafin ta mike ta saki kafa, tasan Umma ta koma bacci shiyasa batayi mata sallama ba, su Samha kuma ko tashin sallan asuba basuyi ba balle su wani koma, koda ta ishesu da tashi ma tsawa sukayi mata kamar bata girmesu ba.


tafiya take domin da kafa zataje kuma da kafa zata dawo, saida ta huta a hanya domin ta gaji, kafin ta iso kofan school nasu, international university, inda take karanta low, so take ta zama lowyer me zaman kanta, tafiya take cikin sauri tana kallon kasa hannunta akan jakanta kamar yadda ta saba.


zagayeta aka fara da keke kamar zai bugeta, yi tayi kamar bata ganshi ba, ganin ta shareshi taci gaba da tafiyanta yasa yabi bayanta saida ya ɗan buge kafarta "wash" ta faɗa tana rike kafa, hakika taji zafin bugeta da yayi, ajiye jakan tayi tana danna kafar domin har yayi jaa sosai, sauka yayi daga kan keken yana shu'umin murmushi yace "sorry innocent beb meyasa har yanzu ba zakiyi magana ba"


a hankali ta ɗago manyan idanunta wanda suka cika da hawaye tace "kayi hakuri"

tunawa da gargaɗin Baba, dariya yayi harda rike ciki, a girma bazai wuce 26years ba, domin yaro ne matashi, yana da kyau sosai gashi jikinshi na hutu ne sosai, saide shi ɗin chocolate color ne, kalanshi me kyau ne, shafa gemunshi ya fara yana murmushi cikin mugunta ya matso da bakinshi dab kunnenta yace "ba anan zaki bani hakuri ba"


tashi yayi yabar wurin, itama ta mike ta ɗau jakanta, ɗingishi take har ta isa class, ajiye jakanta tayi akan desk kafin ta zagaya ta zauna a kujeran book ta ciro ta fara rubuta assignment da aka basu jiya, aiki ya mata yawa shiyasa batayi ba, saida ta gama rubuta assignment kafin mutane suka fara taruwa, dama sun sani itace ake samu a class ko mai za'ayi bata taɓa zuwa laiti, domin tana da buri a rayuwarta, malamin ya shigo suka fara lectures, yau kam da sauki da shike jumma'a ne zasu tashi da wuri, sauri tayi ta fita bayan ta gaisu da frends ɗinta, tafiya take cikin sauri domin yunwa yana azalzalar cikinta, suna zaune akan wani dakali wanda yake da tsayi a school ɗin, shi Kabir ya haɗa kafa ya ɗaura ɗaya akan ɗaya, abokanshi su uku suna daga gefe suna tayashi hira, sai dariya suke duk wanda yazo wucewa sai sun tsokaneshi, sunkuyar da kai tayi zata wuce da karfi yace "ke?"

bata amsa ba kuma bata juyo ba, da sauri ya dira akan dakalin yaje wajenta, ta bayanta ya janyo gefen hijabinta, da karfi ta kwace tana nuna shi da yatsa domin ranta ya ɓaci sosai, yau yana nema ya kaita bango duk da tsoro amma zata daƙe, dariya suka kwashe dashi da abokansa, sharesu tayi taci gaba da tafiya idonta yana cika da hawaye, a gida ba'a barta ba haka ma a school ba za'a barta ba? 

fashewa tayi da wani ɗan marayan kuka ta rasa wani irin baƙin jini ne da ita, wanda yasa basa sonta, wannan yaron ya kulla mata yana cutar da ita, ba dan karatun zai zame mata gata zuwa nan gaba ba wallahi da saita bar school ɗin, saide ruhin mahaifinta da kanwarta yafi mata wannan zalunci da suke mata.


Saida yaga tana kuka kafin ya koma, Kabir ɗane ga me neman takaran governor yaro ne ɗan masu kuɗi wanda aka shagwaɓa da kuɗi, anso yayi karatu a kasar Canada amma yaki yadda saboda waɗannan abokan nashi, su ba yaran kowa bane saide rayuwa dashi yasa yana basu kuɗaɗen kashewa idan ka gansu zakace yaran masu kuɗi ne, ya shagwaɓa yaran ya maidasu kamar kannenshi wanda suka fito ciki ɗaya, muhseen, Umar, Khalid, Khalifa sune abokan nashi duk inda zaka ganshi to suna biye dashi suna shashanci, babu wacce suka kullawa a school ɗin kamar Hamida, Kabir ya tsaneta ba kaɗan ba, hakan yasa koda bayida niyan zuwa school sai yazo domin ya sata kuka yaci mata mutunci.


Tana hakuri da su ko mai zasuyi mata bata tankawa, hakan yasa suke cigaba dayi mata hakan, ta kai kara wa shugaban makaranta bai ɗau mataki ba, bataso tayi loosing school shiyasa ta share bata kuma kai karan ba.



