Doctor Mansoor 18


 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸    Na

_Jiddah S Mapi_

*Chapter 18*

                ~A rikice ta fita daga ɗakin, a inda ta barsu anan ta gansu, nutsuwa tayi tace "na kaishi Ammi"

da sauri Man yazo wajenta yace "bai miki komai ba?"

girgiza kai tayi "babu abinda yamin"

Ahmar yace "yanzu ya zamuyi dashi? ko dai koranshi zamuyi idan ya huta?"


Man yace "dole ma ya tafi taya zamu rike mahaikaci bamu san daga ina ya fito ba?"

"zamu rikeshi domin ya bani tausayi kasan mahaukaci shi yake zaɓan inda zai zauna, to wannan ma haka ne idan yaga dama gobe zai tafi idan kuma nan yayi mishi mu kyaleshi taimako ne"

ba dan sun so ba kowa yayi shiru, Jahad da jikinta bai saketa ba tace "bari naje na kara girka wani breakfast ɗin"

"ki bari ƴan aiki za suyi"


kin bari tayi saida taje kitchen ɗin ta fara shirin girki, hankalinta a tashe yake tasan halin Jalal kamar yunwar cikinta, zai iya tabka kuskuren da kowa saiya fahimci halinda ake ciki, gashi da bakin kishi ta tabbata har kisa zai iya yi, ji tayi an rungumeta ta baya, baki ta buɗe cikin tsoro domin tasan Jalal ne yake mata irin wannan rungumar da karfi haka "J..." 

kunnenta yayi magana "sunanki zaki kira?"

gabanta ne ya faɗi jin muryan Man, tabbas da ta tafka kuskure, zuwan Jalal gidannan zai jawo mata matsala, tana aikinta cikin kwanciyar hankali gashi ya ɓullo yana shirin tona musu asiri, murmushin yaƙe tayi, ta shafa hanunshi cikin sanyin murya tace "inason cewa jarkan mai ya faɗi"

kara matseta yayi a jikinshi yace "ohh me zaki dafa mana?"

"me kake so?"


"abinda kike so shi nake so"

juyo da ita yayi yana kallon cikin idonta, tun zuwan wannan mahaukacin ta tsorata sosai, yana ganin idonta yasan tana cikin tsoro, janyota yayi jikinshi yace "ki daina tsoro zai bar gidannan very soon kinji?"

jijjiga kai tayi, matso da ita yayi yace "kiss me"

kawar da kanta tayi, cikin fushi yace "bakya sona ne Jahad?"

"Ina sonka"


"to meyasa kike gujemin haka?"


matso da fuskarta ta fara saita tazo dab da nashi kafin tasa bakinta a nashi tana bashi kiss me zafi, karan faɗuwan glass sukaji da sauri ta sakeshi tana kallon kofa, jikinshi yana rawa ya taka glass ɗin yana kallon su, da sauri Man yaje wurinshi yana ɗaga kafarshi wanda ya fara jini, kwace kafar yayi, ganin Man ya zuba mishi ido ya kwashe da dariya, Jahad a gefe ta tsaya tana murza yatsunta, ita kaɗai tasan halin Jalal, Man ya kalleta yace "zo mu taimaka mishi yaji ciwo"

a hankali ta karaso, kafar ta ɗaga da karfi ya bugeta, baya-baya tayi ta faɗi gefe, saida kafarta ya bugu da jikin gini kafin Man ya ɗagata, fita Jalal yayi yana dariyanshi sosai, tasan kishi ne yasa yayi mata hakan "nashiga uku"

ɗagata yayi suka fita daga kitchen yana cewa "sannu Baby, zai tafi soon"

runtse ido tayi, idan yana cewa zai tafi haushi yake bata, baisan waye Jalal ba.



*Prison*


Hamida ta goge bata bari kowa ya shiga hakkinta bata yadda aci mata mutunci kamar da, rama da ɓacin jiki duk tayi shi, kwalba take fasawa ta ajiye a gefenta duk wanda yayi mata ba daidai ba nuna mishi take tace zata yanka shi, haka yasa suka fara shakkunta musamman wannan ƙatuwar matar, yanzu ta samu sarari bata shan wuya kamar baya, burinta shine ta samu hanyan gudu a wanan cell ɗin, so take ta ganta free taje ta ɗau fansar abinda akayi mata, a koda yaushe idan ta tuna wannan sharrin ba karamin kuka take ba, har kanta yana ciwo tsabar wahala da tashin hankali, a shekarunta 20 ake mata wannan sharrin basu duba ƙanƙantar ta ba, basu duba rashin wayewanta ba, Man yace itace ta sace Kabir, ga kuma sharrin kisa wanda basu da tabbacin itace tayi, dan mahaifinta ya mutu shine zasu wulakanta ta?.


