Doctor Mansoor 1


Chapter 1*                 ~Da sanyin la'asar lokacin da bishiyoyi suke kaɗawa, yanayin gari yayi sanyin ni'ima, babu abinda kake ji sai karan kukan tsuntsaye da kaɗuwar iska mai daɗi, cikin wani garden wanda aka wadata da

kayan more rayuwa, bishiyoyin fruits masu gyaran jiki da ƙara lafiya sune acikin garden ɗin, kasa kuwa an kewaye da grass carpet wanda ya karawa wurin kyau da armashi, kana ganin wurin kasan mamallakinta yanada abin hannu ma'ana me kuɗi ne sosai, zaune yake akan wani kujera wanda aka ƙawata da kyawawan flowers jikinshi sanye da bakar riga wanda yake daidai gwiwa daga sama an ɗaure da igiyoyi, kanshi ya jingina da jikin kujeran yana kallon sama, yayinda kafufunshi suke kasa wanda suke ɗauke da kwantaccen gargasa, hannunshi na hagu rike da glass cup me ɗauke da drinks blue aciki, jikin Cup ɗin yayi zufa sosai alaman abin ciki yana da sanyi, yafi minti biyar a haka kafin ya ɗago yana kallon agogon dake ɗaure jikin tsintsiyar hannunshi, ɗan kurɓan drinks ɗin yayi kafin ya ajiye daga gefe, kare mishi kallo nayi sosai, matashine wanda bazai wuce 29 years ba, kyakkyawane ajin karshe, yana da dogon hanci sosai me tsini, bakinshi ɗan karami me ɗauke da jajayen lips, idanunshi su ake kira da sexy eyes, suna da girma ɗauke da dogayen eyelashes, gashin giranshi har suna haɗewa, suman kanshi a kwance yake lup kamar na balarabe, fari ne sol, kirjinshi da faɗi ga kuma yanayin jikinshi ne kwarjini ne sosai, cikin idonshi har wani brown-brown yake, wayarshi dake gefe ne ya fara ringing, a hankali ya sa hannu ya ɗaga, ganin sunan da yake yawo yasashi ɗagawa ya kara a kunnenshi, murya ƙasa ƙasa kamar wanda aka sashi yin magana dole yace "hello"


ɗayan ɓangaren aka amsa tare da nemanshi cikin gaggawa, yatsine face yayi yana cijan lip nashi na kasa, hannu yasa a cikin suman kanshi yana wasa dashi, cikin shagwaɓa kamar zaiyi kuka yace "Kamal kaima fa zaka iya, wallahi am very tired yanzu haka ina ɗan hutawa ne, yaushe ma na bar hospital ɗin?"


Kamal wanda yake zaune akan kujeranshi na office, gabanshi wasu ƴammata ne guda biyu, ɗayan ta durkusa akan kafarta tana kuka, da alama rokonshi take, a hankali yace "please Dude kazo badan niba kaji?"


jijjiga kai kawai yayi, saida ya shanye drinks nashi hadda na cikin kwalban kafin ya ɗau wayarshi ya fita daga wurin, saida yayi tafiya me ɗan nisa kafin ya fita daga wani kofa ya shige ta kofan baya, haɗaɗɗen ɗaki ya shiga wanda yake ɗauke da fararen furnitures, daga sofa har carpet na ɗakin fari ne, Tv stand ma fari ne kal, da alama bashi da ƙazanta ko kaɗan.