*Hamida Umar Arɗo*


shine asalin sunanta, mahaifinta Umar arɗo bafulanin Gombe ne, na asali, matarshi A'isha ya aureta ne domin itace ƴar mai unguwar garinsu, Allah ya azurta su da yara guda biyu sune Amrah da kanwarta Hamida, Amrah tana da nutsuwa sosai batada kauɗi gata da bawa manya daraja, saɓanin Hamida wacce batada hakuri ga tsokana, Yana da kani Malam Ibrahim shima yana da mata amma Allah bai basu haihuwa ba, Amrah ta taso cikin kula da nutsuwa itada kanwarta, sun shaƙu sosai komai tare suke domin Hamida tana da saurin kafa, suna Secondary school wani government ne wanda Baba yayi kokari ya sasu, Amrah tana da ilimi sosai domin itace take zuwa ta ɗaya ko ta biyu a class nasu, itace take yiwa Hamida assignment a duk lokacin da aka basu.


shaƙuwa me tsanani shine a tsakaninsu basu da kawa ko aboki su biyu suke rayuwarsu, a iya sanin Hamida basu da abokin gaba, saide Amrah tana soyayya da wani wanda suke waya kullum, idan tace zata haɗashi da kanwarta su gaisa sai yace ba yau ba, haka dai har Hamida ta fara masifa domin bata son wannan wanda suke wayan wallahi haka kawai ta tsaneshi, abin mamaki shine ya fara janye Amrah daga jikinta, mahaifinsu ya fahimci hakan ita kuma taki yadda ta rabu dashi, Hamida taso sanin wanene domin maza huɗu ta sani suna son Amrah.


Wata rana Amrah ta taso daga school sun saba komawa gida tare sai kuma ta tafi ta bar Hamida, abin ya ɓatawa Hamida rai domin ta dubata cikin school ɗin bata ganta ba, bayan ta tambaya akace ai sun tsaya da wani yaro akan mashin besper, irin mashin me kyau ɗinnan baki, saide yaron da facemask a fuskarshi babu wanda yaga fuskan, komawa gida tayi ranta a  ɓace ta sanar wa Umma, tasan halin yayarta bata bin maza tana da kamun kai da nutsuwa, aiko bayan Amrah ta dawo umma ta kamata ta jibga domin ta kai kusan mangrib hankalinsu gaba ɗaya ya tashi, duk dukan da ake mata batayi kuka ba, saida ta koma ɗaki Hamida ma ta shiga tana cin magani batason yi mata magana, saide abinda ya karya mata zuciya shine yadda Amrah ta haɗa kai da gwiwa tana kuka sosai, bataso asan kuka take hakan yasa take toshe baki, ɗan taɓa ta tayi tace "Lafiya?"


Ɗago kai tayi idanunta wanda sukafi na Hamidan girma da kyau yayi red sosai, bakinta da yake ɗan karami har yafara jini tsabar tauna, fuskarnan yayi jaa, domin Amrah tafi Hamida fari da kyau nesa ba kusa ba, a hankali ta mike ta rungume ta, ji tayi jikinta yayi sanyi, ta san ba kukan dukan take ba, tambaya ta fara "meya faru adda Amrah?"


Kasa magana tayi saida ta bubbuga bayanta tana rarrashi kafin ta iya buɗe baki tace "ku yafeni?"

jikinta ya kuma yin sanyi tace "menene ki faɗa min dan Allah"

kuka taci gaba dayi tareda cewa "ba komai"


tun daga ranan Hamida bata kara ganin fara'a a fuskar Amrah ba, tayi iya bakin kokarinta dan ganin ta samu amsa amma ta rasa, tayi tambayar duniya Amrah taki bata amsa, Umma tayi iya bakin kokari a matsayin ta na uwa domin sanin damuwar Amrah amma bata gano amsa ba.


haka sukaci gaba da zuwa school, rayuwarsu ta canja ba kamar da ba, da suke tafiya suna hira, wani lokacin Amrah tayi ta tsokanarta, yanzu kam shiru suke koda tayi maganan saide tayi murmushi kawai, abin yana damun Hamida amma babu yadda ta iya, akwai ranan data tadda Amrah tana kuka acikin toilet, har kuka saida tayi mata domin sanin damuwarta haka fafur taki faɗa sai kuka.


wata rana da safiya sun shirya zasu school Baba ya kirasu yayi musu nasiha akan rayuwa, saida ya gama yace subi duniya a hankali, tashi sukayi bayan nasihan ya shiga jikinsu sosai, suna tafiya har suka isa school, da ke lokacin break Hamida ta kai mata abinci saide akace mata ai tunda suka zo ta shiga class Amrah tace kanta na ciwo ta tafi gida, abin ya bata mamaki domin babu wani ciwon kai a tare da ita, da kyar ta daure har aka tashi.




*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.