kowane Asabar ana fitar dasu suyi aiki a cikin prison ɗin, wani lokacin hadda wanki da noma, sun kullawa Hamida domin bata basu haɗin kai a duk wani abu mummuna da zasuyi, blue ɗin riga dogo irin na ƴan prison shine a jikinta, wanki take tana tunanin abin duniya, ji tayi an watsa mata ruwa, tana ɗagowa taga matar da suke yawan faɗa ce, bata kulata ba taci gaba da aikinta, kara watsa mata ruwan tayi, cikin zafin rai Hamida ta nunata da yatsa tace "idan kika kara watsamin ruwa zan rama, ina baki daraja a matsayinki na wacce ta gurmeni kada ki yadda raina ya ɓaci"

tureta tayi tareda bugun kirjinta "me kika isa kiyi?"

ran Hamida ya idan yayi dubu to ya ɓaci yau, mari ta ɗauke matar dashi, nan ta fara kawo mata duka Hamida tana kaucewa, wasu mata da jikinsu ya haɗu da Hamida sune sukazo wurin suna gargaɗan matan data kyale yarinyar, nan ta juyo kansu suka fara dambe a su duka, rasa abinyi Hamida tayi, ganin wasu daga gefe sun shiga faɗan yasa taje tana janye wanda suka shigan mata, nan take gidan ya kaure da dambe, ma'aikatan suka zo da gudu suna rabasu, matar ta cire bindiga daga jikin ɗayan ta harba sama, gudu suka fara kowa yana neman hanya, Hamida ji tayi an riko hannunta, a tare suka fara gudu, batasan wace ba kawai de tana binta, ta katanga suka haura, basu kaɗai ba dayawa daga cikinsu sun gudu, da kyar ta diro daga saman ginin da yake da mugun tsayi, kafarta ce tayi kara rikewa tayi ta saki wani ihu na azaba, hannunta matar wacce ba zata wuce 30years ba ta riko "ki daure ki tashi dan Allah kada su zo"

jan kafar tayi tana jin wani raɗaɗin azaba, da ɗingishi ta fara gudu tana kuka domin ba karamin zafi take ji ba, saida sukayi nisa da prison kafin matar ta zaunar da ita a kan wani dutse tace "bari na duba miki kafar"

duba mata tayi babu abinda zata iya akai domin gurɗiya ne, cikin tausayi tace "zaki iya daurewa mu tafi a haka? zuwa bakin titi"


jijjiga kai tayi "zan iya Unty"

riko hannunta tayi suka fara tafiya a hankali, bakin titi suka isa da hannu ta tari ne taxi, yana tsayawa tace "bypass"

shiga sukayi yana kallonsu ta cikin madubi, ta lura da hakan, muryanta da tausayi tace "dan Allah ka taimaka kada ka faɗawa kowa kaji?"

"toh insha Allah bazan faɗawa kowa ba" ya lura da uniform ɗin, Hamida sai cije baki take domin kafarta yana zugi, sannu kawai matar take ce mata, saide ta girgiza kai kawai.


bypass ya kaisu, acikin aljihu ta ciro kuɗi ta mika mishi, kin karɓa yayi domin ya tausaya musu, kana ganinsu kasan suna cikin tashin hankali, godiya suka mishi, tafiya suka fara dan sunada nisa da inda ya ajiyesu, bata barshi ya kaisu har kofan gida ba saboda mutane ba abin yadda bane, kada ya sanarwa police suzo su kamasu "daure Hamida mun kusa isowa gida"


wani katafaren gida me kyaun gaske Hamida taga sun tsaya a kofan, makulli taciro ta buɗe, shiga tayi Hamida na biye da ita, hawaye take sharewa tunda ta shigo gidan tana karewa ko ina kallo, kallonta kawai take ba tareda ta tambayeta meyasa take kuka ba, babban palour me ɗauke da kayan more rayuwa suka shiga, anan kukanta ya karu, jikin tv taje wanda ya ɗan tsage, tana shafawa tana sharan kwalla, shiru Hamida tayi jikinta yayi sanyi sosai, da alama matar tana tuna baya ne, cikin dauriya ta kalli Hamida "muje ciki mu haɗamin kayana yau zamu tafi Abuja"