wani bedroom ya shiga bayan ya murɗa handle ɗin kofar, cikin bedroom ɗin ma komai fari ne, da alama yana son white color, kwance igiyan rigan yayi kafin ya cire ya wurga kan bed ɗin, ya rage daga shi sai wani karamin wando baƙi, kasancewar shi kaɗai ne a ɗakin ya shiga cikin toilet ɗin, shima abin kallo ne, domin sabulai da shampoo da kuma turare shi akayi ado dasu acikin toilet ɗin, tara ruwa yayi acikin bathtub saida ya taɓa yaji daidai kafin ya ɗau sabulu me menthol, gogawa yayi a jikin soft skin nashi, soso me laushi ya ɗauka yana goga jikinshi da shi a hankali yake yin komai, saida ya tabbatar babu wani datti a tare dashi kafin ya fara watsa ruwan yana lumshe ido, ba karamin daɗi yake ji ba idan yana wanka, bayan ya gama ya ɗau karamin towel ya ɗaura a waist ɗinshi, fitowa yayi saida jikinshi ya bushe sakamakon Ac da yake aiki a ɗakin kafin ya shafa lotion me ƙamshin gaske, wardrobe yaje ya buɗe, wani jins fari da riga orange color ya dauko, sawa yayi nan ya kara yin kyau, agogo ya ɗaura bayan yaga time 5 na yamma yayi, turare ya fesa, ya ɗau wani jaka wanda yake ratayawa a gefe, riganshi na doctor ya ɗauko wanda yake kamshi, sawa yayi akan kayan jikinshi, wani abin gwaji ya rataya a wuyanshi, wayanshi da makullin mota ya ciro, fita yayi daga ɗakin bayan yasa takalminshi sahu ciki wanda yake fari ne tas.


sauka yake akan stair cikin nutsuwa yana kallon agogo, baifi 20mins da dawowa ba gashi har sun kara kiranshi, shifa wallahi ya fara gajiya, bayan ya sauka ya ɗaura hannu akan handle ɗin kofar fita na jiyo muryan wata ƴar karamar yarinya tana cewa "Ya Mansoor ka dawomin da biscuit"


juyowa yayi yana kallonta, bazata wuce 12years ba, saide tana da tsayi sosai kana ganinta kasan kanwarshi ce domin suna kama sosai, amma ta fishi fari, "hospital zanje ban miki alkawari ba"


haɗe fuska tayi ta haura sama ba tare da ta kuma yimishi magana ba, murmushi yayi na gefen baki domin shi ba ma'abocin yin dariya bane, koda yaushe fuskarshi babu fara'a, fita yayi daga gidan ya nufi parking space, cikin gidan babba ne sosai da flowers da kuma manyan motoci a gefe, da alama su ba kananan masu kuɗi bane.


wata bakar mota kirar benz ya shiga tare da yin horn, getman ne ya buɗe mishi, cikin nutsuwa yake tuki har yabar gidan, kan titi yake tafiya ya kunna waka na baby calm down yana saurara yanabin bakin wakar, yayi tafiya me nisa kafin ya iso wani babban asibiti wanda aka yishi me kyau ne na gaske, a sama an rubuta DR MAN HOSPITAL da manyan harafi, farin fenti da fulawoyi sune suka kara haska wurin, buɗe mishi get akayi a hankali ya danna hancin motar zuwa ciki, saida yayi Parking kafin ya fito rike da jakan hannunshi, da gudu wani me bakin kaya yazo ya amshi jakan, shiga ciki sukayi yana taka mishi baya, sai durkusawa ma'aikan asibitin suke suna aika mishi gaisuwa, saide ya ɗaga hannu kawai ya wuce, bai tsaya ko ina ba sai ofishin da aka rubuta Dr kamal a sama, tura kofan yayi bayan ya mishi knocking, cikin haɗin fuska yace "kai dalla meyasa ba zaka barni na huta ba?"


Tsayawa yayi ganin yarinya a gaban Kamal ɗin tana aikin kuka, hannunta akan kafafuwanshi tana roko, gefe guda kuma kawarta ce take aikin lallashi, hamdala kamal yayi ganin Mansoor yazo, da sauri yace "gashi yazo"

sakinshi tayi da rarrafe taje gaban masur ɗin tana kuka, ganin bai wani kulata ba ta rike kafafunshi tana cewa "ka taimaka min dan Allah"


ɗan janye kafarshi yayi kafin yace su biyoshi office nashi, kafin suce komai ya fita, share hawayen ta tayi kafin suka fita ita da kawar tata.