jijjiga kai tayi, taka matattakala sukayi har suka isa wani ɗaki a sama, kayanta ta fara haɗawa tana mikawa Hamida ita kuma tana sawa cikin akwati, saida suka shirya komai ta dau wani hoto wanda yake manne a jikin bango, bugawa tayi da kasa nan ya tarwatse, ya rage hoton ne kawai a kwance kasa, hannu yasa ta yayyaga ta watsar, tana kuka take yin hakan, sai kallonta Hamida take har yanzu batace kala ba, ko wanka basuyi ba suka canja kaya, Hamida dogon rigan material me tsada tasa, sai wani mayafinshi baki, da ratsin baki a jikin material ɗin, jaka babba wanda ta cika musu da lemon kwalba dasu yoghourt da snacks wanda zasuyi amfani dashi a hanya, Hamida ta rataya babban jakan a bayanta matar kuma ta ɗau akwati da jaka wanda ta zuba kuɗi a ciki, ga kuma Atm nata, fita sukayi daga gidan Hamida sai ɗingishi take, sannu take faɗa mata har ta rufe kofar, facemask tasa tareda bawa Hamida itama tasa facemask, saboda tsaro, kallon gidan matar tayi bayan ta rufe, a hankali tasa hannu tana share hawayen da suke sauka a fuskarta, sai yanzu Hamida tace "Unty kiyi hakuri"

kallonta tayi idanunta har yayi jajur "Hamida kuka ya zama dole"


"ki barwa Allah komai"


"Tom shikenan, amma sunana Maryam"


"Tom Unty maryam" tafiya suka fara a taxi suka isa tasha, Hamida sai tunanin Umma take, ko a wani hali take? Allah ne kaɗai ya sani, batayi kuka ba saida motarsu ta tashi zuwa Abuja, ba karamin kuka tayi ba saida Unty Maryam ta lallasheta sosai tareda kwantar da ita a jikinta, bacci ne ya ɗauke ta, haka kawai takejin yarinyar a zuciyarta, tun a prison bata son abinda zai taɓa ta, sunyi nisa sosai kusan rabi kafin ta farka tana murza ido, kallon Unty maryam tayi "bamu iso ba?"


murmushi tayi "bamu isa ba, amma mun kusa"

"gidan waye zamuje ne Unty maryam?"


"gidan mahaifina"

ji tayi hankalinta ya kwanta yanzu, dama tambayar yana cikin zuciyarta, Allah yasa su karɓe ta idan sunje Ameen.


tsakar dare suka isa garin Abuja, wani taxi suka kama ta faɗa mishi sunan unguwa kafin suka shiga, nan suka kara cigaba da tafiya, sunci snack da yoghourt shiyasa basa jin yunwa, ga kuma ruwa da hamida take aikin sha tun ɗazu, wani silent area suka shiga, manyan gini ne a wurin bana wasa ba, ko ina da haske kamar rana, a kofar wani katafaren gida suka tsaya kallonta tayi tace "muje mun iso"

a tsorace ta fito daga motar domin gidan ya fara bata tsoro, tun daga waje girma ne dashi sosai ga kuma kyau, biyan driver tayi sannan ta ɗaga akwatin, Hamida ta ɗau jaka tana rarraba idanu, har yanzu bata daina dingisa kafa ba, knocking tayi, getman yace "waye?"

a hankali tace "Maryam ce" da sauri ya buɗe jin muryan Maryam ɗin da gaske, kallonta yayi sama da kasa yaga ta rame sosai sai hasken da tayi "Maryam kece wannan?"

jijjiga kai tayi hawaye yana taruwa a idonta "bismilla ku shigo"

banda ido babu abinda Hamida takeyi sai kallon ko ina take, gaba ɗaya ta zama ƴar kauye, gidansu Man me kyau ne amma wannan yafi nasu sau goma, murmushi Maryam tayi mata "nan ne gidan mahaifina, bismilla"

jan kafarta take tana addu'a, ciki suka shiga, ashe daga waje ba komai bane saida ta shiga ciki, haɗaɗɗen palour suka tarar "Momy!!! Momy"


Maryam ta fara kiran Momynta, wata matace fara sosai me kama da Maryam ɗin ta fito daga ɗaki, rigan bacci ne a jikinta fuskarta ɗauke da siririn glass, zata wuce shekara hamsin, ta sani mafarki take kamar yadda ta saba kullum sai tayi mafarkin Maryam ɗin ta, juyawa tayi zata koma ɗaki, da wani irin gudu Maryam taje ta rungumeta kafin ta fashe da kuka, taɓata tayi tana gyara glass ɗin idonta, "Maryam ce wannan ko waye?"


"nice Momy ki yafemin"


da karfi itama ta rungume Maryam "kin dawo gareni Maryam? kin dawo wurin mahaifiyarki?"


"eh Momy na dawo"

Hamida tsayawa tayi tana rarraba manyan idanunta wanda suka cika da hawayen tausayin Unty maryam, jakan dai har yanzu bata ajiye ba, tama rasa inda zata fara ajiye ɗuwawunta ta zauna, wannan gida yafi karfin zamanta.




*kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.