Office nashi sukaje wanda yake up hawa na biyu, knocking sukayi murya ƙasa yace "Come in"

tura kofar sukayi, Office ɗin ba karamin kyau yayi ba, sai ƙamshi yake tashi kota ina, yana zaune akan bakin kujera wanda yake juyawa dashi, biro a hannunshi yana kallonta, kanta a kasa  yace "ɗago ki kalleni"


ɗagowa tayi, kallo ɗaya ya gane ciki ne da ita, "wata nawa?"

shine tambayan da yayi mata, a hankali tace "wata 2"

jijjiga kai yayi kafin ya bata wani karamin takadda yace su karanta itada kawarta da karfi, karantawa sukayi.


_ni na yadda Dr mansoor ya zubar da cikin jikina, da amincewata kuma nice na kawo kaina, koda na mutu babu komai saboda banson cikin, kuma nayi rantsuwa nice nazo domin kaina_


tana gama karantawa tace "na yadda"

baiyi magana ba ya mika mata biron, karɓa tayi ta sa hannu kafin ya bata wani karamin takadda ta sameshi a dayan room ɗin, karɓa tayi tana kuka ta bishi, kawarta sai hakuri take bata, a ranta kuma cewa take "koda kuɗi ba zanbi maza ba, domin wannan yarjejeniyar kaɗai ya isheni ishara, ace kasa hannu koda ka mutu kaine ka jawa kanka?"

dafe kirji tayi tana zaune a tsorace, ganin abin baiyi mata ba ta bisu tare da cewa  Mansoor itakam zata tafi ana nemanta a gida.


ya fahimceta yasan irin wannan case ɗin da yawa, so take ta gudu domin kada wani abu ya faru, kallon banza yayi mata kafin yace "tare kuka zo tare zaku tafi"

zama tayi tana rarraba ido.


saida ya zubar da cikin kafin suka biyashi manyan kuɗaɗe ta hanyar yimishi transfer ta account nashi, daurewa take tana cijewa har suka isa wurin motarsu, kwarta ce tayi driving suka tafi.


Kamal da yake gefe yana addu'a Allah yasa suyi a sa'a, harara mansoor ya aika mishi yana ɗan jan tsaki, murmushi yayi "Dr mansoor babban doctor idan babu kai yaya ƴammata zasuyi?"

murmushi kawai yayi "kaga idan ina gida kada ka sake kirana kanaji ko?"


"Yanzu da kazo ba kayi taimako ba? kasan ai idan ba kai ba ni bazan iya ba, wannan aikin ai da wahala"

tafiya kawai yayi yabar Kamal a wurin, saida ya leka patients nashi kafin ya shiga mota ya koma gida, a palour da yake kasa ya hango Ammi, cikin nutsuwa ya karasa, kyakkyawar mata ce sosai, harma tafishi kyau kamar balarabiya, kwanciya yayi akan Sofa ya ɗaura kanshi a cinyarta, cire farin glass na idonta tayi tana murmushi tace "kai kam baka girma ne? Noor ce zatayi wannan abin ai"


shagwaɓe fuska yayi yana turo baki "Ammi na daga hospital fa nake kuma na gaji sosai"


"Aikin lada dole saida gajiya Man fatana Allah ya baka lada yasa hakan shine hanyan shiga aljannarka, mutane da yawa suna yabonka kowa yana cewa kana taimako sosai, man abinda yafi birgeni shine yadda mata suke yabonka, kaga mata? Iyayene sune idan suka samaka albarka zai bika da wuri"

shiru yayi yana lumshe ido, Allah ka rufamin asiri a gaban Ammi na "Ammi ina Jawad?"


"yaje shopping wallahi tun ɗazu bai shigo ba, kasan bai saba fita ba ranan da yafita kuma sai ankai ruwa rana yake dawowa, hala ma yana can yana cin abinci ka sanshi da ci"


murmushi yayi domin shima shaida ne akan halin Jawad indai ta wurin abinci ne, shafa kanshi tayi "ka kira Abbanku?"


Jijjiga kai yayi alaman eh ya kira 

"Yaushe zai shigo Nigeria?"


"This week"

yana faɗa ya mike ya haura sama, tunawa da baiyi wanka ba tunda ya gana wancan aikin, faɗawa toilet yayi ba ɓata lokaci yayi wanka tareda alwala, yana fitowa ya zura jallabiya ash color da bakin hula irin na ƴan makka, anan ya fito kamar asalin balarabe, shimfiɗa sallaya yayi ya tada salla, karanta fatiha yayi kafin ya fara rera karatun Kur'ani cikin zazaƙan murya da kwantar da hankalin me sauraro, bayan ya idar ya ɗaga hannunshi zuwa sama yana rokon Allah ubangiji ya yafe mishi.*ASALINSHI*


mansoor Muhammad Dikko, wanda akafi sani da Dr MAN, ɗa ne ga babban hamshakin ɗan kasuwan nan mai saida gwala-gwalai da kuma motoci wanda yake kawowa daga kasashen ƙetare, Alhaji Muhammad Dikko babban mutum ne wanda yake kula da iyalanshi sosai, Maryam Umar malumfashi itace matarshi, ƴa ga wani balarabe wanda suke zaune a cikin saudi arabia, sunzo nan nigeria ne sanadiyyar mutuwar mahaifinta wanda mahaifiyarta ƴar nan kasa nigeria ce, asalin Alhaji Muhammad bafulanin jihar Gombe ne, anan kuma yake da zama shida iyalanshi, Mansoor shine babban ɗansu sai kaninshi Jawad sai kuma ƴar auta wato Noor, Mansoor tun yana yaro yake maganan son zama likita hakan yasa mahaifinshi ya kudiri aniyan kaishi kowani kasa domin yayi karatu ya zamo babban likita, hakan kuwa akayi saida aka fita dashi zuwa kasar malysia ya karanci doctor ya fito da satificate me kyau, kafin abbanshi ya buɗe mishi asibiti, mutum ne da baya son hayaniya, bai fiye magana ba, yana da girman kai da rashin ganin darajan mutane, baison raini, ko Jawad idan ya kalla saiya sha jinin Jikinshi, gashi da kwarjini hakan yasa ƴammata suke rubuta mishi letter da jinin jikinsu suna aiko mishi, bai kula kowacce aikin gaban shi kawai yakeyi,

wani abu guda da MAN yakeyi shine ɗabi'an zubda ciki, duk cikin ƴammatan garinsu kaɗanne wanda basu sanshi ba, sai kamammu, wannan ɗabi'a nashi mutanen gidansu basu sani ba, abbanshi da amminshi sunyi mishi kyakkyawan shaida, musamman Abba da ya ɗau yadda da rashin ganin laifi ya ɗaurawa Man, Abba yana da Yaya wanda suke cikin garin, shi yayan yana neman kujeran minister, yana da yara dayawa maza da kuma mata, sun shaƙu sosai dasu Man, akai-akai suna zuwa gidansu sometimes har hospital ɗinshi suna zuwa.
                  "Ki tashi akace, a hankali ta mike tana karkaɗe jikinta tana sharan kwalla, wani tsohone daga gefe yace "sannu ƴata garin yaya haka?"

ɗagowa tayi tana kallonshi, wasu irin dara-daran ido Allah ya bata, bakinta ɗan karami ga gashin idonta dogaye har suna nema su rufe idon, hancinta yana da tsini sosai, goshinta kwance yake da gashi me laushin gaske, gashin giranta har yana nema ya haɗe tsabar yawa da kyau gashi baƙi kirin, nuna mishi hannunta tayi wanda yayi jaa sosai kamar zaiyi jini, da sauri yace "jini hannun yake"

cikin muryanta me sanyi ta riko bakin hijabinta wanda yake pink ne ta fara gogewa "ba jini bane haka jikina yake"

tabbas ba tayi karya ba, domin fuskarta ya nuna, haka jikin nata yake, fara ce kamar ka wanke hannu ka taɓa ta jini ya fito, yatsun hannun nan dogaye farare sosai, tana magana tana motsa baki ga wanda bai santa ba zaice yanga ne da ita, hawayen fuskarta ta kuma sharewa tana ɗan murmushi tace "ban musu komai ba Baba haka kawai suka tsaneni ko a school basa barina"


"kiyi hakuri Allah yana tare da mai hakuri kinji?"

jijjiga kai tayi sannan ta durkusa ta kwashe kayan da yake kasa wanda kayan miya ne, yakuwa da alayyahu sai tumatur da attarugu, zubawa tayi a ledan bayan ƙasa ya ɓata sosai, a hijabinta ta sa kafin ta bar wurin tana tafiya kanta a ƙasa, ita kaɗai tasan zafin da zuciyarta take mata, saide bata iya magana koda tayi niyan yin hakan, dan sun gansu yaran masu kuɗi shiyasa suke yimata haka, sai su rinƙa tsokanarta dan tayi musu magana ba kulasu take ba, domin taga su ɗin maza ne babu mutunci mace ta tsaya tana biye maza suna faɗa, amma basa ganin hakan, yanzu haka binta sukayi da mashin nasu da gangan sukayi kamar zasu bigeta a tsorace ta faɗi a gefe saida mutane suka taru kafin suka fara yimata dariya suna nuna ta, abin ba karamin ci mata rai yayi ba, ita kaɗai take tafiya tana magana azuciyarta, cikin unguwansu ba me kyau bane, kana gani kasan marasa karfi ke zaune a layin, a kofar wani ɗan karamin gida ta tsaya, saida ta gyara hijabinta ta maida fuskar kamar ba abinda ya faru kafin tayi sallama ta shiga.


mahaifiyarta dake zaune akan kujera tana tuƙa tuwo harma ta fita kyau saide ita tafita haske, domin ba karamin farantaka take dashi ba, "HAMIDA sai yanzu? ina kika tsaya mamana?"


murmushi tayi tana kawar da kai "Umma nabi gidansu Afrah ne"


"to ke kuwa Hamida nida miya zanyi ina jiranki inake ina zuwa gidansu Afrah? ya kika samu Umman nata suna lafiya?"

jijjiga kai kawai tayi kafin ta kwaɓe hijabin jikinta ta rataya a jikin bishiya ta janyo kujera ta zauna tana tsinan kayan miyan, abinda ya faru ɗazu yake kara dawo mata cikin kwakwalwar ta, a hankali tace "Umma? nikam anya karatun lowyer ɗinnan zaiyi kuwa?"


da mamaki Umma ta ajiye muciyan bayan ta gama tuƙa tuwo tace "meyasa kika ce haka? Keda kike da kwazo da dagiya, kada ki fara wannan tunanin Hamida ta, kinga karatun nan zaiyi miki amfani zuwa gaba, ko akwai matsala ne?"

girgiza kai tayi idanunta suna cika da hawaye, batason umma tagani shiyasa tace "dolene nayi karatu domin kwatowa yayata hakkinta duk da bata raye, saina hukunta duk wani mesa hannu akan mutuwarta" share hawayen tayi "bazan yafewa wanda ya kashe adda Amra ba tare da mahaifina saina ɗau musu fansa umma"


shiru umma tayi jikinta duk yayi sanyi, tausayin Hamida ya cika mata zuciya, fatanta da burinta shine Allah kada ya kawo abinda zai rusa karatunta koma menene, addu'an ta yana karɓuwa domin duk takuran da waɗannan samaran suke mata a school hakan baisa ta daina zuwa ba.
_da farko ina mai bawa mabiya litattafaina hakuri kan yin cancel ɗin littafin zubar hawaye, an samu akasi ne akan hakan mahaifiyata ta hanani yin wancan labarin, ku gafarceni amma ga wannan wanda inada tabbacin zaima fi wancan daɗi"*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_  *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan  gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.* 

We have 

*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su

*Atampha of all kinds*

*Veils*

*shadda*

*shoes*

*qualitative handbags*

*Jewelries* etc

Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181* 

Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu


https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo *kuɗin littafi 300 ta wannan account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin Mtn ta wannan layin 08144818849*

No comments

Powered by Blogger.